Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ɗan sanda ya harbe mutumin da ya yi masa barazana da wuƙa

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da suaran ƙasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah ya kai mu

  2. Haramta wa mata rera waƙa ya haifar da ruɗani a Afghanistan

    Ma’aikatar ilimi ta Afghanistan ta ce tana gudanar da bincike kan wata sanarwa da daraktan ilimi a Kabul babban birnin ƙasar ya fitar kwanan nan da ta haramta wa mata da suka haura shekara 12 rera waƙa a bainar jama’a.

    Haramcin ya janyo suka a kafofin sadarwa na intanet. Ƴan mata da dama sun ta yaɗa bidiyonsu suna rera waƙa tare da amfani da maudu’in AmMySong, wato “Ni ne waƙata” domin nuna adawa da haramcin.

    Ce-ce-ku-cen ya biyo bayan damuwar da wasu ƴan ƙasar ke nuna kan abin da zai biyo bayanyarjejeniyar sulhu da ƙungiyar Taliban.

    Wasu matan sun dandanta matakin da rayuwa cikin mulkin Taliban – waɗanda aka kawo ƙarshen ikonsu a 2001 inda aka haramta wa mata zuwa makaranta da kuma yin waƙe.

  3. An kama mutanen da ake zargi sun ci zarafin musulmi ɗan shekara 14 a Indiya

    Ƴan sanda a Indiya sun ce an kama wasu maza guda biyu da ake zargi sun ci zarafin wani yaro musulmi ɗan shekara 14 saboda ya shiga wurin ibadar mabiya addinin Hindu domin ya sha ruwa.

    Yaron ya ce ya shiga harabar wurin ibadar na Hindu a Ghaziabad domin ya samu ruwan sha.

    Wani hoton bidiyo da aka yaɗa a kafofin sadarwa na intanet ya nuna yadda wani ke dukan yaron yana harbinsa da ƙafa.

    Wasu ƙungiyoyin masu fafutikar kare haƙƙin ɗan Adam sun bayyana damuwa kan ƙaruwar cin zarafi a Utter Pradesh da mabiya Hindu ke wa mata da kuma tsiraru

  4. Ɗan sanda ya harbe mutumin da ya yi masa barazana da wuƙa

    An harbe wani mutum a Faransa har lahira bayan ya yi wa ɗan sanda barazana da wuka.

    Lamarin ya faru ne a Paris babban birnin ƙasar. Hukumomi sun ce ɗn sandan na sintiri ne saman babur lokacin da ya ci karo da mutumin.

    Ɗan sandan ya buɗe masa wuta bayan mutum ya yi ƙoƙarin daɓa masa wuka.

    An kaddamar da bincike kan lamarin yayin da ƴan sandan Faransa suka ce ba harin ta’addanci ba ne.

  5. Mafi ƙarancin sadaki ya haura naira dubu 22

    Kuɗin sadaki mafi ƙanƙanta ya kai sama da naira dubu 22 a watan Maris na 2021.

    Duk wata Kwamitin Fadar Sarkin Musulmin Najeriya na fitar da bayani kan nisabin Zakka da sadaki da diyya.

    Kuma kwamitin ya ce daga ranar 28 ga watan Rajab shekarar 1442 bayan hijira daidai da 12 ga watan Maris na 2021, nisabin Zakka ya kai N1,767,520, wato adadin kuɗin da za a fitar wa Zakka.

    Kudin sadaki mafi ƙankanta kuma da haddin sata ya kai N22,094.

    Kuɗin da mutum kuma zai biyya na diyyar musulmi da aka kashe ya kai Naira miliyan 88 da dubu 376.

  6. An ceto ƴan ci-ranin da aka kulle wani ‘gidan yarin ɓoye’ a Libya

    Rahotanni daga Libya sun ce an saki ƴan ci ranin da aka kulle a wani gidan yarin ɓoye a kudu maso gabashin ƙasar.

    Bayanai sun ce mutum 47 aka samu a wani gidan yari da ke cikin gona, kuma yawancinsu ƴan Sudan ne da Habasha.

    An ceto mutanen ne bayan wani samame da jami’an tsaron Libya suka ƙaddamar bayan ɗaya daga cikin mutanen da ake tsare da su ya gudo kuma ya sanar da jami’an tsaron.

