Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ƴan bindiga sun sace shugaban kwaleji a Jihar Zamfara

Wannan shafin na kawo muku rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotannin kenan

    Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya Kai mu.

    Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

  2. Manyan 'yan adawar Ivory Coast za su haɗe don kayar da Shuagaba Allasane Ouattara

    Biyu daga cikin tsofaffin shugabanni kuma daɗaɗɗun abokan gabar siyasa, Laurent Gbagbo da Henri Konan Bedie, sun sanar da cewa za su hade a jam'iyya ɗaya domin hambarar da Shugaba Allasane Ouattara a zabe mai zuwa.

    Mutanen uku dai su ne suka mamaye siyasar kasar tsawon shekaru da dama.

    Mr Gbagbo mai shekara 76 ya koma kasar bayan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke Hague ta wanke shi daga zargin aikata laifukan yaki.

    Ana zarginsa da hannu a rikicin bayan zabe na shekarar 2010 a lokacin da ya ki amincewa da shan kaye a zaben inda mutane da dama suka mutu.

    A wannan lokaci, Mr Bedie mai shekara 86 sun hade ne da shugaba mai-ci Ouattara, amma daga bisani gayyar ta watse.

  3. Ranar 20 ga Yuli za a yi Idin Babbar Sallah a Najeriya

    Sarkin Musulmi a Najeriya Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bayyana Lahadi a matsayin 1 ga watan Zul-Hijja na shekarar hijira ta 1442, wadda ta yi daidai da 11 ga Yulin 2021.

    Hakan na nufin za a gudanar Idin Babbar Sallah ranar Talata, 10 ga Zul-Hijja wanda ya yi daidai da 20 ga watan Yulin 2021.

    Bayanin na cikin wata sanarwa da Farfesa Sambo Wali Junaidu ya sanya wa hannu, wanda shi ne shugaban kwamatin shawarwari na Fadar Sarkin Musulmi.

    Al'ummar Musulmi na yin bikin Idin Babbar Sallah - ko kuma sallar layya - duk ranar 10 ga watan 11 na kalandar Musulunci.

    Bikin na bana zai kasance cikin matsin tattalin arziƙi musamman sakamakon annobar korona da kuma faɗuwar darajar kuɗi a ƙasashe masu tasowa kamar Najeriya.

  4. 'Mazauna sansanin gudun hijira a Borno sun haifi jarirai 17,053 cikin shekara 3'

    Ƙungiyar kula da 'yan gudun hijira ta duniya ta ce an haifi jarirai 17,053 a sansanonin 'yan gudun hijira na Jihar Borno kaɗai cikin shekara uku.

    Ƙungiyar ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) mai suna International Organisation for Migration (IOM), ta faɗa wa kamfanin labarai na NAN cewa an haifi yaran ne a sansani 18 da ke jihar, waɗanda kuma aka yi wa rajista daga 2019 zuwa watan Mayun 2021.

    Mista Frantz Celestin wanda shi ne shugaban IOM, ya ce sun haɗa gwiwa da hukumar ƙidaya ta Najeriya da kuma asusun yara na MDD domin sama wa jariran takardun haihuwa.

    Ya ƙara da cewa yi musu takardun haihuwa na da matuƙar amfani sannan kuma yana cikin ayyukansu na tattara bayanai domin bai wa masu bayar da tallafi ga yankin arewa maso gabashin Najeriya.

    "Mu ne muka fi kowa taimnakawa da matsuguni a Arewa maso Gabas, mafi girma a cikin masu kula da sansanoni, inda muke kula da sansani 115," in ji shi.

  5. Abin fashewa ya kashe mutum huɗu a filin wasa a Sudan

    Wani abin fashewa ya kashe mutum aƙalla huɗu tare da raunata uku a wani filin wasa da ke ƙasar Sudan.

    An kai harin ne a filin wasa na ƙungiyar Al-Amir da ke Port Sudan ranar Asabar. Likitoci sun ce an raunata mutanen ne ta hanyar harbi ko kuma caka musu wuƙa.

    Wata sanarwa daga ƙungiyar likitoci ta Sudan ta ce wani yunƙuri na kai wa wani otel hari a yankin bai yi nasara ba.

    Babu tabbacin wanda ya kai harin, wanda ƙungiyar ta siffanta shi da "na ƙabilanci".

