Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yan sanda sun kashe wasu kwamandojin IPOB a Imo

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Buhari Muhammad Fagge

  1. Gwamnatin Kano ta hana sayar wa ko ba da hayar gidaje ba tare da saninta ba

    Gwamnatin Kano ta bayar da umarnin cewa daga yanzu babu wani gida ko fili da za a sayar ko a bayar da haya a jihar ga wani mutum ko kungiya ba tare sahalewar dagaci ko kuma wasu wakilai da aka aminta da su ba a hukumance.

    Cikin wata sanarwa da kakakin sakataren gwamnatin ya fitar Musa Tanko Muhammad, ya ce an dauki wannan mataki ne saboda tabbatar da aminci da kuma tsare rayukan da dukiyoyin mutan jihar Kano.

    Ya ce wannan mataki ya zama dole ne domin tabbatar da cewa ayyukan da sojojin Najeriya ke yi na fatattakar 'yan fashin daji a wasu sassan kasar ya tafi daidai.

    Ya kara da cewa matakin na tafiya kafada da kafada da abin da gwamnatin tarayya ta sanya a gaba na kawo karshen matsalar rashin tsaro da kuma 'yan bindiga a wasu sassan kasar, lokacin da 'yan bindigar ke fama da wahala to suna tsallaka wa jihohin da ke makwabtaka ciki kuma har da Kano.

  2. Qatar da Taliban sun tattauna kan lamuran diflomasiyya

    Wani mai magana da yawun Taliban ya ce ministan harkokin wajen Qatar ya isa Kabul, babban birnin Afghanistan inda ya tattauna da shugabannin ƙungiyar a fadar shugaban ƙasa.

    Sheikh Mohammad bin Abdulrahman Al-Thani na ɗaya daga cikin manyan jami'an wata gwamnati da ya kai ziyara ƙasar tun bayan da ƙungiyar ta Taliban ta ƙwace mulki kusan wata guda da ya gabata.

    Wata sanarwa da aka fitar bayan ganawar ta ce sun tattauna kan alaƙa tsakanin ƙasashen biyu da agaji da ci gaban tattalin arziki da mu'amalarsu da sauran kasashen duniya.

    Masana na ganin ziyarar tasa ita ce alama ta baya-bayan nan da ke nuna matsayar yankin kan halin rashin tabbas ɗin da ake ciki a fannin siyasa a Afghanistan.

  3. Jirgin agaji na MDD ya sauka a Kabul

    Shirin samar da abinci a duniya na Majalisar Dinkin Duniya ya ce wani jirginsa na agaji ya sauka a Kabul a karon farko tun bayan da Taliban ta ƙwace babban birnin Afghanistan kusan wata daya da ya gabata.

    Hukumar ta ce tana taimaka wa ma'aikatan agaji daga hukumomi sama da ɗari da hamsin don isa zuwa ga mutanen da ke cikin tsananin buƙata a Afghanistan.

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mutane sama da dubu ɗari biyar ne rikicin na baya-bayan nan ya daiɗaita.

    Ko kafin ƙungiyar Taliban ta ƙwace mulki, Afghanistan na fama da rashin ruwa da annobar cutar korona, inda kusan rabin al'ummar ƙasar ke karɓar kayan agaji.

  4. Mohamed Salah ya ci kwallo na 100 a Premier League

    Mohamed Salah ya zura kwallo na 100 a raga a gasar Premier League a karawa da Leeds United ranar Lahadi.

    Liverpool ta ziyarci Leeds United domin buga wasan mako na hudu a gasar Premier League, inda Salah ya fara cin kwallo a minti na 20 da fara tamaula.

    Kwallon da Salah ya ci shine na 100 da ya zura a raga a Premier League, kuma na biyar da ya yi wannan bajintar a karancin wasanni, bayan Alan Shearer a wasa na 124, sai Harry Kane a karawa ta 141 da kuma Sergio Aguero a fafatawa ta 147.

