Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ƙungiyar ƴan Naija Delta ta bai wa Buhari wa'adi

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. EU ta kaddamar da fara rigakafin korona a Turai

    Kungiyar Tarayyar Turai ta fara riga- kafin korona a dukkan nahiyar, a wani mataki da ta kira "Hadin kai don yaki da annoba".

    Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce allurar rigakafin ta isa dukkan kasashen nahiyar 27 zuwa yanzu.

    uTni dai wasu daga cikin kasashen suka fara yiwa mutane rigakafin, inda suka ce babu bukatar sake jira sai wata rana.

    Fiye da mutane Miliyan 14 ne aka tabbatar sun kamu da cutar korona a nahiyar, kana fiye da dubu 300 sun mutu.

  2. Ministar al'amuran mata ta Najeriya ta kamu da korona

    Ministar al'amuran mata ta Najeriya Paulinee Tallen ta kamu da cutar korona.

    Ministar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta aikawa manema labarai mai dauke da sa hannunta.inda tace cutar bata ci karfinta tukuna.

    Adadin mutanen da ke kamuwa da cutar korona a Najeriya dai na ci gaba da karuwa a dai dai wannan lokaci.

    A makon da ya gabata ne hukumomi suka sake rufe makarantu da wuraren shakatawa domin dakike yaduwar cutar.

  3. Ƙungiyar ƴan Naija Delta ta bawa Buhari wa'adi

    Wata ƙungiyar masu ɗauke da makamai a yankin Naija Delta, ta buƙaci shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta umartar jami'an hukumar EFCC su janye daga harabar gidan jagoransu Tompolo, sannan a bude masa asusunsa na banki.

    Kungiyar mai suna 21st Century Youths of the Niger Delta and Agitators ta bayyana damuwa dangane da yadda aka ki mutunta umarnin wata kotu na wanke jagoran nata.

    Cikin wata sanarwar Email da kungiyar ta fitar kamar yadda jaridar The Natiins ta rawaito, ta ce jan hankalin ya zama dole domin gudun haddasa danyar fitina a yankin na Naija Delta.

    "A bawa Tompolo kadarorinsa da aka karbe, matasan kabilar Ijaw da kuma na Naija Delta ba za su sake naɗe kafa su tsaya suna kallon irin wannan cin fuska ba" " ini sanarwar.

    Kungiyar ta kara da cewa idan har aka gaza yin abinda ta nema, to kuwa za ta tura mutanenta su mamaye gidan da har ywnzu jami'an EFCC ke ci gaba da mamaya a cikinsa.

  4. Ministar Harkokin Mata ta Najeriya Pauline Tallen ta kamu da korona

    Ministar Harkokin Mata ta Najeriya Dame Pauline Tallen ta kamu da cutar korona, a cewarta.

    Cikin wani saƙon Twitter da ta wallafa a yau Lahadi, Madam Pauline ta ce gwajin da ta yi ne ya tabbatar ta kamu da cutar bayan ta yi mu'amala da wasu da suka kamu da ita.

    Sai dai ba ta bayyana lokacin da ta yi gwajin ba, amma ta ce ta killace kantsa.

    Kazalika ta ce iyalanta ba su kamu da cutar ba, kamar yadda nasu gwajin ya nuna.

    "Ya zuwa yanzu, alamun cutar ba su bayyana a jikina ba amma na killace kaina na tsawon lokacin jinya. Ina roƙon addu'o'inku," in ji ta.

  5. Shugaba Mahamadou Isoufou ya kaɗa ƙuri'arsa

  6. Kusan mutum 40 sun mutu a hatsarin mota a Kamaru

    Kusan mutum 40 ne suka mutu wasu 18 suka jikkata sakamakon hatsarin mota da ya auku a birnin Yaounde na Jamhuriyar Kamaru.

    Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:00 na daren Asabar lokacin da wata motar fasinja ta kauce wa hanya kuma ta faɗa cikin babbar kwatar da ke gefen titi.

    "Mun tantance mutum 37 da suka mutu da kuma 18 da suka ji munanan rauni," a cewar babban jami'in ofishin 'yan sanda na Mbam, Absalom Monono Woloa.

    An kai waɗanda suka ji rauni asibitoci a Ndikkiminiki da Makenene, yayin da waɗanda suka mutu kuma ake kai su mutuwaren Babban Asibitin Yaounde, inda 'yan uwansu za su karɓe su," in ji shi.

    Ministocin cikin gida da na sufuri, Paul Atanga Nji da Jean Ernest Ngalle Bibehe, na kan hanyarsu ta zuwa Ndiki domin tattara bayanan abin da ya faru.

  7. Mun gamsu da shirye-shiryen hukumar zaɓen Nijar - Tawagar ECOWAS

    Kungiyar raya tattalin arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO, ta bayyana gamsuwa kan shirye-shiryen da Hukumar zaɓen Niger wato CENI ta yi, game da zaɓen ƙasar na yau.

    Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Architech Muhammad Namadi Sambo, shi ne jagoran wakilan ECOWAS ɗin kuma ya shida wa BBC cewa fatan da Shugaba Buhari yake da shi kenan.

  8. Labarai cikin minti ɗaya

  9. Sanata Saidu Umar Kumo ya rasu

    Allah Ya yi wa Sanata Saidu Umar Kumo rasuwa da safiyar yau Lahadi, 27 ga watan Disamban 2020.

