Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wani mutum ya yi tsalle daga cikin jirgin sama a Amurka
Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran kasashen duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau
Malaman addini masu lasisi ne kawai za su dinga wa’azi a Masallatan Masar
Wata kotu a Masar ta sake tabbatar da hukuncin da ke cewa masu wa’azin da ke da lasisi ne kawai za su iya yin wa’azi ko jawabi ga masu ibada a Masallatan kasar.
Yayin da ta ke yin watsi da ɗaukaka ƙarar da aka yi, Kotun ƙolin ta kuma ƙara tabbatar da cewa cibiyoyin addini na jihohi ne kaɗai ke da izinin gabatar da fatawa ko wani ra'ayoyi na addinin Islama.
Wata sanarwa a hukumance ta ce an yanke hukuncin ne da nufin daƙile masu tunanin tsattsauran ra'ayi.
Sanarwar ta ce ana amfani da Masallatai don sauya tunanin mutane da haifar da rarrabuwar kai.
Shugaban Masar, Abdul Fattah al-Sisi ya sha yin kira da a sake fasalin batutuwan da suka shafi tattaunawar addini domin yaƙi da ta'addanci.
Ministan lafiya na Birtaniya ya yi murabus bayan saɓa dokar korona
Sakataren kula da harakokin kiwon lafiya na Birtaniya Matt Hancock ya yi murabus saboda saɓa ka'idojin gwamnati na korona bayan ya sumbaci sabuwar mataimakiyarsa da ya ɗauka aiki.
Hotunan yadda Mista Hancock ya rungume ma’aikaciyar kuma matar aure Gina Coladangelo, ya ja hankali a shafukan sada zumunta tare da haifar da fushin jama'a.
Ita ma dai ta yi murabus.
A cikin takardar murabus dinsa, Mista Hancock ya ce dole ne ya kasance mai gaskiya kan saɓa ka'idojin.
Firaministan Birtaniya, Boris Johnson, wanda da farko ya goyi bayan ya ci gaba da aikinsa, ya ce ya kamata ya yi alfahari sosai da nasarorin da ya samu.
Shugaban jam’iyyar adawa ta Labour Sir Keir Starmer ya ce tun tuni ya kamata Mista Johnson ya tuɓe shi.
Wani mutum ya yi tsalle daga cikin jirgin sama a Amurka
Wani mutum ya yi tsalle daga cikin jirgin sama da ke tafiya a filin jirgin sama na Los Angeles bayan da ya yi koƙarin shiga ɗakin matukin jirgin.
Mutumin wanda ba a bayyana ba, ya buɗe ƙofar jirgin ya fice a ranar Juma’a, kamar yadda hukumomin sufurin jiragen sama suka bayyana.
An tsare shi sannan aka tafi da shi asibiti bayan ya samu rauni.
An sha samun irin wannan matsalar a jiragen Amurka, kusan sau 3,000 a wannan shekarar.
Al’amarin na ranar Juma’a ya faru ne misalin ƙarfe 7 na yamma a SkyWest da ke kan hanyar zuwa Salt Lake City.
Yadda mutane ke gudun kullen korona a Bangladesh
Mutane da dama ne ke yin tururuwa zuwa tashoshin jiragen ruwa a Dhaka, babban birnin Bangladesh, yayin da dubban mutane ke ƙaƙarin tserewa kada kullen korona da zai fara aiki ranar Litinin ya rutsa da su.
Mutane da yawa sun koma hayar motoci suna tafiya saboda an riga an dakatar da hanyoyin sufuri na gwamnati masu jigilar jama'a.
Jami'ai sun ce jami'an tsaro za su tilasta aiwatar da matakan dokar kullen.
Za a dakatar da harakokin kasuwanci sannan mutane za su kasance a gidajensu, sai dai idan wata matsalar gaggawa ce.
An samu ƙaruwar yawan masu korona a Bangladesh tun daga tsakiyar watan Mayu, yawancinsu sun kamu ne da nau’in cutar da ake kira Delta.
