Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mayakan ISWAP da iyalansu sama da 100 sun mika wuya a Najeriya

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Najeriya ta fasa dauko koci dan kasar waje

    Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta sanar da sauya fasalin yadda tawagar kasar, Super Eagles za ta kasance.

    NFF ta ce mai horad da kungiyar na riko Augustine Eguavoen zai ci gaba da aikin da yake kai, yayin da tsohon dan wasan Eagles din Emmanuel Amuneke zai zame masa mataimaki.

    A sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun sakatare janar nata Dr Muhammad Sanusi ta ce " hukumar kwallon kafar Najeriya ta kai karshen barin Augustine Eguavon ya ci gaba da horar da Super Eagles a matsayin kocin riko, yayin da Emmanuel Amuneke zai yi masa mataimaki.

    Haka ma hukumar ta ce tsohon dan bayan kasar Joseph Yobo da kuma Salisu Yusuf za su shiga cikin mataimaka hudu da kungiyar ta nada.

    Daman Amuneke ya yi aiki da NFF a matsayin kocin 'yan-kasa da shekara 20.

    Sanarwar ta kuma fito karara ta bayyana cewa ta dakatar da yarjejeniyar da ta tsara kullawa da Jose Peseiro, wanda aka sa ran cewa zai karbi aiki daga Eguavoen da zarar an kammala gasar cin kofin nahiyar Afrika.

    Emmanuel Amuneke ne ya ci wa Nigeria duka kwallaye biyun da ta ci kofin nahiyar Afrika a shekarar 1994 a karawarsu da Zambia.

    Kazalika shi ne ya ci kwallon da ta bai wa Najeriya damar cin lambar zinare a gasar Olympics ta Atlanta 96 da aka yi a Amurka.

    Tsohon dan kwallon ya kuma kai Tanzania gasar AFCON a 2019, haka nan mamba ne a kwamitin bincike da nazari na hukumar kwallon kafa ta duniya da ma CAF ta Afrika.

    NFF ba ta fito ta bayyana dalilin fasa dauko mai horarwa ba daga kasashen waje, to amma ana ganin sauye-sauyen da ta bullo da su na da nasaba da kasa tabuka abin a-zo-a-gani da Super Eagles ta yi a gasar AFCON da aka kammala ranar Lahadi a Kamaru, wadda Senegal ta yi nasara cin kofin a wasan karshe da Masar.

    A wata mai zuwa ne Najeriya za ta kara da Ghana gida da waje, a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar cikin watan Nuwamba.

  2. Sarki Sanusi II ya gargadi masu neman shugabancin Najeriya a 2023

    Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi gargadin cewa Najeriya za ta fuskanci mawuyacin hali fiye da wanda take ciki a yanzu daga 2023.

    Sanusi ya gargadi masu neman shugabancin kasar da su shirya wa katutun matsalolin da ke fuskantar kasar.

    Tsohon gwamnan babban bankin Najeriyar kuma Khalifan Tijjaniya a kasar, ya yi gargadin ne a Abeokuta babban birnin jihar Ogun, inda ya halarci bikin cika shekara 80 da haihuwar jagoran addini na kasar Yarabawa (Babanla Adinni of Egbaland) Chief Tayo Sowunmi.

    Sarki Sanusi ya ce, ‘’A gaskiya muna rayuwa ne a kan siradi. A 2015, muna cikin mawuyacin hali. A 2023, za mu kasance a cikin mawuyacin halin da ya fi na 2015.’’

    “Ina fatan wadanda suke fafutukar zama Shugaban Kasa, sun fahimci cewa matsalolin da za su fuskanta suna da yawa sosai ninkin-ba-ninkin wadnd muka fuskanta a 2015,’’ in ji shi

    Ya kara da cewa, ‘’ Dole ne dukkanninmu mu shirya wa matakai masu tsauri, kuma idan aka dauke su dukkaninmu sai mun dandana kudarmu.’’

    Ya ce, ‘’maganin abin ba wai shi ne dukkanninmu mu tsunduma a siyasa ba. Wannan kasar na bukatar ‘yan siyasa na-gari.

