Masu amfani da shafin Twitter a arewacin Najeriya sun sako tauraron fim Ali Nuhu a gaba saboda ya ƙi shiga zanga-zangar neman daƙile matsalar tsaro.
Kusan mako guda kenan matasa 'yan Arewa na amfani da maudu'ai kamar #EndNorthBanditry da #SecureNorth da #EndInsecurity domin kira ga gwamnati ta samar da tsaro a yankin, yayin da 'yan uwansu na kudancin ƙasar ke neman rushe rundunar 'yan sanda ta SARS bisa zargin cin zarafi da kashe mutane ba bisa ƙa'ida ba.
Ko a jiya Asabar an gudanar da zanga-zangar #EndInsecurity a Kano da Kaduna da wasu jihohin Arewa. Sai dai ba a ji ɗuriyar Ali Nuhu ba da kuma wasu manyan taurarin Kannywood.
Cikin hira da wata kafar yaɗa labarai, Ali Nuhu ya bayyana cewa 'yan Kannywood "ba sa shiga gaba-gaba a irin waɗannan lamura saboda irin zagin da suke sha a hannun masu amfani da shafukan sada zumnta".
Wannan cewa yake: "Ali Nuhu ya ce ba zai shiga zanga-zanga a Arewa ba saboda mutane na zaginsa. Ba zai goyi bayan mutanen da ke kallon fina-finansa ba. Ya kamata a tambaye shi, shin za mu iya kallon fim ɗinsa idan ba mu da rai?"
Shi ma wannan cewa yake: "'Duk irin zagin da 'yan Najeriya ke yi wa Shugaba Buhari, matarsa ta shiga zanga-zangar #SecureNorth. Ali Nuhu daga Kano na cewa ba zai shiga zanga-zanga ba saboda ana zaginsa."
Wannan kuwa kare Ali Nuhu yake yi: "Gaskiya ya faɗa muku. Ko yanzu maimakon abin da kuka saka a gaba ya yi shuhura, Ali Nuhu ne yake shuhura saboda kun dage a kan abin da kuka fi ƙwarewa a kai; zagin mutane."
Taurarin Kannywood da mawaƙa da yawa sun shiga zanga-zangar a shafukan sada zumunta irinsu Rahama Sadau da Aminu Saira da Ali Jita da Dj Ab da Deezell da Classic.
Sai dai ba Ali Nuhu ne kaɗai ba a ji ɗuriya ba a cikin manyan taurarin Kannywood, Hadiza Gabon da Fati Washa da Adam Zango da Hafsat Shehu, su ma ba a ji ɗuriyar tasu ba.