Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Za a yi wa matasa biyu bulala 12 a Kano

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a yau.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Laraba idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan labaran da muka wallafa ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. Babajide Sanwo-Olu ya yi ta'aziyya bisa rasuwar Sarkin Hausan Legas

    Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi ta'aziyya bisa rasuwar Sarkin Hausawan Legas, Muhammadu Sani Kabir.

    Sarkin Hausawan na Legas ya rasu ne a ranar Alhamis yana da shekara 57.

    A wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana sarkin a matsayin mai hangen nesa kuma mai son jama'a na ƙasa da shi.

    Ya kuma bayyana shi a matsayin wanda ya bayar da gudunmawa wurin ci gaban Dimokraɗiyya, musamman a matsayinsa na ɗan jam'iyyar NADECO a 1993.

  3. Sama da mutum dubu 53 sun sake kamuwa da korona a Birtaniya

    An sake samun mutum fiye da mutm dubu 53 da aka tabbatar sun kamu da cutar korona a Birtaniya cikin kwana guda.

    Wannan adadi na zuwa ne yayin da gwamnatin ƙasar ke fuskantar ƙarin matsin lamba bayan tsaurara matakan hana kamuwa da cutar.

    Farfesa Andrew Hayward, wani mai bai wa gwamnati shawara, ya shaida wa BBC cewa Birtaniya na shiga wani sabon yanayi mai hatsari, kuma ana bukatar daukar kwararan matakai don hana afkuwar wani mummunan bala'i.

    Ya bayyaba cewa muddin ana son dakile irin yanayin da ake ciki ya kamata a dauki mataki a yanzu.

  4. LABARAN WASANNI - NA YAMMA - 29/12/2020

  5. Za a yi muhawara kan amincewa da kudurin halarta zubar da ciki a Argentina

    Majalisar Dattawan Argentina na shirin tafka muhawara kan wani kudiri da ake sa ran zai halarta zubar da ciki a ƙasar, duk da sukar wannan lamarin da Cocin Katolika ta ƙasar ke yi.

    Tuni dai majalisar wakilai a ƙasar ta amince da halarta zubar da cikin.

    Masu goyon baya da kuma rashin goyon bayan wannan kudiri za su taru a wajen majalisar da ke a babban birnin ƙasar, Buenos Aires.

    Ana dai kyautata zaton za a shafe lokaci mai tsawo ana tafka wannan muhawarar inda ƴan majalisar za su kaɗa ƙuri'ar amincewa ko rashin amincewa tun da safiyar Laraba.

    Idan wannaan kudirin ya zama doka, zai bayar da dama ga mata su zubar da ciki har wanda ya kai mako 14.

    Dokar da ake da ita a yanzu ta halarta zubar da ciki ne kawai idan akwai alamun lafiyar uwa na cikin mummunan hatsari ko kuma wadda aka yi wa fyaɗe

  6. Jami'an tsaro sun kashe ɓarayin shanu 9 hanyar Kaduna-Abuja

    Rundunar sojin Najeriya, ta samu nasarar kashe ɓarayin shanu takwas, yayin da suke ƙoƙarin tsallaka hanyar Kaduna zuwa Abuja da shanun da suka sato.

    A wani saƙo da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa tun farko makiyayan da aka sace wa shanu a gabashin Kaduna ne suka shaida wa sojoji halin da ake ciki.

    Hakan ya sa sojojin suka yi wa ɓarayin shanun kwanton ɓauna inda suka kashe takwas daga cikinsu.

    Ko da BBC ta tuntuɓi kwamishinan domin tabbatar da wannan labari, ya bayyana mana cewa an ƙwato shanun daga wurin ɓarayin sai dai 16 daga ciki sun mutu, uku kuma sun samu rauni sakamakon bata kashin da aka yi da ƴan bindigan.

    A wani samamen na daban kuma, ya shaida mana cewa jami'an soji da ƴan sanda sun samu nasarar kashe wani ɗan bindiga ɗaya yayin da gungunsu ke tafe da wasu shanu da suka sato a gefen hanyar Kaduna-Abuja, sai dai ƴan bindigan sun harbe ɗaya daga cikin jami'an sa kai da ke nuna wa sojojin hanyar da ƴan bindigan suka bi.

  7. Za a yi wa matasa biyu bulala 12 a Kano

    Wata Kotun Majistare a Kano ta yanke hukuncin bulala 12 ga wasu matasa bisa samun su da laifin safarar tabar wiwi da kuma wasu miyagun ƙwayoyi.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa matasan wato Mohammad Sani mai shekara 24 da kuma Sadam Ali mai shekara 12 waɗanda ba a bayar da adireshinsu ba, an gurfanar da su ne a gaban kotun bayan kama su da tabar wiwi da wasu abubuwa da ake zargin kayan maye ne.