    Tana bukatar malamai na Musulunci da na Kirista wadanda za su iya tashi tsaye su gaya wa ‘yan siyasa cewa su ji tsoron Allah.’’

    ‘’Kasar na kuma bukatar kwararrun ma’aikata wadanda za su kalubalanci manufofin ‘yan siyasar.

    Tana bukatar shugabannin gargajiya wadanda za su fadi abin da ke zuciyar jama’a. Kowa yana da rawar da zai taka, kuma dole ne mu tashi tsaye mu yi iya.” In ji Sarki Sanusin II

  3. Mayakan ISWAP da iyalansu sama da 100 sun mika wuya a Najeriya

    A Najeriya, wasu mayakan kungiyar ISWAP da iyalansu, su fiye da dari daya sun tuba, kuma sun mika wuya ga rundunar sojan kasar a jihar Borno.

    Mutanen dai sun kunshi maza majiya karfi da mata da kuma kananan yara. A can baya ma wasu daruruwan 'yan kungiyar Boko Haram sun mika wuya.

    Wasu bayanai da hedikwatar rundunar sojan Najeriya, ta wallafa a shafinta na Facebook, sun nuna cewa, mayakan na ISWAP da iyalinsu, da yawansu ya kai dari da hudu sun mika wuya kuma suka mika kansu ga dakarun rundunar sintirin soja ta runduna ta 25 da ke Damboa a jihar Borno.

    Adadin 'yan kungiyar ta ISWAP da suka mika kansu ga sojojin, ya hada da maza 22, da mata 27, da kuma yara 55.

    Rundunar sojan Najeriyar ta kuma wallafa hotunan da ke nuna mutanen da suka mika wuyan, bayan ta kwaso su daga dajin Sambisa, suna sauka daga wasu motocin jigila na soja, da kayansu irin su kwanikan cin abinci da tukwane, da sahani ko buta, da bokitai, da kunshin tufafi, da kekunan hawa da dai sauransu.

    Duk da rahoton da ake samu na mika wuyan da mayakan ke yi yakin d shekara 13 na ci gaba da wakana a yankin na arewa maso gabashin Najeriya, musamman jihar ta Borno, da surn makwabtan kasashe.

    Ko a ranar Adabar mayakan ISWAP din sun sace fara hula uku a kauyen Mandaragirau a abin da ake gani kamar wani hari ne na ramuwar gayyabayan da mayakan kungiyar 25 suka nitse a ruwa a kusa da tafkin Chadi, yayin da suke kokarin tsere wa harin sama na sojin Najeriya.

    Tun a shekarar da ta gabata mayakan na Boko Haram ke ta ajiye makamansu, suna mika wuya su da iyalansu ga sojoji, kuma an kiyasta yawansu ya kai kusan dubu shida.

    Masu sharhi kan sha'anin tsaro suna ganin, mayakan suna mika wuyan ne, a sakamakon rikicin shugabanci, da yankewar makamai, da gajiyar zama cikin kungurmin daji, da tsoron makomar rayuwarsu.

    Kuma sun kasance ba su da wani zabi da wuce, ko dai su mika wuya ga gwamnatin Najeriya, ko kuma su ci gaba da dawwama karkashin mayakan da ke ikirarin jihadin Islama.

    Wani kiyasi da majalisar dinkin duniya ta yi, ya ce kimanin mutum dubu 350 ne suka rasa rayukansu a rikicin na Boko Haram, da aka shafe shekara 12 ana fama da shi, wanda kuma ya fallatsa cikin kasashen jamhuriyyar Nijar da Chadi da kuma Kamaru, wadanda ke makwabtaka da Najeriyar.

  4. Isra'ila za ta binciki 'yan sandanta kan leƙen asiri a wayoyin mutane

    Gwamnatin Isra'ila ta sanar da kafa wani kwamitin bincike kan cewa 'yan sanda na amfani da wata manhajar leƙen asiri ga tsoffin masu taimaka wa tsohon firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu da sauran manyan ma'aikata.

    Ministan tsaron cikin gida Omer Barlev ya ce kwamitin zai binciki zarge-zargen da wata jaridar ƙasar ta rubuta mai suna Calcist (kalsayit).