    Na hudu a wannan namijin kokarin shine Thierry Henry da ya ci kwallo na 100 a Premier League a wasa 160, sannan Salah wanda ya ci a karawa ta 162

  5. Shugabannin Fulani sun yi taro kan dokar hana kiwo a fili a jihohin Kudancin Najeriya

    Shugabannin al'ummar fulani da ke kudu maso yamma cin Najeriya sun yi wata tattaunawa domin samo mafita mafita kan dokar hana kiwo a fili da wasu jihohin yankin kudancin suka sanya.

    An gudanar da taron ranar Lahdi a fadar sarkin Fulanin jihar Legas, Alhaji Muhammadu Abubakar Bambado dake a Surulere a Legas.

    Shugabannin sun yi shirin bin wannan doka sau da kafa da hukumomin yankin suka sanya, tare da shirin nemo wasu hanyoyin yin kiwo na daban.

    Gwamnonin yankin kudancin Najeriya sun yi wata doka domin hana Fulani kiwo a fili da kuma dazukansu.

    Shugabannin Fulanin karkashin jagorancin sarkin Fulanin Legas Alhaji Muhammad Abunakar Bambado sun ce za su nemi tattaunawa da gwamnonin Yarbawa da suran masu ruwa da tsaki a yankin domin neman mafita kan wannan doka.

  6. MDD za ta sanya kyamara a wajen da Iran ke ajiye makaman nukiliyarta

    Iran da Hukumar da ke kula da nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya sun cimma matsaya wadda ake sa rai za ta sassauta rikici bisa sa ido kan wasu wuraren da Iran ke ajiyar makamanta na nukiliya.

    A wata tattaunawa a Tehran, an amince cewa masu sa ido na ƙasa da ƙasa za su maƙala na'urorin ɗaukar hoto don tattara bayanai a wuraren.

    Iran ta kwashe tsawon watanni tana ƙin amincewa da wannan buƙata, kuma hukumar IAEA ta yi gargaɗin cewa hakan na matuƙar yi wa ayyukanta zagon ƙasa.

    Tarayyar Turai ta yi maraba da matsayar inda ta ce ta buɗe wani sabon fage na diflomasiyya.

    Iran ta jima tana taƙaita haɗin kan da take bai wa hukumar IAEA, don mayar da martani kan takunkumin tattalin arziƙin da Amurka ta ƙaƙaba mata.

  7. Babu wanda ya tsira a Najeriya - Sule Lamido

    Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP Sule Lamido ya bayyana damuwarsa kan halin tsaron da Najeriya ke ciki, yana cewa "jini ne ke zuba a ko ina a kasar.

    Yayin wata ziyara da ya kai wa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, a Abeokuta ya ce har yanzu Najeriya na zuciyar shugaban duk da kalubalen da take fuskanta.

    Cikin wata sanarwa da mataimakin Obasanjo kan harkokin yada labarai Kehinde Akinyemi, ya fitar ya ce Lamido ya ga Obasanjo cikin koshin lafiya.

  8. Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Bundesliga a bana

    Ranar Lahadi za a karkare wasannin mako na hudu a gasar Bundesliga, wadda tuni aka samu 'yan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye.

    Robert Lewandowski ne ya zama na daya a yawan cin kwallaye a gasar Bundesliga a bara mai 41. Shin ko a kakar bana zai ci gaba da jan ragama ko kuma Erling Haaland ko Andre Silva ko kuma wani da ba a yi tsammani ba.

    Robert Lewandowski

    Kungiya:Bayern Munich

    Shekarar haihuwa:33

    Wasannin da ya buga:4

    Kwallon da ya ci:6

    A sabuwar kakar bana ta 2021/22 Lewandowski ya ci kwallo a karawar mako na daya da na biyu ya kuma ci uku rigis a wasan mako na uku a fafatawa da Hertha Berlin, hakan ya yi bajintar cin kwallo a wasa 16 a jere a kungiyar.

