Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An ceto wani yaro bayan ya shafe sa’a takwas a motar markade shara

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Muhammad Annur Muhammad

  1. NNPC ya bayar da umarnin dako da sayar da mai ba dare ba rana a fadin Najeriya

    Kamfanin man fetur na Najeriya,NNPC, ya ce ya bayar da umarnin dakon mai daga manyan rumbuna da kuma sayar da shi a gidajen mai a fadin kasar, ba dare ba rana - sa’a 24 a kokarin kawo karshen matsalar man da ake ciki a yanzu.

    A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Talatar nan 15 ga watan Fabrairu 2022, ya ce yana ba wa ‘yan kasar tabbacin daukar matakan da suka dace domin hanzarta samar da man a fadin kasar.

    Sanarwar ta ce manyan kamfanonin mai da dukkanin masu harkar sayar da man suma sun kama aiki ba dare ba rana domin wadata ko'ina.

    Kamfanin ya shawarci jama’a da su daina tururuwar sayen man saboda fargabar karancinsa, domin a cewarsa yana da sama da lita biliyan daya ta man, domin amfanin ababan hawa da manyan injina.

    Sanarwar ta ce masu sanya ido na kamfanin da hadin guiwar jami’an tsaro sun dukufa aiki don tabbatar da raba man a fadin kasar.

    Bugu da kari sanarwar ta ce a kokarin da kamfanin yake na tanadar da wadataccen mai a kasar, ya tsara adana man lita biliyan 2.3 daga yanzu zuwa karshen watan nan na Fabrairu, wanda hakan zai sa a samu man wadatacce fiye da na kwana 30, da ake tanada ko da an shiga karanci.

    An shiga matsalar man a Najeriya tun kusan mako biyu da ya gabata sakamakon gurbataccen mai da aka shigar da shi kasar, wanda ya haddasa lalacewar ababan hawan jama’a.

  2. Kotu ta kwace kadarori 24 da suka hada da gidajen mai a Kano ta ba gwamnatin Najeriya

    Wata babbar kotun tarayyar Najeriya ta bayar da umarnin kwacewa tare da mallaka wa gwamnatin kasar wasu kadarori 24 wadanda yawancinsu gidajen sayar da man fetur ne sabbi a jihohin Kano da Kaduna da Borno da Cros River na wani babban soja.

    Hukuncin wanda alkalin Justice N.E. Maha ya yanke ya biyo bayan bukatar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriyar, EFFCC ta shigar ne, wadda a watan Mayu na 2020 ta samu izinin kotu na karbe kadarorin a matsayin wucin-gadi.

    Hukumar ta ce kasancewar ba wanda ya fito ya kalubalanci matakin kwacewar saboda haka ne alkalin kotun, Justice Maha a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu, 2022 ya bayar da umarnin mallaka wa gwamnatin tarayyar Najeriya kadarorin.

    Kadarorin guda 24 wadanda suna warwatse ne a jihohin Kano da Kaduna da Borno da Cross River sun hada da filaye da manyan shagunankasuwanci da gidajen man fetur, kudinsu jumulla ya kai naira biliyan 10 da miliyan 935

  3. Shugaban Rasha ya ce ba ya son yaki a Turai amma dole a duba bukatarsa

    Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce ko kadan kasarsa ba ta son yaki a Turai, amma kuma dole ne a dauki damuwarsa ta tsaro da muhimmanci kuma magance ta.

    Shugabanya yi kalaman ne yayin da hukumomin sojin kasar suka ce wasu daga cikin dakarunsu na janyewa daga kusa da iyakarsu da Ukraine, wanda wannan ita ce alama ta farko daga Moscow ta sassauta halin da ake ciki.

    Sai dai kuma shugabannin kasashen Turai sun ce ba su ga wata alama ta janyewar ba zuwa yanzu.

    Mista Putin ya bayyana hakan ne a Moscow bayan wata ganawa da suka yi ta tsawon sa’a hudu da Shugaban Gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, wanda shi ne shugaba na baya bayan nan daga Turai da ya ziyarci yankin domin kwantar da hankali.

