Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gobara ta lakume dukiya mai dimbin yawa a Unguwar-Guragu da ke Abuja

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Shugaba Macron ya sanar da gagarumin shirin Faransa na samar da makamashi

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da shirinsa na zuba dinbin jari a fannin makamashin nukiliya da makamashi maras gurbata muhalli, kamar mai amfani da hasken rana da Iska.

    Mista Macron ya kuduri hakan ne domin mayar da kasar tasa wadda ba ta fitar da hayaki mai haifar da dumamar yanayi nan da shekara ta 2050.

    Shugaban yana son gina tashoshin makamashin nukiliya akalla shida, inda ake sa ran ta farko ta fara aiki zuwa shekara ta 2035.

    Faransa na samun kashi 70 cikin dari na wutar lantarkinta daga makamashin nukiliya.

    Ana daukar makamashin nukiliya a matsayin wanda ba ya fitar da hayaki mai gurbata muhalli sosai, amma kuma kwararru a bangaren muhalli na cewa yana da tsada sosai.

    Sannan yana sa a karkatar da hankali daga zuba kudi wajen samar da makamashi maras gurbata muhalli, kana kuma yana haifar da matsalar sharar nukiliya mai hadarin gaske.

  2. Tarayyar Turai za ta habaka Afirka da jarin dala biliyan 170

    Kungiyar Tarayyar Turai ta yi alkawarin yin wani shiri na zuba jari har nadala biliyan 170 domin kasashen Afirka.

    Shugabar hukumar Turan, Ursula von der Leyen ce ta gayawa hukumomin Senegal a yayin da ta kai ziyara babban birnin kasar Dakar.

    Ta ce wannan shi ne wani shiri na farko na nahiya a karkashin sabon shirin habaka harkokin jin dadin jama’a na gwamnati da na ‘yan kasuwa a kasashe masu tasowa, mai suna Global Gateway.

    Ana yi wa wannan manufa ta kungiyar ta Tarayyar Turai kallo a matsayin wata kishiya ga ayyukan da China ke yi a kasashe masu tasowa, mai suna Belt and Road Initiative.

  3. Aisha Buhari ta je ta'aziyyar Hanifa da Sheik Ahmad Bamba Kano

    Mai dakin shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta ziyarci Kano domin ta’aziyya ga iyalan Sheik Ahmad Bamba da kuma Hanifa Abubakar, yarinyar nan ‘yar shekara biyar da mai kamarantarsu ya kashe ta.

    A jawabin da ta gabatar a gidan gwamnatin jihar Kano a yau Laraba, Aisha Buhari ta ce ta je jihar ne a ziyarar ta kashin-kanta domin jajanta wa gwamnan Kano da matarsa, da Sarkin Kano da kuma al’ummar jihar a kan rasuwar Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba da kuma Hanifa Abubakar.

    Game da kisan da aka yi wa Hanifa, matar shugaban kasar ta ce tana fata tare kuma da addu’ar za a yi wa yarinyar adalci.

    Ta ce: ‘’A matsayina na uwa ina da ‘ya’ya da jikoki wadanda tuni suna makarantar firamare. Sun amince da malamansu sosai haka mu ma kuma.

    Saboda haka a yanayin da za a ce ‘ya’yanmu ba su tsira ba a makarantunsu, to lalle hakan na nuna ba shakka al’umma ta zama wani abu daban. Ina ganin ya kamata a yi hukuncin domin kwantar da hankali a Najeriya.’’

    Gwamnan jihar ta Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ba wa Aisha Buhari tabbacin cewa lalle za a tabbatar an yi adalci a kan kisan na Hanifa, wadda ya ce, ‘’Hanifa ‘yarmu ce kuma ‘yar ‘yan Najeriya ce,’’

    Mai dakin shugaban Najeriyar ta kai ziyarar ta’aziyya gidan su Hanifa, inda ta yi wa iyayen yarinyar, wadda kisanta ya dauki hankali a Najeriya, ta’aziyya.