    Libya dai ta kasance hanyar da ƴan ci-rani yawanci ƴan ƙasashen Afirka ke ratsa wa suna kwarara turai.

  7. An dakatar da yin rigakafin korona ta AstraZeneca a Jamhuriyyar Ireland

    Ƙasar Jamhuriyar Ireland ta dakatar yin allurar rigakafin korona ta Oxford-AstraZeneca.

    Kwamitin kula da allurar rigakafi na ƙasar ne ya bayar da shawarar bayan samun rahotannin toshewar jini da rigakafin ta haddasa a ƙasar Norway.

    A cikin wani sakon Twitter, Ministan Kiwon Lafiya na Ireland Stephen Donnelly ya ce wannan "matakin rigakafi ne."

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce babu wata alaƙa tsakanin allurar da kuma matsalar toshewar jini.

    A makon da ya gabata ƙasashen Denmark da Norway suka dakatar da yin allurar.

    A ranar Juma'a Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kira ga ƙasashe kada su daina yin rigakafin kan fargabar cewa tana haddasa toshewar magudanar jini domin babu wata alama da ta tabbatar da hakan.

  8. Buhari ya umarci gwamnoni su farfaɗo da tsarin tsaro a matakin farko

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya kamata a koma tsari "irin na da" domin samar da tsaro "a kowane mataki" na gwamnati a ƙasar mai fama da hare-haren 'yan bindiga.

    Kazalika, shugaban ya koka cewa "duk sanda wani abu ya faru sai mutum ya garzaya fadar shugaban ƙasa", yana mai cewa a da ba haka ake yi ba.

    "Bayan na gama sakandare na shiga aikin soja, daga laftanar zuwa janar, na san a kowace ƙaramar hukuma akwai majalisar tsaro ƙarƙashin basaraken gargajiya da shugaban 'yan sanda na yankin da baƙi makiyaya da 'yan kasuwa," in ji shi.

    "Akwai irin wannan majalisar (ta tsaro) a duk faɗin Najeriya. Suna kai rahotonsu ne ga gwamnan jiha, sai dai idan akwai wani abu muhimmi sai a je wajen shugaban ƙasa.

    "Ina umartar ku da ku gyara tsarin tsaro...saboda a yi maganin matsalar a kowane mataki. Yanzu mun shantake, duk sanda wani abu ya faru sai mutum ya bazama zuwa fadar shugaban ƙasa.

    "Kamar yadda na faɗa, za mu dirar wa masu aikata laifuka. Wajibi ne a dawo wa da mutane ƙwarin gwiwa a kan gwamnati a cikin mako shida masu zuwa, idan ba haka ba kuma za mu shiga cikin yunwa saboda manoma ba za su iya komawa gonakinsu ba."

    Buhari ya yi waɗannan kalamai ne fadarsa da ke Abuja a makon da ya gabata, inda ya bayar da umarnin a harbi duk wanda aka gani da ɗauke da bindiga ƙirar AK-47.

  9. Gwamnatin Somalia ta ce 'yan ƙasar miliyan 2.5 na fama da yunwa

    Gwamnnatin Somalia ta ce mutum miliyan biyu da rabi na fama da yunwa a ƙasar sakamakon fari da kuma annobar korona.

    Ministan Agaji da Kiyaye Afkuwar Bala'i Khadijo Mohamed Diriye ya ce fari da kuma ƙarancin ruwa sun ta'azzara matsalar a Somalia.

    "'Yan Somalia miliyan 2.5 na fama da ƙarancin abinci mai gina jiki da ruwan sha da kuma haɗarin cutuka. Ƙarancin kayan agaji da kuma ruwan sama ne ke haddasa matsalar ta rashin abinci da ruwan sha," in ji shi.

    Ministan ya bayyaan haka ne yayin taron ministoci a Mogadishu yau Lahadi, inda suke duba tasirin da ƙarancin abincin ya yi a kan al'ummar ƙasar.

  10. 'Yan sanda sun kama masu zanga-zanga a birnin Landan

    Yan sanda a Landan na shan suka kan tarwatsa taron girmama wata mata da wani ɗan sanda ya sace, sannan ya kashe ta.

    An ga 'yan sanda na korar matan da suka taru a wani wurin shaƙatawa kusa da inda aka yi wa Sarah Everard gani na ƙarshe.

