Rufewa
Masu bibbiyar mu a wannan shafin da haka muka kawo muku ƙarshen labarai kai tsaye daga wannan shafin sai kuma gobe Juma'a. A huta Lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran ƙasashen duniya.
Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin
Masu bibbiyar mu a wannan shafin da haka muka kawo muku ƙarshen labarai kai tsaye daga wannan shafin sai kuma gobe Juma'a. A huta Lafiya.
A Najeriya yayin da mahukunta ke laluben hanyoyin daƙile aika-aikar masu satar mutane don karbar kuɗin fansa, wata ƙungiyar ƴan-sa-kai mai suna NATFORCE ta ce jami`anta sun shirya za su yi aiki da jami`an tsaron ƙasar don magance wannan matsalar.
Shugabannin ƙungiyar sun ce an kafa ta fiye da shekaru goma da suka wuce kuma zaratanta na taimakawa wajen yaƙi da miyagu.
Sai dai ƙungiyar tana fuskanta ƙalubale, sakamakon rashin tattabatar da ita a hukumance.
Hukumar da ke kula da ingancin magunguna ta Tarayyar Turai ta yanke hukuncin cewa riga-kafin korona ta AstraZeneca na da inganci sosai kuma alfanunta ya fi haɗɗuranta yawa.
Hukumar ta gudanar da bincike bayan da ƙasashen Turai da yawa suka dakatar da amfani da allurar bisa fargabar tana janyo daskarewar jini.
Shugabar hukumar Emer Cooke ta ce riga-kafin ba ta da illa amma ya kamata a sanar da mutane ƴan haɗɗuran da ka iya tasowa.
Ta ce: "Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa muke bayyana abubuwan da muka gano a bincikenmu shi ne don mu wayar wa mutane da kai kan abubuwan da ka iya biyo bayan allurar.
"Idan ni ce, gobe ma zan je a yi min allurar. Amma ko zan yi zan so in sani idan akwai wasu matsaloli tattare da ita. Shi ya sa muka bayyana bincikenmu."
Hukumar ta ce allurar ba ta da wata alaƙa da daskarewar jini.
Rahotanni daga Libya sun ce an gano gawarwaki a ƙalla 15 da hannuwansu a ɗaure a Birnin Benghazi.
Jami'an tsaro sun yi ƙawanya a wurin da ke kusa da wani kamfanin siminti, yayin da suke gudanar da bincike.
Majalisar Dinkin Duniya da Ƙungiyiyoyin kare haƙƙin bil Adama sun yi Allah-wadai da kashe-kashe ba a bisa ƙa'ida ba tsawon shekaru.
Yankin da aka ga gawarwakin, yanki ne da ke hannun dakarun da ke wa Khalifa Haftar mubaya'a.
Gwamnati Najeriya ta ce shida daga cikin jiragen yaƙi 12 ƙirar Super Tucano da ta yi oda za su iso ƙasar a cikin watan Yulin 2021.
Kakakin fadar gwamnati, Garba Shehu, ya bada wannan tabbaci a wata sanarwa da ya fitar kan ranar isowar jiragen
Yanzu haka akwai matuƙan jirgi 14 daga Najeriya da ke karɓar horo a barikin sojojin sama na Georgia.
A watan Fabarairun 2018, gwamnatin Najeriya ta bada odar jiragen 12 kan kuɗi dala miliyan 496.
Hukumomi a Kamaru sun kafa wani kwamiti domin binciker sahihancin allurar riga-kafin annobar corona da ake shirin bayarwa a ƙasar.
Kafa kwamitin ya biyo bayan cece-kucen da ake ta yi game da rashin ingancin allurar riga-kafin AstraZeneca da aka ce tana da illa ga lafiyar dan Adam.
Da farko dai, an tsaida cewa a farkon makonnan ne za a shigo da kashi na farko na allurar daga nahiyar Turai inda rahotanni suka nuna cewa ta haddasa kisa akan wasu mutanen da suka ɗauketa.
Sojoji a Myanmar sun ce suna shirin shigar da ƙara kan Aung San Suu Kyi bisa laifin cin hanci da rashawa.
