Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu
Kuna iya zuwa har ƙasan wannan shafin domin karanta labarai da rahotannin abubuwan da suka faru a sassan duniya
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Buhari Muhammad Fagge and Awwal Ahmad Janyau
Kuna iya zuwa har ƙasan wannan shafin domin karanta labarai da rahotannin abubuwan da suka faru a sassan duniya
Hukumomin Afghanistan sun tabbatar da cewa matashin ɗan ƙwallon ƙafar ƙasar ne ya faɗo ya mutu daga jirgin sama da ke shirin barin Kabul.
Zaki Anwari, mai shekara 19, ya buga wa ƙasar wasa a tawagar matasa.
Amma ba a yi ƙarin bayani ba kan mutuwarsa.
A cikin wata sanarwa a Facebook, Babban jami'in kula da harakokin wasanni ya jinjinawa Anwari inda ya yi masa addu'a tare da jajantawa ƴan uwan da abokanansa.
Tun ƙwace ƙasar Afghanistan da Taliban ta yi, dubban mutanen ƙasar ke tururuwa a filin jirgin sama na Kabul yayin da ƙasashen yammaci ke kwashe ƴan ƙasarsu da kuma abokan aikinsu ƴan Afghanistan.
Jaridun ƙasar sun ce aƙalla mutum biyu suka faɗo suka mutu. Rundunar sojin sama ta Amurka ta tabbatar da samun gawar mutum a maƙale a tayar jirginta bayan ya sauka Qatar.
An samu hatsaniya tsakanin ƴan Shi’a da ƴan sandaa birnin Sokoto yayin muzaharar juyayin ranar Ashura da mabiya Shi’a suka gudanar a ranar Alhamis.
Ƴan Shi’arsun zargin jami’an ƴan sandan da buɗe musu wuta lokacin da suke zagayen gari, lamarin da suka ce ya yi sanadin mutuwar mutum biyu da jikkata wasu da dama, sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta musanta hakan.
Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta ce yan Shi’a ne suka samu saɓani da mutanen unguwa, daga nan rikici ya ɓarke, tare da musanta buɗa wuta.
Ga ƙarin bayani a cikin rahoton Zahraddeen Lawan.
Rahotanni daga Afghanistan sun ce ƴan luwadi da maɗigo a Kabul sun ce suna tsoron rayuwarsu a ƙarƙashin mulkin Taliban, inda suka shiga ɓuya a gidajensu tare da fatan ƙasashen yammaci za su fitar da su daga ƙasar kafin gwamnatin Taliban ta zartar masu da hukuncin kisa.
Duk da Taliban ta nanata wa ƴan Afghanistan cewa su kwantar da hankalinsu, amma tsoron tsohon mulkin mayaƙan na jefe ƴan luwaɗi ya sa masu neman jinsi ɗaya shiga ɓuya.
Wani ɗalibi da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya zanta da shi ya ce hankalinsa ya tashi, kullum kuka da tunani yake kan makomarsa.
Ƴan ƙasar da dama dai na bayyana fargaba da tsoron makomarsu idan Taliban ta mayar da ƙasar bisa tarin shari’a.
Dokar Afghanistan ta 2017 ta haramta maɗigo da Luwadi kuma laifin na ɗauke da hukuncin kisa ƙarƙashin shari’ar musulunci amma ba a aiwatar da dokar ba tun 2001, kamar yadda ƙungiyar ILGA mai kare ƴan maɗigo da luwaɗi ta bayyana.
A karkashin gwamnatin Taliban ta farko, daga 1996 zuwa 2001, akwai rahotannin da suka ce duk wanda aka kama da laifin luwaɗi ana kashe shi ta hanyar maka shi a bango, babbar mota ta take shi.
Dakaru na musamman daga Amurka sun isa gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo domin taimaka wa a yakin da ake da masu ikrarin jihadi da ke buya a cikin daji.
