Ƙarshen rahotannin kenan
Jama'a nan muka kawo ƙarshen rahotannin a wannan shafi. Mu haɗu gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.
Imam Saleh and Umar Mikail
Jama'a nan muka kawo ƙarshen rahotannin a wannan shafi. Mu haɗu gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya ya ce hutun da 'yan majalisar suka tafi na mako shida ba ya nufin ba za su yi aikin komai a wannan lokacin sannan kuma ba su karya wata doka ba.
Femi Gbajabeamila ya ce 'yan majalisar 'yan majalisar za su ci gaba da kewayen duba ayyuka a ma'aikatun Gwamnatin Tarayya.
Gbajabeamila ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafukansa na sada zumunta ranar Litinin.
"Yayin da yake amsa tamnbayoyin manema labarai bayan kammala taron jam'iyyar APC da Shugaba Buhari ya jagoranta, kakakin ya bayyana cewa majalisar ba ta karya kowacce irin doka ba bisa tafiya hutun shekara-shekara da ta yi," a cewar sanarwar.
Ta ƙara da cewa mambobin majalisar za su ci gaba da duba ayyuka "har sai idan ya zama dole sannnan za su ajiye aiki".
'Yan Najeriya da dama sun soki 'yan majalisar game da shirinsu na tafiya hutun yayin da ƙasar ke fuskantar matsaloli daban-daban.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargaɗin cewa amincewa da rigakafi cikin sauri "abu ne da ke buƙatar natsuwa da mayar da hankali".
Babbar likitar hukumar, Soumya Swaminathan, ita ce ta yi gargaɗin a tattaunawarta da manema labarai, inda take cewa kowacce ƙasa na da 'yancin sahale fara amfani da rigakafi ba tare da an kammala dukkanin gwaji ba "amma fa ba abu ne da za a yi cikin sakaci ba".
Rigakafi guda 33 ne yanzu haka ke kan matakin gwaji na ƙarshe, a cewar WHO, sannan wasu 143 na matakin farko-farko.
Rundunar tsaro ta sojojin Najeriya da ke Abuja ta ce ta samu nasarar ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a yankin arewa maso yammacin ƙasar cikin kwana huɗu.
Rundunar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet, inda ta ƙara da cewa dakarunta na rundunar Sahel Sanity sun kashe tare da kama wasu 'yan fashin daji.
An ceto mutanen ne a dazuka daban-daban na JIhar Katsina yayin hare-haren da take kaiwa a yankin daga ranar Litinin, 24 zuwa 28 ga watan Agusta.
Alƙaluman gwamnati sun nuna ƙarin mutum 1,406 da suka kamu da cutar korona cikin kwana ɗaya - ragin kusan mutum 300 a kan waɗanda suka kamu a rana kafin wannan.
Ranar Litinin, yawan mutanen da suke kamuwa a rana ya kai 1,715 - ba a taɓa samun yawan mutanen nan a rana ba tun farkon Yuni.
Mutum biyu ne aka bayar da rahoton mutuwarsu ranar Litinin sakamakon cutar, yayinb da mutum ɗaya ya mutu ranar Lahadi.
Adadin alƙaluman da ake samu na Litinin ba su kai na sauran ranaku ba saboda Asabar da Lahadi babu aiki.
Mutumin nan da ta dalilinsa aka yi wani fim kan kisan kiyashi a kasar Rwanda ya shiga hannun hukumomin kasar.
Ana zargin Paul Rusesabagina da ya zauna a kasashen Turai da Amurka tsawon shekaru da dama da laifin jagorantar wata ƙungiyar yan ta'adda da kuma kitsa hari a Rwanda.
Hukumomi sun ce anyi kuskuren nuna tsohon manajan wani Otal a Kigali, a matsayin mutumin kirki da ya kuɓutar da daruruwan jama'a a fim din Hotel Rwanda, wanda ya fita bayan kisan kiyashin da aka yi a shekarar 1994.
Sun kuma ce ya rika karbar kuɗade ga wadanda ya tseratar yayin da ya juya baya ga wadanda basu da abin bashi.
Mista Rusesabagina dai ya musanta wannan zargi.
Kotun soji a Kamaru ta dage zaman da za ta yi a yau domin yanke hukunci a kan wasu sojoji biyar da ta samu da laifin kisan wasu mata 2 da yaransu a garin Zelevet ta lardin arewa mai nisa a shekara ta 2015.
Kafin soma zaman kotun, alkali ya fitar da sanarwa da ke cewa an dage zaman zuwa ranar 21 ga watan Satumba.