An fitar da sanarwar ne a tashar Talabijin ta ƙasar bayan watsa jawabin wani shaharraren ɗan kasuwa da ya bayyana cewa ya bai wa Aung San Suu Kyi cin hancin Dala dubu ɗari biyar da hamsin tun daga shekarar 2018.
Wannan na zuwa ne mako guda bayan rundunar sojin ƙasar ta yi mata wani zargi mai kama da wannan.
Misis Suu Kyi ta musanta zargin.
Manyan jami'an gwamnatin Afghanistan da ƴan Taliban na ganawa a Moscow babban birnin Rasha don tattaunawa kan shirin gaggauta samar da zaman lafiya a Afghanistan.
A lokacin da ya ke magana da BBC, tsohon shugaban Afghanistan Hamid Karzai ya yi maraba da taron.
Ya ce "Ana iya samun zaman lafiya ne kawai ta hanyar yin sulhu. Idan Taliban da gwamnati na so a kawo ƙarshen tashin hankali, hanyoyi biyu kawai za a iya bi.
Na farko shi ne Ƙungiyar Taliban ta shiga wannan gwamnati, idan ta ƙi amincewa lallai sai dai a miƙa mulki inda ɓangarorin biyu za su amince da tsari guda sannan a gyara kundin tsarin mulkin ƙasar."
Amma Shugaba Ashraf Ghani ya ce sai dai a miƙa mulki ga zaɓaɓɓiyar gwamnati.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya soki gwamnati kan ware dala biliyan ɗaya da rabi domin a gyara a matatan mai na Fatakwal.
A wasu sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku Abubakar ya bayyana matakin da "rashin tattalin kalilan kuɗin da ake dasu" ana fama da dimbin matsalolin tattalin arziki.
Sannan ya ce har yanzu ana kan karbo bashi wajen aiwatar da manyan ayyuka a ƙasar.
"Basusukan da ake bin Najeriya ya ƙaru daga naira tirliyan 12 a 2015 zuwa naira triliyan 32.9 a 2021."
Atiku ya bada misali na taɓarɓarewar tattalin arziki wanda sanin kowa ne a ciki da wajen ƙasar. Ya ce rashin aikinyi ya karu da kashi 33 cikin 100 ga kuma hauhawan firashin kayayyakin masarufi.
Atiku ya ce akwai fannoni da dama da ke bukatar a mayarda hankali wajen farfado da tattalin arziki da rage talauci ba aikin gyara matata ba.
Tsohon mataimakin dai yana ganin sayer da matatun man Najeriya zai fi kasancewa alheri da kawo wa ƙasar ci gaba cikin gaggawa
Hukumar kula da ƴan gudin hijira a Kamaru ta nuna fargaba game da bullar annobar korona a sansanonin ƴan gudun hijira.
Hukumar ta ce sama da mutane ɗari ɗaya sun kamu da annobar yanzu haka. Lamarin da a ganinta ya kamata a tashi tsaye domin shawo kan yaduwar kcutar.
Hukumar ta majalisar Dinkin duniya ta mika wa ma'aikatar kiwon lafiya tallafin wasu kayayyakin da ake bukata domin ba wa wadanda suka harbu da kwayar cutar dauki a asibitocin da ake basu kula.
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya taya gwamnati da al'ummar Tanzania aihini bisa rasuwar shugaba John Pombe Magufuli, mai shekara 61.
Buhari ya ce marigayin ya nuna sadaukarwa ga ƙasarsa da nahiyar Afirka baki ɗaya wanda za a jima ba a manta ba.
Daga cikin ayyukan ci gaba da marigayi ya kawo a cewar Buhari sun hada da rage girma da kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa, mayar da hankali kan kasafi da bai wa fanin ilimi da lafiya fifiko da yaƙi da rashawa.
Sannan shugaban ya aike da sakon ta'aziya zuwa ga iyalansa da abokai da makusanta, da al'umma baki ɗaya.
A yammacin ranar Laraba shugaba Magufuli ya mutu a asibitin Mzena da ke Dar es Salaam sakamakon ciwon zuciya.
Ya shafe fiye da shekara 10 yana fama da larurar.
Ƙungiyar likitoci ta ƙasa ta buƙaci mambobinta su shirya shiga yajin aikin gama gari daga ranar 31 ga watan Maris din 2021.