    Wadanda ke kan gaba a cin kwallo a Bundesliga ta bana:

    • Robert Lewandowski FC Bayern Munich kwallo 6
    • Erling Haaland Borussia Dortmund kwallo 5
    • Taiwo Awoniyi FC Union Berlin kwallo 3
    • Anthony Modeste FC Koln kwallo 3
    • Moussa Diaby Bayer 04 Leverkusen kwallo3
    • Patrik Schick Bayer 04 Leverkusen kwallo3
  9. 'Yan sanda sun kashe wasu kwamandojin IPOB a Imo

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce takai wani samame sansanin 'yan kungiyar IPOB bangaren masu gwagwarmaya da makamai.

    Kakakin rundunar 'yan sandan da ke jihar Imo CSP Michael Abattam, ya ce wannan wata na sara ce ta yunkurin magance kungiyar masu tayar da hankali a yankin.

    Daily Trust ta ruwaito cewa sansanin yana hayin Amaifeke a karamar hukumar Orlu ta jihar Imo.

    Abattam ya ce sun samu cikakken bayanin sirri kan cewa wadannan mutanen na zaune a wani gida da ba a kammala gininsa ba a yankin, kuma suna yunkurin kara kaddamar da hare-harensu kan 'yan sanda da sauran gine-ginen gwamnati..

    " 'yan sanda sun kai wa mambobin kungiyar 'yan ta'addan hari a maboyarsu tare da bude musu wuta, in ji sanarwar da Abattam ya fitar a ranar Asabar.

    "An samu nasarar kashe wasu mambobinsu uku a wannan hari."

  10. Goggon biri 13 sun kamu da korona a gandun dawa

    Gidan namun daji a kudancin Amurka yaɗauki sabbin matakan kare namun dajin daga kamuwa da korona bayan goggon biri 13 daga cikin guda 20 gwaji ya tabbatar da sun kamu da cutar.

    Gidan namun dajin na Atlanta da ke Georgia ya ɗauki matakai da suka haɗa da yi wa namun dajin allurar rigakafi da suka haɗa da damisa.

    Shugabannin da ke kula da gidan namun dajin sun ce suna ganin goggon birin sun kamu da korona ne daga ɗaya daga cikin ma’aikatan da ke kula da su.

    Wadanda abin ya shafa sun hada da Ozzie dan shekara 60, mafi tsufa a cikin maza da ake tsare da su.

    Masana kimiyya sun bayyana damuwa cewa duk yaduwar cutar ga dangin goggon biri na iya yin illa ga jama'a.

  11. SERAP ta buƙaci gwamnatin Najerita ta buɗe layukan sadarwa a Zamfara da Katsina

    Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a Najeriya ta yi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kawo ƙarshen toshe layukan sadarwa a jihohin Zamfara da Katsina.

    Ƙungiyar ta ce toshe hanyoyin sadarwar ya saɓa wa ka’idar doka da buƙatar al’umma.

    “Toshe layukan wani hukunci ne ga ƴan Najeriya a waɗannan jihohin.”

    Hukumomin Najeriya dai sun ce toshe hanyoyin sadarwa na daga cikin matakai na tsaro domin kawo ƙarshen ƴan bindiga masu fashin daji da satar mutane da suka addabi jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

  12. Taliban ta yi magana kan Al Qaeda ƙungiyar Osama bin Laden

    Mai magana da yawun ƙungiyar Taliban ya yi watsi da rahotannin Majalisar Dinkin Duniya da ke nuna cewa kungiyar mayaƙan Al Qaeda na gudanar da harakokinsu a Afghanistan, inda ya kira iƙirarin cewa ba shi da tushe.

    Sohail Shaheen da yake magana da watar kafar labarai ta Pakistan, GEO ya ce Taliban za ta girmama yarjejeniyar da ta ƙulla a Doha wadda ta ƙulla a bara da Amurka kan daƙile yin amfani da Afghanistan a matsayin sansanin kai hare -hare kan wasu kasashe.

    Ya kuma yi watsi da rahotannin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na baya -bayan nan wanda ya nuna cewa akwai mayaƙan Al Qaeda a kusan rabin lardunan Afghanistan.

    Wadannan rahotannin sun dogara ne da bayanan karya da abokan hamayya suka bayar, in ji shi.

    Ya ce nan gaba, jami'an tsaro da na leƙen asiri na Taliban za su kara himma, wajen sa ido kan barazanar.

