Ƴan sanda sun kama mutum 71 a gidajen rawa kan karya dokar hana yaɗuwar Covid-19
Ƴan sanda a jihar Legas da ke Najeriya sun kai samame wuraren rawa na dare da dama, inda suka kama mutum 71 kan zarginsu da laifin take dokokin hana yaɗuwar Covid-19.
Ƴan sandan sun ce an kai samamen ne a unguwannin Lekki da Surulere kuma za a tuhumi dukkan waɗanda ake zargin kan laifin take dokokin da gwamnati ta sanya na daƙile yaɗuwar cutar korona.
Mai magana da yawun ƴan sanda Olumuyiwa Adejobi, ya shaida wa BBC cewa masu zuwa gidan rawar sun take dokar nan da aka sanya ta haramta taruwar mutane da yawa da sake buɗe gidajen rawa da kuma take dokar hana fita da daddare.
Hukumomi sun ce za su tsaurara kai samamen don tabbatar da cewa an bi dukkan dokokin da aka sanya.
Kamen na zuwa ne a yayin da Najeriya ke ƙara samun hauhawar masu kamuwa da cutar korona a kullum.
A ranar Litinin Hukumar Da ke Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa ta NCDC, ta sanar da cewa san samu ƙarin mutum 1,204 da suka kamu da cutar a ranar ɗaya, irin yawan da ba a taɓa samu ba tun da cutar ta ɓulla.
A yanzu dai jumullar waɗanda suka kamu da cutar a ƙasar sun kai 91,351 inda mutum 75,699 suka warke, sai kuma mutum 1,318 da suka mutu.
Jihar Legas ce cibiyar cutar a Najeriya.