Rahotanni daga
kasar Ghana na cewa wani mummunanhatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 16 yayin da dama
suka jikkata a kan babbar hanyar Accra zuwa Kumasi.
Rahotanni
sun ambato ‘yan sanda na cewa lamarin ya auku ne da sanyin safiyar yau,
sakamakon kokarin da wasu direbobin motar safa biyu suka yi na wuce wata babbar
mota ba bisa ƙa’ida ba.
Majiyoyi da dama sun ambato ‘yan sanda na cewa hatsarin, ya
faru ne da safiyar Juma’ar nan, yayin da direbobin motocin safa biyu ke yunƙurin
rige-rigen wuce wata babbar motar dakon kaya.
Ana haka ne kuma jim kadan a dai-dai mahaɗar Akim Asafo
motoci biyun suka yi karo, inda nan take mutum 16 suka mutu.
Wasu hotunan a shafukan intanet sun nuna irin yadda
motocin suka yi kaca-kaca, sannan kayayyakin fasinjojin sun warwatsu a gefen
titi.
Fasinjoji da dama sun ji munanan raunuka inda aka garzaya
da su zuwa asibitin gwamnati na yankin Akim Asafo.
Rahotanni na cewa ‘yan sanda da taimakon wasu jami’an
kwana-kwana suka fitar da gawarwakin waɗanda suka mutu daga cikin tarkacen
motocin, inda suka kai su asibitin Akim Asafo domin gudanar da gwaje-gwaje ta
yadda za a gano ‘yan uwan mamatan.
Bayanai na cewa ana yawan samun haɗarin motoci a kasar
Ghana musamman a kan wasu hanyoyi da ke haɗa sannan kasar daga Accra.
Ko a makon jiya ma, an samu wani haɗarin mota daga Accra
zuwa Cafe coast da kuma daga Tamale zuwa Yandi a arewacin Ghanar, inda mutane
da dama suka rasa rayukansu.
Kawo yanzu dai fiye da mutum 30 ne suka mutu cikin kasa
da mako biyu, sakamakon irin yadda wasu direbobin ba sa tsayawa su huta idan
suna doguwar tafiya da kuma uwa uba rashin hanyoyi masu kyau.