Ban kwana
Nan muka kawo muku karshen rahotannin na yau, Buhari Muhammad Fagge da Awwal Ahmed Janyau ke fatan mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.
Imam Saleh and Buhari Muhammad Fagge
Nan muka kawo muku karshen rahotannin na yau, Buhari Muhammad Fagge da Awwal Ahmed Janyau ke fatan mu kwana lafiya.
Sa'oi kafin gudanar da wata tattaunawa mai muhimmanci, Shugaba Vladmir Putin ya fada wa takwaransa, Joe Biden cewa yana da yakinin tattaunawar da za a yi tsakanin Rasha da Amurka za ta iya kasancewa mai tasiri.
Cikin sakon da ya aika wa takwaran nasa na Amurka, Shugaba Putin ya ce ya kamata tattaunawar ta kasance kan mutuntaka da la'akari da muradun kasashensu.
Gabanin kiran wayar da za su yi a yau, wani jami'in Fadar White House ya ce Amurka a shirye take ta tattauna bukatun Rasha amma kuma a shirye take ta kakaba takunkumai masu tsauri idan Rashar ta sake mamaye Ukraine.
Rasha dai na neman tabbacin cewa kungiyar tsaro ta NATO ba za ta shiga Ukraine ba.
Ma'aikatan Lafiya a Sudan sun ce jami'an tsaro sun kashe mutum hudu yayin zanga-zangar adawa da juyin mulkin da aka yi a kasar cikin watan Oktoba.
Rahotannin farko sun nuna cewa jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar a birane da dama ciki har da Omdurman.
Masu zanga-zangar sun bijirewa dokar kullen da aka sa inda suka yi tattaki zuwa fadar shugaban kasa domin kira ga sojoji su tsame hannunsu daga siyasa.
An katse layukan sadarwa a yunkurin hana mutane gudanar da gangamin.
An kuma dasa sabbin kyamarorin tsaro a manyan tituna. An dai gudanar da irin wannan zanga-zanga a wasu biranen Sudan uku.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ana bibiyar rahoton kudin hukumar raya yankin Niger Delta NDDC da zummar dawo da duk wani kobo da ya bata, tare da gurfanar da duk wanda aka kama da sama da fadi kan kudin.
Da yake magana wajen wani taro na hukumar a jami'ar Uyo dake Akwa Ibom, Shugaban ya ce abin takaici ne yadda wasu mutane tsirari suka cinye kudaden da aka aike wa yankin cikin kusan shekaru 20 domin bunkasar shi suka jefa mafi yawa cikin yanayi mara dadi.
"Wannan hukumar na bukatar cimma manufofin da aka kirkireta akai, domin samar da sauyi mai inganci ga rayuwarv mutanen yankin Niger Delta.
Rayuwar mutanen yankin za ta iya inganta sama da yadda take yanzu, da ace ana tafiyar da wadannan kudaden da ake aikewa sama da shekara 20.
An kashe akalla 'yan bindiga 38 yayin da 'yan sanda biyar suka mutu a samame daban-daban da aka kai cikin jihar Katsina.
Rundunar 'yan sanda jihar Katsina ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana karkashin shugaban 'yan sandan jihar Sanusi Buba.
"Babu shakka wannan shekarar da ta kare an fuskanci kalubale mai yawa a Katsina musamman na tsaro, sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta samu nasarori masu yawa a yakin da take da 'yan bindiga da masu satar mutane da 'yan fashi da sauran manyan laifuka da ake aikatawa.
Duk da haka 2021 cikinta an samu raguwar wadannan laifuka idan aka kwatanta da 2020".
"Cikin rikicin an samu nasarar kashe 'yan bindiga 38 an kuma kashe mana jami'ai 5."
Rundunar ta ce an kama wasu da ake zargi da muggan ayyuka 999 da suke da alaka da manyan laifuka 608.
A gefe daya kuma an kama wasu mutum 874 na daban da aka gurfanar gaban shari'a a jihar.
Ƴan sandan Singapore sun kama wani mutum mai shekara 37 da ake zargi da bayar da aron katin shedarsa ta rigakafin korona.
Mutumin dai na iya fuskantar ɗaurin shekara biyar a gidan yari ko kuma ya biya tara.
Sai dai mutumin bai halarci zaman kotu saboda dalilai na rashin lafiya da ya shafi kwakwalwa.
An kama wani shugaban addinin Hindu mai tsaurin ra'ayi, Kalicharan Maharaj, a tsakiyar Indiya saboda yin kalaman ɓatanci ga shugaban ƴancin kai na kasar Mahatma Gandhi.
Hakan na zuwa ne kwanaki bayan yin jawabi a wani taro inda ya yaba wa mai tsatsauran ra'ayin Hindu da ya harbe Gandhi a shekarar 1948, watanni bayan da Indiya ta sami ƴancin kai daga Birtaniya.
Mahatma Gandhi mutum ne mai daraja a Indiya. Amma wani sashe na masu tsatsauran ra'ayin addinin Hindu na da'awar cewa jagoran ƴancin kai ya fi fifita Musulmi.
