Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mataimakin Shugaban Najeriya ya ziyarci gidan su Hanifa a Kano

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu and Muhammad Annur Muhammad

  1. Najeriya ta tsayar da ranar da za ta yi karon-batta da Ghana don zuwa gasar duniya

    Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ta sanar da ranar 27 ga watan Maris, a matsayin ranar da tawagar kasar, Super Eagles za ta kece raini da Ghana, a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar, a wannan shekara 2022.

    Za a yi karon-battar, wanda zai kasance na biyu kuma na karshe a filin wasa na MKO Abiola da ke babban birnin Najeriyar, Abuja.

    Za su fatata ne bayan tawagar Super Eagles din ta koma gida daga Ghana don buga zagayen farko.

    Sai dai hukumar ta Najeriya ta ce har yanzu takwararta ta Ghana (GFA) ba ta tabbatar mata da ainahin ranar da za a yi karawar farko ba, a filin wasa na Cape Coast, a tsakanin ranar Laraba, 23 ga watan Maris ko Alhamis 24 ga watan na Maris.

    Wasan da Najeriya za ta karbi bakuncin tawagar ta Black Stars zai zama wasa na 60 tsakanin kasashen biyu da aka dade ana damawa da su a nahiyar Afrika.

    .

  2. An tsare 'yan jaridar BBC a Sudan

    An tsare wasu ‘yan jarida na BBC su uku a Sudan a yayin da suke aikin daukar labaran zanga-zangar masu fafutukar tabbatar da dumukuradiyya a babban birnin kasar Khartoum.

    BBC ta fitar da sanarwar tsare ‘yan jaridar nata, na Sashen Larabci, da aka yi ranar Litinin, a lokacin da suke bakin aiki, sai dai ta ce, ta yi farin ciki yadda hukumomi suka iya shawo kan lamarin da sauri

    Wadanda suke cikin jerin gwanon masu zanga-zangarsun dauki hotunan bidyo lokacin da wasu mutane a cikin farin kaya a kan babura da wata a-kori-kura farawadda ba lamba suka tsayar da ‘yan jarida.

    Tun bayan da soji suka yi juyin Mulki a watan Oktoba, hukumomin kasar suke ta kokarintauye hakkin fadin albarkacin baki, inda aka rufe wasu gidajen jarida, tare da yi wa wasu ofisoshin dirar mikiya, ‘yan jarida kuma ake muzguna musu.

    Jakadan Birtaniya a kasar ta Sudan, Giles Lever, ya sanya wani sakon tuwita inda yake cewa ya ji dadi an saki tawagar ta BBC, kuma ya kara da cewa muzguna wa ‘yan jarida abu ne da ba shi da muhalli a kasar da take fafutukar samun dumukuradiyya mai inganci.

  3. An kori jikan shugaban kasa daga gidan haya saboda bashi

    An kori jikan tsohon shugaban kasar Kenya Daniel arap Moi daga gidan haya saboda ya kasa biyan kudin da ya taru na wata shida, dala 2,100.

    Collins Kibet, mai shekara 45, ya gaya wa kotun cewa ba shi da kudi, ya talauce, ba zai iya biyan kudin hayarsa ba kuma ba ya iya ma kula da iyalinsa, inda ya ce a makon da ya wuce ne ma aka kore shi daga gidan.

    Ya zargi danginsa ciki har da matar babansa wadanda ke kula da rukunin gidajen mahaifinsa da ware shi daga cikin masu gadon mahaifinsa.

    Mahaifin Kibet, Jonathan Toroitich, wanda dan tsohon shugaban kasa Moi ne ya rasu a 2019 ba tare da ya bar wasiyya kan yadda za a raba dukiyarsa ba.

    An yi kiyasin cewa iyalan suna da dukiya mai dimbin yawa.

    Shi dai dan yana son kotu ta cire kishiyar babar tasa da danta a matsayin masu kula da rukunin gidajen kuma ta sanya shi a cikin masu cin amfanin dukiyar.

    Daman iyalan marigayi shugaban kasar wanda ya mutu shekara biyu da ta wuce, wanda kuma shi ne ya fi dadewa a kan mulkin kasar, suna shari’a a kan wanda zai kula da rukunin gidajen nasu.

    Mista Moi ya shugabanci kasar tsawon shekara 24, har sai da tsananin matsin-lamba ya sa ya sauka a 2002.