Jaridar The Punch ta rawaito cewa wannan shi ne karo na uku da likitocin ke shiga yajin aiki a cikin watanni 9 a ƙasar.
Ƙungiyar ita ce mafi girma cikin ƙungiyoyin ma'aikata lafiya, kuma mambobinta su suka kasance kan gaba wajen yaƙi da annobar korona.
Ko a watan Yuni da Satumba 2021 sai da suka shiga irin wannan yajin saboda matsalolin albashi da alawus-alawus da rashin walwala a fanin aiki.
Dukiyar Donald Trump ta ragu da kusan dala miliyan 700 a lokacin da yake kan shugabanci, inda yanzu ta koma biliyan $2.3 jumilla, a cewar jaridar Bloomberg mai bayyana jerin masu arzikin duniya.
Annobar korona ta tagayyara dukiyar tasa, yayin da gine-ginen tsohon shugaban da suka haɗa da otel-otel da wuraren shaƙatawa suka yi asarar kuɗin shiga kuma suka rage daraja.
Su ma jiragensa da filayen wasan golf sun gamu da faɗuwa a darajarsu.
Bloomberg ta bincika bayanai da sauran takardu tsakanin Mayun 2016 zuwa Janairun 2021 domin lissafa dukiyar Mista Trump kafin da kuma bayan ya zama shugaban ƙasa.
Yanzu haka yana fuskantar binciken shari'a a kan harkokinsa da kuma na danginsa.
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya halarci ta'aziyyar Sarkin Zulu Goodwill Zwelithini, wadda aka yi bayan binne sarkin mai shekara 71 a yau Alhamis.
"Wata gagarumar bishiya ta karye," in ji Ramaphosa. "Dattako ɗaya ne daga cikin ɗabi'unsa."
Mista Ramaphosa ya yi ta'aziyyar ce cikin wani farin tanti da aka tanada a wajen fadar sarkin a garin Nongoma da ke KwaZulu-Natal.
Fadar ta cika da hada-hada saboda masu makoki da ke tururuwa, a cewar wakilin BBC, Pumza Fihlani.
Da yawa sun kai kyautukan shanu, waɗanda za a yanka a raba wa mutanen gari.
Sarki Zwelithini - basaraken da ya fi daɗewa a Masarautar Zulu - ya mutu a makon da ya wuce sakamakon cutar suga.
Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano a arewacin Najeriya ta bayar da belin Mahadi Shehu, mai kwarmata bayanai game da zargin cin hanci da rashawa a Jihar Katsina.
Da yake yanke hukuncin a zaman kotun na yau Alhamis, Mai Shari'a Ambrose Alagoa ya sharɗanta belin kan kuɗi naira miliyan 10.
Sauran sharuɗɗan sun haɗa da kawo mutum ɗaya da zai tsaya masa wanda ya mallaki kadarar da ta kai darajar naira miliyan 10, sannan kuma dole ne kadarar ta kasance a Kano.
Sai dai kotun ta ce za a ci gaba da tsare shi har sai ya cika ƙa'idojin belin. An saka ranar 19 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraron ƙarar.
Gwamnatin Jihar Katsina ta gurfanar da Mahadi a kotu ne bisa zarginsa da ɓata mata suna da tunzura mutane bayan ya zargi gwamnatin da almubazzaranci da kuɗin da aka tanada don samar da tsaro.
Koriya ta Arewa ta kira yunkurin gwamnatin Amurka na tuntubarta a matsayin wata dabara ta cimma burinta.
Wata jami'a kan harkokin wajen Koriya ta Arewa, Choe Son Hui (We), ta ce Koriya ƙasarta ba za ta ce uffan ba har sai Amurkar ta yi watsi da manufofinta na adawa.
Kalaman na zuwa ne daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ke ziyara a Koriya ta Kudu tare da shugaban ma'aikatar tsaron Amurka, Lloyd Austin.
A cewar wakiliyar BBC, manyan jami'an gwamnatin Amurkar za su gana da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jaa In, yayin da gwamnatin Biden ke kokarin kawo karshen makaman nukiliyar Koriya ta Arewa.
