Sai da safenku
Ƙarshen rahotannin kenan. Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu.
Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin kenan. Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu.
Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.
Hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta amince ta gudanar bincike kan rikicin da ya faru tsakanin Israila da kungiyar Hamas ta Falasɗinu a watan da muke ciki.
Kasashe 24 daga cikin 47 sun kaɗa ƙuriar amincewa da ƙudurin da kungiyar haɗin kan ƙasashe Musulmi da wakilan Falasdinu a MDD suka gabatar.
Kungiyar Hamas da ke da iko da zirin Gaza ta yi maraba da matakin.
Sai dai a ɗaya ɓangaren, Israila ta bayyana yunƙurin a matsayin rashin sanin ya kamata kuma ta ce ba za ta bayar da haɗin kai ga binciken ba.
Ita ma Amurka ta nuna takaici a kan binciken.
Ɗalibar jami'ar kimiyya da fasaha ta Jihar Kano (KUST Wudil) wadda wasu ɗalibai maza suka tsangwama saboda ta saka Abaya ta faɗa wa BBC cewa ta yi "kuka" saboda abin da aka yi mata.
Ɗalibar wadda aka gani a wani bidiyo maza na yi mata ihu a cikin jami'a, ta ce ta ji daɗi da matakin da hukumar makarantar ta ɗauka a kan waɗanda ake zargi.
"Ban san abin zai faru ba saboda da ma ni ba na saka kaya waɗanda iyayena ba sa so. Ko da zan fito ma sai da mahaifina ya ce na yi kyau," in ji ɗalibar wadda muka ɓoye sunanta saboda dalilai na tsaro.
A karon farko, Shugaban Angola Joao Lorenzo ya nemi gafara a madadin gwamnati game da kisan dubban mutane yayin rikicin siyasa shekara 44 da suka gabata.
Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam sun ce kimanin mutum 90,000 sojojin Angola da na Cuba suka yi wa kisan gilla bayan da aka samu rarabuwar kawuna a jamiyyar MPLA mai mulki.
Wakiliyar BBC ta ce a jawabin da ya yi wa al'ummar kasar, Mista Lourenzo ya bayyana kashe-kashen a matsayin mugun abu kuma ya nemi afuwa a madadin gwamnati.
Ya kuma ce gwamnati za ta fara aiwatar da tsarin nema da kuma tono gawarwakin wadanda aka kashe domin mika su ga iyalansu.
Kungiyiyi na likitoci a Japan sun jagorancin kiraye-kiryen sake duba yiwuwar gudanar da wasannin motsa jiki na olympics ya yinda ake cigaba da samun karuwa a yawan masu kamuwa da cutar.
Shugaban wata kungiyar likitoci da ke Tokyo ya ce za a samu koma-baya idan dubban mutane daga kasashen waje suka isa kasar idan ba a samu raguwa a yawan masu harbuwa da cutar ba.
Wakilin BBC ya ce ba a samu raguwa a yawan masu kamuwa da cutar a birnin Tokyo ba duk da cewa an sanya dokar ta-ɓaci.
Likitocin sun yi gargadin cewa idan aka gudanar da wasannin Olympics din to zai iya jawo a samu ɓullar sabon na'uin cutar ta korona.
Ya yin da aka shiga rana ta biyu na aikin neman waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a jihar Kebbi, ya zuwa yanzu an gano gawar mutum 60.
A jiya Laraba ne jirgin ya rabe gida biyu ɗauke da fasinjoji fiye da 100, lamarin da ya yi sanadiyar nutsewarsa.
Kawo yanzu mutum 22 ne hukumomin jihar suka ce sun tsira da rayukansu.
Sai dai mutum fiye 100 ne suka rasu a hatsarin, yayin da har yanzu ba a san inda fiye da 50 suke ba.
A Najeriya, a yau ne `yan Majalisar Dattawan ƙasar suka kammala sauraron ra`ayin jama`a game da gyaran fuskar da suke so a yi wa kundin tsarin mulkin kasar.
An yi zaman ne a shiyyoyi shida na kasar kuma ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da dama sun gabatar da bukatunsu.
Birnin Kaduna na cikin wurare 12 da tawagar `yan majalisar suka yi zama don tattara ra`ayoyin `yan kasar, kuma a nan ne wakilai daga jihohin Kaduna da Kano da Jigawa da kuma Katsina suka gabatar da nasu bukatun.
Mafi yawan bukatun dai sun karkata ne ga batun saka wa ƙananan hukumomi da ɓangaren shari`a mara.
Sai kuma masu bukatar a kirkiri sabbin jihohi da maganar samar da daidaito da inganta rayuwar mata.
Kowa da abin da ya dame shi! Saboda haka kunshin ra`a`yoyin tamkar hatsin bara ne.