Ofishin Shugaba Felix Tshisekedi a ranar lLahadi ya ce kasar ce ta nemi a kai mata ɗaukin soji a yankin domin taimaka wa wajen yakin da take yi da kungiyar 'yan ta da kayar baya ta ADF.
Har yanzu dai ba a bayyana adadin sojin da aka kai ba sai dai an nuna wasu hoto dauke da soji masu yawa.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin ganowa da tantance dazukan kiwo 368 da ake da su a jihohi 25 na ƙasar.
Shugaban ya bayar da wannan umarnin ne bisa amincewa da shawarwarin da kwamitin da ya kafa kan dazukan kiwon ƙarƙashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Farfesa Ibrahim Gambari.
Sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ranar Alhamis ta ce shugaban ya buƙaci a gano girman mamayar da aka yi wa dazukan na kiwo a ƙasar.
Daga cikin shawarwarin da kwamirin ya ba shugaban ƙasar sun haɗa da samar da taswirar dazukan da kuma tsara hanyoyin sadarwa da suka dace da ayyukan dazukan.
Sanarwar ta kuma ce haƙƙin kwamitin ne ya tantance matsayin dukkanin dazukan da halin da suke ciki na filayen da za a iya amfana da su.
Ƴan sandan Amurka na gudanar da bincike kan "barazanar harin bam" a kusa da ginin Majalisa a birnin Washington DC.
Ƴan sandan ginin Capitol a Amurka sun ce suna tattaunawa da direban motar da ake zargi na ɗauke da abin fashewar kusa da ɗakin karatu na majalisar da ke gefen titi daga ginin Capitol da Kotun Ƙoli.
Ba a san manufar direban ba, kuma yana yaɗawa kai-tsaye a cikin motar, kamar yadda suka bayyana.
An kwashe ma’aikata da dama da ke aiki kusa da wurin.
Majalisa na gudanar da hutu, amma akwai ma’aikata da ke yin aiki a ginin.
Mutumin ya ajiye motar ne gefen hanya kuma ya shaida wa wani jami’in da ya tunkare shi cewa yana ɗauke da bom, tare da riƙe wata na’ura mai kama da ta tayar da bom ɗin, kamar yadda babban jami’in ƴan sandan ginin Capitol Chief J Thomas Manger ya shaida wa manema labarai.
Wasu bayanan Majalisar Dinkin Duniya da BBC ta gani ya ce ƴan Taliban sun tsananta farautar mutanen da suka yi aiki tare dasojojin Nato da na Amurka.
Bayanan sun ceTaliban ta lissafa jerin sunayen mutanen da suke son kamawa.
Bayanan kuma sun ce manyan jami’an soji da ƴan sanda da masu binciken sirri sun fi fuskantar barazana.
Kuma a cewar bayanan Taliban suna kamawa ko kuma yin barazana ga dangin waɗannan mutanen har sai sun mika kansu.
Takardun bayanan sun ƙara da cewa mayaƙan na Taliban suna binciken mutanen ne yayin da suke ba da izinin kwashe wasu ma’aikatan kasashen waje daga filin jirgin saman Kabul amma halin da ake ciki ya ci gaba da zama mai sarƙaƙiya.
Babban malamin addinin Islama a Gaza ya yi kira ga Falasdinawa su tabbata sun karbi alluran rigakafin korona ba tare da ɓata lokaci ba.
Ya kuma bayyana duk wanda ya jinkirta yin haka a matsayin wanda ya aikata zunubi.
Babban malamin ya kuma ce duk wanda ya harbi wani da kwayar cutar ya zama wanda ya aikata laifin kisa amma ba da gangan ba.
Sanarwar da babban malamin, Sheikh Hassan al-Lahham ya fitar na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwar masu kamuwa da cutar korona a Zirin Gaza.
Mutanen da suka karbi alluran rigakafi akalla guda ɗaya, da kadan suka wuce mutum dubu 120, wanda bai wuce kashi biyar cikin dari na jama'ar Zirin Gaza ba.