  4. Kotu a Kaduna ta umarci mata ta bayar da gidan mijinta haya ta rika amfani da kudin

    Wata kotun Shari’ar Musulunci da ke unguwar Rigasa, a Kaduna ta umarci wata matar aure, Rabi'atu Alhassan, da ta bayar da gidan mijinta haya domin ta samu kudin da za ta ciyar da ‘ya’yansu kuma ta biya kudin makarantarsu.

    Alkalin kotun, Malam Abubakar Salisu-Tureta, ya yanke hukuncin ne a ranar Talatar nan, bayan da matar ta roki kotun ta sa mijin nata Kabir Saidu, ya rika ciyar da su da kuma biyan kudin makarantar ‘ya’yan.

    Alkalin ya zartar da cewa matar ce za ta karba kuma ta ajiye kudin hayar a wajenta, ba mijin ba, domin ta rika sarrafa kudin yanda ya kamata domin kula da iyalin.

    Tun da farko matar ta sheda wa kotun cewa ita ce take ciyar da kanta da kuma ‘ya’yansu takwas ta hanyar dan kasuwancin da take yi, amma kuma kudin da take samu ba zai isa ta sa su a makaranta ba.

    Ta ce, ‘’A yanzu duka yaran suna gida ne. Ba sa zuwa makaranta; a gaskiya ma har sai da aka ci zarafin daya da lalata saboda an yaudare shi da abinci.’’

    Da yake mayar da martani na kariya, mijnin nata, ya ce ya kasa kula da ‘ya’yan nasu takwas ne saboda ba shi da aiki.

    Ya kara da cewa, ”Ina zuwa da abinci gidan idan na samu kudi.”

    Alkalin kotun ya dage shari’ar har zuwa ranar takwas ga watan Maris domin bangarorin biyu su je masa da bayanin aiwatar da wannan hukunci da ya yi.

  5. Mataimakin Shugaban Najeriya ya ziyarci gidan su Hanifa a Kano

    Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyarar ta’aziyya gidan su Hanifa, yarinyar nan ‘yar shekara biyar da ake zargin mai makarantarsu ya hallaka ta a Kano.

    Osinbajo ya kasance wani babban jami’in gwamnati kuma dan siyasa da ya ziyarci iyayen yarinyar, wadda ake shari’ar mutum uku da hannu a kisanta, bayan mai makarantar ta su ya sace ta.

    Mataimakin shugaban na Najeriya ya je Kano ne a yau Talata a matsayin babban bako a wurin taron shekara-shekara karo na 53 na kungiyar malaman da ke koyar da aikin lauya.

  6. Sanatoci sun amince da kara sabbin makaratun koyon aikin lauya 7 a Najeriya

    Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudurin dokar kafa karin makarantun koyon aikin lauya a bangarorin kasar shida.

    Majalisar ta amince da kudurin a zaman da ta yi yau Talata, 08 ga watan Fabrairu na 2022, bayan nazarin rahoton kwamitinta a kan harkokin shari’a da hakkin dan-Adam, kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.

    Makarantun da ake da su a yanzu su ne wadda take a Abuja; yankin arewa ta tsakiya, sai ta Kano, wadda ke Bagauda; yankin arewa maso yamma, sai ta Yola; yankin arewa maso gabas, sai ta Lagos; yankin kudu maso yamma da ta Enugu; yankin kudu maso gabas, da kuma ta Yenegoa a yankin kudu maso kudu.

    Wadanda aka amince a kara sun hada da wadda za a yi a Kabba jihar Kogi a arewa ta tsakiya, da wata a Jos a yankin arewa maso tsakiyar ita ma,

    da ta Maiduguri a jihar Borno domin arewa maso gabas, sai ta Argungu a jihar Kebbi yankin arewa maso yamma.

    Sauran su ne ta Okija a jihar Anambra a yankin kudu maso gabas sai ta

    Orogun a jihar Delta yankin kudu maso kudu, sai kuma ta Ilawe da ke jihar Ekiti a kudu maso yamma

  7. Wata rundunar jami'an tsaron Israila ta harbe Falasdinawa uku

    Jami'an Falasdinawa sun ce wata rundunar jami'an tsaro ta Israila ta harbe Falasdinawa uku a garin Nablus da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan.

    Wasu jerin bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda al'amarin ya faru tare da bayyana yadda sojojin Isra'ila ke tsaye a bayan wata mota ruwan toka.

    An ga kofofin motar a bude sannan harsashi ya yi mata kaca-kaca sannan kuma ga fasinjoji a ciki.

    Har yanzu dai babu cikakken bayani dangane da haƙiƙanin abin da ya faru.