  4. Za a hana wasu 'yan wasan Chelsea gasar Turai saboda rigakafin korona

    Yan wasan Chelsea da ba a yi wa allurar rigakafin korona za su rasa damar buga wasan zakarun Turai da kungiyar za ta buga da Lille ta Faransa a wata mai zuwa.

    Hakan ya biyo bayan matakin hukumar kwallon kafa ta Turai na yin garambawul kan dokokinta na yaki da korona.

    Dama hukumomin Faransa sun hana duk wanda ba a yi wa rigakafin ba shiga kasar.

    Chelsea ta so mika bukatar mayar da wasan zuwa wata kasa don samun damar amfani da dukkanin 'yan wasanta, to amma matakin na UEFA na nufin hakan ba zai yiwuwa ba.

    Kungiyar ta Stamford Bridge za ta buga wasan farko da Lille a London ranar 22 ga watan Fabrairu, sai kuma ta je wasan ramako Faransa ranar 16 ga watan Maris.

    To amma kawo yanzu Chelsea wadda yanzu haka ke Abu Dhabi don buga gasar zakarun kungiyoyin duniya ba ta bayyana 'yan wasan da ba a yi wa rigakafin ba.

    Mai horar da kungiyar Thomas Tuchel ya ce wannan matsala ce da za ta iya shafar makomar wasansu a wannan mataki, ganin cewa za su tafi buga gasar zakarun Turan ba tare da wasu manyan 'yan wasa ba.

  5. Jose Peseiro ya ce shi ne ya ki karbar aikin kocin Najeriya

    Jose Peseiro ya ce ya fasa karbar aikin horar da tawagar Super Eagles ta Najeriya ne bisa rashin jituwa da suka samu kan yadda kwantiraginsa zai kasance da kuma batun albashinsa.

    Tsohon kocin na Sporting Lisbon da Porto, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram, kwana uku bayan hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ta fitar da sanarwar cewa ta fasa daukar mai horarwa daga waje.

    Kuma ta tabbatar da cewa kocin riko Agustine Eguavon zai ci gaba da jan ragamar tawagar tare da taimakom Emmanuel Amuneke.

    Sai kuma ta sa Salisu Yusuf da Joseph Yobo a matsayin mataimaka na uku da kuma na hudu.

    NFF ta kuma ce tana fatan za a ba su wadataccen lokaci ta yadda za su kawo sauyi a kungiyar ta Super Eagles.

    A jiya Talata ne hukumar kwallon kafar ta Najeriya, NFF, ta sanar da ranar 27 ga watan Maris, a matsayin ranar da tawagar kasar, Super Eagles za ta kece raini da Ghana, a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar, a wannan shekara 2022.

    Za a yi karon-battar, wanda zai kasance na biyu kuma na karshe a filin wasa na MKO Abiola da ke babban birnin Najeriyar, Abuja.

    Za su fatata ne bayan tawagar Super Eagles din ta koma gida daga Ghana don buga zagayen farko, a filin wasa na Cape Coast, a tsakanin ranar Laraba, 23 ga watan Maris ko Alhamis 24 ga watan na Maris.

  6. Ya kamata jami'o'i su bullo da tsarin yi wa dalibai gwajin miyagun kwayoyi - Buba Marwa

    Shugaban hukumar yaki da masu sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (murabus) ya bukaci jami’o’in kasar da su bullo da tsarin yi wa dalibai gwajin miyagun kwayoyi domin raba matasa da ta’adar.

    Ya nemi jami’o’in na Najeriya da su sa tsarin gwajin amfani da miyagun kewayoyin a kan sabbi da kuma daliban da ke karatu a cikinsu ya zama cikin manufofinsu.

    Janar Marwa wanda ya bukaci hakan a yayin kaddamar da kamfe na yaki da miyagun kwayoyi a jami’o’i, Larabar nan 09 ga watan Fabrairu, 2022, a bikin da aka yi a Jami’ar Abuja, ya kuma nemi hadin kansu domin kafa kananan ofisoshin hukumar a makarantu domin taimaka musu a yaki da miyagun kwayoyi.

    Marwa ya ce bullo da tsarin gwajin kwayoyin a kan dalibai ba yana nufin wani mataki na hukunta su ba ne, illa dai kawai ya zama wata hanya ta gano masu amfani da kwayoyin da wuri domin dakile matsalar tun daga tushe da yi musu magani.