Majalisar malaman Musulunci ta ƙasa a Najeriya, Nigeria Council of Ulama, ta yi kira ga Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya ɗage haramcin yin wa'azi kan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara tare da buɗe makaranta da masallacinsa.
Jaridar Vanguard ta ruwaito muƙaddashin shugaban majalisar, Sheikh Dan’azumi Tafawa Balewa, yana magana da manema labarai a garin Bauchi a yau Alhamis, inda ya ce majalisar ta damu da haramcin da aka yi wa malamin.
Ya ce bisa damar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowa na yin addinin da yake so da kuma adalci, ya kamata Ganduje ya ƙyale Abduljabbar ya ci gaba da wa'azi.
"Wannan 'yanci da kundin tsarin mulki ya bayar ya yi daidai da koyarwar Alƙur'ani mai tsarki a wajen da Allah ya ce 'Babu tilastawa a addini," in ji malamin.
"Muna girmama ra'ayoyin mutane mabambanta kuma burinmu shi ne mu yi tayin tattaunawa da fahimta tsakanin Musulmai masu mabambantan ra'ayoyi.
"Muna roƙon mai girma gwamna kuma ƙwararren ɗan siyasa wanda muke girmamawa da ya sake duba matakin kuma ya ɗabbaƙa koyarwar Alƙur'ani irin yadda Allah Ya umarci shugabanni irinsa su yi adalci ta hanyar bai wa kowa dama iri ɗaya."
A watan kwanakin baya ne Gwamna Ganduje ya hana Abduljabbar gudanar da wa'azi tare da yi masa ɗaurin talala a gidansa bayan an zarge shi da yin kalaman da za su iya tayar da fitina a cikin wa'azin nasa.
Wani kwamitin tuntuɓa da jam'iyyar adawa ta PDP ta kafa a Najeriya ya bayar da shawarar a duba cancanta maimakon bin tsarin karɓa-karɓa yayin tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 mai zuwa.
Mambobin kwamitin sun ce duk da cewa wasu na ganin ya kamata a fifita yankunan arewa maso gabas da kudu maso yamma, kowane ɗan Najeriya ya cancanci a ba shi damar yin takara ƙarƙashin tutar jam'iyyar.
Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed wanda shi ne shugaban kwamitin mai mamba 14, ya bayyana matsayar tasu a jiya Laraba yayin da yake gabatar da rahoto ga shugabanni a sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa da ke Abuja.
An kafa kwamitin ne domin gano dalilin da ya sa jam'iyyar ta yi rashin nasara a babban zaɓen 2019 da zummar bayar da shawarar yadda za ta sake ɗarewa mulkin Najeriya.
Sai Majalisar Ƙoli ta Ƙasa ta jam'iyyar wadda ake kira National Executive Committee (NEC) ta amince da shawarwarin da kwamitin ya bayar kafin a aiwatar da shi.
Yayin da ake shirin shiga babban zaɓe a 2019, PDP ta miƙa tikitin takarar shugaban ƙasa zuwa yankin Arewa, abin da ya sa Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, ya yi mata takarara bayan ya doke mutum 11 a zaɓen cikin gida.
Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun halaka wani matashi mai suna Sabo Yusuf a yankin Kawo na Jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya.
Kakakin rundunar 'yan sandan Jigawa, Zahraddeen Aminuddeen, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Ya ce maharan sun kai wa gidan mahaifin Sabo hari da tsakar daren Laraba, inda suka yi awon gaba da mahaifiyarsa da kuma ɗan uwansa.
Zahraddeen ya ƙara da cewa 'yan bindigar sun harbi Yusuf a ƙirji kuma ya rasu ne bayan an garzaya da shi asibitin Birnin Kudu.
"Da misalin ƙarfe 3:25 na daren Laraba, 'yan sandan Birnin Kudu sun samu rahoton cewa wasu 'yan bindiga sun kutsa kai cikin gidan Alhaji Abubakar mai shekara 50 a Kawo, suka harbi ɗansa a ƙirji mai suna Sabo Yusuf mai shekara 25," in ji Zahraddeen Aminuddeen.
A cewarsa, kwamishinan 'yan sandan jihar ya tura rundunar yaƙi da fashi da makami zuwa yankin.