Jami'an hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya reshen Jihar Legas sun kama mutum 21 bisa zargin aikata zamba ta intanet.
EFCC ta ce ta kama mutanen ne na wata ƙungiyar aikata laifuka ta intanet yayin wani samame da asubahin ranar Laraba bayan ta samu wasu bayanan sirri game da ayyukan nasu.
Bayan kama sun ne kuma, hukumar ta ƙwace ababen hawa guda 12 da suke amfani da su da kwamfutar laptop da kuma wayoyin hannu.
Hukumar ta bayyana sunayen mutanen kamar haka: Shittu Yakubu, Akinsola Afeez, Adeniyi Joseph, Opeyemi Wahab, Idris Sunday, Lawal Moshood, Jubril Yusuf, Olusegun Mohammed, Adekunle Adesanya, and Damilola Abijide.
Sauran su ne Sola Adio, Oladipo Ademola, Damilola Adewale, Akinsola Ridwan, Ogunlaye Damilare, Falaye Peters, Magnus Toni, Onanuga Ahmed, Bolarinwa Segun, Onanuga Olawale, and Ayomide Afeez.
EFCC ta ce za ta gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.