    Shugaban na NDLEA ya ce babu wani lokaci da ya wuce yanzu da ya kamata a tashi tsaye domin maganin matsalar ta amfani da miyagun kwayoyi saboda ta’ada ce da ta zama abar damuwa a Najeriya

  7. An bai wa 'yan wasan Senegal kyautar filaye da kudi

    Senegal ta bai wa dukkanin ‘yan tawagar wasan kwallon kafa na kasar ladan kudi da filaye saboda nasarar da suka yi ta cin kofin kwallon kaf ana kasashen Afirka.

    An bai wa kowanne daga cikin ‘yan wasan sama da dala dubu 87, da fili a babban birnin kasar Dakar da kuma birnin Diamniadio mai makwabtaka, a yayin bikin da aka yi na karrama ‘yan wasan a fadar shugaban kasar.

    Shugaba Macky Sally ya kuma bai wa ‘yan wasan babbar lambargirmamawa ta kasar (Order of the Lion), inda magoya baya suka halarci bikin a kofar fadar gwamnatin.

    Shugaban ya yaba wa tawagar kan yadda ta kai kololuwar Afirka da kuma janyo wa kasar da al’ummarta daraja da girmamawa.

    Ya kuma jinjina wa mai horad da ‘yan wasan, Aliou Cissé.

    Senegal ta doke Masar 4-2 a wasan bugun fanareti, inda kasar ta zama zakara a karon farko a tarihinta.

  8. Gobara ta lakume dukiya mai dimbin yawa a Unguwar-Guragu da ke Abuja

    Wata gobara ta tashi dazu da rana a unguwar guragu da ke Karmajiji a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

    Gobarar ta kone matsugunai da dama na mazauna yankin mafi yawansu masu nakasa a kafa.

    Wasu da lamarin ya shafa sun ce sun yi mummunar asara, inda yawancinsu suka ce ba su tsira da komai ba sai kayan jikinsu.

    Wata mata, Fatima, ta ce kudinta da suka kai tsabar naira dubu 500 sun kone a gobarar, da sarkarta ta gwal, da tufafinta kusan guda 100 da sauran kayanta na aure.

    Babu dai asarar rai ko jikkata a cikin gobarar.

    Mazauna unguwar wadanda sun hada da masu larurar kafa da kuma ta ido da iyalansu, suna zaman wucin-gadi ne a unguwar ta Karmajiji tsawon shekaru da dama.

    Sarkin masu bukata ta musamman na Abuja Alhaji Muhammad Sulaiman ya yi kira ga hukumomin Abuja da su gaggauta gina musu gidajensu na dundundun a filin da aka ware musu a Gwagwalada.

    Mazauna unguwar sun ce wannan ne karo na uku da aka samu gobara a unguwar ta Guragu a Karmajiji a cikin shekara bakwai.

    Kuma a gobarar da aka fuskanta a shekarun baya an samu asarar rayuka biyu.

  9. Za a yi dokar cin tarar jami'an gwamnatin Najeriya da suka je waje magani miliyan N500

    Wani kudurin doka da zai sa a rika cin tarar jamia’n gwamnnati da suka fita neman magani kasar waje da kudin gwamnati ba tare da izini ba, naira miliyan 500 ya wuce domin karatu na biyu, a majalisar Wakilan Najeriya.

    Kudurin na neman a yi sauyi ne a dokar kula da lafiya ta kasar ta 2014, ta yadda dokar za ta kunshi hukuncin da za a yi wa duk jami’in da ya saba tanade-tanadenta.

    Dan majalisa Sergius Ogun wanda ya gabatar da kudurin ya ce ya yi hakan ne da nufin rage yawan tafiye-tafiye zuwa kasar waje da jami’an gwamnati ke yi domin neman lafiya, su yi watsi da asibitocin kasar.

    Mista Ogun ya ce matakin zai sa a mayar da hankali sosai wajen gyara asibitocin Najeriya, wadanda suke cikin hali na rashin kulawar da ta kamata.

