Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 617 da suka kamu da cutar korona a ranar Asabar.
Kazalika ƙarin mutum huɗu sun mutu, abin da ya kawo jumillar adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar zuwa 1,194 a kasar.
A saƙon da ta wallafa a shafinta na intanet, NCDC ta ce an samu sabbin kamuwar ne a jiha 15 da suka haɗa da Legas (225), FCT (181), Kaduna (125),Adamawa (25), sai Nasarawa (20).
Sauran sun hada da Kano (12), Rivers (8), Edo (4), Ekiti (4), Bayelsa (3), Ogun (3), Plateau (3), Akwa Ibom (2).
Sai a karshe jihohin Delta da Sokoto na da mutun 1-1 kowannensu.
Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 72,757 ne suka harbu da cutar a Najeriya, 65,850 daga cikinsu sun warke.
A ranar 28 ga watan Fabrairu ne aka samu mutum na farko mai ɗauke da cutar a Najeriya, wani dan Italiya da ya shiga birnin Legas ranar 25 ga watan.
Sannan a ranar 23 ga watan Maris mutum na farko ya mutu sakamakon cutar a Najeriya.