Sun sha bayyana wanda ya kashe shi a matsayin mai kishi.
Haka kuma shugaban addinin na Hindu Kalicharan Maharaj ya caccaki addinin Islama a cikin jawabinsa.
Jawabinsa na zuwa kwanaki bayan wasu shugabannin Hindu masu faɗa a arewacin jihar Uttarakhand sun fito fili sun yi kiran farwa musulmi.
Sharhin Jaridu da dama sun yi kira ga Firaminista Narendra Modi da sauran shugabanni na jam’iyyar BJP mai mulki su fito su yi Allah wadai da jawaban. Har yanzu Mista Modi bai ce komi ba.
An dawo da bayar da tazara don kauce wa yaduwar korona a Masallacin Ka'aba da ke Saudiyya yayin sallar Azahar a ranar Alhamis.
Hukumomin da ke kula da Masallacin Ka'aba da Madina sun ce yanzu saka takunkumi da bayar da tazara ya zama wajibi a Masallatan biyu
Hukumomin sun ce matakin ya shafi masu aikin Umrah da masu ɗawafi da sauran masu Ibada a masallatan biyu.
Dubban mutane ne suka wayi garin safiyar Kirsimeti da samun saƙon ban mamaki na ba zato ba tsammani daga bankin Santander.
Bankin ya yi kuskure ya tura fam miliyan 130 zuwa asusun mutum 75,000 a ranar 25 ga Disamba.
Yanzu haka ma’aikatan Santander na koƙarin ganin yadda da za a dawo da kuɗin cikin gaggawa, duk da cewa aikin na tattare da ƙalubale saboda yawanci an tura kuɗin ga asusun mutane na wasu bankunan da ke hamayya, in ji The Times.
An samu matsalar ne bayan biyan asusun abokan ciniki 2,000 sau biyu.
“Muna neman afuwa saboda matsalar na’ura, wurin biyan abokan ciniki an yi kuskurer an biya kuɗin sau biyu a asusunsu," a cewar sanarwar da bankin ya fitar.
Bankin ya ce yana aiki da sauran bankunan Birtaniya domin ƙoƙarin dawo da kuɗaɗen.
Al'umma a Afirka ta Kudu na bankwana da marigayi Archbishop Desmond Tutu da ya yi yaki da mulkin wariyar launin fata wanda gawarsa ta isa cocin St George's Cathedral da ke Cape Town.
Daya daga cikin masu alhinin mutuwar Archbishop Desmond Tutu take mika sakon ta'aziyya ga dukkan iyalan marigayin.
An yi wa akwatin gawarsa ado da furanni dai-dai da burinsa. Magajinsa, Archbishop Thabo Makgoba ya ce lokacin alhini ne kuma lokaci na godiya ga rayuwar da ya yi.
Mutane za su rika zuwa bankwana da gawar har ranar 1 ga watan Janairu lokacin da za a kona ta sannan a ajiye tokar a cikin cocin.
Masu da'awar kishin addinin Islama a Somalia sun kai hari kan wani gari mai nisan kilomita kusan 30 daga arewacin Mogadishu, babban birnin kasar.
Yan sanda sun ce kimanin mutum bakwai ne suka mutu a fadan tsakanin kungiyar Al Shabab da dakarun gwamnati a Balad.
Wani wakilin BBC a Somalia ya ce masu ikirarin Jihadin na amfani da rikicin siyasar da ake samu a kasar.
Sojojin da ke goyon bayan yan siyasa na bangaren hamayya sun mamaye sassa daban-daban na babban birnin bayan Shugaba Mohamed Abdullahi Farmajo ya yi kokarin dakatar da Firaministan kasar inda yake zarginsa da aikata cin hanci.
Mohamed Hussein Roble ya bayyana matakin a matsayin wani yunkurin juyin mulki inda kuma ya nemi jami'an tsaro da su karbi umarni daga ofishinsa a maimakon daga Shugaban kasa.
Dubban mutane ne suka bijirewa dokar kulle a Khartoum, babban birnin Sudan inda suka fita zanga-zangar adawa da juyin mulkin da aka yi a watan Oktoba.
An katse layukan waya da intanet domin hana masu fafutuka shirya gangamin.
An tsaurara matakan tsaro a babban birnin sannan an dasa na'urorin nadar hoto a manyan hanyoyi. Wakiliyar BBC ta ce an girke sojoji da yan sanda da sauran jami'an tsaro amma duk da haka mutane sun fita zanga-zangar.
Bangaren hamayya a Sudan ya ce kusan mutum 50 aka kashe sannan daruruwa sun jikkata a jerin zanga-zangar da ake yi tun bayan da aka yi juyin mulkin.
Masu zanga-zangar na neman sojoji su tsame hannunsu daga gwamnati a yayin gudanar da zabukan da za su kai ga mika mulki hannun farar hula.
Wata sabuwar doka a China ta haamta wa ƴan ƙwallo a ƙasar yin Tatto, sannan waɗanda suka yi ma su je su goge.