  10. Sojin Najeriya sun kashe wani kwamandan mayakan Biafara da wasu uku

    Dakarun Najeriya na kasa sun yi nasarar harbe 'yan bindigar kungiyar aware ta Biyafara, IPOB, guda hudu a garin Ihiala na jihar Anambra da ke kudu maso gabashin kasar.

    'Yan bindigar suna tilasta bin umarnin da suka yi ne na zama a gida, inda suka bude wuta suna harbin kan mai-uwa-da-wabi a wani gidan mai a garin na Ihiala town.

    bayan da sojojin suka samu kiran kai dauki suka nufi wurin inda suka shiga musayar wuta da 'yan awaren, kamar yadda wata sanarwa da darektan hulda da jama'a na rundunar sojin kasa ta Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ta bayyana.

    Rundunar ta ce a yayin ba-ta-kashin ta yi nasara kashe jagoran mayakan Ejike da wasu mutum uku.

    Ta kuma kwato makamai da suka hada da babur daya da bundugogi masu baki biyu guda biyu da harsasai da wasu abubuwa da ake ganin ganyen tabar wiwi ne da sauran abubuwa.

    Sai dai sojojin sun ce motarsu daya da ke dauke da dakaru ta yi hatsari sakamakon wata matsala, a lokacin inda a sanadiyyar haka sun rasa babban jami'i daya da kuma wani sojan, yayin da wasu biyu suka ji rauni.

  11. Gwamnatin Najeriya za ta yi 'gagarumin bincike' kan gurɓataccen man fetur

    Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta gudanar "gagarumin bincike" don gano musabbabin samun gurɓataccen man fetur a ƙasar.

    Ƙaramin Ministan Fetur Timipre Sylva ne ya bayyana hakan a yau Laraba yayin wani taron manema labarai bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa a fadar shugaban ƙasa.

    Duk da cewa ministan bai bayyana kamfanonin da lamarin zai shafa ba ministan ya ce za a bayyana sunayensu idan an kammala binciken.

    "Za a yi gagarumin bincike don fayyace komai. Akwai buƙatar mu gano komai da komai kafin mu dawo mu faɗa muku abin da zai faru da miyagun," a cewar ministan.

    'Yan Najeriya da dama na kokawa kan gurɓataccen man fetur da suka sha a gidajen mai na ƙasar da kuma dogayen layi da ake yi kafin samun sa.

    Sai dai shugaban sashen dakon man na kamfanin NNPC ya bayyana dalilin da ya sa ake samun layukan da kuma matakin da aka ɗauka.

  12. Zanga-zangar Hijabi: 'Yan sanda a Indiya sun kama mutum 15

    'Yan sanda a kudancin Indiya sun kama mutum 15 da ke da alaƙa da rikicin da ya barke bayan zanga-zangar da mata Musulmai ke yi na haramta musu sanya hijabi.

    Zanga-zangar na zuwa ne bayan matakin da wasu makarantu suka dauka na hana matan shiga aji da hijabi, wanda hakan ya janyo tashin hankali a wasu yankunan jihar Karnataka.

    An rufe duka manyan makarantu da kwalejoji har na tsahon kwanaki uku.

    Babbar kotun kasar na duba koken da wasu dalibai suka kai mata na kalubalantar wannan mataki.

    Tasmeena Sultan daliba ce kuma ta ce Musulmai na da 'yancin su yi yaki domin kwatar 'yancinsu.

    "Za mu ci gaba da yin zanga-zanga matukar gwamnati za ta ci gaba da cin zarafin dalibai. Muna son a dawo mana da 'yancinmu, babu wanda ya isa ya kwace mana 'yanci," in ji ta.

  13. Majalisar Wakilan Najeriya ta nemi a saka dokar ta-ɓaci kan kisan gilla don yin tsafi

    Majalisar Wakilai ta Najeriya ta nemi gwamnatin Shugaba Buhari ta ayyana dokar ta-ɓaci kan aikata kashe-kashe don yin tsafi a faɗin ƙasar.