  8. An rufe makarantu a jihar Karnataka ta Indiya kan batun sanya hijabi

    Hukumomi a jihar Karnataka da ke kudancin kasar India sun rufe dukkanin manyan makarantu da kwaleji-kwaleji na tsawon kwana uku, sakamakon karuwar zanga-zanga da ake yi kan mata ɗalibai Musulmai da ke sa hijabi.

    Babban ministan ilmi na jihar, Basavaraj Bommai ya buƙaci jama'a da su kwantar da hankalinsu.

    'Yan sanda sun yi amfani da kulake domin tarwatsa daliban masu zanga-zanga da ke jifa da duwatsu a wasu sassan jihar.

    A 'yan makonnin da suka gabata ne dai al'amarin ya fara, bayan da wasu kwaleji-kwaleji suka hana mata ɗalibai Musulmai sanya hijabi su shiga azuzuwa domin ɗaukar darasi.

    Hukumomin makarantun dai sun bayar da dalilinsu na hana sanya hijabin da ya yi karo da tsarin kayan bai ɗaya na 'yan makaranta.

  9. Saudiyya ta bai wa ƙwararriyar masaniyar lissafi ƴar Yemen shaidar zama ƴar ƙasa

    Saudiyya ta ba wata kwararriyar masaniyar lissafi da harkokin kasuwancin duniya Dokta Manahil Thabet damar zama 'yar kasar saboda kwarewar da ta nuna a bangaren bincike da na kimiyya.

    Wannan matakin na Saudiyya na ba fitattu da kwararrun mutane damar zama 'yan kasar ya biyo bayan wani sabon shiri ne da kasar ta fitar domin inganta kwarewar da kasar ke bukata tsakaninta da sauran kasashen duniya.

    Dokta Thabet ta bayyana fari cikinta a shafinta na Twitter bayan da Saudiyyar ta tabbatar ma ta da zama 'yar kasar.

    Ta ce: "Ina son bayyana jin dadina da godiyata ga mai yi wa masallatai biyu masu tsarki Sarki Salman bin Abdulaziz da Yarima Muhammad bin Salman Abdulaziz, saboda bani damar zama 'yar Saudiyya, ina kuma rokon Allah ya ci gaba da kare su."

    Ana kallon Dokta Manahil Abdul Rahman Thabet a matsayin 'yar baiwa cikin wadanda suka yi fice a fadin duniya, kuma ita ce Balarabiya ta farko da aka taba ba lambar "Mai Baiwa ta Shekara" wanda kamus mai na World Genius Dictionary a shekarar 2013.

    An kuma taba ba ta lambar yabo ta Sheikh Hamdan bin Rashid Al Maktoum saboda ta yi zarra a fagen Ilimi, bikin da aka yi a birni Dubai.

    Ga yadda Dokta Thabet ta bayyana kanta:

    "Ni daga Yemen na fito, kuma tun farko Allah ya ba ni baiwa, kuma tun ina mai shekara hudu da haihuwa aka gano ina da baiwa, saboda haka na sami damar shiga wani tsarin bunkasa baiwar da nake da ita."

    Ta kuma ce, "Tun ina da shekara 14 na kammala babbar makarantar sakandare, kuma na shiga jami'a ina da shekara 15 inda na koyi ilimin tattalin arziki a wata jami'ar Amurka. Ni ce mace mafi kankancin shekaru da ta sami digiri na uku a fannin ilimin fasahar tattalin arziki, wanda na samu tun ina da shekara 25 da haihuwa."

  10. Yawan shan paracetamol ka iya sa masu hawan hawan jini su kamu da ciwon zuciya

    Mutanen da ke da cutar hawan jini da suke yawan shan ƙwayar paracetamol na iya ƙara barazanar su kama da ciwon zuciya ko shanyewar jiki, a cewar wani rahoto.

    Masu bincike na Jami'ar Edinburgh sun ce ya kamata a lokaci guda likitoci su dinga tunanin barazana da amfanin shan maganin na tsawon watanni.

    Amma sun jaddada cewa shan maganin saboda ciwon kai da masassara ba shi da wata illa.

    Sauran ƙwararru sun ce ana buƙatar binciken da aka yi kan mutane da dama na tsawon lokaci don tabbatar da abin da aka gano ɗin.

    Ana yawan amfani da paracetamol a faɗin duniya saboda ciwon kai ko ciwon jiki na ɗan taƙaitaccen lokaci, amma kuma ana iya amfani da shi ga ciwuka masu tsanani na tsawon lokacin ma.

