Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ƴan bindiga sun sace mutum 15 a asibitin kutare a Zaria

Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu

  2. An kashe sojojin Mali 4 a harin kwanton ɓauna

    Rundunar sojin Mali ta sanar da kisan sojojinta hudu a wani harin kwanton bauna.

    An kai musu harin ne a lokacin da suke sintiri yankin Timbuktu.

    Duk da cewa kawo yanzu babu wata kungiyar da ta yi ikirarin kai harin, mayakan Al-Qaeda na gudanar da ayyuka a yankin.

    A ranar Juma'ar da ta gabata ne Faransa ta sanar da dawo da yakar mahara a Mali, kuma dama ta girke sojoji dubu biyar a can.

    Hare hare na karuwa a Mali wadda ta fuskanci juyin mulki har sau biyu a kasa da shekara daya.

  3. Buhari ya taya Amurka murnar cika shekara 245 da samun ƴancin kai

    Shugaban Najeriya ya taya shugaba Biden da al’ummar Amurka murnar bikin ranar samun ƴancin kan Amurka.

    Buhari ya ce yana kuma nuna goyon baya ga gwamnatin shugaba Biden kan yadda ta ke koƙarin magance manyan ƙalubalen da Amurka ke fuskanta da suka haɗa da nuna wariyar launin fata da kuma yaƙi da annobar korona da ta addabi Amurka, ɗaya daga cikin ƙasashen da cutar ta fi yin kisa.

    Sannan ya ce yana cike da sha’awar yadda gwamnatin Biden ke ƙoƙarin inganta alaƙar Amurka da ƙasashen Afrika da kuma tabbatar da ci gaban nahiyar, tare da bayyana fatan hulɗar Amurka da Najeriya za ta ci gaba da bunƙasa domin amfanin mutanen ƙasashen biyu.

  4. Ƴan bindiga sun sace mutum 15 a asibitin kutare a Zaria

    Rahotanni a Najeriya sun ce wasu ƴan bindiga sun abka gidajen ma’aikatan asibitin kutare a garin Zaria suka yi awon gaba da mutum 15.

    Wani ma’aikacin asibitin ya shaida wa BBC cewa mutanen da ƴan bindigar suka sace sun ƙunshi maza da mata da kuma ƙananan yara.

    Ya ce an ƴan bindigar sun kai harin ne tsakiyar dare zuwa wayewar safiyar Lahadi.

    Wasu rahotanni sun ce cikin mutanen da ƴan bindigar suka yi garkuwa da su har da jarirai.

    Zuwa yanzu gwamnatin Kaduna da rundunar ƴan sandan jihar ba su fitar da sanarwa ba game da harin.

  5. An kwantar da Fafaroma Francis asibiti

    An kwantar da Paparoma Francis a asibiti a Rome domin shirin yi masa tiyata a cikinsa domin magance matsalar da ta shafi hanji.

    Kakakin fadar Vatican Matteo Bruni ya ce za su yi ƙarin bayani bayan an kammala tiyatar da za a yi a asbitin jami’ar Gemelli.

    Kafin kwantar da shi asibiti, Fafaroma ya gabatar da jawabi ga ɗimbin mabiya da suka ziyarci dandalin St Peter da safiyar Lahadi

    Wannan ne karon farko da aka kwantar da shi asibiti tun zaɓensa a 2013.

    Sanarwar da fadar Vatican ta fitar ta ce Fafaroman na son a magance masa matasalar da ta shafi wani ɓangare na babban hanji.

  6. ISWAP da Boko Haram sun 'sanya sabon haraji' ga manoma da masunta

    Rahotanni sun ce mayaƙan Boko Haram da ISWAP sun naɗa sabbin kwamandoji tare da sanya sabon haraji ga manoma da ƴan kasuwa da kuma masunta.

    Jaridar PRNigeria ta ce mayaƙan sun yi sabbin naɗe-naɗen ne bayan kashe shugabannin ƙungiyoyin biyu da sojojin Najeriya suka yi.

    “Bayan mutuwar Abubakar Shekau da kumahaɗewar mayaƙan, kwamitin Al-Barnawiy ya sake dawo da Ba-Lawan don jagorantar abin da suka kira Daular Islama taAfrika,” in ji jaridar.