    Kiran na cikin ƙudirorin da wakilan suka cimma a zamansu na yau Laraba bayan gabatar da wani ƙudirin gaggawa kan rayuwar jama'a mai taken ‘Need to Curb the Rising Trend of Ritual Killings in Nigeria’ - buƙatar daƙile kisan gilla don aikata tsafi a Najeriya.

    Shugaban Marasa Rinjaye Toby Okechukwu ne ya gabatar da ƙudirin.

    Buƙatar tasu na zuwa ne yayin da ake samun rahotannin kisan gilla da zimmar neman kuɗi ta hanyar tsafi a sassan Najeriya, wanda na baya-bayan nan shi ne Sofiat Okeowo a Jihar Ogun.

    'Yan majalisar sun yi kira ga hukumar wayar da kai ta ƙasa National Orientation Agency (NOA) da iyaye da shugabannin makarantu da malaman addini da 'yan jarida da su fara kamfe don daƙile ci gaba da faruwar kashe-kashen.

  14. Fina-finan da ke takarar lashe kyautar Oscar

    Za a karrama taurarin fina-finai na shekarar da ta gabata daga masana'antar fim ta Hollywood da kuma fina-finan kansu a ƙarshen watan Maris.

    Ga fim 16 da ke takarar lashe kyautar ta Oscar wadda ke kan gaba a waɗanda suka fi shahara a duniya:

    • The Power of the Dog
    • Dune
    • Belfast
    • West Side Story
    • King Richard
    • Don't Look Up
    • Nightmare Alley
    • Drive My Car
    • Licorice Pizza
    • The Lost Daughter
    • Coda
    • The Tragedy of Macbeth
    • Being The Ricardos
    • No Time to Die
    • Flee
    • Encanto
  15. Afcon: An saka wa 'yan wasan Senegal da kyautar filaye da kuɗi

    Sengal ta saka wa tawagar 'yan wasan ƙasar da suka ciyo mata gasar Kofin Ƙasashen Afirka da kyautuka fda kuma iliyae.

    Kowane ɗan wasa ya samu kyautar dala 87,000 (fiye da naira miliyan 36) haɗi da fili a cikin birnin Dakar da kuma Diamniadio yayin wani biki a fadar shugaban ƙasa.

    Haka nan Shugaban Ƙasa Macky Sall ya kuma girmama tawagar da lambar yabo ta Order of the Lion.

    Tun farko shugaban ya gode wa tawagar saboda kai wa "matsayin ƙololuwa a Afirka" da kuma "samo wa manyan mutane girmamawa".

    Ya kuma yi yabo na musamman ga kocin tawagar, Aliou Cissé.

    Senegal ta doke Egypt 4-2 a bugun finareti kafin ta lashe kofin a karon farko a tarihi.

  16. 'Yan fashin daji sun kashe DPO na Jibiya a Jihar Katsina

    Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashin daji ne sun kashe jami'in ɗan sanda (DPO) yayin wani hari a garin Jibiya na Jihar Katsina ranar Talata da dare.

    DSP A. A. Rano wanda shi ne DPO na Jibiya, ya rasa ransa ne lokacin da 'yan fashin suka afka wa garin suna harbe-harbe kan mai tsautsayi don firgita mazauna yankin.

    Ƙoƙarin da muka ji daga bakin rundunar 'yan sandan Katsina bai yiwu ba amma mai magana da yawun rundunar, SP Gambo Isa, ya yi ta'aziyyar marigayin a dandalin sada zumunta na WhatsApp.

    Wasu rahotanni da BBC ba ta tabbatar da ingancinsu ba na cewa maharan sun harbi wani soja a ƙafa kuma daga baya ya rasu.

    Wani mazaunin yankin ya faɗa wa BBC Hausa cewa lamarin ya faru a kan idonsa, yayin da tawagar haɗin gwiwar jami'an tsaro ta 'yan sanda da sojoji suka fafata da 'yan bindigar kafin daga bisani su gudu cikin daji da mutanen da suka yi garkuwa da su.

    A ranar Litinin da dare ma wasu 'yan fashi sun kashe mutum 12 tare da kama wasu da ƙona gidajen garin Guga na Ƙaramar Hukumar Bakori ta Katsina.