    A shekarar 2018 an rubutawa mutane rabin miliyan damar shan paracetamol.

    Binciken ya gano cewa duk masu hawan jini da ke yawan shan maganin na cikin barzanar ciwom ya munana.

  11. Ƴan bindiga sun hana ɗauko gawarwakin waɗanda suka kashe a Maru don yi musu jana'iza

    Kwana huɗu bayan kai wani hari da ya yi sanadin mutuwar mutum aƙalla 12 a ƙaramar hukumar Maru cikin jihar Zamfara, har yanzu 'yan bindiga sun hana a je a ɗauko gawarwakin don yi musu jana'iza.

    Harin na ranar Juma'a a Daraga, ya yi sanadin tarwatsewar mazauna garin zuwa gudun hijira.

    'Yan sanda a Zamfara sun ce suna ƙoƙarin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi jihar.

    Latsa hoton da ke sama domin sauraren rahoton da wakilin BBC Abdussala Ibrahim Ahmed ya hada kan batun.

  12. Mutum miliyan 13 na cikin barazanar yunwa a gabashin Afirka - MDD

    Hukumar Shirin Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta ce mutum miliyan 13 ne suke fuskantar matsananciyar yunwa a fadin kusuwar Afrika saboda fari da ake ci gaba da fuskanta.

    Rashin amfanar girbi da ƙarancin abinci na tursasa wa iyalai barin gidajensu a cewar WFP, kuma ana buƙatar taimakon gaggawa don kare afkawa cikin bala'i.

    Shekara uku aka yi a jere ba a samun damuna mai albarka - kuma farin na ci gaba.

    Amfanin gona na ta lalace, dabbobi na ta mutuwa sannan mutum miliyan 13 a Habasha da Somaliya da Kenya na cikin yunwa.

    Kayayyakin abinci na ta tsada, kuma rashin samun amfanin gona sosai ya sa babu ayyukan yi a bangaren noma, wanda hakan ya sa iyali ke shiga cikin matsi wajen ciyar da kansu.

    WFP ta ce idan har ba a samu taimako ba to za a faɗa cikin bala'in jin ƙan da ake gudu.

    WFP ta ce tana neman taimakon dala miliyan 327 don magance farin - wajen samar da abinci da kuɗaɗe a tsakanin al'ummun da abin ke shafa.

  13. Ana Allah-wadai da Boris Johnson kan ƙin bai wa jagoran 'yan adawa hakuri

    'Yan siyasa na bangaren gwamnati da na 'yan adawa sun yi Allah-wadai da matakin Firaministan Birtaniya Boris Johnson na ci gaba da yin kunnen ƙashi da gaza ba da haƙuri kan zargin ƙarya da ya yi wa jagoran 'yan adawa Keir Starmer.

    Kalaman Mista Johnson sun janyo dandazon mutane sun yi wa Mr Starmer iho a jiya Litinin.

    Wata tsohuwar minista ta jam'iyyar Conservative, Julian Smith, ta ce yana da matukar muhimmanci ga Dimiukradiyyar Birtaniya ta fatattaki duk wanda ya yi ƙarya.

    Masu zanga-zanga dai sun yi wa Mr Starmer ihu a birnin Londan, kan zargin ƙin ɗaukar mataki ga Jimmy Savile, kwanaki kadan bayan Mr Johnson ya zarge shi da ƙin yanke wa Mr Savile hukuncin alkalancin da yake babban mai shigar da ƙara na kasar.

  14. Abubakar Malami: Za mu mika Abba Kyari ga Amurka idan suka bukaci haka

    Hukumomi a Najeriya na iya mika wa Amurka jami'in dan sanda Abba kyari domin ya fuskanci tuhume-tuhumen da hukumar 'yan sandan Amurka ta FBI ke yi masa idan bukatar haka ta taso.

    Ministan shari'a na Najeriya Abubakar Malami ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da yayi da tashar talabijin ta Channels.

    Ministan ya ce hukumomin Najeriya na aiki tare da jami'an Amurka kan tuhume-tuhumen da ake wa Abba Kyari da mutumin da ake tuhuma da aikata damfara ta intanet wato Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi: "Wannan batu ne da ya shafi yin aiki tare tsakanin kasa da kasa kuma muna aiki tare, kana ana samun ci gaba."

    Sai dai Minista Malami bai ce komai ba kan abin da gwamnatin Najeriya za ta yi idan Amurka ta bukaci a mika ma ta Abba Kyari in ban da cewa kawo yanzu kasashe na ci gaba da duba batun.