    Wasu hotuna da aka yaɗa a shafukan Internet sun nuna ‘yan sanda na danne wata mata a kasa tare da zarga wa wasu da dama ankwa a hannu.

    Sun ce ba a nemi izininsu kafin gudanar da taron ba, wanda ya saɓa da ka'idojin yaƙi da annobar korona.

    Magajin birnin Landan Sadiq Khan ya ce ba za a lamunci halayyar da jami'an tsaro suka nuna a wajen ba.

    Masu shirya taron sun ce abin takaici shi ne yadda 'yan sanda suka ci zalin mata a wajen da aka taru don girmama matar da ɗaya daga cikinsu ya zalunta ta hanyar sacewa kuma ya kashe ta.

  11. Masu zanga-zanga sun yi wa shugaban Argentina ruwan duwatsu

    Gomman masu zanga-zanga ne suka kai wa motar da Shugaban Argentina ke ciki hari a yankin Patagonia na ƙasar.

    Dandazon mutanen sun taru a kan motar Alberto Fernández kuma suka fara jifansa da duwatsu da dukan motar a ƙofar wata cibiyar mazauna yankin Chubut.

    Shugaban ƙasar na yin ziyarar jaje ne ga mutanen da gobarar daji ta shafa, wadda ta kashe mutum ɗaya tare da raunata wani.

    Sai dai ana gudanar da znaga-zangar ce domin neman sake buɗe wani wurin haƙar ma'adanai a Chubut.

    Mutanen na fushi da shirin gwamnati na amincewa da manyan ayyukan da ake shirin farawa a yankin wanda ke da arzikin zinare da tagulla da uranium, a cewar rahoton jaridar Clarín, abin da ka iya kawo cikas ga harkokin haƙar ma'adanan.

  12. An kashe Fulani makiyaya 6 'yan gida ɗaya a Jihar Osun

    Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari rugar Fulani da ke Irewole a Jihar Osun ta kudancin Najeriya, inda suka kashe mutum shida 'yan gida ɗaya.

    Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Opalola Yemisi, ita ce ta tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, tana mai cewa an kai harin ne da tsakar daren jiya Asabar.

    Ta ƙara da cewa tuni rundunar ta ƙaddamar da bincike kuma yanzu haka Kwamishinan 'Yan Sanda Wale Olokode da sauran jami'an tsaro sun je wurin domin tantance haƙiƙanin abin da ya faru.

    Rahotanni sun ce maharan sun kutsa kai rugar ce kuma suka buɗe wa iyalin wuta tare da kashe mutum shida nan take.

    A makon da ya gbata ma 'yan bindigar sun kashe wasu makiyaya huɗu a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriyar.

    Hare-haren na zuwa ne yayin da wasu mutane ke korar Fulani makiyaya daga wasu jihohin kudu maso yammacin ƙasar, suna masu zarginsu da aikata fashi da garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, zargin da makiyayan ke musantawa.

  13. Litinin ce 1 ga watan Sha'aban a Najeriya da Nijar

    Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya, Sa'ad Abubakar III, ta ce ranar Litinin 15 ga watan Maris ita ce 1 ga watan Sha'aban na Hijira 1442.

    Matakin ya biyo gaza ganin jinjirin watan Sha'aban ranar Asabar a faɗin ƙasar, a cewar fadar.

    Hakan na nufin yau Lahadi 14 ga Maris ta zama 30 ga watan Rajab.

    Kazalika, Litinin ɗin ce 1 ga Sha'aban a ƙasashen Nijar da Saudiyya da Iran da Indonesia da Malaysia da Daular Larabawa (United Arab Emirates) da Oman da Jordan da Falasɗin da Syria da Sudan da Libya.

    Sai dai a ƙasashen Masar da Turkiyya da Iraƙi da Tunisiya, Lahadi 14 ga Maris, ita ce 1 ga watan na Sha'aban.

    Sha'aban ne wata na takwas a jerin watannin kalandar Musulunci, wanda daga shi sai na Azumin Ramadana mai alfarma.

    Bisa ƙa'idar kalandar ta Musulunci, idan aka kasa ganin jinjirin sabon wata a daren 29, akan cika watan ya zama kwana 30 sannan washe gari ta zama 1 ga sabon wata.