  13. Isra’ila ta ce Iran na ‘koya wa ƴan ta’adda yadda ake kai hari da jirgi marar matuki’

    Ministan Tsaron Isra’ila Benny Gantz ya zargi Iran da horar da ƴan ta’adda daga Yemen da Iraƙi da Syria da Lebanon inda ya ce ana koya masu yadda ake kai hari da jirage marar matuki a sansanin jiragen sama na Kashan.

    Gantz ya ce ana koya wa mayaƙan ne yadda za su yi aiki da jiragen mallakar Iran a sansanin na Kashan da ke arewacin Istafan, kamar yadda Jaridar Haaretz ta Isra’ila ta ruwaito a ranar Lahadi.

    Jaridar ta kuma ambato ministan yana cewa makamai ne masu cin dogon zango waɗanda Iran take samarwa kuma take aikawa mayaƙan da take alaƙa da su.

    Ya yi kira ga ƙasashen da suka ƙulla yarjejeniyar nukiliya da Iran su ƙaƙaba mata sabbin takunkumai.

  14. Taliban ta ce mata za su iya karatu a jami’a amma ba cuɗanya da maza

    Gwamantin Taliban ta ce mata za su iya yin karatu a jami’a amma ba za su yi cuɗanya da maza ba, kamar yadda ministan Taliban na ma’aikatar ilimi mai zurfi ya bayyana a ranar Lahadi.

    Ministan ilimin na Taliban Abdul Baqi Haqqani ya ce dole ne ya kasance babu cuɗanya tsakanin maza da mata. “Musulmai ne kuma dole su yarda da haka,” in ji shi.

    A farkon watan nan ne Taliban ta sanar da cewa mata za su iya yin karatu a jami’a amma sai idan sun sanya abaya da rufe fuska da nikabi, kuma babu cuɗanya da maza.

    Haqqani ya ce tsarin ya sauya a yanzu saɓanin zamanin mulkin Taliban na farko inda aka haramta wa mata zuwa makaranta da jami’o’i.

  15. Yadda matan Nijar ke zuwa ci-rani

    Filin ci-rani a Nijar ya tattauna ne kan ci rani a yankin Kanche na jihar Damagaram a Jamhuriyyar Nijar.

    A wannan karon, filin ya tattauna ne kan matan da ke tafiya ci-rani da irin kalubalen da suke fuskanta.

  16. Mutanen Chadi sun yi zanga -zangar adawa da mulkin soja

    Ɗaruruwan mutanen Chadi sun gudanar da zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin soja inda suka fito kan titunan birnin N'Djamena, kamar yadda kamfanin dillacin labaran AFP ya ruwaito.

    A halin yanzu sojoji ne ke mulkin Chadi karkashin jagorancin Mahamat Idriss Déby Itno.

    Ya ɗare kan karagar mulki bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Déby Itno a watan Afrilu, wanda tun 1990 yake mulki a Chadi.

    Masu adawa na ganin, sojojin na neman ci gaba da riƙe madafan ikon ƙasar.

    Sun zargi Faransa da goyon bayan gwamnatin sojin, inda rahotanni suka ce masu zanga-zangar sun fito suna yayata cewa “Chadi ba masarauta ba ce, ba ma son goyon bayan Faransa da kuma tsarin gado na Deby da ɗansa.

    Sojojin sun ce za su gudanar da zaɓe bayan wata 18 na tattaunawa, amma har yanzu ba a fara ba kuma har yanzu ba a kafa kwamitin rubuta sabon kundin tsarin mulki ba.

  17. Ƴan bindiga sun aika wa al’umomin Sokoto ‘wasikar barazanar hare-hare’

    Al’umomin wasu yankuna na jihar Sokoto a arewacin Najeriya na zaman ɗar-ɗar sakamakon wata wasika da ake zargin ta fito daga ƴan bindiga masu fashin daji inda suke barazanar ƙaddamar da hare-hare.

    Wasiƙar da aka yi da rubutun Hausa, kamar yadda wasu jaridun Najeriya suka wallafa, tana ƙunshe da barazanar ƙaddamar da hari kan yankunan Dange da Shuni da Kwanar Kimba da Rikina.

