Wani bincike da sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya gudanar ya nuna cewa wasu ma'aikata a asibitocin ƙasar Ghana suna sayar da kayan kariya daga cutar korona don samun makudan kuɗaɗe.
Fiye da ma'aikatan kiwon lafiya 2,000 ne a ƙasar suka kamu da cutar korona, tun bayan ɓarkewar cutar.
Ghana ta fuskanci ƙarancin kayan aikin kariya kamar takunkumi fuska.
Ɗan jarida Anas Aremeyaw Anas ya yi shigar burtu don gano yadda wasu ke saka rayuwar abokan aikinsu cikin haɗari domin samun kuɗi.
Anas Aremeyaw ya shaida jana'izar wani likita da ya mutu sakamakon cutar korona a kasar Ghana kuma mutane sanye da kayan kariya tun daga sama har ƙasa su ne ke aikin binne gawar, sannan kuma masoya da 'yan uwa ɗauke da furanni sun tsaya daga nesa.
Dr. Adu wani abokin aikin mamacin ne. Ya ce: "Babban likita ne mai ƙwazo. Mutuwarsa babbar hasara ce sosai ga asibitin da kuma Ghana baki ɗaya."
Fiye da likitoci 200 ne a Ghana suka kamu da cutar korona. Kullum ma'aikata na cikin kukan rashin isassun kayan kariya.
Lokacin da cutar korona ta ɓulla a kasar, gwamnati ta umarci asibitoci da su nemi kayan kariya daga cutar ta korona adadin da suke buƙata.
Ƙasar ta dogara ne wajen samun dubban kayan aiki daga masu bayar da tallafi, ciki har da tsohon shugaban kasar John Mahama.