    Jaridar ta rawaito cewa 'yan sandan sun yi amfani da manhajar kutse wajen tattara bayanan sirri da suke tona asirin ministoci da magadan gari da 'yan jarida da ma makusantan firaministan.

    Ta ƙara da cewa suna yin hakan ne ba tare da doka ta amince ba.

  5. An janye karar neman cire shugaban riko na APC Gwamna Mai-Mala Buni

    Wasu ‘yan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, karkashin gamayyar da suka kira Progressive Youth Movement (PYM), sun janye karar da suka shigar ta neman cire shugabanta na riko, kuma gwamnan jihar Yobe Mai-Mala Buni.

    ‘Yan kungiyar ta PYC karkashin jagorancin shugabarsu Princess Zahrah Mustapha-Audu, sun halarci babbar kotun tarayya a Abuja, a yau Litinin 07 ga watan fabrairu 2022, inda suka gabatar da bukatar dakatar da shari’ar

    Shugabar ta ce sun shigar da karar ne tun da farko saboda wani sabi a jam’iyyar, abin da ta ce tuni an sasanta.

    “An shawo kan wadannan matsaloli, ta amfani da hanyoyi na cikin gida na jam’iyyar.Abin da ya sa ke nan muka zo mu janye karar. Da bukatar da muka gabatar ta dakatar da shari’ar ranar Litinin, an dakatar da shari’ar a hukumance,’’ in ji ta.

    A watan Disamba na 2021 ne kungiyar ta shigar da kara a kan jam’iyyar APC da Gwamna Buni da kuma hukumar zabe ta Najeriya INEC, inda take korafi daga cikin abubuwa cewa bisa tanadin tsarin mulkin Najeriya sashe na 183, Buni a matsayinsa na gwamna mai-ci ba zai iya rike wani mukami kuma ya gudanar da aiki a APC ba.

    A don haka ta bukaci kotun ta tsayar da ranar da shugabncin rikon jam’iyyar karkashin jagorancin Gwamna Buni ya sanya na gudanar da babban taron jam’iyyar.

    Kuma kotun ta zartar cewa kwamitin amitattu na jam’iyyar ne y kamata ya sanya rana kuma ya gudanar da babban taron.

  6. Kwaleji a Indiya ta ba wa mata damar shiga aji da hijabi

    Wata kwaleji a kudancin Indiya ta sahhale wa wata ƙungiyar ɗalibai Musulmi mata da su sanya hijabi su shiga makarantar bayan ta haramta musu hakan na 'yan kwanaki.

    Ssai dai an umarci ɗaliban da su kasance a keɓantaccen aji.

    An dai yi ta sukar kwalejin bisa hukuncin hana 'yan matan shiga makarantar da ta yi sakamakon sanya hijabi.

    Masu rajin kare 'yancin dan Adam sun ce ƙudirin makarantar wani ƙoƙari ne na tozarta Musulmai marasa rinjaye a yankin da jam'iyyar Hindu Nationalist ke da iko.

    Gwamnatin jihar Karnataka ta haramta sanya tufafi da ta ce ya ci karo da daidaiton al'umma.

  7. Shugaba Buhari ya koma Najeriya bayan halartar taron Tarayyar Afirka

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja babban birnin kasar bayan kwana hudu da ya yi a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia inda ya halarci taron kungiyar tarayyar Afirka karo na 35.

    A lokacin da yake Addis Ababa, Shugaba ya halarci taruka da dama tare da gudanar da tattaunawa, wadda ta hada ta ministar harkokin wajen Guinea Bissau Suzi Barbosa wadda ta yi wa shugaba na Najeriya bayani game da yunkurin juyin mulkn da aka yi a kasar.

    Buhari ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe uku na rana agogon kasar.

  8. Kotu ta daure Sadiya Haruna wata shida

    Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin daurin wata shida ba zabin tara a kan tsohuwar ‘yar fim din Hausa na Kannywood, kuma fitacciyar mai sayar da kayn mata, Sadiya Haruna a bisa laifin batanci ga wani darekta a harkar fina-finan, Isa I. Isa.