    Bayan da matasan suka amsa laifin su, sai alƙalin kotun, Farouk Ibrahim ya bayar da umarnin yi wa kowane daga cikin matasan bulala 12 a matsayin hukunci bayan sun nemi alƙalin ya yi musu sassauci.

  8. Kotu ta ɗaure matashi saboda tura wa mata hotunan batsa

    Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa wani mutum da aka tuhuma da cin zarafin mata a shafukan sada zumunta ɗaurin shekara uku a kurkuku.

    Kotun tattalin arziki da ke birnin Alkahira ta samu Ahmed Bassam Zaki da laifin cin zarafin mata biyu ta hanyar tura musu hotunan batsa da rubutu a wayoyinsu.

    Bugu da ƙari, an kuma tuhumi matashin mai shekara 21 a wata kotun hukunta masu laifuka kan zargin cin zarafin mata da kokarin yaudarar wasu ‘yan mata uku ‘yan kasa da shekara 18.

  9. Girgizar ƙasa ta ɗaiɗaita babban birnin Croatia

    Wata girgizar ƙasa mai karfin maki 6.4 ta auka wa tsakiyar ƙasar Croatia,

    Lamarin ya yi sanadiyar rushewar gine-gine masu ɗimbin yawa.

    Magajin Garin, Derinko Dumbovic ya ce girgizar ƙasar ta lalata rabin garin kuma ya yi kira da a kai musu daukin gaggawa.

    Wakilin BBC ya tabbatar da cewa Firaministan Croatia Andre Plenkovic ya tura ɗaruruwan sojoji zuwa yankin.

    Lamarin dai ya fi shafar babban birnin Croatia, Zagreb, inda aka samu katsewar wutar lantarki.

    'Yan sanda sun bukaci jama'a su kaurace wa bin hanyoyi kuma su zauna a gida.

  10. Dakarun sojin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka na tserewa cikin Kamaru

    Dakarun Jamhuriyar Tsakiyar Afirka fiye da 100 ne suka tsere zuwa cikin Kamaru.

    Jami’an tsaron na tserewa ne daga guraben aikinsu saboda dannowar da dakarun 'yan tawaye suke yi musu.

    Kazalika, wasu dubban 'yan gudun hijira na bin su domin tserewa faɗan zuwa cikin Kamaru.

    Sai dai Bangui, babban birnin ƙasar, na da zaman lafiya idan aka kwatanta da sauran sassan ƙasar.

  11. Sabon na'uin cutar korona ya ɓulla a ƙasashen duniya fiye da 20

    Pakistan ta zama ƙasa ta baya-bayan nan da ta bayar da rahoton ɓullar sabon nau'in cutar korona, wanda aka fara ganowa a Birtaniya.

    Hukumomin lafiya a yankin Sindh sun ce mutum uku ne suka kamu da sabon nau'in cutar a Karachi.

    Dukkanin mutum ukun sun shiga ƙasar ne daga Birtaniya, a cewarsu, suna masu cewa an fara bin diddigin waɗanda mutanen suka yi mu'amala da su.

    Pakistan ta hana shiga ƙasarta tun bayan ɓullar sabon nau'in amma an yi sassauci ga 'yan ƙasar mazauna Birtaniya masu taƙaitacciyar biza waɗanda suka nuna takardar gwajin da ke nuna ba sa ɗauke da cutar.

    Ya zuwa yanzu, sabon nau'in cutar ya ɓulla a ƙasa fiya da 20 a faɗin duniya.

    Ƙasashen sun haɗa da:

    • Nahiyar Turai:Netherlands, Denmark, Faransa, Italiya, Spain, Switzerland, Sweden, Finland, Ireland, Jamus, Iceland, Belgium
    • Nahiyar Amurka:Canada
    • Nhiyoyin Asiya da Australia: Indiya Japan, Singapore, Hong Kong, South Korea, Australia
    • Gabas Ta Tsakiya:Lebanon, Pakistan

    Kar a manta kuma da cewa, ƙasashen Afirka ta Kudu da Najeriya sun gano wani nau'in cutar daban da na Birtaniyar.

  12. 'Yan bindiga sun sace babban limamin Katolika a Jihar Imo

    'Yan bindiga ɗauke da makamai a Jihar Imo sun yi garkuwa da wani babban limamin Cocin Katolika mai muƙamin Bishop, Most Rev. Dr. Moses Chikwe.

    Mutanen sun yi awon gaba da malamin cocin ne ranar Lahadi a garin Owerri tare da direbansa, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito.