  14. An kama gurɓatattun ƙwayoyin magani na biliyan 6 a Jihar Kano

    Kwamitin da ke yaƙi da gurɓatattun ƙwayoyi da abinci a Jihar Kano ya ce ya ƙwace tare da lalata ƙwayoyin magani na boge da suka kai darajar naira biliyan shida a cikin shekara tara da suka gabata.

    Shugaban kwamitin Gali Sule ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a hedikwatar ƙungiyar 'yan jarida ta Kano ranar Asabar, kamar yadda NAN ya ruwaito.

    A cewarsa, tun bayan kafa kwamitin a 2012 sun kama da kuma lalata ƙwayoyi na boge a wurare daban-daban kusan 20 na jihar.

    Shugaban ya ce yanzu Kano ta sauko daga matsayi na 1 a jerin jihohin da suka fi ta'ammali da ƙwayoyin boge zuwa mataki na 6.

    "Idan aka kuɓutar da Kano daga ta'ammali da miyagun ƙwayoyi an kuɓutar da ƙasashe da yawa a Afirka saboda ƙasashe kamar Nijar da Chad da Sudan suna sayen ƙwayoyi ne daga Kano." in ji shi.

  15. 'Yar Birtaniya Nazanin Zaghari za ta sake gurfana a gaban kotun Iran

    Nan gaba a yau ne wata mata ‘yar asalin Burtaniya da ke Iran Nazanin Zaghari za ta bayyana a gaban kotu, mako guda bayan an ‘yanta ta daga daurin talala.

    Sammacin na yanzu wani sabon cajin ne na daban wanda ya shafi harkokin tsaro.

    Iyalanta sun yi imanin cewa Iran na amfani da ita don cimma wasu bukatu na kashin kai, sannan hakan na da nasaba da aniyar hana ta komawa Burtaniya.

    An kama Zaghari ne a 2016 bayan shiga kasar daga Burtaniya tare da ‘yarta don kai wa iyayenta ziyara.

    An zarge ta da shirya makarkashiya ga gwamnatin Iran - zargin da ta musanta.

  16. Shugaban Chadi Idriss Déby ya ƙaddamar da takara a karo na 6

    Shugaban Chadi Idriss Déby ya gudanar da wani taron gangami domin ƙaddamar da yaƙin neman zabensa a wa’adi na shida a zaben da za a yi a watan Afrilu.

    An cika maƙil a babban filin wasa na birnin Ndjammena da ke cin kujera 15,000.

    Sai dai cikin watannin bay-bayan nan, an riƙa hana kungiyoyin 'yan gwagwarmaya da jam'iyyun adawa gudanar da taruka irin wannan da zummar kushe kamun ludayinsa da kuma bukatar ya hakura da mulki haka nan.

    Kotun ƙolin kasar ta hana jagororin 'yan adawa da dama tsayawa takara a zaben, yayin da wasu kuma suka janye a kashin kansu saboda zargin Mista Déby da amfani da karfi wajen murkushe 'yan adawa.

  17. Cutar korona a Najeriya: Mutum 4 sun mutu, 205 sun kamu ranar Asabar

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 205 da suka kamu da cutar korona a ƙasar ranar Asabar, sannan huɗu suka mutu.

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, jihar Ondo ce ke kan gaba a jerin jihohin da aka samu ɓullar cutar da mutum 33 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

    Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 25 a Legas, da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.

    A Abuja mutum 22 ne suka kamu, sai Bauchi, mai mutum 22 da Akwa Ibom mai mutum 21, sa Kaduna da aka gano mutane 15 da suka mau, baya ga Katsina mai mutum 14.

    Ga yawan wadanda aka samu a wasu jihohi:

    • Ogun -13
    • Rivers -11
    • Edo -8
    • Ekiti -4
    • Imo -4
    • Kano -3
    • Nasarawa -2
    • Neja -2

    Kazalika an sallami masu cutar 439 daga cibiyoyin da suke kwance a Abuja, bayan da suka warke a yanzu. sai kuma karin wasu mutum 96 da suka warke a jihar Legas.

    Ya zuwa yanzu, alƙaluman masu cutar ta korona a ƙasar sun kai 160,537 , sannan an sallami 144,714 jumulla, baya ga mutum 2,013 da suka mutu kawo yanzu.

  18. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da hantsin Lahadi da fatan hutun ƙarshen mako na tafiya lafiya.

    Umar Mikail ke muku maraba. Ku biyo ni domin sanin yadda duniya ke ciki a yau.