Hujjar ɗage ƙarar kamar yadda take kunshe a sanarwa ita ce bai wa jami’an kotun baki daya damar haduwa a lokacin yanke hukuncin.
China ta yi watsi da iƙirarin Indiya cewa dakarunta sun yi ƙoƙarin tada husuma a kan iyakar Ladakh.
Mai magana da yawun gwamnati a Beijing ya ce sojojinsu ba su taba ƙetara iyakar da aka shata ba.
Yanzu haka wakilan kasashen biyu sun koma kan teburin tattaunawa.
Indiya na ikirarin cewa China na wasu take-take a kokarin harzuƙata.
A watan Yuni sojojin Indiya ashirin sun mutu, bayan wani kazamin fada da takwarorinsu na China a kan iyakar da ke yankin Ladakh.
Akalla mutane uku ne suka gamu da ajalinsu, sakamakon wata fashewa da ta auku a Abu Dhabi, babban birnin hadaddiyar daular larabawa wato Dubai.
Ofishin watsa labarai na gwamnatin jihar Abu Dhabi ya rawaito cewa lamarin ya auku ne a wani wurin cin abinci da ake kira Hardees, da ke hanyar Rashid Bin Saeed.
Karin wasu mutane da dama sun samu raunuka, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya rawaito.
Hanyar ta zarce har zuwa babban filin sauka da tashin jiragen sama na birnin, in da ake sa ran shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Isra'ila Benjamin Netanyahu za su sauka nan gaba a yau.
Tsohon shugaban India Pranad Mukherjee ya mutu, kwanaki 21 bayan kamuwa da cutar korona.
Kamfanin dillacin labaran Faransa AFP ya rawaito cewa tshon shugaban mai shekaru 84 ya rasu ne bayan an kwantar da shi a asibiti.
Kafin ya zama shugaban kasa daga 2012 zuwa 2017, Mista Mukherjee ya rike manyan mukamai da dama a shekaru 51 da ya kwashe ya na aikin gwamnati.
Dansa Abhijit ya tabbatar da labarin a shafinsa na twitter.
Tsohon shugaban na daya daga cikin fitattun 'yan siyasar kasar, sannan daya daga cikin manyan 'yan adawa.
Gwamnatin Lagos da ke kudancin Najeriya ta ce Kwamishinan Lafiya na jihar ya warke daga cutar korona.
A sakon da aka wallafa a shafin Twitter na gwamnatin jihar, an ambato Gwamna Babajide Sanwo-Olu yana cewa Farfesa Akin Abayomi ya warke daga cutar ta korona kuma a hankali zai komo bakin aiki.
"Zai koma bakin aikia hankali kuma yana da kwarin gwiwar aiwatar da alkawuran da Gwamna Babajide Sanwo-Olu, wanda ya ce ya kasance tare da shi a mawuyacin halin da ya shiga," a cewar sakon.
A makon jiya ne Kwamishina ya killace kansa bayan ya sanar da kamuwa da cutar korona.
Shi ne yake jagorantar shirin gwamnatin jihar ta Lagos, wadda ta fi fama da cutar a Najeriya, na yaki da korona..
Kananan yara a turai sun soma komawa makarantu a wannan makon. sai dai bude azuzuwa bayan shafe watanni a kulle ya haska abubuwa da dama.
Ga yadda wasu kasashe ke yiwa dalibai marhabun zuwa makarantu.
Gwamnatin rikon kwarya a Sudan ta rattaba hannu da kungiyoyi biyar na 'yan tawayen kasar yayin wani biki da aka gudanar a makociyarta Sudan ta kudu.
Yarjejeniyar na da manufar kawo karshen zub da jinin da aka kwashe shekaru 17 ana yi a yammacin Darfur da wasu jihohin kudancin kasar.
Wannan wani gagarumin ci gaba ne a kudurin magance matsalolin tsaron da ake samu a wasu yankunan Sudan, kamar yadda wakiliyar BBC kan harkokin Afrika Anne Soy ta rawaito.
Sai dai biyu daga cikin manyan kungiyoyin 'yan tawayen sun yi shuri da yarjejeniyar, wadda ta yi tanadi kan batutuwa da dama, ciki har da batun mallakar filaye, da raba madafun iko, da kuma mayar da miliyoyin mutanen da yaki ya daidaita zuwa gidajensu.
Kotun Ƙolin Najeria ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Kogi Musa Wada ya daukaka, inda yake kalubalantar nasarar Gwamna Yahaya Bello na jam'iyyar APC.