Sojojin Nijar da Burkina Faso sun ce sun kashe ƴan bindiga sama da 100
Jami'an soji a Burkina Faso da Nijar sun ce an kashe ƴan bindiga da dama masu da’awar jihari a wani samamen haɗin gwiwa da aka ƙaddamar a iyakokin ƙasashen biyu.
Kamfanin dillacin labaran AFP ya ruwaito wata sanarwa da ta ce an kashe mayaƙa kusan 100 a farmakin na mako biyu da ya ƙunshi ɗaruruwan sojoji.
Rahotannin sun ce an kwace makamai, da bama-bamai da aka kera a gida da kuma babura sama da 100.
Mayakan masu da’awar jihadi da ke addabar ƙauyukan ƙasashen biyu da na Mali - galibi suna amfani da babura ne yayin kai hare-hare.
A farkon watan Yuni sama da mutane 170 aka kashe a wasu kauyuka biyu da ke arewa maso gabashin Burkina Faso - hari mafi muni a cikin shekaru.
Gwamnati ta zargi masu da’awar jihadi - wasu daga cikinsu ta ce yara ne ƴan shekara 12.
Amurka za ta ci gaba da tallafa wa Afghanistan - Joe Biden
Shugaba Joe Biden ya sake bai wa takwaransa na Afghanistan Ashraf Ghani tabbacin ci gaba da samun goyon bayan Amurka.
Bayan wani taro a fadar White House, Shugaba Biden ya ce mai yiwuwa a janye dakarun Amurka amma kuma Afghanistan din za ta ci gaba da samun tallafi ta bangaren sojoji da kudi da siyasa.
Shugaba Ghani ya ce ya mutunta matakin Amurka na janye dakarunta.
A cewar wakiliyar BBC, Shugaba Ghani ya kira janye sojojin na Amurka a matsayin wani sabon babi na alakarsu sannan ya yi watsi da zarge-zargen cewa Amurka za ta fice daga Afghanistan.
Zamantakewa: Matakan gyara zaman aure
Zamantakewa wani sabon shiri ne na BBC Hausa da zai dinga lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashi na farko, shirin ya fara ne da zamantakewar aure da yadda za a kyautata ta.
Za mu ci gaba da kai wa matatun fetur na Najeriya hari – Tsagerun Neja-Delta
Ƙungiyar tsageru ta yankin Neja-Delta a kudancin Najeriya mai suna Niger Delta Avengers ta yi barazanar ci gaba da kai hare-hare a kan matatun man fetur na ƙasar da kuma 'yan siyasar yankin da ke "haɗa kai da gwamnati".
Wata sanarwa da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na intanet ta ce gwamnatin Najeriya ta "ta sha yin buris da buƙatunta".
Ƙungiyar ta taƙaita ayyukan haƙar mai a Najeriya a 2016 sakamakon hare-hare da ta dinga kaiwa, ciki har da wanda ta kai kan wani bututun mai na ƙarƙashin ruwa.
Tun daga lokacin ne kuma ta dinga yin barazanar kai hari amma ba ta yi hakan ba tun 2017, a cewar kamfanin labarai na Reuters.
"Gwamnatin Najeriya ta sha yin buris da buƙatunmu da kuma halin da ƙasar ke ciki," a cewar sanarwar. "Duk bututun da muka tsara kai masa hari ba za mu ƙyale ba sai mun lalata."
Barazanar tasu na zuwa ne yayin da majalisar tarayya ke muhawara kan kasafin kuɗin da ya kamata a dinga bai wa yankunan da ake haƙo man da zummar yi wa dokokin man fetur ɗin ƙasar babbar kwaskwarima.
Al'ummomin yankunan na son a dinga ba su kashi 10 cikin 100 na kuɗin man da aka haƙo mai maimakon 2.5 da ake ba su a yanzu.
Abin da na fi jin daɗi shi ne taimaka wa 'yan gudun hijira - Gwamna Zulum
Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zullum ya shahara a Najeriya sakamakon salon mulkinsa, musamman ma yadda yake yin kasada wajen shiga yankunan jihar da ke fama da rikicin Boko Haram.
Kuma irin wannan jagorancin nasa ya sama masa tagomashi a ciki da wajen jiharsa, har wasu na ganin cewa ya kai a fafata da shi a siyasar ƙasa baki ɗaya.