    Kotun ta majistare wadda ke zama a filin jirgin sama na mallam Aminu Kano, ta same ta da laifin batanci ga darektan wanda ya kai ta kara, a shafinta na Istagram, a yau Litinin 07 ga watan Fabrairun 2022.

    Kotun ta kuma zartar da cewa kada wadda aka samu da laifin ta kara wani rabutu ko sanya wani abu a wani shafinta na sada zumunta da muhawara, wanda zai zama na batanci ga wani nan da shekara daya, idan ba haka ba za a sake yanke mata wani hukuncin na shekara biyu.

    Sai dai kuma Sadiya Harunar tana da damar daukaka kara kan hukuncin kotun.

  9. An ji amon bindigogi a babban birnin Guinea-Bissau

    An ji amon wuta na bindigogi a kusa da wani gidan rediyo mai zaman kansa, Capital, wanda aka fi saurare a Guinea-Bissau a yau Litinin.

    Rahotani sun ce 'yan bindiga da suka kai harin sun lalata kusan dukkanin kayan aikin gidan rediyon da ke babban birni kasarm Bissau, wanda ke da alaka da rediyon ''Muryar Amurka'' (VOA), na gwamnatin Amurka.

    A watan Yuli na 2020, ma an taba kai wa gidan rediyon na Capital hari.

    An kuma ji karar harbe-harben bindiga a cikin gidan gwamnati ma.

    Lamarin ya tayar da hankali inda jama'a suka rinka guje-guje da tserewa daga ofisoshinsu suna komawa gida.

    An shawarci ministoci da sauran mambobin majalisar zartarwa wadanda suka kasance a fadar gwamnatin kasar da su bar ginin.

    Akwai tarin sojoji dauke da manya da kananan makamai, kuma an killace harabar ma'aikatar cikin gida aka hana ababen hawa wucewa.

    Lamarin ya faru ne kwana shida bayan yunkurin juyin mulki da aka yi wanda bai yi nasara ba.

    An kashe akalla mutum 11 in ji hukumomi a yunkurin na ranar Talata lokacin da sojoji suka yi kokarin hambarar da gwamnatin Shugaba Umaro Sissoco Embalo.

    Shugaban ya kaddamar da bincike kan yunkurin juyin mulkin.

  10. Sojojin Tunusiya sun ceto 'yan cirani 160 daga teku

    Rundunar sojin ruwa ta Tunusiya ta ce ta ceto 'yan cirani fiye da 160 - mafi yawansu 'yan ƙasar.

    An yi aikin ceton ne a kusa da tekun Sfax da ke kudu maso gabashin ƙasar.

    'Yan ciranin ciki har da yara, suna yunƙurin shiga Italiya ne.

    A shekara da ta wuce, mutum aƙalla 55,000 ne suka tsallaka daga Tunusiya ko Libya, kusan ninki biyu kenan na adadin waɗanda suka tsallaka a shekara kafin haka.

  11. Al'ummar Moroko na shirin binne Rayyan da ya faɗa rijiya

    Al'ummar Moroko na shirin binne Rayyan, yaro mai shekara biyar da ya rasu bayan ya faɗa cikin wata rijiya tsawon kwana huɗu.

    Rayan Oram ya faɗa rijiyar ce mai tsawon mita 30 ranar 1 ga watan Fabarairu, abin da ya jawo gagarumin aikin ceto kuma ya ja hankali a faɗin duniya.

    Ɗaruruwan mutane ne suka taru a bakin rijiyar sannan dubbai suka dinga bin aikin ceton ta intanet.

    Za a gudanar jana'izarsa a yau Litinin a ƙauyensu da ke arewacin tsaunin Rif, wurin da tsautsayin ya faru.

    A lokacin da aka ciro yaron daga ƙarshe a yammacin Asabar, an yi ta shewa da murna. Sai dai murna ta koma ciki bayan an gano cewa Rayan ya rasu.

  12. Mutum uku ne suka mutu a tarwatsewar jirgin dakon mai a Najeriya

    An tabbatar da rasuwar mutum uku bayan wani jirgin dakon mai na wani kamfani ya tarwase a yankin Neja-Delta mai arzikin mai ranar Laraba, a cewar kamfanin ranar Litinin.