    Sannan mayaƙan za su dinga karɓar N5,000 duk wata daga hannun ƴan kasuwa da manoma, masunta kuma za su biya harajin N2,000 ga duk jakar kifi ɗaya.

    Mayaƙan Boko Haram da ISWAP ba su sha da daɗi ba a ƴan kwanakin nan, inda sojojin Najeriya ke ci gaba da fatattakarsu a sansanonin da suke ɓuya.

    A ranar Asabar rahotanni sun ce an kashe mayaƙan kusan 30 a jihar Yobe bayan harin kwatan ɓauna da suka yi wa ayarin ƴan sanda a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

  7. Rundunar MNJTF ta ƙaryata iƙirarin Boko Haram da ISWAP na kashe sojojinta a Kamaru

    Rundunar haɗin gwiwa ta sojojin ƙasashen Tafkin Chadi ta zargi ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi na ISWAP da Boko Haram da yaɗa labaran ƙarya don samun gindin zama a zukatan jama'a.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Multinational Joint Taskforce (MNJTF) Kanal Muhammad Dole ya fitar, mayaƙan ISWAP na yaɗa labarin cewa sun kai wa dakarun MNJTF hari a Mora da ke cikin Kamaru.

    Ya ce labaran da suke yaɗawa a shafukan intanet, ciki har da Sembe TV, sun yi iƙirarin kashe sojoji da kuma kwashe makamansu.

    "Waɗannan bayanai ba gaskiya ba ne kwatakwata," a cewar sanarwar.

    "Gaskiyar lamarin shi ne, mayaƙan Boko Haram da ISWAP na fuskantar zafafan hare-hare daga dakarun MNJTF da kuma watsi da mutanen yankunan suka yi da su.

    "Domin a ci gaba da jin su da kuma yaudarar mabiyansu, sai suka koma yaɗa labaran samun nasara na neman kuɓuta."

  8. Babbar mota ta murƙushe 'yan kasuwa a JIhar Oyo

    Mutum aƙalla biyar ne suka rasu yayin da wata babbar motar dakon iskar gas ta afka kan 'yan kasuwa a JIhar Oyo da ke kudancin Najeriya ranar Lahadi, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.

    Lamarin ya faru ne a Kasuwar Bode da ke Ibadan, inda motar ta ƙwace wa direban, kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya bayyana, yana mai cewa mutum biyar ne suka rasu.

    Sai dai Daily Trust ta ce bincikenta ya gano cewa mutanen da suka mutu a hatsarin sun kai 10.

    Mista Osifeso ya ce mutane da dama sun jikkata amma sai sun gama bincike za su yi cikakken bayani.

    Jami'an kashe gobara da sauran jami'an tsaro na wurin domin daƙile abin da ka faruwa.

  9. Tawagar shugabannin Afirka na taimaka wa Eswatini magance rikicin siyasa

    Wata tawagar ministoci daga kasashen Kudancin Afirka za ta isa Masarautar Eswatini yau Lahadi sakamakon kwanakin da aka shafe ana rikici lamarin da ya janyo suka daga kasashen duniya.

    Shugaban Kungiyar kasashen Kudancin Afirka SADC ya ce tawagar za ta taimaka wa Eswatini wajen kamo bakin zaren tashin hankalin.

    Masu goyon bayan tabbatar da dimokradiyya ne dai suke gudanar da zanga-zanga a Eswatinin da a baya aka fi sani da Swaziland inda suke neman a sauya fasalin siyasa da masarautar kasar.

    Akwai ikirarin cewa sojoji sun lakadawa masu zanga-zanga duka sannan kungiyar Amnesty International na zargin an kashe kimanin mutum 20.

  10. An dakatar da aikin ceton mutanen da gini ya rufta da su a Amurka

    An dakatar da aikin ceto mutanen da watakila suke da sauran numfashi a ruftawar gini mai hawa 12 a Miami da ke Amurka.

    An ɗauki matakin ne domin bayar da damar rushe sauran ginin.