A filinmu na Gane Mani Hanya, Ibrahim Isa ya tattauna da shi a kan ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban jihar Borno da kuma irin burin da yake da shi a harkar siyasa a Najeriya.
Da sanin gwamnati nake shiga daji, babu wanda ya kama ni – Sheikh Gumi
Malamin Musuluncin nan na Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi ya musanta rahotannin da ke cewa hukumar tsaro ta DSS ta gayyata ko ta kama shi domin amsa wasu tambayoyi game da alaƙarsa da 'yan fashin daji.
Shehin malamin ya faɗa wa BBC Hausa cewa "da ma muna da alaƙa" a lokacin da aka tambaye shi ko da gaske ya amsa gayyatar jami'an tsaron.
"Babu wanda ya gayyace ni", in ji shi. Sai dai tun farko mai magana da yawun DSS, Peter Afunaya, ya faɗa wa Channels TV cewa "mun gayyaci malamin domin amsa tambayoyi".
Da yake magana da Channels, Sheikh Gumi ya ce: "Tun sanda na fara shiga daji, ina shiga ne da jami'an tsaro; tare da sanin 'yan sanda da DSS da sarakunan gargajiya da shugabannin Fulani. Ban taɓa shiga ni kaɗi ba."
Kazalika malamin wanda ya sha nema wa 'yan fashin daji afuwa, ya jaddada cewa bai taɓa zargin rundunar sojan Najeriya ba baki ɗayanta da taimaka wa 'yan bindigar da suka addabi jihohin arewa.
Haka nan, an san malamin da shiga dazukan da ke arewacin Najeriya domin yin abin da ya kira wa'azi da faɗakar da 'yan fashin da ke kashe mutane kusan kullum da kuma kama wasu domin karɓar kuɗin fansa.
Sojojin Najeriya sun 'kashe' 'yan fashi masu yawa a Zamfara
Dakarun sojan Najeriya sun kashe 'yan fashi "masu yawa" a Ƙaramar Hukumar Talata Marafa ta Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.
Wata sanarwa daga kakakin rundunar, Onyema Nwachuku, ta ce dakarun sun yi arangama ne da 'yan bindigar a yankunan Mayanchi da Dogo Karfe da Fagantama, inda suka yi nasarar kashe da yawa daga cikinsu sannan suka ƙwace bindiga ɗaya da harsasai masu yawa.
A wata fafatawar daban, sojojin sun kashe 'yan fashi biyar a ƙauyen Bingi na Ƙaramar Hukumar Bungudu ta Zamfarar tare da jikkata wasu da dama.
Kazalika, sojojin sun ƙwace bindigar AK-47 ɗaya da babur ɗaya da wayoyin salula uku.
Da safiyar Juma'a ne mazauna Bingi da kewaye suka toshe hanyar shiga garin Gusau daga Sokoto don nuna fushinsu game da hare-haren 'yan bindigar, suna masu cewa sojojin da ke gadin ƙauyukan nasu sun fice daga garin.
Sai dai wani mazaunin yankin ya faɗa wa BBC a safiyar Asabar cewa mutanen, waɗanda akasarinsu mata ne da yara, sun koma garuruwansu bayan jami'an tsaron sun koma.
Masu iƙirarin jihadi sun kashe sojan Mali shida
An sake kai hare-hare a Mali inda rikicin masu ikirarin Jihadi ya halaka dubban sojoji da farar hula.
An kashe sojojin Mali shida a wani samame da aka kai jiya Juma'a kan wani sansanin soji da ke Boni a tsakiyar ƙasar.
Sannan an raunata sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya 13 - Jamusawa 12, ɗaya kuma ɗan Belgium a wani harin bam da aka kai.
An kai harin kan sansanin soji na wucin gadi da ke kusa da kauyen Ichagara a yankin Gao.
A watan Yuni na 2020, 'yan bindiga sun kashe sojoji kusan 24 a wani harin kwanton-ɓauna da suka kai musu shi ma a tsakiyar ƙasar.