Kungiyar Taliban ta dora alhakin hargitsin da ya auku a filin jirgin saman Kabul kan abin da ta kira harbe-harben da "baki daga kasashen waje" suka yi domin tarwatsa jama'a a can.
Wani jami'in Taliban ya ce an kashe akalla mutum goma sha biyu a filin jirgin saman Kabul daga ranar Lahadi zuwa yau.
Sai dai manema labarai sun ce mayakan Taliban ma sun rika yin harbi a iska, kuma wasu mutane sun ce mayakan sun yi mu su duka.
Wakiliyar BBC ta ce rahotanni daga Kunar a gabashin Afghanistan na cewa mayakan Taliban sun harbe akalla matasa uku har lahira yayin da suke maci dauke da tutocin kasar domin nuna farin cikinsu da zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar.
Kakakin Taliban din ya kuma ce an umarci mata ma'aikatan gwamnati da su zauna a gida saboda rashin ingancin tsaro.
Bayan an bayar da sanarwar cewa 'yan kasar da ke gujewa daga kasar za su isa Uganda, ministar harkokin iyali ta yi wata raha a kan kyawawan matan da ke cikinsu.
"Na ga mazanmu na Uganda suna yin addu'ar Allah Ya sauki 'yan gudun hijirar Afghanistan lafiya, sannan suka wallafa hotunan wasu daga cikin 'yan matan kamar yadda suke a sakon kasa," in ji Betty Amongi a sakon da ta wallafa a Tuwita.
"Sun yi alkawarin ba su goyon baya da hadin kai tare da gwamnati a wannan lamari! Muna fata ba 'ya'yan kungiyar maza marowata ba ne," a cewarta, cikin raha.
Wasu sun yi ta dariya bisa kalamanta a shafukan intanet ko da yake wasu suna ganin hakan bai dace ba.
Ms Amongi ta shaida wa BBC ta yi hakan ne kawai domin tskaci kan sakonnin da wasu suka wallafa a shafukan sada zumunta.
Hotuna sun nuna yan Afghanistan dauke da tutar kasa suna zanga-zanga a birane masu yawa ranar Alhamis, wanda hakan yazo daidai da bikin murnar cika shekara 102 da samun yanci.
Wannan dai na zuwa ne a lokacin da kasar ke fuskantar rashin tabbas da kuma barazanar rugujewa.
Wani hoto da aka wallafa a shafin sada zumunta ya nuna taron mutane a Kabul suna fadin ''tutar mu, asalin mu'' akan tutar da ke dauke da kaloli uku baki ja da kore.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce shaidu sun sanar da cewa da yiwar rasa rayukan mutane dayawa sakamakon irin wannan zanga-zangar ranar Alhamis a Asadabad sakamakon harbin bindiga ko kuma turmutsutsu.
Rahoton wadanda suka jikkata na zuwa ne kwana guda bayan da mace-macen mutane masu yawa da aka samu a Jalalabad a wani taro irin wannan na daga tutoci.
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sake bude makarantu a jihar daga ranar Laraba 18 ga watan Agusta 2021.
Ko da yake tace komawar za ta shafi yan aji uku na sakandare ne kadai.
Kwamishinan ilimi na jihar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Laraba.
Yace daliban za su rika zuwa makarantar ne da da kayan gida.
A satin da ya gabata gwamnatin jihar ta rufe makarantu sakamakon ayyukan soja da suke ta gudana akan yan fashi a arewacin Najeriya.
Gwamnati ta amine komawar yan aji uku na sakandare wanda za su rubuta jarabawar NECO BECE daga 23 ga Agusta zuwa 6 ga watan Satumba 2021.
Don haka makarantun sakandare za su koma aiki saboda yan aji uku kadai daga 18 ga watan Agusta sannan kuma ba za su saka kayan makaranta ba a cewar kwamishinan.