    Akwai fargabar cewa mahaukaciyar guguwar Elsa na iya ruguza ɓaraguzon ginin, abin da zai jefa rayuwar masu aikin agajin cikin haɗari.

    Har yanzu ba a ji ɗuriyar mutum 121 ba da rufatawar ginin ta ritsa da su a makon da ya gabata.

    Mutum 24 aka tabbatar da mutuwarsu kawo yanzu.

  11. El-Rufai ya sake yin rusau a Kaduna

    Mazauna unguwar Malali sun wayi garin Lahadi cikin ɓaraguzan rukunin gidaje da ke Malali Low-Cost sakamakon rusau da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi.

    Bayanan da BBC Hausa ta tattara sun nuna cewa da misalin ƙarfe 11:30 na daren Asabar ne jami'an tsaro suka isa unguwar da ke ƙwaryar birnin Kaduna, inda suka fara rushe gine-ginen.

    Wani mazaunin unguwar mai suna Titus Katuka ya ce tun shekarar 1976 suke haya a gidajen waɗanda mallakar gwamnatin jihar ne amma a 2017 gwamnatin Nasir El-Rufai ta ce za ta sayar musu da su.

    Ya ce lokaci guda kuma gwamnatin ta ce za ta rushe su domin gina kasuwa a wurin bayan ta mayar wa da waɗanda suka fara biya kuɗaɗensu, abin da ya sa suka kai ƙara kotu.

    "Ni ba a zo kan layinmu ba amma ban sani ba gobe ko jibi za su iya ƙarasowa," in ji shi.

    An gina rukunin gidajen na Malali Low-Cost ne domin masu ƙaramin ƙarfi.

    Rushe-rushen na daren jiya Asabar sun shafi rukunin gidaje ne da ke kan layukan Gambia da Siera Leon na unguwar.

    Kazalika mutanen sun ce jami'an tsaro sun harba musu hayaƙi mai sa hawaye kafin fara aikin rusau ɗin.

    Wasu hotuna da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna ɓaraguzan gidajen da aka rusa.

    A 'yan shekarun nan gwamnatin Kaduna ƙarƙashin jagorancin Nasir El-Rufai na rusa wurare da ta ce an gina su ba bisa ƙa'ida ba, ciki har daa kasuwanni.

  12. Mutum 29 ne suka mutu a hatsarin jirgin soja a Philippines

    Wani jirgin soja na dakon kaya da ke ɗauke da mutum 92 ya yi hatsari a kudancin Philippines, inda ya kashe mutum 29.

    Mutum 50 sun jikkata sannan ba a ga 17 ba, a cewar sojoji. Sauran waɗanda suka tsira an kai su wani asibitin sojoji da ke kusa.

    Jirgin mai suna C130 Hercules wanda mafi yawan fasinjansa sojoji ne, na yunƙurin sauka a filin jirgi na Jolo lokacin da ya zarce titinsa, a cewar Sakataren Tsaro, Delfin Lorenzana.

    An ga wuta da hayaƙi na tashi daga ɓaraguzan jirgin.

    Kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya wallafa hotunan hatsarin da ke nuna jirgin na ci da wuta a wani gwalalo da ke kusa da gidajen mutane.

  13. 'Yan fashi sun kashe mutum bakwai a Jihar Kaduna

    'Yan bindiga da ake zargin 'yan fashin daji ne sun kashe aƙalla mutum bakawai a yankunan Jihar Kaduna.

    Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa ranar Asabar, inda ya ce jami'an tsaro ne suka shaida wa gwamnati faruwar lamarin.

    A cewarsa, 'yan fashi sun harbe mutum huɗu a wajen garin Tsohon Gayan da ke Ƙaramar Hukumar Chikun.

    Kazalika, an kashe wasu mutum biyu da aka bayyana da suna Solomon Bamaiyi da Francis Moses a Kakau, sannan aka kashe wani da ba a bayyana sunansa ba a Kachia.

    Ya ƙara da cewa wani mai suna Danjuma Alhaji mazaunin Tsohon Farakwai na Ƙaramar Hukumar Igabi ya rasa ransa a hannun 'yan fashin a garin Galadima na Ƙaramar Hukumar Giwa.