    A cikin wasiƙar da jaridar Punch ta wallafa a shafinta, marubucin ya yi barazanar cewar “sai mun shigo garin naku kuma idan ƙarya ce ku ajiye ma’aikata miliyan ku gani.”

    Rahotannin sun ce an tsinci wasiƙar ne a gindin bishiya.

    Zuwa yanzu hukumomi daga jihar Sokoto ba su fitar da wata sanarwa ba game da barazanar, kuma BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓar kakakin rundunar ƴan sandan jihar amma bai amsa kira ba.

  18. Amurka ta fitar da bayanai kan zargin alaƙar Saudiyya da harin 9/11

    Hukumar FBI mai binciken manyan laifuka ta Amurka ta fitar da bayanan farko daga binciken da ta gudanar kan zargin alaƙar Saudiyya da maharan da suka kai harin 11 ga watan Satumba, bayan umarnin Shugaba Biden.

    Bayanan binciken da aka sake yin nazari sun fayyace mu'amala tsakanin biyu daga cikin maharan da kuma wani da ake zargi jami’in leken asirin Saudiyya ne.

    Ba a bayar da ƙwararan hujjoji ba da ke tabbatar da goyan bayan gwamnatin Saudiyya ga shirin kai harin.

    Mutum 15 daga cikin maharan su 19 ƴan ƙasar Saudiyya ne, amma gwamnatin Riyadh ta sha musanta cewa tana da hannu a harin.

    Shugaba Biden ya bayar da umarnin fitar da bayanan binciken bisa buƙatar iyalan wasu daga cikin wadanda abin ya shafa.

  19. Ba a ga Trump ba a taron tunawa da harin 9/11

    Ba a ga Donald Trump ba a duka tarukan da aka yina tunawa da harin 11 ga watan Sataumban 2001

    Sai da an ga tsohon shugaban na Amurka a New York yana caccakar janye dakarun Amurka daga Afghanistan.

    A ranar Asabar Amurka ta yi bikin tunawa da harin shekaru 20 da suka gabata.

    Shugaba Biden ya ziyarci duka wurare ukun da jiragen saman suka faɗi, inda suka kashe kusan mutum dubu uku.

    Mitsa Biden ya ce tunawa da irin waɗannan abubuwa na da amfani matuƙa, sai dai kuma akwai wahala ga waanda abin ya shafa, sakamakon ana tuna musu da lokacin da aka yi musu waya kuma ana tuna musu da lokacin da suka samun labarin afkuwar lamarin.

    Amma Mista Biden ya mayar da martani ga kalaman na Trump inda ya kare matakin Amurka, kuma ya ce Amurka ba za ta iya cewa za ta kai hari a kowace ƙasa da ƴan Al Qaeda suke ba ba.

    Tsoffin shugabannin Amurka biyu Barack Obama da George W Bush, sun halarci taron.

    George W Bush wanda shi ne shugaban ƙasa a lokacin da lamarin ya faru shi ma ya halarci taron ya yi gargaɗi kan tsatsauran ra'ayi.

  20. Ƙarin mutum 5 sun kamu da korona a Kaduna

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 547 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Asabar.

    Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu da cutar a jihar Legas suke inda aka samu ƙarin mutum 110 da suka kamu da cutar a jihar yayin da jihar Oyo aka samu mutum 72 da suka kamu da cutar sai kuma Ribas mutum 56.

    Ga jerin jihohin da aka samu bullar cutar ranar Asabar:

    • Legas-110
    • Oyo-72
    • Ribas-56
    • Anambra-50
    • Osun-49
    • Delta-48
    • Abuja (Babban Birnin Najeriya)-42
    • Ekiti-29
    • Akwa Ibom-26
    • Abia-19
    • Kano-16
    • Edo-10
    • Benue-7
    • Ogun-6
    • Kaduna-5
    • Bayelsa-2

    A jimillance, adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 198,786 sai dai 185,075 sun warke.

    Akwai kuma mutum 2,590 da suka mutu