Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yan sanda 'sun ceto karin mutum 97 a Zamfara'

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotannin kenan

    Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi.

    Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu. Kafin lokacin, ku duba ƙasa domin karanta rahotannin da muka kawo muku a yau Talata.

    Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Dakaru mata na Civil Defence za su fara kare makarantu daga satar ɗalibai a Jihar Kwara

    Hukumar tsaro ta Civil Defence (NSCDC) reshen Jihar kwara da ke tsakiyar Najeriya ta shirya tawagar dakarunta mata da za su yi gadin makarantun jihar.

    An ƙirƙiri sabuwar tawagar ce, a cewar Kwamanda Makinde Ayinla, da zimmar daƙile sace-sacen ɗalibai daga azuzuwansu.

    Kwamandan ya bayyana haka ne a birnin Ilorin a yau Talata yayin da yake hira da manema labarai game da ayyukan hukumar a shekarar 2021.

    "A wannan watan (Janairu) za mu ƙaddamar da sabuwar rundunar da za ta yi gadin makarantunmu," a cewarsa.

    Tun a watan Yulin 2021 hukumar ta bayyana aniyarta ta tura dakaru mata dukkan jihohin Najeriya 36 domin kare makarantu daga sace-sacen ɗalibai.

  3. Taurarin da za su haska a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2022

    Ranar 9 ga watan Janairu ne za a soma gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2022 a kasar Kamaru.

    A wannan bidiyon, Ibrahim Mijinyawa, ya yi mana nazari kan taurarin da ake sa ran za su haskaka a gasar, wadda taurari irin su Salah da Ahmed Musa da Mane da Mahrez da Ndidi za su fafata.

  4. Nijar ta dakatar da shirin korar fitattun 'yan Rwanda daga ƙasar

    Nijar ta dakatar da shirinta na korar wasu fitattun 'yan ƙasar Rwanda takwas da aka kai su ƙasar daga Tanzania.

    An kyale su su ci gaba da zama tsawon kwana 30 har zuwa sanda za a kammala bincike.

    Jami'an soja ne da kuma harkokin siyasa a lokacin kisan ƙare-dangi na Rwanda da aka aikata a shekarar 1994, waɗanda ko dai kotu ta wanke daga zargi ko kuma aka sake su bayan sun gama zaman gidan yari.

    Matakin na zuwa ne bayan ƙarewar wa'adin da gwamnatin Nijar ta ba su na kwana bakwai cewa su bar ƙasar.

    Sun koma Nijar ne bayan ƙasar ta cimma yarjejeniya da Majalisar Ɗinkin Duniya a watan Nuwamba inda ta yarda ta ba su izinin zama na dindindin, sai dai Rwanda na cewa ba a shirya hakan da ita ba.

  5. 'Yan sanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan 'yan zanga-zanga a Sudan

    Jami'an tsaro a Sudan sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar neman mulkin kasar ya koma hannun farar hula.

    Mutane da dama a wasu biranen sun yi ta rera wakokin sukar sojoji da kuma neman rushe gwamnatin rikon kwaryar kasar.

    Gwamnatin rikon kwaryar na karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan wanda ya jagoranci juyin mulki a watan Oktoba.

    A Omdurman, mutane da dama sun kafa shingaye.

    Zanga-zangar na zuwa ne kwana biyu bayan murabus din Abdallah Hamdok wanda ya rike mukamin firaminista.

    Mutum 56 sun mutu yayin jerin zanga-zangar da aka soma tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan Oktoba.

  6. Buhari ya naɗa Doyin Salami mai ba shi shawara kan tattalin arziki

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa Dr. Doyin Salami a matsayin Babban Mai Ba da Shawara kan Tattalin Arziki.

    Kakakin fadar shugaban ƙasa Femi Adesina ya faɗa a yau Talata cewa ana sa ran Dr. Salami zai yi wa Shugaba Buhari jawabi game da lamuran tattalin arziki na cikin gida da kuma muhawarar da ake yi a kan su.