    Garin Port Sudan ya fuskanci rikicin ƙabilanci a kwanan nan ciki har da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati.

    Ranar Talata da ta gabata ne aka harbe mutum uku a garin sannan aka jikkata 14 yayin wani tashin hankali.

  6. Fafaroma ya fito bainar jama’a karon farko bayan kwantar da shi asibiti

    A karon farko Fafaroma Francis ya fito bainar jama’a bayan yi masa tiyatakan matsalar da ta shafi hanji.

    Fafaroma ya fito cikin ƙoshin lafiya inda ya jagoranci addu’oi daga benen asibitin Gemeli da yake jinya a Rome.

    Ɗaruruwan mutane suka taru harabar asibitin, suna yi wa Fafaroma fatan tsawon rai.

  7. Labarai da dumi-dumi, Ƴan bindiga sun sace shugaban Kwalejin Gona da Lafiyar Dabbobi a Zamfara

    Ƴan bindiga sun sace shugaban Kwalejin gona da lafiyar dabbobi a Zamfara

    Ƴan bindiga sun sace shugaban kwalejin gona da lafiyar dabbobi da ke Bakura a jihar Zamfara Malam Habibu Mainasara

    Ƴan bindigar sun abka cikin gidansa ne suka tafi da shi, kamar yadda ɗaya daga cikin shugabannin Kwalejin ya tabbatar wa BBC.

    Ya ce cikin tsakiyar dare ƴan bindigar suka shiga gidansa da ke cikin wata makarantar sakandare ta kimiya a Bakura.

    “Ba su tafi da iyalinsa ba shi kaɗai suka tafi da shi,” in ji shi.

    Wannan na zuwa bayan ƴan bindiga sun kashe mutum sama da 40 a yankin mulkin Maradun da ke maƙwabtaka da Bakura a jihar Zamfara.

  8. Buhari ya buƙaci sojojin Najeriya su gaggauta murƙushe ƴan fashi

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen ƴan fashi a jihohin Zamfara da Kaduna.

    A cikin wata sanarwa da Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya buƙaci sojojin ƙasar da su gaggauta yin maganin matsalar a “yaren da ƴan fashin za su fahimta.”

    Wannan na zuwa bayan harin da ƴan bindiga suka kai a yankin Maradun a jihar Zamfara inda suka kashe gomman mutane.

    Haka kuma ƴan bindiga sun kai jerin hare-hare a Kaduna inda suka sace ɗaliban makaranta a makon da ya gabata

    Matsalar hare-haren ƴan fashi na ƙara ta’azzara musamman a arewa maso yammacin Najeriya, yankin da shugaba Muhammadu Buhari ya fito.

    Kuma duk da shugaban ya sha cewa za a kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga amma matsalar sai ƙaruwa ta ke.

    Kusan ɗalibai sama da 1,000 ƴan bindiga suka sace a bana, baya ga kashe-kashen bayan Allah da suke yi.

  9. Mawaƙin Najeriya Sound Sultan ya rasu

    Ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan Najeriya Sound Sultan ya rasu sakamakon fama da cutar kansa, kamar yadda danginsa suka sanar a cikin wata sanarwa.

    Mawaƙin wanda asalin sunansa Olanrewaju Abdul-Ganiu Fasasi ya rasu ne yana da shekara 44.

    Kuma an samu labarin mutuwarsa ne a safiyar Lahadi.

    A matsayinsa mawaƙi a Najeriya, marubucin waƙa, mai barkwanci, ana masa kallon ɗaya daga cikin fitattun masu waƙoƙin hip hop na zamani a Najeriya.

  10. Ƙungiyar Ohanaeze ta ƙabilar Igbo ta ce za ta sa ido kan shari’ar ɗanta Nnamdi Kanu

    Ƙungiyar Ohanaeze ta ƙabilar Igbo ta ce ta kafa kwamitin da zai sa ido kan shari’ar Nnamdi Kanu jagoran fafutikar ɓallewar yankin na ƙabilar Igbo daga Najeriya.

    Ƙungiyar Ohanaeze ta faɗi haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar bayan kammala babban taron da ta gudanar a Enugu a ranar Asabar.

    Sanarwar ta ce “Ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo ta lura da nuna buƙata kan sake gurfanar da ɗan mu, Mazi Nnamdi Kanu.”