    "Akwai batutuwa masu yawa da muke dubawa tare, ciki har da yiwuwar mika Abba Kyari, saboda haka ne hadin kai kan batun ke da muhimmanci matuka kan wadannan batutuwan."

    'Yan sandan Najeriya sun fara binciken tuhume-tuhumen da ake wa Abba kyari ne bayan da wasu bayanai suka fito daga hukumar 'yan sanda ta FBI kan alakarsa da dan damfara Hushpuppi wanda a halin yanzu ke tsare a wani kurkukun Amurka.

  15. Majalisar Zamfara ta sanar da mataimakin gwamna Mahdi cewa za ta tsige shi

    Majalisar Jihar Zamfara a Najeriya ta ce ta aika wa mataimakin gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau sanarwar cewa za ta tsige shi daga mukaminsa.

    Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Shamsudeen Hassan ya shaida wa tashar talabijin ta Channels wannan labarin a Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara.

    Ya ce majalisar za ta tsige mataimakin gwamnan daga mukaminsa ne saboda tuhumar da suke yi masa cewa ya aikata laifuka karkashin sashe na 190 da 193 (1), (2) (a)(b)(c) na tsarin mulkin Najeriya.

    Majalisar ta kuma tuhumi Mahdi Aliyu Gusau da azurta kansa da kudin al'umma ta haramtacciyar hanya bayan da ta ce ya karkatar da kudaden jihar ga wasu bukatun kansa, baya ga kitsa wani shiri na damfarar jihar.

    Yayin da mataimakin gwanan ke cewa bai aikata wani laifi ba, majalisar ta ce ta aika wa Mahdi Aliyu Gusau sanarwar tsige shin ta hannun sakataren gwamnan jihar ne.

  16. Ma'aikatan sufurin sama sun janye yajin aiki, sun kulla sabuwar yarjejeniya da gwamnatin Najeriya

    Da safiyar yau Talata gamayyar kungiyoyin ma'aikatan da ke aiki a bangaren sufurin jirgin sama a Najeriya sun janye yajin aikin da suka shirya yi a fadi kasar.

    Kungiyoyin sun fasa daukar matakin ne bayan da suka rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da gwamnatin Najeriya yayin wani zama na musamman da aka yi a shalkwatar ma'aikatar kwadago ta Najeriya a ranar Litinin a Abuja.

    Manyan batutuwan da suka janyo barazanar yajin aikin sun hada da rashin biyan ma'aikata sabon albashi mafi kankanta, wanda tun 2019 ya kamata a fara biya.

    Batu na biyu kuma shi ne jinkirin fara amfani da sharuddan aiki kamar yadda suka shafi ma'aikatan da ke aiki a hukumomin gwamnatin tarayyar Najeriya.

    Ministan kwadago da ayyukan yi na Najeriya, Mista Chris Ngige ya tabbatar da kulla yarjejeniyar:

    "Mun yarda tsakaninmu cewa hukumar da ke tsara albashin ma'aikata a Najeriya za ta aika wa dukkan ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya - har da wadanda ba ma'aikatan gwamnati ne ba - wata wasika da ke fayyace matakan da ya dace su dauka kan biyan albashin ma'aikata karkashin dokar Albashi ta bai daya na 2019."

  17. 'Yan Senegal na bikin nasarar kungiyar kwallon kafa ta Les Lions de la Téranga

    Al'ummar Senegal sun cika titunan babban birnin kasar Dakar, suna rawa da waka domin yiwa 'yan wasan kasar maraba lale, bayan yin nasarar cin kofin kwallon kafar Afirka a karon farko da suka yi a ranar Lahadi.

    Shugaba Macky Sall ya tarbesu cikin farin ciki da annusha, ya kuma yi jawabin godiya ga 'yan wasan da suka fito da kima da martabar kasar.

    Mista Sall ya jinjinawa mai horas da 'yan wasan Aloiu El-Tactico:

    "Ina godiya ga Koci Aliou El Tactico, kamar yadda ake fada bai cika magana ba, baya hayaniya, amma ya na da kwakwalwa, ya kuma jagoranci 'yan wasan mu da suka kawo wannan abin alfahari ga kasarmu."

  18. Maraba

    Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa barkanmu da safiyar Talata.

    Sunana Sani Aliyu kuma ni zan dinga wallafa muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya a wannan rana, kafin daga bisani abokin aikina Annur Muhammad ya karbe ni.

    Sai ku biyo mu don samun duniya a tafin hannunku.