    Kazalika, zai dinga bin sawun abubuwan da ke faruwa a cikin ƙasa da kuma wajenta tare da samar da tsarin da ya fi dacewa sannan ya bai wa shugaban ƙasa shawara a kan su.

    Kafin naɗa shi a muƙamin, Dr. Salami mai shekara 59, shi ne shugaban kwamatin tattalin arziki na shugaban ƙasa.

    'Yan adawa da masana tattalin arziki sun daɗe suna sukar Buhari kan ƙin naɗa cikakken mai ba shi shawara kan tattalin arziki.

  7. 'Yan sanda 'sun ceto karin mutum 97 a Zamfara'

    Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta yi ikirarin ceto mutum 97 bayan jami'an tsaro sun yi luguden wuta a sansanonin 'yan bindiga.

    Wata sanarwa mai sa hannun Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ayuba N. Elkana, ta ce an ceto mutanen ne a kananan hukumomin Tsafe da Shinkafi ranar 3 ga watan Janairu.

    "Da yardar Allah, a yau muna masu sanar da ku gagarumar nasarar da hadin gwiwar jami'an tsaro suka samu a kananan hukumomin Shinkafi da Tsafe, inda aka ceto mutum 97 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata masu ciki 7, jarirai 19 'yan tsakanin wata 2 zuwa 7 da kuma kananan yara 16 'yan tsakanin shekara 2 zuwa 7 ba tare da wani sharadi ba," a cewar sanarwar.

    A cewar Kwamishinan 'yan sandan, daga cikin wadanda aka ceto, mutum 68 a dazukan Shinkafi aka ceto su, yayin da aka ceto mutum 29 a dazukan Tsafe.

    Ya kara da cewa an sace dukkan mutanen ne fiye da kwana 60 da suka wuce daga kauyuka uku; Adarawa, Gana da Bayawuri da ke yankin Rijiya a karamar hukumar Gusau.

    Kwamishinan 'yan sandan ya ce yanzu haka ana duba lafiyar dukkan mutanen da aka ceto daga tawagar likitoci ta gwamnatin jihar da 'yan sanda, kuma daga bisani za a mika su ga 'yan uwansu.

  8. Isra’ila ta ba masu auren jinsi ɗaya damar ɗaukar ciki

    Isra'ila za ta ƙyale waɗanda suka yi auren jinsi ɗaya, samun damar ɗaukar ciki ta hanyar bayar hayar uwar da za ta ɗauki cikin.

    Kafin wannan sanarwar, ma’aurata namiji da maceda kuma matar da ba ta da aure ne kawai ke da ƴancin ɗaukar cikin.

    Ministan lafiya na Isra'ila, Nitzan Horowitz, ya ce matakin zai kawo ƙarshen rashin adalci da nuna wariya na tsawon shekaru.

    Ƴan maɗigo da Luwaɗi a ƙasar sun daɗe suna neman ƴancin ɗaukar cikin ta hanyar saka maniyi a cikin wata kuma da za ta reni cikin ta haihu.

    Sabon tsarin zai fara aiki ne a ranar 11 ga Janairu.

  9. Ƴan sanda sun ɗakile yunƙurin ƙona fadar Basaraken Imo

    Rundunar ƴan sandan jihar Imo ta ce ta yi nasarar murƙushe yunƙurin cinna wa fadar babban basaraken wuta.

    Rahotanni sun ce wasu ƴan bindiga ne suka abka fadar Eze na Imo Emmanuel Okeke da ke ƙaramar hukumar Orlu inda suka yi yunƙurin ƙona fadar a cikin dare.

    Sanarwar da rundunar ƴan sandan Imo ta fitar ta ce ta yi nasarar murƙushe harin tare da taimakon ƴan banga.

    Yan sandan sun ce an kashe ɗaya daga cikin maharan.