    An gano gawa biyu a ka jirgin ranar Lahadi bayan wadda aka gano da safiyar ranar.

    Masu jirgin dakon man, Shebah Exploration & Production Company, sun ce "abin da muka sa a gaba shi ne gano inda sauran ma'aikatan jirgin suke da lafiyarsu waɗanda har yanzu ba a san inda suke ba".

    An ceto ma'aikata uku daga tarwatsewar jirgin ranar Lahadi da safe, ana sa ran sauran ma na da rai.

    Jirgin mai suna Trinity Spririt na dauke da gangar mai akalla 50,000 lokacin da ya tarwase a Laraba da dare kuma ya ƙone ƙurmus zuwa Alhamis.

    Hukumomi na bincike kan abin da ya haddasa fashewar jirgin kuma ba su da tabbacin ko ya janyo kwararar mai.

  13. Matsalar da shafin NIMC ya samu ta hana 'yan Najeriya sabunta layuka a ƙarshen mako

    Masu amfani da wayar salula da ke kokarin sabunta layukansu a fadin Najeriya sun kasa yin hakan saboda matsalar shafin hukumar rajistar katin ɗan ƙasa ta Najeriya National Identity Management Commission (NIMC).

    Da yake magana kan korafe-korafen mutane, kamfanin sadarwa na MTN a Najeriya ya ce, shafin NIMC ba ya aiki a yanzu.

    "Ku yi hakuri da mu, ba za mu iya sabunta layukanku ba ko ingantawa a yanzu. Idan muka magince matsalar za mu yi muku ƙarin bayani. Muna neman afuwa da halin da kuka shiga," a cewar MTN.

    A gefe guda kuma, NIMC ta tabbatar da samun matsalar a ranar Asabar, wadda ta alaƙanta da aikin gyara da take gudanarwa.

    "NIMC na sanar da jama'a cewa shafin rajistar katin ɗan ƙasa ba ya aiki a yanzu saboda wani aikin gyara da ɗaya daga cikin kamfanonin da ke samar da sabis ga hukumar ke yi," in ji NIMC.

    Ta ƙara da cewa "NIMC na tabbatar wa 'yan Najeriya cewa sabis din tantance layuka zai dawo da zarar an kammala aikin".

  14. Kisan Hanifa: Gwamnatin Kano za ta ba wa waɗanda ake zargi lauya

    Babban wanda ake zargi da kisan Hanifa Abubakar mai shekara biyar a Kano, Abdulmalik Tanko, ya faɗa wa kotu cewa ba shi da lauya sannan ya buƙaci gwamnatin jihar ta sama masa lauyan.

    "Ba mu da lauya a yanzu saboda ba ma iya magana da kowa, amma ina roƙon gwamnati ta ba mu lauya," in ji Abdulmalik a zaman kotun na yau Litinin.

    Su ma sauran mutum biyun; Fatima da Hashin Isiyaku, sun amince da abin da Abdulmalik ya faɗa na neman lauyan.

    Lauyan gwamnati Musa Lawal ya ce gwamnatin za ta ba su lauyan kamar yadda suka buƙata. Da ma dai haka doka ta tanada saboda laifin da ake zargin su da aikatawa mai girma ne.

    Mai Shari'a Sulaiman Na Abba ya ɗaga zaman shari'ar zuwa 14 ga watan Fabarairun 2022 da ƙarfe 2:00 na rana.

    A watan da ya gabata ne 'yan sanda suka kama mutum uku da ake zargi da sacewa da kuma kashe 'yar shekara biyar ɗin a unguwar Dakata Kawaji da ke birnin Kano.

  15. Guguwar Batsirai ta yi mummunar ɓarna a Madagascar

    Ma’aikatan agajin gaggawa a Madagascar na tantance irin ɓarnar da guguwar Batsirai ta yi, inda bayanai ke cewa ta yi awon gaba da kauyuka da dama.

    Guguwar mai karfi wacce ta yi mummunar barna ta afkawa tsibirin ne a karo na biyu cikin mako biyu, kana ta kashe akalla mutane goma.

    An ba da rahoton cewa mutane Dubu 50 sun kauracewa matsugunansu.