    “Don haka domin tabbatar da ganin an yi wa Mazi Nnamdi Kanu adalci, mun kafa kwamitin lauyoyi ƙarƙashin babban mai ba Ohanaeze Ndigbo shawara na ƙasa domin sa ido ga shari’ar.”

    Ƙungiyar ta ƙabilar Igbo ta kuma goyi bayan matakan da gwamnonin kudu suka ɗauka kan hana kiwon-sake da miƙa mulki ga yankin a 2023.

    Amma Ohanaeze Ndigbo ta yi kira ga matasanta su kaucewa tayar da rikici inda a cikin sanarwar da ta fitar ta ce ba ta goyi bayan amfani da kowane irin nau’i na rikici ba a matsayin mafita ga nuna adawa da rashin adalci da ake nuna wa wani ɓangare na ƙasar.

    Maimakon haka Ƙungiyar ta ƙabilar Igbo ta yi kira ga matasanta su tabbatar da sun yi rijistar zaɓe a matsayin makamin tabbatar da burin yankin.

  11. Yadda Ingila da Italiya ke shirin haduwa a wasan ƙarshe na Euro 2020

  12. An zargi Saudiyya da azabtar da fursunonin siyasa

    Kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Human Rights Watch ta ce ta samu wasu sabbin bayanai na zargin azabtar da manyan fursunonin siyasa a gidajen yarin Saudiyya.

    Ƙungiyar ta ce ta samu saƙwanni daga wasu majiyoyi da suka bayyana kansu a matsayin jami’an gidan yari.

    Sun yi bayani dalla-dalla game da cin zarafin da aka yi yi wa mai rajin kare haƙƙin mata da aka saka, Loujain al-Hathloul.

    Ma’aikatan kuma sun ce akwai lokacin da suka fuskanci ƙalubale bayan da wata da ake tsare da ita ta suma, sun jin tsoron cewa ta mutu sakamakon azabtar da ita da aka yi.

    Hukumomin Saudiyya ba su ce komi ba game da zargin. Amma Saudiyya ta sha musanta amfani da azabtarwa a gidajen yarin ƙasar.

  13. Matar shugaban Haiti ta ce maƙiya ne suka kashe mijinta

    Matar marigayi Shugaba Jovenel Moise na Haiti ta zargi makiyansa a siyasa da amfani da sojin haya wajen halaka shi domin a dakile duk wani yunkurinsa na yin garambawul a kundin tsarin mulkin kasar da kuma inganta rayuwar jama'a.

    Cikin wani sakon murya da aka wallafa a Twitter, matar marigayin ta yi kira ga al'ummar kasar Haiti da su ci gaba da gwagwarmaya tare da alkawarin mara musu baya.

    Martine Moise ta ji rauni lokacin da ƴan bindigar suka yi dirar mikiya a fadar shugaban kasa da sanyin safiyar Laraba.

  14. Yadda Messi da Argentina suka yi murnar lashe kofi

    Dubban mutane sun bazu a titunan Buenos Aires, babban birnin Argentina domin murnar nasarar da ƙasar ta samu na lashe Copa America, karon farko cikin shekaru 28.

    Yadda dubban mutanen suka yi murnar nasarar da Argentina ta samu ke nan.

    Argentina ta doke Brazil ci 1-0 a wasan karshe na gasar nahiyarsu da aka buga a filin wasa na Maracana da ke Rio De Janeiro na Brazil

    Dan wasa Angel Di Maria da ke buga wa kungiyar PSG wasa ne ya zura kwallo dayan da Argentina ta samu kafin a kai ga zuwa hutun rabin lokaci.

    Wannan ne karon farko da tauraron dan wasan Argentina Lionel Messi ya lashe wata babbar gasa tare da tawagar Argentina.

    Ya sha zuwa wasan ƙarshe a tawagar Argentina amma sai bana Allah ya cika masa burinsa na lashe kofi

    Yadda Messi da tawagar Argentina suka yi murnar lashe kofi

  15. Ƙarin mutum 98 sun kamu da korona a Najeriya

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta NCDC a Najeriya ta ce an samu ƙarin mutum 98 da suka kamu da korona a ranar Asabar.