    • 'Yan fashi sun kashe mutum 12 da sace dagaci a Bakori, an kuma kashe mutum 44 a Neja
  17. An hana amfani da amsa-kuwwa a tashoshin mota don rage hayaniya a Legas

    Gwamnatin Jihar Legas ta hana amfani da amsa-kuwwa da makirfo da sauran abubuwan ɗaukaka sauti a tashoshin mota da zimmar rage hayaniya a faɗin jihar.

    Da yake magana a wurin taron manema labarai a Ikeja jiya Talata, Sakataren Ma'aikatar Muhalli Dr Omobolaji Gaji ya ce yawan hayaniya a yankunan jihar abin damuwa ne.

    Gaji ya ƙara da cewa hayaniya ce ƙorafin da mazauna Legas suka fi yi duk shekara, inda take da kashi 75 cikin 100 na dukkan ƙorafe-ƙorafe.

    A cewarsa, ƙorafin ya shafi sauran wurare ba ɓangaren sufuri ba kawai; har da hayaniya a ɓangaren addini da kasuwanci da nishaɗantarwa da ƙarar jannareto da sauransu.

    Ya kuma ce lamarin na haifar da matsaloli ga lafiyar ɗan Adam.

  18. Ghana ta ci tarar kamfanin Sifaniya dala miliyan 6 bayan fashewar da ta kashe mutum 13

    Ghana ta ce kamfanin da ya mallaki motar dakon kaya da ta tarwatse ta kashe mutum 13 a watan da ya gabata ta karya dokokin ajiya da kuma safarar kaya.

    An ci tarar kamfanin mai suna Maxam Corp dala miliyan shida.

    Motar na ɗauke da abubuwan fashewa a kan hanyar zuwa wani wurin haƙar ma'adanai lokacin da ta yi karo da wani babur kuma ta tarwatse a kusa da garin Bogoso.

    Fashewar ta lalata ƙauyen Apiatse tare da raunata mutum 100.

    Kamfanin ya musanta hannunsa a lamarin, yana mai zargin wani ɗan kwangila.

  19. 'Abin da ya sa aka samu gurbataccen mai a gidajen mai a Najeriya'

    Hukumomi a Najeriya sun yi ƙarin bayani kan gurɓataccen man fetur da aka shigar da shi ƙasar.

    Tun a makon da ya wuce ne 'yan Najeriya da dama suka fara ƙorafi cewa man da suke sha a gidajen mai ya lalata musu abubuwan hawa.

    Amma a yanzu hukumomin sun ce an gano matsalar kuma an magance ta.

  20. Buhari ya karrama ƙwararru uku da lambar yabo ta NNOM

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya girmma wasu ƙwararrun 'yan ƙasar uku da lambar yabo ta Nigerian National Order of Merit (NNOM) ta shekarun 2020 da 2021 ranar Talata.

    Mutanen sun yi fice ne a ɓangarorin ilimi da suka haɗa da kimiyya da fasaha, da kuma likitanci.

    Wata sanarwa da Femi Adesina, mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, ya fitar ta ce Shugaba Buhari ya ce makomar Najeriya ta dogara ne kan yunƙurin ƙasar na shiga harkokin kimiyya da fasaha.

    Ƙwararrun su ne: Dr. Oluyinka Olurotimi Olutoye, ƙwararre a likitanci (2020), da marigayi Farfesa Charles Ejike Chidume, kimiyya (2020), da Farfesa Godwin O. Samuel Ekhaguere, kimiyya (2021).

    "Ina roƙonku da ku yi hoɓɓasa a kodayaushe don ƙarfafa gwiwar matasan Najeriya kuma ku tuna musu cewa makomarmu a matsayin ƙasa ta dogara ne kan shiga a dama da mu a cigaban duniya, musamman a ɓangaren kimiyya da fasaha," kamar yadda shugaban ya faɗa wa mutanen.

    Bai wa mutum ukun wannan lambar girma ta sa jumillar mutanen da suka same ta sun zama 79 tun bayan fara bayar da ita shekara 43 da suka gabata, a cewar Shugaba Buhari.