  14. Cirani a Nijar: Kotun hukunta ma'auratan da suka aikata baɗala

    A cikin shirinmu na musamman kan ciranin mutanen Tahoua na jamhuriyyar Nijar, AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya ziyarci kotun da ke yin sasanci da hukunta mazajen da suka yi lalata da matan aure.

    Yawan tafiye-tafiyen don neman kuɗi kan sa maza su bar matansu tsawon lokaci, abin da ke jawo wasu yin amfani da wannan damar domin aikata kwartanci.

    Shirin na zuwa muku ne a madadin filin Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu.

  15. Za mu haɗa gwiwa da Najeriya don fatattakar masu iƙirarin jihadi - Bazoum

    Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar ya sha alwashin "fatattakar" masu iƙirarin jihadi da ke kai hare-hare a kudancin ƙasar da ke kusa da Najeriya.

    Shugaban na magana ne a kwana na uku na ziyarar musamman da ya kai yankin, wanda 'yan bindiga suka matsa wa da hare-hare tun 2015.

    Ya bayyana wani ƙauye da ya ce cike yake da 'yan bindigar, yayin da Boko Haram ke katse hanyoyin shiga garin.

    "Za mu bayar da umarnin kakkaɓe 'yan bindiga daga waɗannan ƙauyuka," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa aikin haɗin gwiwa da Najeriya zai fatattaki 'yan bindigar da ke kai hare-hare a ɓangare biyu na kan iyakar ƙasashen biyu.

    Ƙungiyoyin Boko Haram da Islamic State (IS) da masu alaƙa da Al-Qaeda na kawo wa ƙasashen Afirka da yawa barazanar tsaro, abin da ke jawo zanga-zanga daga mazauna yankunan saboda gazawar gwamnatocinsu.

  16. Hatsarin jirgin soja ya ritsa da mutum 92 a Philippines

    Wani jirgin soja na dakon kaya da ke ɗauke da mutum 92 ya yi hatsari a kudancin Philippines.

    An ga gawa 17 a wurin da hatsarin ya faru ranar Lahadi da ke Tsibirin Jolo, amma mutum 40 sun tsira kuma an kai su wani asibitin sojoji da ke kusa.

    Jirgin mai suna C130 Hercules wanda mafi yawan fasinjansa sojoji ne, na yunƙurin sauka a filin jirgi na Jolo lokacin da ya zarce titinsa, a cewar Sakataren Tsaro, Delfin Lorenzana.

    An ga wuta da hayaƙi na tashi daga ɓaraguzan jirgin.

    Kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya wallafa hotunan hatsarin da ke nuna jirgin na ci da wuta a wani gwalalo da ke kusa da gidajen mutane.

  17. Wutar daji ta kashe mutum biyu a Canada

    Wutar daji na ci gaba da ruruwa a Lardin British Columbia na ƙasar Canada.

    Yanayin zafi da kuma walkiya sun haifar da bazuwar wutar dajin a sassan yammacin kasar.

    Wakilin BBC ya ce tuni aka bai wa mutane umarnin ficewa daga wajen sannan gwamnati na tura kayayyakin agaji har da jiragen sojoji domin taimaka wa masu aikin ceton.

    A gefe guda kuma, an bayar da rahoton mutuwar mutum biyu a Lytton, ƙauyen da wutar dajin ta ƙone ƙurmus inda matakin zafi ya kai 49.6C - mafi tsanani a tarihin ƙasar.

  18. Ƙarin mutum 71 sun kamu da korona a Najeriya

    Ƙarin mutum 71 ne suka kamu da cutar korona ranar Asabar a Najeriya, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a ƙasar.

    Mutanen sun fito ne daga jiha huɗu. Sai dai babu wanda ya rasa ransa sakamakon cutar.

    Jihohin su ne: Legas - (63), Oyo (4O), Ogun (3), Kano (11).

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 167,803 aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Najeriya. Haka nan, cutar ta yi ajalin mutum 2,121, sai kuma 164,378 da aka sallama bayan sun warke.

  19. Maraba

    Umar Mikail ke mana barka da hantsin Lahadi.

    Ku biyo mu domin samun rahotanni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman ma a Najeriya da Nijar da maƙotansu.