  10. 'Yan biyun da aka haifa a shekara daban-daban a 2021 da 2022

    An haifi wasu ƴan biyu a shekara daban-daban a Amurka, a shekarar 2021 da kuma 2022.

    Minti 15 ne tsakanin haihuwar tagwayen wanda ya raba shekarunsu.

    An haifi tawagyen ne a wata asibiti da ke Salinas, jihar California.

    An fara haihuwar namiji a 2021, bayan minti 15, kuma bayan shiga sabuwar shekara aka haifi mace a 2022.

    Asibitin Navidad da aka haifi jaririnan ne ya sanar da al'amarin a Twitter wanda ba a saba gani ba.

    Hakan na nufin an samu banbamcin rana da wata da kuma shekara a takardar shedar haihuwarsu.

  11. Rundunar sojin ruwan Najeriya ta gargaɗi al’umma kan shafukan rijistar aikin soja na bogi

    Rundunar sojin ruwan Najeriya ta yi gargadi ga jama’a kan su yi hankali da wasu shafukan bogi da ke yaudarar mutane da sunan rijistar shiga aikin soja.

    A sanarwar da ta fitar, rundunar ta ce tana da shafi na musamman na ɗaukar sabbin jami’an soja www.joinnigeriannavy.com inda ta shawarci al’umma cewa a nan ne kawai za su iya yin rijistar neman shiga aikin sojan ruwa.

    Rundunar sojin ta kuma ce tun a ranar 3 ga Janairu aka bude shafin da masu buƙata za su iya yin rijistar aikin na soja wanda za a rufe 13 ga Fabrairu.

  12. Za a yi wa waɗanda aka kama da laifin yin maɗigo da luwaɗi a shekarun baya afuwa a Ingila da Wales

    Mutane da dama a Ingila da Wales za su cancanci afuwa kai tsaye bayan yanke masu hukunci a shekarun baya kan aikata luwaɗi da maɗigo da aka yarda da su a yanzu - da kuma share laifukan daga bayanansu.

    Masu fafutuka sun ce dokar ta yanzu tana rauni, wacce ta mayar da hankali kan ayyukan masu neman jinsi ɗaya suna masu cewa ya kamata a faɗaɗa ta.

    Sun ci gaba da cewa ya kamata a haɗa da sauran laifukan a baya kamar tuntuɓa, wanda ‘yan sanda ke yawan amfani da shi wajen kama masu luwaɗi da maɗigo.

    Da take amincewa da kokensu, sakatariyar harkokin cikin gida, Priti Patel, ta ce tana fatan sabuwar dokar za ta bihanyoyin na "gyara kurakuran da aka yi a baya".

  13. An hana mutane fita a yankin Yuzhou na China

    Hukumomin China sun saka dokar kulle ba fita ba shiga bayan mutum uku sun kamu da korona a birnin Yuzhou.

    Yuzhou, da ke da yawan mutum miliyan ɗaya, an dakatar da zirga-zirgar sufuri, da kantina da wuraren nishadi. Wuraren sayar da abinci ne kawai aka amince a buɗe, kuma ma’aikatan da ke aikin korona ne kawai aka amince su fita.

    Xi'an, wanda lardi ne a Yuzhou, tsawon mako biyu aka saka kulle.

    Duk da ƙasashen duniya na ƙoƙarin rayuwa cikin annobar korona, amma China na ɗaukar matakai na hana cutar gaba ɗaya.

  14. El-Rufai ya ce ƙona dazukan arewa ne kawai zai yi maganin ɓarayin daji

    Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayar da shawarar a ƙona dazukan arewa domin ƙakkabe ɓarayin daji da suka addabi yankin.

    “Na sha faɗa cewa, abin da ya kamata shi ne a ƙona dajin, a kashe su gaba ɗaya, daga baya mu sake shuka bishiyoyi,” kamar yadda gwamna El-Rufai ya shaidawa kafar Arise TV a wata hira ta musamman.