    Tsohon sanatan wanda ya wakilci mazabar Jihar Gombe ta Tsakiya, ya rasu ne a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

    Kafin rasuwarsa, shi ne Garkuwan Gombe. Ya riƙe shugaban kamfe ɗin Alhaji Atiku Abubakar a shiyyar arewa maso gabas a zaɓen shugaban ƙasa na 2019.

    Sai dai Sanata Kumo ya koma jam'iyyar APC mai mulki a watan Janairun 2019 kafin a shiga zaɓen da Muhammadu Buhari ya lashe a watan Fabarairu.

    An zaɓe shi zuwa Majalisar Dattawa a shekarar 1999 zuwa 2003 kafin daga baya ya yi takarar gwamnan Gombe a 2011, inda ya sha kaye a hannun Ibrahim Hassan Dankwambo.

    Za a yi jana'izarsa a Masallacin Ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 2:00 na rana.

  10. Kyan ɗan ƙasa ya jefa ƙuri'a, a cewar wani mai zaɓe bayan ya jefa tasa

    Malam Amadou Abdou ya ce ya ji daɗi sosai saboda ya kaɗa ƙuri'arsa.

    "Kyan ɗan ƙasa da ma shi ne ya kaɗa ƙuri'arsa," kamar yadda ya faɗa wa wakilinmu Ibrahim Isa a Damagaram.

    A yau ne 'yan Nijar fiye da miliyan bakwai za su zaɓi sabon shugaban da zai jagorance su a tsawon shekara biyar masu zuwa bayan wa'adi biyu na Mahamadou Isoufou na shekara 10 ya cika.

  11. Ɗan takarar RDR ya kaɗa ƙuri'arsa

    Ɗan takarar jam'iyyar RDR a zaɓen shugaban Nijar, Mahamane Ousmane, ya kaɗa ƙuri'arsa a Jihar Damagaram.

    Baya ga zaben shugaban kasa, ana kuma jefa wa 'yan majalisar tarayya ƙuri'a.

    Kamar yadda ake gani a hoton sama, Mahamane ya jefa ƙuri'ar ce tare da mai ɗakinsa.

  12. An kashe masu iƙirarin jihadi 12 a Mali

    Sojoji a Mali sun ce sun kashe masu iƙirarin jihadi kimanin 12 lokacin da suka auka wa wata kwambar motocin soja a kusa da kan iyaka da Burkina Faso.

    Rundunar sojin Mali ta ce babu wani dakarenta da aka kashe yayin harin na ranar Alhamis.

    'Yan ta-da-ƙayar-baya kan kai hare-hare a yankunan kan iyaka tsakanin ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar.

    A makon jiya, masu bincike na Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce sun tattara shaida cewa dakarun tsaron Mali na aikata laifukan yaƙi.

    Rahotonsu ya ƙra da cewa masu iƙirarin jihadi da kuma sauran ƙungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai suke keta 'yancin ɗan Adam.

  13. Manyan 'yan takara

    'Yan takara 30 ne ke fafatawa da juna don karɓar ragamar mulki daga Shugaba Mahamadou Issoufou, bayan ƙarewar wa'adinsa biyu tsawon shekara goma.

    Zaɓen shi ne irinsa na farko da wani zaɓaɓɓen shugaban ƙasa zai miƙa mulki cikin ruwan sanyi ga wani takwaransa da za a zaɓa.

    Kuma ko ma wane ne zai zamo sabon shugaban Jamhuriyar Nijar a Lahadin nan, zai fuskanci ƙalubala iri daban-daban ciki har da taɓarɓarewar tsaro da cin hanci da rashawa da kuma talauci.

    Za a fara kaɗa ƙuri'a ne da ƙarfe 08:00 agogon Nijar a rufe da ƙarfe 07:00 na dare.

    Daga cikin manyan 'yan takarar akwai:

    • Mohamed Bazoum, ɗan takarar jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya
    • Mahamane Ousmane, zababben Shugaban Ƙasa na farko a 1993
    • Seini Oumarou, tsohon Fira Minista a gwamnatin Shugaba Tandja Mamadou
  14. Mutum fiye da miliyan bakwai ne za su kaɗa ƙuri'a

    Daga cikin mutane fiye da miliyan bakwai da ke kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen har da ɗumbin matasa da suka kai shekarun yin zaɓe, kuma suka zaƙu don fid da shugaban Nijar na gaba.

    Suna dai fatan shugaban mai zuwa zai kawo gagarumin sauyi a rayuwarsu ta hanyar bunƙasa ilmi da harkokin kula da lafiya da kuma samar da aikin yi.

    Wani matashi mai suna Suleiman Ibrahim a jihar Damagaram ya ce yana jin daɗi sosai ganin lokaci ya yi da shi ma ƙuri'arsa za ta yi tasiri wajen nema wa ƙasarsa mafita.

  15. Inda Shugaba Mahamadou Isoufou zai jefa ƙuri'a

  16. An buɗe rumfar zaɓe a Damagaram

  17. Assalamu Alaikum

    Umar Mikail ke muku fatan an tashi lafiya.

    Ku biyo mu a wannan shafi domin ganin yadda take kayawa a zaɓen shugaban ƙasa da 'yan majalisa a Jamhuriyar Nijar da kuma sauran labarai a Najeriya da sassan duniya.