    Rundunar 'yan sandan Jihar Imo ta jaddada cewa ta baza jami'anta domin ganin an ceto Reverend ɗin mai shekara 53.

    Kakakin 'yan sandan jihar, SP Orlando ikeokwu, ya ce sashen yaƙi da masu garkuwa da mutane na rundunar ƙarƙashin jagorancin CSP Linus Nwalwu ya bazama domin kama miyagun.

    "Muna roƙon mutane da su kwantar da hankulansu a irin wannan yanayi maras daɗi," in ji shi.

  13. Ƙasashen da suka tabbatar da ɓullar sabon nau'in cutar korona

    Indiya ta zama ƙasa ta baya-bayan nan da ta bayar da rahoton ɓullar sabon nau'in cutar korona, wanda aka fara ganowa a Birtaniya.

    Ya zuwa yanzu, aƙalla ƙasa 20 sun bayyana ɓullarsa cikin ƙasashensu.

    Ƙasashen su ne:

    • Nahiyar Turai: Netherlands, Denmark, Faransa, Italiya, Spain, Switzerland, Sweden, Finland, Ireland, Jamus, Iceland, Belgium
    • Nahiyar Amurka: Canada
    • Nhiyoyin Asiya da Australia: Japan, Singapore, Hong Kong, South Korea, Australia
    • Gabas Ta Tsakiya: Lebanon

    Kar a manta kuma da cewa, ƙasashen Afirka ta Kudu da Najeriya sun gano wani nau'in cutar daban da na Birtaniyar.

  14. Iran ta fara yin gwajin riga-kafin korona da ta samar

    Iran ta fara yin gwajin allurar riga-kafin cutar korona da ta samar da kanta a karon farko.

    Kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun ce Tayebeh Mokhber, wata 'yar babban jami'in gwamnati Mohammad Mokhber, ita ce aka fara yi wa allurar mai suna Cov-IranBlessing a yau Talata.

    "Wannan saƙo ne ga Iraniyawa cewa muna da tabbas game da allurar da za mu yi musu, kuma idan akwai wata matsala iyalanmu ne baki ɗaya za su fuskance ta," a cewar Ministan Lafiya Saeed Namaki.

    Mista Mokhber ya ce ƙasar za ta iya samar da riga-kafin guda miliyan ɗaya da rabi a cikin 'yan makonni.

    Iraniyawa kusan 55,000 ne suka mutu sakamakon cutar, adadi mafi yawa kenan a yankin Gabas Ta Tsakiya. Kazalika, fiye da miliyan ɗaya ne suka kamu da cutar a ƙasar.

    Shugabannin Iran sun ce takunkumin da Amurka ta saka mata ya sa ba za ta iya samun riga-kafin korona ba, duk da cewa takunkuman sun yi sassauci kan magunguna da kuma kayan agaji.

  15. An cinna wa mutum biyu wuta kan zargin aikata fashi a Jihar Oyo

    Wasu fusatattun matasa sun cinna wa mutum biyu wuta bisa zargin fashi da makami a birnin Ibadan na Jihar Oyo da ke kudancin Najeriya.

    Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Olugbenga Fadeyi, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya faru ne da safiyar jiya Litinin.

    Ya ƙara da cewa rundunar Amotekun ta ceto ƙarin mutum ɗaya daga hannun matasan kuma ta miƙa shi ga 'yan sandan.

    "Ɗaukar doka a hannu da mutane ke yi abin Allah-wadai ne duk da cewa ya zama ruwan dare a jihar," in ji Mista Fadeyi.

    "Idan aka bari ya ci gaba da faruwa zai iya zama matsalar da babu mai iya magance ta."

    Ya ce rundunarsu ta ƙaddamar da bincike kan lamarin kuma ba za ta lamunci ɗaukar doka a hannu ba a nan gaba.

  16. Ana sake sauya wa Musulmin Rohingya matsuguni a Bangladesh

    Rundunar sojin ruwan Bangladesh ta ce ta ƙaddamar da wani aikin kwashe ƙarin 'yan Rohingya 1,800 zuwa wani tsibiri da ke mashigin ruwan Bengal.

    Jiragen ruwa bakwai ne ke safarar 'yan gudun hijirar zuwa sabon matsugunninsu, kuma a jiya Litinin, an kawo su daga sansanonin da ke kudancin ƙasar zuwa birnin Chittagong mai tashar jiragen ruwa.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun ce ana tilasta wa wasu 'yan gudun hijirar ne don su tafi.

    Hukumomin Bangladesh sun ce suna son 'yan gudun hijira kimanin ɗubu ɗari su baro sansanoni masu cunkoso da suke zaune ciki tun bayan tsere wa tarzomar ƙabilanci a Myanmar.