    Alƙalumman hukumar sun nuna cewa mutum 94 cutar ta kama a jihar Legas

    A jihar Ekiti kuma cutar ta kama ƙarin mutum uku, yayin da kuma aka samu ƙarin mutum ɗaya a Abuja birnin Tarayya.

    Kusan mako ɗaya cutar ba ta yi kisa ba a Najeriya. Jimillar mutum 2,122 cutar ta kashe a Najeriya

  16. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin inda za mu ci gaba da kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya a yinin Lahadi

    Za ku iya zuwa ƙasan shafin domin sanin wasu abubuwan da suka faru a ranar Asabar.

  17. 'Yan sanda na caje gida-gida don neman 'yan bindiga a Venezuela

    Dakarun tsaron Venezuela na ci gaba da kokarin dawo da doka da oda a babban birnin kasar Caracas bayan kwashe kwana biyu ana gwabza kazamin faɗa da kungiyoyin masu dauke da makamai.

    Fiye da jami’ai 800 ne ke shiga gida-gida suna zakulo mutanen da suka buya tare da kwace makamansu.

    Wakilin BBC ya ce a ranar Alhamis ne hukumomi suka sanya tukwicin dala 500,000 ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka taimaka wajen gano shugabannin maharan da ke kokarin faɗaɗa ikonsu.

    A halin da ake ciki babban fatan 'yan bindigar shi ne karɓe iko da ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da suka haɗa birnin na Caracas da yammacin kasar.

  18. Hatsarin jirgin ruwa ya kashe mutum 350 a Najeriya a 2020

    Aƙalla mutum 350 ne suka mutu sakamakon hatsarin jiragen ruwa a Najeriya a shekarar 2020, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito shugaban hukumar raya yankunan da ke samar da wutar lantarki na bayyanawa.

    Joseph Ityav wanda shi ne shugaban hukumar Hydroelectric Power Producing Areas Development Commission (HYPPADEC), ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Jihar Neja yayin da yake ƙaddamar da aikin sare itatuwa a ruwan Kainji da Shiroro.

    Ya ce ana gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar hukumar kula da tafkuna ta Najeriya, National Inland Waterways Corporation.

    Mista Ityav ya ɗora alhakin faruwar hatsarin a kan rashin cikakkiyar lafiyar jiragen da ɗibar mutane fiye da kima da ƙarancin rigar tsira da kuma itatuwan da ke cikin ruwan.

  19. Haiti ta nemi taimakon Amurka wajen samar da tsaro bayan kashe shugaban ƙasarta

    Haiti ta nemi Majalisar Dinkin Duniya da Amurka su ba ta dakaru don kare muhimman ababen more rayuwa yayin da kasar ke kokarin farfaɗowa daga zaman zullumin da kisan shugaba Jovenel Moise ya haifar.

    Manyan jami'an gwamnatin Shugaban Amurka Joe Biden sun ce babu wani shiri a halin yanzu na tura sojoji amma jami'an ƙasar za su taimaka wajen bincike.

    Jen Psaki kenan mai magana da yawun fadar mulki ta White House ta ce "za mu tura manyan jami'an hukumar bincike ta FBI don duba halin da ake ciki, daga baya mu ga ta fuskar da za mu taimaka".

  20. Kwalara ta kashe mutum 325 a Najeriya

    Cutar kwalara ta kashe mutum 325 a Najeriya tun daga watan Janairun 2021 zuwa 27 ga watan Yuni, a cewar Dr Chikwe Ihekweazu shugaban hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta NCDC.

    Dr Ihekweazu ya faɗa wa kamfanin labarai na NAN ranar Asabar cewa an samu mutum 1,786 da suka kamu da cutar a jiha shida daga 20 zuwa 26 ga watan Yuni.

    Jihohin su ne: Bauchi (1,239), Kano (362), Neja (62), Zamfara (55), Kaduna (59), Filato (9).

    A cewarsa, daga 13 zuwa 19 ga Yuni, jiha biyar - Bauchi, Kano, Kaduna, Filato, Zamfara - sun samu mutum 1,757 da ake zargin sun kamu da cutar.

    Jihohin da cutar ta ɓulla zuwa yanzu su ne: Benue, Delta, Zamfara, Gombe, Bayelsa, Kogi, Sokoto, Bauchi, Kano, Kaduna, Filato, Kebbi, Cross-River, Nasarawa, Neja, da kuma Abuja.