    Jibge dakarun da Rasha ta rika yi dare daya a kan iyakar kasar da Ukraine tun watan Nuwamba ya sanya fargaba cewa tana son mamayar Ukraine din ne.

    To amma kuma Mista Putin a kullum cewa yake ba su da wata niyya ta yin kutse a Ukraine

    Rasha tana da alaka ta kurkusa da Ukraine, wadda tana cikin tsohuwar tarayyrar Soviet.

    Mista Putin yana son tabbacin cewa kungiyar tsaro ta kasashen Yamma, Nato ba za ta fadada ta shigar da Ukraine cikinta ba saboda yana ganin shigar Ukraine a matsayin barazana ga Rasha, amma kuma Nato ta ki yarda da bukatar tasa.

  4. An ceto wani yaro bayan ya shafe sa’a takwas a motar markade shara

    An ceto wani yaro dan shekara 10 bayan da ya shafe sa’a takwas a cikin na’urar da ke markade shara ta wata mota a babban birnin Sudan, Khartoum.

    Yaron wanda ‘yan sanda suka bayyana sunansa da Majed Mubarak Ibrahim, yana aiki ne da motar kwashe shara ta hukumar tsaftace birnin na Khartoum.

    Ana ganin nau’rar ta fizge shi ne a lokacin da yake kokarin jefa shara.

    'Yan sanda ba su bayar da wani karin bayani game da halin da yake ciki ba, amma dai yana asibiti.

    An rika sanya hotuna a shafukan sada zumunta da muhawara kan yadda ake ta faman kokarin cetonsa har cikin dare.

    Wasu da ke wurin ceton sun ce ana iya ganin daya daga cikin hannayensa, ya makale a bakin hakoran na’urar.

    Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun ce hadarin ya nuna yadda ake ci da gumin yara a Sudan, inda ake sanya su ayyukan da suke masu hadari, wasu ma ana sa su aikin soji.

  5. Liberia na bikin shekara 200 da kafuwa cikin matsalar tattalin arziki

    A Liberia an fara bikin da ake shafe shekara guda ana yi na tunawa da lokacin da aka kafa ta bayan da aka ‘yanta bakaken fata daga Amurka suka isa kasar, karni biyu da ya wuce.

    Bayan isarsu ne can suka kafa kasarsu mai cin gashin-kanta a shekarar 1847.

    Dubbai ne suka halarci bikin a ranar Litinin a babban birnin kasar Monrovia, bisa jagorancin Shugaba George Weah, wanda kuma shugabannin kasashen Afirka ta Yamma da dama da taurarin mawaka da kuma sauran jama’a daga sassan duniya, galibinsu Amurkawa ‘yan asalin Afirka suka halarta.

    Matsalar tattalin arziki da Liberia ke fama da ita a yanzu ta sa mutane da dama ke ganin ya kamata a soke bikin.

    Jakadiyar Amurka a kasar Dana Banks, wadda ta yi jawabi a bikin ranar Litinin, ita ma ta bukaci hukumomin na Liberia su kara tashi tsaye domin raba kasar da cin hanci da rashawa.

    Sai dai Ministan watsa labarai Ledgerhood Rennie ya gaya wa BBC cewa Liberia na bukatar ta nuna wa duniya tarihi da al’adarta masu armashi.

    ‘’Kuma mu gaya wa sauran duniya cewa mun dawo a matsayinmu na kasa, tauraruwar kasar bakar fata mafi dadewa mai ‘yancin kanta, wadda ke kudu da hamadar Sahara.’’ in ji ministan.

    Ya kara da cewa, ‘’Liberia kasa ce da ta kasance matattakala ta ‘yancin bakar fata a kudu da hamadar Sahara da wasu sassan duniya, inda wasu kasashen bakar fata ke kallon Liberia a matsayin tauraruwar kasa a nahiyar Afirka.’’

  6. An yankewa malamin da ya yi wa dalibansa 13 fyade daurin rai da rai

    Wata kotu a Indonesia ta yanke wa wani mai makarantar kwana hukuncin daurin rai-da-rai bayan da ta same shi da laifin yi wa ɗaliban makarantar su 13 fyade.