    Wakiliyar BBC ta ce rufin gidaje da dama sun rufta, baya ga gine-gine da suka rushe, ga kuma ƙaƙƙarfar iska mai tafiyar kilomita 160 cikin sa'a guda.

    A wasu wurare ana ma fargabar zaftarewar kasa ta yi gagarumar barna.

  16. Sojojin Najeriya sun ce mayaƙan ISWAP da iyalansu 104 sun yi saranda

    Dakarun ƙungiyar Islamic State of West Africa Province (ISWAP) da iyalansu 104 sun miƙa wuya ga sojojin Najeriya, a cewar rundunar sojan ƙasar.

    Wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na zumunta, rundunar ta ce mayaƙan da suka yi saranda a ranar Asabar sun ƙunshi maza 22 da mata 27 da yara 55.

    Ta ƙara da cewa sun kai kan su ne ga dakarun rundunar musamman ta 25 da ke Damboa a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Yaƙin Boko Haram ya yi sanadiyyar kisan mutum aƙalla 300,000 sannan ya raba fiye da miliyan 2.5 da muhallansu, a cewar alƙaluman Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

  17. Buhari ya kama hanyar komawa Abuja

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kama hanyar komawa gida Abuja daga Addis Ababa babban birnin Habasha (Ethiopia) a yau Litinin.

    Buhari ya bar Abuja ranar 3 ga watan Fabarairu don hallartar taron Ƙungiyar Haɗin Kan Afirka ta African Union karo na 35.

  18. Hatsarin mota ya kashe mutum 13 tare da jikkata 34 a Indonesia

    Aƙalla mutum 13 ne suka mutu sannan wasu gwammai suka ji raunuka bayan wata motar bas ɗauke da ma'aikata zuwa hutu ta yi hatsari a tsibirin Java na Indonesia.

    'Yan sanda sun ce motar da ke ɗauke da fasinja 47 na kan hanyar Sukoharjo wajen wani taro a yankin Yogyakarta lokacin da direban ya kasa sarrafa motar sannan ya nufi ƙasan tsauni a ranar Lahadi.

    "Shaidun da muka yi magana da su sun ce sun ga direban a firgice a lokacin da yake kickici da hannun giyar motar, saboda haka akwai yiwuwar birkin motar ne ke da matsala ko kuma ba ya aiki," in ji shugaban 'yan sandan yankin mai suna Ihsan.

    Ana yawan samun hatsarin mota a ƙasar mai mutum miliyan 270, inda ake yawan amfani da tsoffin ababen hawa da kuma saɓa dokokin tuƙi.

    "Mutum 13 ne suika mutu. Wasu nan take, wasu kuma a asibiti, yayin da 34 suka ji raunuka," a cewar Ihsan.

  19. Cutar korona ta sake kama mutum 36 a Najeriya

    Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta NCDC a Najeriya ta ce ƙarin mutum 36 ne suka kamu da cutar korona ranar Lahadi.

    A rahoton da ta wallafa ranar Lahadi da dare, cutar ba ta kashe kowa ba.

    Jihohin da aka samu sabbin kamuwar biyar ne, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar. Su ne:

    • Legas - 23
    • Abuja - 5
    • Osun - 4
    • Taraba - 3
    • Nasarawa - 1

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 253,727 ne suka harbiu da cutar a Najeriya, sannan ta kashe 3,139 tun bayan ɓullarta a Fabarairun 2020.

  20. Rasha da Ukraine: Macron ya tattauna da Biden kafin isarsa Rasha

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tattauna ta wayar tarho da Shugaba Biden na Amurka don lalubo bakin zaren shawo kan rikicin Rasha da Ukraine ta lallami da lumana.

    Nan gaba a yau Litinin ne ake sa ran Mista Macron zai isa Moscow babban birnin Rasha don tattaunawa da takwaransa na Rashar wato Vladmir Putin.

    Ita dai Rasha na ci gaba da girke dakaru masu yawa a kan iyakar Ukraine, amma ta musanta shirin mamaye ƙasar.

    Jiya Lahadi ne mai ba wa Biden shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan ya yi gargadin cewa mamayewar Rashar na iya faruwa daga nan zuwa kowanne lokaci.