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya kai wa takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari ziyara a Abuja yau Alhamis.
Mista Akufo-Addo ne shugaba na uku Buhari ke karɓar baƙunci a makon nan, wanda ya isa tare da shugaban ƙungiyar haɓaka tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS).
Shugabannin Libya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ne suka fara kai masa ziyara a farkon mako domin tattauna alaƙa tsakanin ƙasashen nasu.
Aƙalla soja biyu ne suka rasa rayukansu a yankin Arewa Maso Yammacin Kamaru, a cewar hukumomi.
Sojojin suna kan hanyarsu ce ta zuwa Nkambe daga Ako a lokacin da wani bam da aka haɗa a gida ya tashi da su a gefen titi kusa da ƙauyen Jeyu.
Harin ya zo ne kwana ɗaya bayan wani bam a yankin ya kashe soja biyar a garin Lassin.
A cewar alƙaluman Majalisar Ɗinkin Duniya, an kashe aƙalla mutum 3,500 tun bayan ɓallewar rikicin 'yan tawaye a yankin rainon Ingila a shekarar 2017.
Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana kiwon sake a matsayin "abin da ya saɓa wa Musulunci", yana mai goyon bayan haramta shi da gwamnonin kudancin ƙasar suka yi.
Gwamnan wanda ya tattauna da manema labarai ranar Talata, ya jaddada buƙatar samar da hanyoyin kiwo na zamani domin hana makiyaya fita yawon kiwo da dabbobinsu.
"Me ke sa makiyayan daga Kastina yawo? Abu biyu ne: ruwa da abincin dabbobi," a cewar gwamnan, kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka ambato shi. "Idan muka samar da su me zai sa su yi yawo?
"Wannan yawon ba Musulunci ba ne kuma ba shi ne ya dace ba. Yana cikin matsalolin da muke fuskanta a yanzu. Ba na goyon bayan mu ci gaba da tsarin kiwon sake.
Kazalika, Gwamna Masari ya ce yana goyon bayan a sake fasalin ƙasa ta yadda za a ƙara wa jihohi ƙarfin iko.
A ranar 11 ga watan Mayu ne gwamnonin jihohin kudancin Najeriya suka haramta kiwon sake a yankin a yunƙurinsu na magance matsalar tsaro da suka ce salon kiwon na haifarwa.
Sai dai Ministan Shari'a Abubakar Malami ya ce haramcin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya nemi Rwanda ta yi wa Faransa afuwa kan rawar da ta taka a yayin kisan kiyashin da aka yi a ƙasar da ya yi sanadin mutuwar mutum 800,000.
Ya bayyana hakan ne yayin wani bikin tunawa da mutanen a Kigali, babban birnin Rwanda, yana mai cea Faransa ba ta kula da gargaɗin da aka yi mata ba sannan ta yi shuru game da batun ba tare da ta binciki gaskiyar lamarin ba.
"Amma Faransa ba ta shiga cikin kashe-kashen ba," in ji shi.
Shugaba Paul Kagame ya yabi jawabin Macron.
Kungiyar Tottenham ta tuntubi tsohon kocinta, Mauricio Pochettino kan idan zai sake komawa aiki a karo na biyu.
An kori kocin mai shekara 49 daga Tottenham cikin Nuwambar 2019, bayan shekara biyar da ya ja ragamar kungiyar.
Pochettino dan kasar Argentina ya karbi aikin horar da Paris St Germain a watan Janairun 2021.
Sai dai kuma PSG ta kasa cin Ligue 1 a bana kuma karo na biyu a kaka tara kenan, ta kuma yi rashin nasara a hannun Manchester City a Champions League a wasan daf da karshe.
A watan jiya ne Tottenham ta kori Jose Mourinho, wanda ya maye gurbin Pochettino a kungiyar.
Tanzania ta ce ba za ta aika da dakarunta ba zuwa Mozambique domin tunkarar 'yan bindiga da ke yankin Cabp Deldago ba mai arzikin mai da ke iyakar kasashen biyu. in ji jaridar Citizen.
Maimakon haka, gwamnatin kasar ta ce tattaunawa ce za ta kawo zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, tare da kira ga kasashen duniya su taimaka wajen sake gina kasar.
A cewar jaridar Ministan harkokin wajen Tanzania Liberata Mulamula ne ya bayyana hakan a wani taro na mako biyu kan yadda za a shawo kan matsalar masu ikirarin jihadi a Mozambique, wanda yake gudana a Dar es Salam.
Kwamitin da aka kafa ya bayar da shawara kan cewa kamata ya yi a ajiye sojoji 3,000 da na sama domin taimaka wa a yaki da 'yan bindiga.
Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta ce kusan mutum 7,000 ne hare-haren ƴan bindiga ya shafa a ƙananan hukumomin Sabon Birni da Isa a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A wani aikin hadin gwiwa tsakanin NEMA da hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Sokoto SEMA, kimanin mutum 6,200 da hare-haren suka shafa yanzu suna zaune a sansanonin da ke makarantar Firaimari a Sabon Birni da kuma garin dan Isa da ke Jihar, da kuma garin shinkafi na Zamfara da ke makwantaka.
Shugaban NEMA a Jihar Alhaji Aliyu Shehu Kafindangi, wanda ya jagoranci aiki a madadin babban daraktan hukumar AVM. Muhammed Muhammed, ya jajenta wa mutane da abin ya shafa tare da yin alkarin za a taimaka musu.
Mutane da yawa a Sabon Birni da Isa sun yi ta fama da hare-haren 'yan bindiga, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama wasu kuma suka jikkata yayin da aka rasa dukiya mai yawa, ciki har da gidaje da gonaki.
Saboda tsaron da aka kara a wurin tawagar NEMA ba za ta iya shiga yankin ba kai tsaye.
Kafindangi ya nuna farin cikinsa kan yadda aka kai jami'an tsaro wurin cikin gaggaywa, musamman sojoji da 'yan sanda da suka taimaka aka yi wannan aiki tare da hadin gwiwar mutanen da abun ya shafa.
Hukumomi a birnin Goma na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun umarci mutane da su fice daga wasu bangarorin birnin sakamakon aman wutar da dutse ya yi a karshen makon da ya gabata.
Dutsen Nyiragongo na gabashin kasar na daga cikin duwatsu masu yawan aman wuta a fadin duniya-kuma akwai fargabar cewa aman wutar da yayi a ranar Assabar abin da ya kashe a’kalla mutum talatin da daya-ba zai zama na karshe ba.
Shugaban sojin da suka yi juyin mulki a Mali Kanar Assimi Goïta, ya nada kansa a matsayin shugaban kasar da zai jagoranci mika mulki ga fararen hula, bayan hambarar da shugaban rikon kwaryar da Firaministansa daga kan mulki.
An saki shugaba Bah Ndaw da Firaministansa Moctar Ouane daga inda soji suke tsare da su.
An kai su wani sansanin soji ne a ranar Litinin a wani abu da ake kallo a matsayin juyin mulki na biyu cikin wata guda a kasar ta Mali cikin wata tara.
Kanar Goita ya yi korafin cewa tsohon shugaban bai tuntube shi ba kan ya nada 'yan majalisarsa.
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ajiye aikinsa na horas da kungiyar a karo na biyu.
Real ta gaza cin ko wane irin kofi a wannan kakar ta bana, a La Liga kuma abokiyar hamayyarta da gari daya Atletico Madrid a ranar Asabar din da ta gabata.
Zidane mai shekara 48, ya lashe Champions sau uku a jere a lokaci na farko da yake tafiyar da kungiyar tsakanin shekarar 2016 da 2018.
Ya kuma koma kungiyar inda ya yi watanni 10 kuma ya kammala gasar La Liga a matsayi na biyu.
Tun shekarar 2009-10 rabon da ace Real ta gaza cin kofi ko daya a tarihi.
Kimanin dalibai 100 ne a kwalejin lafiya ta Jihar Ekiti aka kwantar da su a asibiti a ranar Laraba, biyo bayan feshin magananin wasu mutane da ake zaton daga hukumar kashe gobara suke, su ka yi a makarantar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, daliban wadanda warin maganin ya janyo suka rika faduwa wadanda dukansu mata ne, sun yi zanga-zanga kan wannan lamari.
An kuma ruwaito cewa sun lalata gine-gine da motoci a marantar.
Wata majiya daga makarantar ta shaida wa manema labarai cewa, "Menene ya kawo maganar feshin magani kan annobar korona lokacin da ake cikin karatu kuma dalibai kuma suke rubuta jarrabawa? warin maganin ya baibaiye ko ina ya sanya makarantar ta zama wata iri.
"Da yawa daga cikin daliban abin ya cutar da su."
Shugaba kasar Amurka Joe Biden ya nemi a tsagaita wuta sannan a kawo karshen cin zarafin bil adama a yankin Tigray na Habasha yayin da gwamnatinsa ke kara kaimi wajen ganin an kawo karshen rikicin.
Mista Biden ya ce dole ne dakaru daga Eritrea da jihar Amhara su janye daga yankin na Tigray sannan a ba da izinin kai kayan agaji wajen, domin magance matsalar yunwa.
Dubban mutane aka kashe wasu da dama suka rasa muhallansu tun bayan da rikicin ya barke wata shida da ya gabata.