    Ya ƙara da cewa ƙona dajin ne kawai mafita duk da matakin zai shafi waɗanda ba su ji ba su gani ba.

    “Ya fi a kakkabe su a dawo da zaman lafiya mutane su koma noma,” in ji shi.

    Ya ce yadda ake tunkararsu ba zai kawo ƙarshen matsalar ba - “domin idan an kore su daga Sokoto, za su tsere su tsallaka Kebbi.”

    “Abin da za a yi kawai a yi masu ruwan wuta ta sama da ƙasa a dukkanin jihohi shida na arewa maso yammaci da Neja.”

    “Idan aka yi haka ina ganin cikin makwanni ana iya maganin matsalar ”

  15. Ohanaeze ta ce dole Jonathan ya goyi bayan takarar ɗan kaɓilar Igbo a 2023

    Ƙungiyar ƙabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, ta ce ya kamata tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya goyi bayan ganin tabbatar da an zaɓi ɗan ƙabilar a matsayin shugaban ƙasa a 2023.

    Jaridar Punch ta ambato, jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar Alex Ogbonniana cewa, halin da Ndigboke ciki zamanin mulkin shugaba Buhari saboda goyon bayan da ƴan kaɓilar Igbo suka ba Jonathan.

    Ogbonnia ya yi tsokaci ne kan rahotannin cewa tsohon shugaba Jonathan ya gana da shugabannin kudu maso kudu yana neman goyon bayansu domin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.

    “Mu a tunanin mu, zai hoyi bayan Igbo, domin a rama wa kura aniyarta,” in ji shi.

  16. An zargi tsohon Ministan Tunisia da ta'addanci

    Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Tunisia ta ce ana zargin tsohon ministan shari'a da ake tsare da shi da "ta'addanci".

    An tsare Noureddine Bhiri na jam'iyyar Ennahdha a karshen mako.

    Ya ƙi amincewa da abinci da magani yayin da aka mayar da shi asibiti a ranar Litinin inda rahotanni suka ce ya ci gaba da yajin cin abinci.

    Ministan cikin gida Taoufik Charfeddine ya ce a ranar Litinin akwai rahotannin ayyukan ta’addanci wanda ya sa hukumomi suka ɗauki mataki.

    Jam’iyyar Ennahdha ta shiga hamayya da shugaba Kais Saied bayan ya kori Firaminista da kuma dakatar da majalisa a bara.

  17. Korona ta kama mutum 199 a Kaduna

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce an samu karin mutum 670 da suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar.

    Daga cikin sabbin wadanda suka kamu jihar Legas ce ta fi yawan mutane inda ta ke da 277.

    Korona ta kuma kama mutum 199 a Kaduna daga farkon Janairu zuwa ranar Litinin.

    A babban birnin Najeriya Abuja mutum 120, sai kwara mai 20 yayin da Abia ke da 14.

    A Katsina da Gombe mutum tara tara cutar ta kama a jihohin, a Bauchi mutum shida

    Yawan masu kamuwa da cutar na ƙaruwa a Najeriya, tun ɓullar sabon nau’in cutar korona na Omicron a ƙasar

  18. Korona ta kama shugaban Mozambique da matarsa

    Shugaban Mozambique Filipe Nyusi da uwar gidansa Isaura Nyusi gwaji ya tabbatar da sunkamu da korona inda suka killace kansu.

    Sanarwa daga fadar shugaban ƙasar ta ce Mista Nyusi da matarsa sun amince su killace kansu kamar yadda ka’idojin ƙasa kan matakan korona suka tanada, duk da cewa ba su nuna alamomin cutar ba.

    Ta ce sun amince su yi gwaji bayan “abubuwa da dama da muka yi akwanakin da suka gabata.

    Korona na ƙara bazuwa a kwanakin nan

    Mutum 193,000 suka kamu da cutar a Mozambique, yayin da ta kashe 2,031 yayin da mutum 158,680.

  19. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da ku a wannan shafin da muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya.