Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Buhari ya amince da tsawaita dokar kulle da mako huɗu

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu rahotannin.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin

    • An sanya dokar ta ɓaci a Gambia
    • Gobara ta kona masu cutar korona a India
    • Saudiyya za ta kai kayan agaji Lebanon
    • Rashin tabbas kan farashin man fetur a Najeriya
    • Wata sabuwar kungiyar ‘yan tawaye ta ɓulla a Kamaru
    • 'Yan sanda sun kama kwantena cike da 'ƙwayoyi' a Legas

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. An maka gwamnatin Uganda kotu saboda kwaroron roba

    Sakamakon kamuwa da nau'ukan cututtuka da ake samu ta hanyar saduwa, mutum uku 'yan ƙasar Uganda sun kai ƙarar hukumar da ke sa ido kan magunguna da kuma wata ƙungiya mai zaman kanta ta Marie Stopes

    Sun kai ƙarar hukumar da kuma ƙungiyar ne sakamakon wani kwaroron roba 'mara kyau' da ya jawo musu jangwam.

    A 2019 ne ƙungiyar Marie Stopes ta kawo kwaroron roba samfarin Life Guard, amma daga baya hukumar sa ido kan magunguna a ƙasar ta bayar da umarnin hana amfani da shi

    Ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗaukaka ƙarar ya bayyana cewa ya yi amfani da kwaroron roban amma ya fashe yayin da ya ke saduwa, hakan ya sa ya kamu da cutar HIV.

    Mutum na biyu cikin mutanen shi kuma ya ce sakamakon fashewar kwaroron roban ya kamu da gwanoriya.

    Wata mace ma ta ce ta samu ciki duk da an yi amfani da wannan kwaroron.

    Koken da suka gabatar gaban kotu na cewa ba a yi gwajin ingancin kwaroron ba kafin aka tura shi ga al'umma

  3. Wani jirgi ya yi hatsari a Masar

    Wasu matuƙan jirgin sama sun mutu bayan da ƙaramin jirginsu ya yi hatsari a filin jirgin jihar Hurghada da ke Masar.

    Mai magana da yawun hukumar sufurin jiragen sama ta ƙasar ya bayyana cewa matuƙa jirgin sun mutu sakamakon raunuka da suka samu da suka haɗa da buguwa a kai.

    Rahotanni sun bayyana cewa jirgin wanda mallakar kamfanin Airman Sky Sports ne ya faɗi yayin da ake gwajinsa.

    Jihar Hurghada da ke gaɓar teku a Masar ta yi suna wurin yawon buɗe ido, kuma akasari ana amfani da ire-iren waɗannan jirage wurin zagayawa da masu yawon buɗe ido.

    Tuni dai aka fara bincike kan musabbabin hatsarin jirgin

  4. Covid-19: Buhari ya amince da tsawaita dokar kulle da mako huɗu

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tsawaita dokar kullen da aka sassauta kashi na biyu da makonni huɗu.

    Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa na yaƙi da cutar korona Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani bayani ga 'yan jarida kan cutar.

    Wannan ne dai karo na uku da ake tsawaita kashi na biyu na sassaucin dokar kullen a faɗin ƙasar.

    Akwai shawarwari da sakataren gwamnatin ya bai wa shugaban ƙasar kan ci gaba da sassaucin wannan doka, sai dai ba a fito da bayanai kan shawarwarin ba.

  5. Saura ƙiris adadin waɗanda suka kamu da korona a Afrika ya kai miliyan 1

    Saura ƙiris adadin waɗanda suka kamu da korona a Afrika ya kai miliyan ɗaya, kamar yadda ƙididdiga daga shafin BBC da ke bin diddiƙin annobar korona a Afrika ya nuna.

    A halin yanzu adadin waɗanda suka kamu da cutar a nahiyar ya kai 995,293.

    Ƙasar Afrika Ta kudu ke kan gaba a yawan masu cutar a nahiyar da mutum 529,877.

    Sa'annan sai ƙasar Masar da ke da mutum 94,875.

  6. 'Yan sanda sun kama kwantena cike da 'ƙwayoyi' a Legas

    Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta samu nasarar kama wata kwantena mai tsawon kafa 40 cike da kwayoyin da ake zargin Tramadol da codeine ne.

    Kafar yaɗa labarai ta Channels a kasar ta ruwaito cewa rundunar 'yan sandan ta ce ta kama kwantenar ne tun daga kan ruwa sannan ta kawo ta tashar da ke Apapa a birnin na Legas.

    Wasu jami'ai daga hukumar kwastam da kuma na yaki da miyagun kwayoyi sun taya rundunar 'yan sandan wurin aiwatar da kamen.

    Ko a ranar Talata sai dai mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno ya bayyana cewa safarar miyagun ƙwayoyi na daga cikin abubuwan da ke ƙara kawo rashin tsaro a ƙasar

  7. Obaseki ya cire rufin Majalisar Dokokin Edo

    Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki da ke kudancin Najeriya ya cire duka rufin majalisar dokokin jihar da zimmar hana kowa zama cikin ginin majalisar.

    Wannan na zuwa ne bayan da ‘yan sanda a jihar suka yi wa ginin majalisar jihar kawanya wadda ke Benin babban birni jihar.

    Kakakin gwamnan Obaseki ya shaida wa BBC cewa ya yi hakan ne da nufin hana wasu 'yan siyasa ciki har da gwamnan wata jiha cika burinsu na kwace jihar lokacin da ake daf da gudanar da zaben gwamna a jihar.

    Gwamman jami’an tsaro ne suka sanya shinge a wajen ginin majalisar.

    Kakakin ‘yan sandan jihar Chidi Nwabuzor ya bayyana cewa jami’an sun je ne da nufin kare rikicin da ake zaton zai iya tashi.

    Rikicin siyasa na kara ƙamari a jihar da aka tsara yin zaben gwamna a watan Satumbar gobe.

    Rahotanni sun ce babu dai kowa a cikin ginin majalisar. Kimanin mutum 200 ne suka yi carko-carko a wajen ginin majalisar, kuma mafi yawansu magoya bayan gwamna mai ci ne.

    Al’amura na kara rikicewa tun bayan tuɓe mataimakin kakakin majalisar Yekini Idaiye da aka yi a ranar Laraba kan zargin shi da karya doka.

    A baya ya fito ƙarara ya nuna goyon bayansa ga abokin hamayyar gwamna mai ci.

    A sauya shekar da yayi na ban mamaki a watan Yuni, Gwamna Godwin Obaseki, ya sauya daga jam’iyya mai mulki ta APC zuwa babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.

  8. Babu haramcin tafiya tsakaninmu da Najeriya - UAE

    Hadaddiyar Daular Larabawa ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sadarwa da ke cewa an sanya dokar tafiye-tafiye tsakanin kasashen biyu.

    Cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar da ke birnin tarayyar Abuja ya fitar ta ce, babu wani mataki da aka dauka tun bayan na bayan takaita tafiye-tafiye da aka yi ga ko wacce kasa saboda annobar korona a ranar 7 ga wata Maris, a wani mataki na dakile annobar korona a kasar.

    Bayan samun sauki da aka yi na wannan annoba, sai aka janye haramcin tafiye-tafiyen da aka sanya a ranar 7 ga wata Yuni ga duk wani mai zuwa ziyara kasar, tare da umarnin cika sharuddan da aka gindaya.

    Kuma dukkan sharudan da aka sanya babu wanda aka ware Najeriya cikinsu.

    Sanarwar ta ce a yanzu da ba a yin tafiya, hakan na da alaka da rashin saukar jiragen kasashen duniya a Najeriya, ma'ana Najeriya ba ta buɗe filayane jiragenta ba.

    UAE na ta kokarin tattaunawa da Najeriya domin ganin an dawo da yin tafiye-tafiye tsakanin kasashen biyu.

    Ofishin jakadancin da ya wallafa sanarwar a shafinsa na Twitter, ya shawarci mutane da su rika tuntubar hukumomi domin samun labarai masu inganci.

  9. Ana jimamin mace-mace a Beirut, korona na kara yaɗuwa a Lebanon

    Lebanon na cikin jimami bayan wata gagagrumar fashewa da aka samu a Beirut kusa da tashar ruwa wadda ta yi ajalin mutum 137 ya zuwa yanzu tare da lalata duniya mai yawa.

    Muna ta kawo muku koma bayan da annobar ta haifar, sai dai ba ita kadai ce matsalar da ke damun Lebanon ba a wannan lokacin.