A ranar Laraba ne babban malamain ya kai wa shugaban ziyarar sai dai babu wani rahoto da ke bayyana abin da suka tattaauna ya zuwa yanzu.
Halifa Abdullahi wanda mazaunin unguwar Yola a Kano, wanda aka zarga da fasa tagar masallacin Tudun Maliki a daren Lahadi tare da kwashe kur'ani mai tsarki guda takwas.
Wani jami'i da ya yi magana da kamfanin dillancin Labarai na Reuters a boye, ya ce mutanen sun mutu ne dalilin turmutsutsu ko kuma an harbe su ne.
Wasu mutum 19 na daban kuma sun jikkata bayan wasu da ake zargi masu ikirarin jihadi ne suka farwa tawagar wasu fararen hula da sojoji ke yi wa rakiya a ranar Laraba, kamar yadda ma'aikatar yada labarai ta kasar ta bayyana.
Kila Arsenal ta fito da fam miliyan 34 daga lalitarta domin sayen gwanin dan wasan Real Madrid Marco Asensio, mai shekara 25.
Rahotanni a Najeriya sun ce Jihar Legas da ke kudancin kasar ta haramta bara a kan titina, ta kuma kafa hukuma ta musamman domin dakatar da wannan matsalar.
Ana sa ran hukumar za ta fara aiki a cikin 'yan kwanakin masu zuwa.
Wani jami'in jihar da ke kula da ci gaban matasa ya shaida wa manema labarai cewa mabarata a kan titina suna cutar da 'yan kasa masu bin doka.
Olusegun Dawodu ya ce ana yin safarar mabarata da masu talla ,wadanda suka hada da yara daga wasu sassan kasar zuwa birnin.
Ya ce kasuwancin yana kaskantar da kai da sawa a ci zarafin bil'adama,musamman yaran da aka tilastawa musu shiga.
Ya kara da cewa wasu daga cikin mabarata da masu sayar da kaya a titi suna da alaka da aikata laifuka a cikin gari ta hanyar kai hari da fashi ga mazauna birnin.
Kafofin yada labaran yankin sun ruwaito Mr Dawodu yana cewa ,''Ayyukan wadannan mutane akan tituna suna janyo koma bayan ga zirga-zirgar mutane da ababen hawa, yana haifar da illa ga muhalli da barazanar tsaro.''
Matakin ya zo ne kwanaki bayan yan sanda sun yi kira ga masu aikata miyagun laifuka da ke rikidewa kan su mabarata ne da ke kai hari kan mazauna Legas.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Sheik Dahiru Bauchi a fadarsa da ke Abuja.
A ranar Laraba ne babban malamain ya kai wa shugaban ziyarar sai dai babu wani rahoto da ke bayyana abin da suka tattaauna ya zuwa yanzu.
Duk da cewa babu tartibin abin da suka tattauna, amma rahotanni na cewa hakan ba ya rasa alaka da kisan da aka yi wa wasu matafiya a makon da ya wuce a jihar Plateau da ke arewacin Najeriya.
Kimanin mutum talatin ne suka mutu sakamakon wani hari da ake zargin `yan kabilar Irigwe da kaiwa kan motar matafiyan a cikin birnin Jos, amma sun musanta wannan zargi.
Kungiyoyin farar-hula a kasar, sun nuna takaici da kuma alhini game da kisan-gillar da aka yi wa matafiya Musulmin a gada-biyu da ke titin Rukuba a cikin birnin Jos.
Kisan da hatta mahukunta na zargin `yan kabilar Irigwe da aikatawa, duk kuwa da cewa shugabanninsu sun fito sun musanta.
Shugaban kungiyar amintattun kungiyar Nastura Ashiru Sharif, ya shaida wa BBC cewa sun yanke kauna game da ikirarin da mahukunta ke yi cewa za a hukunta mutanen da ake zargi da kashe matafiyan.