    Ta'asar da mai makarantar ya aikata ta bayyana ne bayan da iyalin wata daliba suka kai karar Herry Wirawan a ofishin ƴan sanda bayan da suka gano cewa ta ɗauki ciki.

    Bincike ya tabbatar cewa cikin shekaru biyar mutumin ya yi wa daliban fyade - 'yan matan da shekarunsu na haihuwa ke tsakanin 11 zuwa 16.

    Wakilin BBC ya ce ɗalibai takwas sun haifi jarirai 9 a sanadiyyar fyaɗen da mai makarantar yayi musu, saboda ɗaya daga cikin 'yan matan ta haifi ƴan biyu ne.

    Shari'ar ta tayar da hankulan ƴan Indonesia, ƙasar da kimanin yara miliyan biyar ke halartar makarantun kwana na addinin Musulunci.

    Sai dai gwamnatin ƙasar ta ba kowace yarinyar da aka yi wa fyade diyyar dalar Amurka kimanin dubu shida.

  7. Da a yi min riga-kafin korona gara na ƙi shiga gasar French Open da Wimbledon - Djokovic

    Shahararren ɗan wasan kwallon Tennis na duniya Novak Djokovic ya shaida wa BBC cewa gara ya kaurace wa gasar French Open da ta Wimbledon maimakon a yi masa allurar riga-kafin korona.

    A watan Janairu kasar Australia ta kori ɗan wasan bayan da ya isa birnin Melbourne saboda kin amincewa da yayi a yi masa riga-kafin.

    Mista Djokovic ne ɗan wasan Tennis lamba daya a duniya - amma ya ce bai taɓa cewa ba ya son a yi masa allurar ba.

    "Ra'ayina shi ne kowa na da damar amincewa ko kin amincewa da wannan riga-kafin, amma ban taba cewa ina goyon bayan masu adawa da allurar riga-kafin korona ba," in ji Mista Djokovic.

    Ya kuma ce abin takaici ne yadda ake kokarin cusa masa wani ra'ayin da ba nasa ba.

  8. Ƙungiyar Musulman Tigray ta yanke hulɗa da majalisar harkokin Musulunci ta Ethiopia

    Wata ƙungiyar Musulmai reshen yankin Tigary na ƙasar Habasha (Ethiopia) ta yanke hulɗa da babbar ƙungiyar da ke Addis Ababa babban birnin ƙasar.

    Reshen ƙungiyar Ethiopia’s Islamic Affairs Council (EIAC) ya ɗauki matakin ne 'yan kwanaki bayan wata ƙungiyar Kirista ta katse alaƙa da tata uwar ƙungiyar sannan suka ƙirƙiri tasu.

    Jagororin Musulmin sun ce sun ɗauki matakin ne saboda uwar ƙungiyarsu ta gaza wajen yin Allah-wadai da yaƙin basasar da ake yi a ƙasar tun 2020.

    Majalisar ta kafa misali da harin da aka kai kan ɗaya daga cikin masallatanta mafiya daraja na Al-Nejashi, wanda aka yi wa ruwan wuta kuma aka ɗaiɗaita shi a farkon yaƙin.

    An yi imanin cewa sahabban Annabi Muhammadu S.A.W ne suka gina masallacin tun a ƙarni na 7 a lokacin da suka yi hijira zuwa can sakamakon matsi da suka fuskanta a farko-farkon addinin Musulunci.

    Masu sharhi na ganin cewa wannan ɓallewa na da tasiri ƙwarai game da yaƙin a ƙasar da ke da kashi 40 cikin 100 na mutanen da ke bin gargajiyar Kriistanci, yayin da Musulmi ke da kashi 34 cikin 100.

    Cocin Tewahodo ta gargajiyar Kiristanci ta fi saura yawan mabiya sannan kuma tana da tasiri sosai a ɓangaren siyasar ƙasar da kuma harkokin zamantakewa.