A yanzu dole ne yan wasan su kai kansu a goge zanen duk da wahalar hakan ke tattare da shi, ko kuwa su rasa damar wakltar tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasa da kuma ƙarin wasu hukunce-hukunce.
Tun a shekarar 2018 ne hukumomi a ƙasar suka fara take-taken ɗaukar irin wannan mataki, inda aka buƙaci yan wasan da suka yi wa kansu zanen su riƙa rufe shi kafin wasa.
Mahukuntan China na da ra'ayin cewa barin ƴan ƙasar su yi Tattoo na iya sa wa a riƙa kallon al'ummar ƙasar a matsayin marasa dattaku.
Ma'aikatar tsaron Iran ta ce ta yi nasarar harba wani maɗaukin tauraron dan adam zuwa sararin samaniya.
An ce maɗaukin mai suna Simorgh ya kai tsayin kilomita dari hudu da saba'in.
Ma'aikatar ta ce yana dauke da wasu na'urori uku na bincike da aka samar a kaon farko, k da yake babu wai ƙarin bayani a kan su.
Wasu rahotanni sun nuna cewa Simorgh SLV bai kai isasshen gudun da zai iya sanya tauraron dan adam guda uku ba.
Shugaba Joe Biden na Amurka da Vladimir Putin za su sake zantawa ta wayar tarho a yau Alhamis yayin da Amurka ke kokarin hada kai da kasashen Turai wajen daukar mataki iri daya game da kara tura dakaru zuwa iyakarta Ukraine da Rasha ke yi.
Wani babban jami'i a gwamnatin Biden ya ce mutanen biyu za su tattauna batutuwa daban-daban na tsaro kuma Amurka a shirye take ta tattauna da Rasha game da damuwar da take da.
Jami'in ya ce Washington shirye take da a nemo mafita ta hanyar diflomasiyya; amma tare da haka, shirye take ta mayar da martani da tsauraran takunkumai idan Moscow ta mamaye Ukraine.
Shugabannin biyu dai sun wani taro ta na'ura a wannan watan wanda a ciki Mr. Biden ya sake jaddada goyon bayansa ga ci gaba da kasancewar Ukraine kasa mai cikakken 'yanci.
Jagoran kungiyar Taliban a Afganistan Hibatullah Akhundzada, ya jaddada cewa dole ne a mutunta afuwar da aka tsara yi wa jami'an gwamnatin da ta gabata a watan Agusta.
Mista Akhundzada ya shaidawa jami'an yankin Taliban a birnin Kandahar cewa bai kamata a hukunta tsoffin ma'aikatan gwamnatin Afganistan ba saboda kurakuran da suka yi a baya.
Rahotanni sun ce mayakan Taliban sun kashe wasu tsaffin sojoji da jami’an ‘yan sanda a Afghanistan a yankuna daban-daban.
Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta yi gargaɗin cewa zaɓukan ƙasar na 2023 na iya kasancewa cikin hadari, matukar ba a yi kokarin daƙile matsalar rashin tsaro ba.
A cewar hukumar kalubalen tsaron da ke kara ta'azzara da rashin hukunta masu kawowa shirinta saiko ba zai taimaka wajen cimma burinta na yin ingantaccen zabe ba.
INEC ta ce tun yanzu ta ara tsoron tura ma'aikatan wucin gadi zuwa yankunan da ake fama da rikici, wadanda kuma dole ne a yi zaɓen a cikinsu.
Ta kara da cewa su kansu da yawa daga cikin sama da ma'aikata miliyan daya da ba na dindindin ba da take amfani da su sun nuna fargaba tun yanzu.
Hukumomin Mexico sun ce akalla mutane 8 ne cikin har jaririn dan shakara daya da yarinya 'yar 16 aka kashe a cikin wasu tagwayen harbe-harbe masu alaka da safarar miyagun kwayoyi.
An yi kashe-kashen ne a wasu gidajen maƙwabta biyu da ke kusa da juna a jihar Guanajuato da ke tsakiyar kasar.
Wasu mutane uku sun samu raunukka.
Masu aiko da rahotanni sun ce fadan da ake tsakanin manyan kungiyoyin biyu na dillalan kwayoyi ya sa Guanajuato ta kasance jihar da aka zub da jini a duk kasar.
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 1,355 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar ranar Laraba 29 ga watan Disamba 2021.
Daga cikin sabbin wadanda suka kamu jihar Legas ce ta fi yawan mutane inda take da 1,036 sai Nasarawa mai 92, sai babban Delta inda aka samu 58 sai Abuja mai 57 yayin da Edo take da 44.
Sauran su ne jihar Rivers mai mutane 25, sai jihar Kano inda aka samu mutum 23 sai Enugu mai 11, sai Plateau mai 7, sai kuma Bayelsa mai 3.
Yanzu dai adadin waɗanda suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan ɓullarta ya kai 240,374 amma kuma an sallami 213,491 daga asibiti.
Yawan waɗanda suka rasa rayukansu sanadin cutar ta korona kuwa ya kai 3,028.