An kwashe rukunin farko na yan Kenya uku daga Afghanistan, yayin da tara ke suka maƙale a cikin kasar bayan kwace ikon da Taliban ta yi a ranar Lahadin da ta gabata, in ji wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar.
Mutum 12 sun yi aiki da kungiyoyin kasa da kasa ciki har da bankin duniya da kungiyar da aikin ceto na duniya.
Sanarwar ta ce, Kenya ba ta da ofishin jakadanci a Afghanistan kuma ta bukaci kungiyar da ta dauki mutanen 12 aiki da ta yi hanzarin kwashe su.
Daya ya na aiki da kungiyar kyautata harkar shari'a ta duniya, ya koma Kenya a ranar Laraba, yayin da biyu ke aiki da Contre la Faim,an kwashe su.
Ana sa ran za su dawo gida a daren yau.
Turkiyya na shirin kare filin jirgin Kabul babban birnin Afghanistan, biyo bayan ficewar da dakarun Amurka suka yi daga kasar, in ji shugaba Recep Tayyip Erdogan.
Turkiyya ta nemi ci gaba da iko da kuma gudanar da filin jirgin, wanda zai taimaka wa kasashen duniya wajen dawo da jami'an diflomasiyyarsu a Afghanistan.
Amma kwace iko da Taliban ta yi cikin gaggaywa ya janyo kokonto a kan shirin, wanda ake tattaunawa da jimi'an Turkiyya.
A gidan talabijin a ranar Laraba, Erdogan ya ce har yanzu Turkiyya na da niyyar ci gaba da iko da filin jirgin.
"Da zarar mun samu ikon ci gaba da gudanar da kasar, hakan zai sauya yadda ake kallon kasarmu," in ji shi.
"Amma yanzu muna sauya shirinmu da yanayin da muke ganin halin kasar a yanzu."
Aljeriya ta yanke hukuncin sake bibiyar alakarta da Moroko, inda ta zargi makociyarta ta a matsayin mai hadari.
Wannan na zuwa ne biyo bayan binciken kisan da aka yi wa wani mutum da ake zargin shi ne ya tayar da wutar dajin da ake fama da ita.
"Rashin amincin da ake zargin Moroko da shi wanda ta nuna wa Aljeriya, ya sa akwai bukatar a sake bibiyar alakar da ke tsakanin kasashen biyu da suka hada iyaka daya," kamar yadda jami'ai suka bayyana a wata sanarwa.
An yanke wannan hukuncin ne a yayin wani babban taro na kwamitin tsaro na kasar kan asarar da wutar dajin da ta tashi a kasar ta janyo.
Hukumomi sun tsaya akan cewa aikata hakan babban laifi ne.
Sun zargi Moroko da goyon bayan 'yan awaren da suke aikata muggan laifuka a yankin Kabyile, ciki har da kashe mutumin da ake zargi da tayar da wutar dajin.
A kalla mutum 47 ne suka mutu cikin har da fararen hula a arewacin Burkina Faso, a wani taho mu gana da aka yi tsakanin masu ikirarin jihadi da dakarun gwamnati.
Wasu mutum 19 na daban kuma sun jikkata bayan wasu da ake zargi masu ikirarin jihadi ne suka farwa tawagar wasu fararen hula da sojoji ke yi wa rakiya a ranar Laraba, kamar yadda ma'aikatar yada labarai ta kasar ta bayyana.
Sun kuma ce sojoji 14 da wasu masu aikin sakai daga Défense de la Patrie sun mutu.
Sojojin gwamnati sun ce sun kashe mutum 58 a wani abu na daukar fansa sun kuma jikkata wasu da yawa da ba a san adadinsu ba.
Tun 2015, Burkina Faso ke fuskantar hare-haren masu ikirarin jihadi abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama dubbai kuma suka gudu suka bar muhallansu.
Rikicin ya tilasta wa sama da mutum 17,000 barin kasar tun daga farkon wannan shekarar, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ce.