  9. Jami'an tsaron Sudan sun harbe 'yan zanga-zanga biyu

    Jami'an tsaro a Sudan sun harbe 'yan zanga-zanga biyu a jiya Litinin, a cewar ƙungiyar likitoci ta ƙasar.

    Wannan lamari ya sa jumillar adadin waɗanda aka kashe tun bayan juyin mulki na watan Oktoba zuwa 80.

    An gudanar da zanga-zangar ta baya-bayan nan a birane da dama da garuruwa na faɗin ƙasar don nuna ɓacin rai ga mulkin sojoji da kuma kiran a saki 'yan zanga-zangar da aka kama.

    Tun cikin makon da ya gabata, an kama 'yan siyasa biyu da suka taɓa shiga gwamnatin riƙon ƙwarya.

    Sun kasance cikin wani kwamati na musamman da gwamnatin Omar al-Bashir ta kafa da zimmar lalata harkokin wasu ƙungiyoyi na siyasa shekara kusan 30 da suka wuce.

  10. Shugaban Jamus Olaf Scholz na ganawa da Shugaba Putin na Rasha kan Ukraine

    Shugaban Jamus Olaf Scholz na ganawa da Shugaba Putin na Rasha a birnin Moscow a karkashin wani yunkuri na diflomasiyya da kasashen Yammacin Turai ke yi domin hana rashar kai wa Ukraine hari.

    Mista Scholz zai nanata gargadin da kasashen Turai ke yi cewa za su kakaba wa Rashar takunkumi mai tsauri idan ta kai harin.

    Sai dai ma'aikatar tsaro ta Rasha ta sanar cewa wasu dakarun kasar da aka tura kan iyakarta da Ukraine sun kammala aikinsu kuma an ba su umarnin komawa sansanoninsu.

    Kakakin ma'ikatar tsaron Rasha Igor Konashenkov ke nan ke cewa wasu dakaru daga sudanci da yammacin gundumomin rundunar sojojin kasar nan tuni sun fara shirin kwashe kayan yaki kuma a yau za su fara komawa barikokinsu.

    A halin da ake ciki, Amurka ta gargadi dukkan 'yan kasarta a Belarus da yankin Transnistria na kasar Moldova da su fice daga kasashen na tare da bata lokaci ba.

  11. Buhari zai ƙara tiriliyan 2.557 a kasafin kuɗi don biyan tallafin man fetur

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa wa majalisun dokokin ƙasar buƙatar gyaran dokar kasafin kuɗi ta 2022 a yau Talata.

    Buƙatar neman gyaran ta biyo bayan dakatar da Dokar Man Fetur (PIA) ce, wadda ta tanadi a soke biyan tallafin man fetur ɗin da kuma mayar da harkar mai ta 'yan kasuwa zalla.

    Wannan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da shugaban ya rubuta wa 'yan majalisar wadda kuma Shugaban Majalisa Sanata Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila suka karanta a zaurukan majalisunsu.

    Gwamnati na neman majalisar ta amince da ƙarin fiye da naira tiriliyan biyu da rabi (triliyan N2.557) don biyan kuɗin tallafin mai daga Yuli zuwa Disamban 2022 da kuma sake duba Dokar Kuɗi ta Finance Act 2021.

    A cikin wasiƙar, Buhari ya ce gyaran ya zama dole don ƙara wasu ayyuka a ciki da suka haɗa da tallafin man fetur, wanda tun farko gwamnatinsa ta yi niyyar daina biya kafin daga baya ta sauya shawara.

    Tun da farko gwamnati ta tanadi kuɗin tallafin na wata shidan farko na shekarar 2022 a kasafin kuɗin, inda aka ware biliyan N443 daga Janairu zuwa Yunin 2022.

  12. Buhari zai tafi Turai a yau Talata

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai tafi Belgium a yau Talata don halartar taron haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar haɗin kan Afirka ta African Union (AU) da takwararta ta Tarayyar Turai (EU).

    Taron wanda zai gudana a birnin Brussels daga 17 zuwa 18 na Fabarairu, inda shugabannin nahiyoyin biyu za su tattauna matsalolin da ke faruwa a yankunansu.

    Wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta ce ana sa ran Buhari zai koma gida ranar Asabar. Ta ƙara da cewa shugaban zai yi amfani da damar wajen tattauna sauran al'amura da wasu ƙasashe.

    Abubuwan da shugabannin za su tattauna sun haɗa da batun ilimi da sauyin yanayi da makamashi da zaman lafiya da harkokin mulki da harkokin tattalin arziki.

  13. 'Yan Abuja na fama da zungura-zunguran layukan man fetur

    Har yanzu mazauna Abuja Birnin Tarayyar Najeriya na fama da dogayen layuka a gidajen sayar da man fetur da ke faɗin birnin.

    Wani layi da tawagar BBC Hausa ta ziyarta a yau Talata a ƙwaryar birnin ya kai tsawon kusan kilomita biyu.

    Kuna iya duba shafinmu na Facebook don gane wa idonku:

  14. Ba za mu iya ci gaba da yaƙi da masu iƙirarin jihadi ba a Mali - Faransa

    Faransa ta ce "babu yanayi mai kyau" da za ta iya ci gaba da yaƙar 'yan bindiga masu iƙirarin jihadi a Mali.

    Shugaba Emmanuel Macron ya nemi a sake fasalin dakarun Faransar a yankin na Sahel.

    Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce ƙasar za ta ci gaba da yaƙar 'yan bindigar a ƙasashe maƙota.

    Tuni Faransa ta rage yawan dakarunta a Mali.

    A shekarar 2020 ne sojoji suka ƙwace mulki a Mali sannan kuma an yi ta samun rikici tsakanin gwamnatin da ƙasashen waje.

    A watan Disamba, ƙasashe 16 - mafi yawansu a Turai - sun yi watsi da matakin gwamnatin Mali na yin aiki da sojojin haya na ƙungiyar Wagner ta ƙasar Rasha.

  15. MOPPAN ta sasanta Naziru Sarkin Waƙa da matan Kannywood

    Gamayyar ƙungiyoyin fim na Kanny wood ta sasanta 'yan masana'antar sakamakon rikicin baya-bayan nan da ya ɓarke tsakaninsu bayan batun da Ladin Cima ta yi na kuɗin da ake biyanta a fina-finan da take yi.

    An yi zaman sulhun ne ƙarƙashin ƙungiyar MOPPAN da haɗin gwiwar AFMAN a zauren taron Kannywood TV da ke birnin Kano jiya Litinin, inda aka yi sasanta tsakanin Naziru M Ahmad (Sarkin Waka) da kuma ƙungiyoyin mata na Kannywood.

    Daga cikin Dattawan da suka halarci taron, akwai Malam Auwalu Masha, Mai’unguwa Ibrahim Mandawari, Ibrahim Gumel, Kabiru Maikaba.

    "Taron ya tattauna abubuwa da dama, daga baya aka yi nasiha da jan kunne gami da fadakarwa daga malamai," in ji wata sanarwa daga MOPPAN.

    Ta ci gaba da cewa: "Haka kuma taron ya yi bayanai na girmamawa ga Hajiya Ladin Cima da irin gudunmawar da ta bayar ga masana’antar fim da kuma ci gaba da lallashinta da girmama dukkanin dattijan masana’antar da guje wa yin lafazi maras kyau a kan su."

    Lamarin ya ƙara zafafa ne bayan da Sarkin Waƙa ya yi zargin cewa ana yin lalata da wasu mata kafin a ba su damar saka su a fim sannan kuma ba a biyan wasu haƙƙinsu, abin da ya jawo martani da dama.

    Wasu ƙungiyoyin mata na Kannywood kamar 'K-WAN' sun nemi Nazirun da ya janye kalamansa ko kuma su kai shi kotu.

  16. Alƙaliyar Alƙalai ta Zamfara ta kafa kwamatin bincikar Mataimakin Gwamna Mahdi

    Alƙaliyar Alƙalai ta Jihar Zamfara Mai Shari'a Kulu Aliyu ta rantsar da kwamatin mutum biyar da zai binciki laifukan da ake zargin Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu Gusau na rashin ɗa'a.

    Kwamatin ƙarƙashin tsohon Alƙali Tanko Soba, an kafa shi ne sakamakon damar da kundin tsarin mulki ya ba wa alƙaliyar, a cewar Mai Shari'a Kulu.

    Ta ƙara da cewa Sashe na 185(5) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ne ya ba ta damar kafa kwamatin sakamakon buƙatar da Majalisar Dokokin Zamfara ta gabatar mata ranar 10 ga watan Fabarairu ta ƙorafi kan mataimakin gwamnan.

    A gefe guda kuma, Babbar Kotun Abuja ta saka ranar 10 ga watan Maris don fara sauraron ƙarar da Mahdi Gusau ya shigar yana neman kotun ta dakatar da yunƙurin tsige shi da 'yan majalisar ke yi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    Mai Shari'a Inyang Ekwo ne ya ɗaga zaman a ranar Talata, yana mai umartar ɓangarorin su kimtsa kafin ranar ci gaba da shari'ar.

    A ranar Alhamis da ta gabata ne 'yan majalisar 18 cikin 22 suka amince a tsige mataimakin gwamnan wanda har yanzu yake a jam'iyyar adawa ta PDP sakamakon zargin sa da rashin ɗa'a. A 2021 ne Gwamna Bello Matawalle ya fita daga PDPn zuwa APC mai mulkin Najeriya.

    • 'Ana barazana da rayuwata kan kin goyon bayan tsige mataimakin gwamnan Zamfara'
  17. Za a fara toshe asusun bankuna na masu zanga-zangar dokokin korona a Kanada

    Firaministan Kanada Justin Trudeau ya sanya wata dokar ta-ɓaci da ba kasafai aka fiya amfani da ita ba a yunƙurin kawo ƙarshen zanga-zangar adawa da matakan yaki da cutar korona.

    Daga cikin tanadin dokar, bankuna za su iya rufe asusun ajiya na duk wanda ke da alaƙa da zanga-zangar ba tare da umarnin kotu ba. Sai dai shugaban ya ce dokar ta "ɗan lokaci ce" kuma "ba za a tura dakarun soja ba".

    Da yake magana a wani taron manema labarai, Mista Trudeau ya ce zanga-zagar na illa ga tattalin arziki da kuma yin barazana ga lafiyar jama'a, don haka matakin da ya ɗauka shi ne daidai.

    Wakilin BBC ya ce dokar ta ba wa gwamnatin Kanada cikakken iko, ciki har da na take hakkin 'yan kasarta idan ta kama, don shawo kan wani al'amari da ta yi imanin cewa na iya zama barazana ga tsaron kasa.

    Wannan shi ne karo na farko cikin shekara 50 da aka sanya irin wannan doka, sannan na biyu a tarihin kasar.

    A yanzu dai 'yan sanda na da damar kamawa da tsare mutanen da suka yi kunnen kashi wajen ci gaba da zanga-zangar.

    Lamarin ya rincaɓe ne a ƙarshen watan Janairu tun bayan da gwamnatin Kanada ta tilasta wa direbobin manyan motoci cewa sai sun yi rigakafin korona ko kuma su killace kan su idan suka tsallaka iyakar ƙasar da Amurka mai maƙotaka.

  18. Korona ta sake kama mutum 75 a Najeriya

    Ƙarin mutum 75 ne suka harbu da cutar korona a Najeriya ranar Litinin, kamar yadda rahoton hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta nuna.

    Mutanen da suka kamu da cutar sun fito ne daga jiha takwas. Su ne:

    • Legas-28
    • Akwa Ibom-18
    • Ondo-10
    • Cross River-9
    • Rivers-6
    • Edo-2
    • Delta-1
    • Kano-1

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 254,091 ne suka kamu da cutar, yayin da ta yi ajalin 3,141 tun bayan ɓullarta ƙasar a Fabarairun 2020.

  19. Assalamu Alaikum

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa, wanda zai kawo rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Umar Mikail ne ke tare da ku a wannan hantsi na Talata.