Jagoran alkalan da suka yanke hukuncin, kana alkalin alkalan Najeriya Tanko Muhammad, ya ce masu kara sun gaza gabatar da kwakkwarar hujja da zata tabbatar da zarginsu, don haka ta tabatar da Yahaya Bello a matsayin wanda ya samu nasara a zaben gwamnan jihar da ya gabata.
Hukumar zaben Najeriya wato INEC ce ta sanar da Yahaya Bello na APC a matsayin wanda ya samu nasara a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a watan Nuwamban 2019.
Ya samu kuri'u 406,222, sai Musa Wada na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 189,704, yayin da Natasha Akpoti ta jam'iyyar SDP ta samu kuri'u 9,482.
Wasu ma'aikata a jihar Zamfara da ke Najeriya sun karyata kalaman da gwamna Muhammad Bello Matawwalle ya yi cewa yakan biya albashi wani lokaci tun kafin ranar 20 ga wata.
Ya bayyana haka ne a shirin BBC Hausa na A-Fada a Cika.
Sai dai galibin ma'aikata da muka tattauna da su sun ce batun ba haka ba ne.
Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraren ra'ayoyin ma'aikatan jihar Zamfara:
Manchester City ta shirya biyan dan wasan Barcelona da Argentina mai shekara 33 Lionel Messi £450m a wani bangare na shirinta na shekara biyar wanda daga karshe zai kai shi ga tafiya New York City FC, in ji jaridar (Sport, via Daily Star).
Dole Barcelona ta biya £12m idan tana so ta soke kwangilar dan wasan Uruguay mai shekara 33 Luis Suarez'. (Goal)
Jaridar Mirror ta rawaito cewa Tottenham ta yi yunkurin yin katsalandan a shirin Manchester United na dauko dan wasan Netherlands and Ajax Donny van de Beek, mai shekara 23.
Manchester United ta tattauna da Aston Villa a yayin da take son cimma matsaya don karbo dan wasan Ingila mai shekara 24 Jack Grealish. (Mail)
Latsa nan don karanta cikakken labarin wasannin:
Wani shugaba a jam'iyyar da ke mulkin Afirka ta Kudu ya ce Shugaba Cyril Ramaphosa zai gurfana a gaban wani kwamiti na jam'iyyar domin amsa tambayoyi kan gudunmawar da aka ba shi ta yakin neman zabe wadda ake ce-ce-ku-ce a kanta.
Sai dai Jessie Duarte, wanda babban jami'i ne a jam'iyyar ta African National Congress, bai bayyana lokacin da Mr Ramaphosa zai gurfana a gaban kwamitin ba.
A wani rahoto da aka fitar, hukumar da ke yaki da rashawa ta kasar ta yi zargin cewa Mr Ramaphosa ya yaudari majalisar dokoki kan kudin da ya karba na gudunmawa a 2017, wanda ya zarta $36,000 (£27,000).
Mr Ramaphosa ya dage cewa an bayar da gudunmawar ce domin yakin neman zabensa na shugabancin ANC.
A matsayinsa na shugaba, Mr Ramaphosa ya rika yaki domin tsarkake harkokin siyasar Afirka ta Kudu tun da ya maye gurbin Jacob Zuma.
Hukumomi a Hamas sun garkame wani sansanin 'yan gudun hijra da ke birnin Gaza sannan ana tilastawa mutane zama a gida a wani yunkuri na magance bazuwar annobar korona.
Yankin na da mutum 177 da suka kamu da annobar cikin makon da ya gabata.
Rahotanni sun ce wasu manyan motoci sun ajiye bulo a sassan titunan kasar da ke kai wa ga sansanin.
'Yan sanda kuma na gargadin mutanen yankin su dubu 95 da kada su bar gidajensu ko kuma su bude shagunansu.
Kungiyar dattawan arewacin Najeriya ta yi watsi da wata gayyata da wani kwamitin wucin gadi na majalisar dattawa ya yi wa jama'ar kasar domin su bayyana ra'ayinsu game da shirin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriyar.
Kungyar ta Northern Elders Forum, wadda Farfesa Ango Abdullahi ke jagoranta, ta ce majalisar na so ne kawai ta bata lkacin 'yan kasar ba tare da ta aiwatar da abubuwan da suka kamata ba.
Kungiyar dattawan arewar, wadda ta yi kira ga sauran kungiyoyin farar hula na yankin da su kauracewa gayyatar da majalisar dattawan ta yi, ta ce a ganinta duk wani shirin gyaran kundin tsarin mulki da za a yi bata lokaci da kudade ne kawai.
Dokta Hakeem Baba-Ahmed, daraktan yada labarai na kungiyar ta Northern Elders Forum, ya yi wa AbdusSalam Ibrahim Ahmed karin bayani.