Hukumomi a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun tabbar da jikkatar gwamman mutane a wata gobara da ta faru a wani gidan mai da ke Unguwar Sharada a Jihar.
Cikin wata tattaunawa da manema labarai kwamishin ayyuka na Jihar Alhaji Garba Idriss Unguwar Rimi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ya na cewalaifun na mahukuntan gidan man ne.
"Kowa ya sani doka ta haramta sauke mai da tsakar rana musamman a irin wannan yanayi da Kano ke ciki na matsanancin zafi, wanda kuma hakan ne ya yi sanadiyyar tashin wannan gobara.
"Wannan gobara ta rutsa da mutum 43 na gari, sai kuma jami'anmu 8 da suke je aikin kashe gobarar, wadanda bayan an kashe ta farko wani ma'aikacin gidan man ya bude wani tanki gobara ta biyu ta kara ta shi ta rutsa da su," in ji Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano.
Sai dai rahotanni na cewa adadin wadanda suka jikkatan ya zarce wanda hukumomin suka zayyana.
Da yake kan babbar hanya gidan man yake, lamarin ya rutsa da gwamman mutane da ke kan hanyarsu ta zuwa inda suka nufa, sai kuma 'yan kallo da suka ciki inda gobarar ta faru.