  17. Dubai ta ƙara wa baƙi wa'adin bizarsu a kyauta

    Mahukuntan ƙasar Daular Larabawa wato UAE sun ce sun yanke shawarar tsawaita wa'adin bizar baƙi 'yan yawon buɗe-ido na tsawon wata ɗaya.

    Ofishin yaɗa labarai na birnin Dubai mai suna Dubai Media Office ya ce Sarkin Dubai Mohammed bin Rashid Al Maktoum ne ya umarci a ƙara wa'adin ba tare da karɓar kuɗi ba.

    Sanarwar da ofishin ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne sakamakon rufe filayen jirgin sama da wasu ƙasashe suka yi a faɗin duniya saboda annobar korona.

    "Matakin zai tallafa wa masu yawon buɗe-ido da iyalansu waɗanda suke cikin UAE yanzu haka domin yin hutun Sabuwar Shekara," in ofishin.

    "Ma'aikatun gwamnati za su tantance tare da haɗa kai da hukumomin da suka dace domin ganin baƙin sun kasance cikin kwanciyar hankali."

    Ɓullar sabbin nau'in cutar korona a 'yan kwanakin nan ta sa wasu ƙasashe sun sake rufe filayen jirgin samansu saboda gudun yaɗuwar cutar.

    Birnin Dubai na Daular Larabawa na cikin manyan biranen duniya da ya fi saura karɓar baƙi a kowane lokaci na shekara.

  18. Sabon nau'in cutar korona ya gauraye Afirka ta Kudu - Ramaphosa

    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanar da tsauraran matakan taƙaita yaɗuwar cutar korona, don shawo kan abin da ya kira ƙarin bazuwar annobar mai tayar da hankali da ba a taɓa ganin irinsa ba.

    Ya ce asibitocin gwamnati da masu zaman kansu tuni sun kusa cika, sannan ana fama da ƙarancin gadaje a sashen kula da masu matsananciyar jinya.

    Mista Ramaphosa ya ce sabon nau'in ƙwayar cutar da ya fi saurin yaɗuwa, ga alama a yanzu ya bayyana a duk faɗin ƙasar.

    Sabbin matakan sun ƙunshi dokar taƙaita fita da kuma sa takunkumi ala tilas a cikin jama'a.

    An kuma hana sayar da barasa da kuma duk wani taro a cikin gida ko waje.

    A ranar Lahadi, adadin mutanen da suka kamu da korona a Afirka ta Kudu ya haura miliyan ɗaya tun bayan ɓullarta a watan Maris.

  19. NAFDAC ta rufe kamfanonin haɗa magani guda shida a Najeriya

    Hukumar kula da abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC ta rufe kamfanonin haɗa magani guda shida saboda rashin tsafta a harkokinsu.

    Mai magana da yawun hukumar, Sayo Akintola, shi ne ya bayyana matakin a madadin shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye.

    Ta ce hukumar ta yi hakan ne bisa haƙƙinta na hana yaɗa kayayyaki marasa inganci a ƙasa baki ɗaya.

    "An rufe kamfanonin ne bayan wani bincike a kan ayyukansu na ƙasa baki ɗaya," in ji Mista Akintola, kamar yadda NAN ya ruwaito.

    "Waɗannan kamfanoni duk da irin gargaɗin da aka yi musu, sun gaza bin tsaftataccen tsarin gudanar da ayyuka na Good Manufacturing Process (GMP) domin tabbatar da tsaftar magunguna."

    Kazalika, shugabar ta koka kan yadda kamfanonin, waɗanda na cikin gida ne, suka gaza bin ƙa'idoji "marasa tsauri" na kiyaye tsafta da ingancin kayayyakinsu.

  20. Korona a Najeriya: Mutum 10 sun mutu, 397 sun kamu ranar Litinin

    Ƙarin mutum 10 ne suka mutu sakamakon cutar korona a Najeriya ranar Litinin, a cewar alƙaluman hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa.

    Sabbin alƙaluman da ta wallafa a shafinta na intanet ya kuma nuna cewa ƙarin mutum 397 ne suka kamu da cutar.

    Ta ce an samu sabbin kamuwar ne a jiha 18 har da Abuja kuma sun haɗa da Legas (144) da Filato (83) da Kaduna (48) da Adamawa (36) da Rivers (22) da Oyo (16) da Kebbi (10).

    Sauran jihohin su ne: Nasarawa (7), Sokoto (7), Abuja (5), Kano (5), Edo (4), Jigawa (3), Ogun (2), Akwa Ibom (2), Neja (1), Bauchi (1), Zamfara (1).

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 84,811 ne suka kamu da cutar a Najeriya, 1,264 da cikinsu sun mutu sannan 71,357 sun warke.