'Yan fashi sun sace mataimakin shugaban ƙaramar hukuma a Kaduna
'Yan fashin daji sun yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Jaba da ke Jihar Kaduna a Najeriya, James Bijimi, da kuma wasu da ba a san adadinsu ba.
Kafar talabijin ta Channels ta ruwaito kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Mohammed Jalige, yana tabbatar da faruwar lamarin ba tare da yin cikakken bayani ba.
Lamarin na faruwa ne kwana biyu bayan wasu 'yan bindiga sun kashe wani direba kuma suka yi garkuwa da mutum 33 a Kachia da ke jihar.
Jalige ya ce jami'an tsaro sun ƙwace abin hawa guda uku mallakar 'yan fashin tare da raunata mutum ɗaya.
Sai dai wani dattijon yankin ya faɗa wa Channels cewa 'yan fashin sun tare hanyar da ta haɗa Gonan Roger da Makyali a Ƙaramar Hukumar Kajuru da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar Juma'a, inda suka ɗauke mutanen ciki har da mataimakin shugaban ƙaramar hukumar.
Mista Jalige ya ƙara da cewa jami'ansu sun yi azamar far wa 'yan bindigar, inda suka ceto mata shida da aka yi garkuwa da su.
Iran ta yi watsi da buƙatar hukumar da ke sa ido kan nukiliyarta
Iran ta yi fatali da buƙatar hukumar IAEA mai binciken ayyukanta na nukiliya bayan hukumar ta nemi ta tsawaita yarjejeniyar da wa'adinta ya ƙare game da sa ido kan cibiyoyin nukiliyar kasar.
Shugaban IAEA, Rafeal Grossi, ya ce yana da matukar mahimmanci idan masu bincike suka ci gaba da samun damar tattara bayanai.
Amurka ta ce abu ne muhimmi hukumar ta ci gaba da tabbatar da cewa Iran na cika alkawuran da ta ɗauka game da shirinta na nukiliya.
Amma jakadan Iran a hukumar ya ce ba a bukatar kasarsa ta amince da bukatar IAEA.
Ra'ayi Riga: Yadda kuke fuskantar daminar bana
Shirin Ra'ayi Riga na wannan makon da ke zuwa muku ta rediyo duk Juma'a, ya tattauna kan yadda kuke fuskantar daminar bana bayan shafe watanni a cikinta ba tare da ruwa mai yawa ba.
Korona a Najeriya: Mutum 29 sun kamu, ta kashe mutum ɗaya
Mutum 29 sun kamu da cutar korona a Najeriya ranar Juma'a, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a ƙasar.
Kazalika an samu mutum ɗaya da cutar ta yi ajalinsa, karon farko kenan cikin fiye da mako biyu.
Alƙaluman da hukumar ta wallafa sun nuna cewa daga jihohi bakwai ne har da Abuja aka samu sabbin kamuwar.
Jihoihin su ne: Legas (16), Rivers (3), Kaduna (3), Kwara (2), Delta (2), Ondo (2), Ogun (1).
NCDC ta ce ya zuwa yanzu mutum 167,430 ne aka tabbatar sun kamu da cutar sannan ta kashe 2,119. Kazalika, an sallami mutum 163,937 bayan sun warke.
Annobar korona ta ɓulla Najeriya ne a watan Fabarirun 2020, wata uku kenan bayan da aka gano ta a ƙasar China.
Mahara sun buɗe wa jirgin shugaban Colombia wuta
An buɗe wa jirgin helikwafta wuta da ke ɗauke da shugaban ƙasar Colombia yayin da yake tafiya a kusa da iyakar ƙasar da Venezuela.
Shugaba Iván Duque na tafiya ne zuwa Cúcuta da ke yankin Norte de Santander tare da ministocin tsaro da na harkokin cikin gida da kuma gwamnan yankin.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa ya ce babu wanda ya ji rauni a harin.
Mista Duque ya yi Allah-wadai da harin wanda ya kira "na matsorata" kuma ya ce "tashin hankali ko ta'addanci" ba za su tsorata shi ba.
Gafaranku dai
Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a wannan hantsi na Asabar tare da Umar Mikail.
Ku biyo ni domin samun rahotannin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.
Mu je zuwa!