    Kamar dai mafiyawan kasashen, Lebanon ma na fama da wannan annoba ta korona wadda ta kara fito da matsalar da ake da ita a bangaren kiwon lafiyar kasar.

    Ya zuwa yanzu, kasar na da masu korona 5,417 kuma tuni 68 suka mutu sakamakon cutar, kamar yadda jami’ar jami’ar Johns Hopkins ta bayyana.

    A ranar Laraba mutane 355 ne suka kamu da cutar a kasar, wanda shi ne adadin mafi yawa da aka taba samu ya zuwa yanzu.

    A farkon makonan ne aka samu wata mummunar fashewar wasu sanadarai wanda ya sauya akalar kasar daga yaki da korona zuwa aikin neman ceto da sake gina kasa.

  10. Wata sabuwar kungiyar ‘yan tawaye ta ɓulla a Kamaru

    Wata sabuwar kungiyar 'yan tawaye ta kunno kai a Kamaru, sai dai ƙungiyar ba ta bayyana sunanta ba. Ƙungiyar ta fara ne da watsa wani bidiyonta na farko a shafukan sada zumunta, wanda yanzu haka suka karaɗe kasar ta Kamaru.

    Cikin bidiyon, ɗaukacin dakarunta da aka hasko na sanye da kayan yaƙi kamar yadda sojojin gwamnati suke yi kuma suna ɗauke da makamai.

    Manufar wannan ƙungiyar da ta bayyana a cikin bidiyon ita ce karɓe mulki daga hannun shugaban ƙasa Paul Biya, wanda ya daɗe yana shugabantar Kamaru, kamar yadda wani mutum ya bayyana da faransanci a cikin bidiyon.

    Cikin bidiyon dai, wani babba daga cikin 'yan tawayen ya ci gaba da bayani da Fulatanci irin na 'yan ƙabilar Umbororo 'yan asalin ƙasar wadɗnda ake samun irinsu a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika.

    BBC ta nemi karin bayani daga kakakin ma'aikatar tsaro ta ƙasar, sai kakakin ma'aikatar tsaro ya ce bidiyon na bogi ne kuma bai kamata a mayar da hankali a kan shi ba. Kamaru ta shafe shekaru tana fama da rikicin ƙungiyoyin 'yan tada ƙayar baya irinsu Boko Haram da masu fafutukar Ambazoniya masu rajin kafa kasa, kuma har ya zuwa yanzu ƙasar ana fafatawa da ƙungiyoyin.

  11. Arsenal ta kusa dauko Coutinho, Tottenham za ta sayar da Aurier

    Jaridar Sport ta ruwaito cewa tattaunawar da dan wasan Barcelona Philippe Coutinho yake yi domin yiwuwar tafiya Arsenal "ta yi nisa". Dan wasan na Brazil mai shekara 28 ya kwashe kakar wasan da ta wuce yana zaman aro a Bayern Munich.

    Arsenal ta yi tayin bayar da kwangilar shekara uku ga dan wasan Chelsea da Brazil Willian, mai shekara 31, a cewar(Sky Sports).

    An samu ci gaba a tattaunawar da Chelsea take yi da dan wasan Real Madrid Sergio Reguilon, mai shekara 23, wanda ya kwashe kakar wasan da ta wuce yana zaman aro a Sevilla.(ESPN)

    Latsa nan don karanta cikakken labarin wasannin:

  12. Yau za a kammala rijistar katin zabe a Ghana

    Yau ne ake sa ran kammala rijistar katin zabe a Ghana wanda hukumar zabe ta kasar ta ke gabatarwa a fadin kasar.

    Rahotanni na cewa wasu da yawa da yawa na korafin ba su samu damar yin rijistar ba, yayin da wasu kuma ke sambarka da yadda ake gudanar da wannan aiki na rijistar.

    An shirya gabatar da babban zabe a Ghana a ranar 7 ga watan Disambar wannan shekarar da muke ciki.

    Sai dai wasu na hasashen cutar korona da ta'addabi duniya ka iya haifar da tsaiko ga zaben.

  13. Yaushe za a samu riga-kafin cutar korona?

  14. Botswana ta haramta sayar da barasa

    Gwamnatin Botswana ta haramta sayar da barasa kuma ta dakatar da duka lasisin kamfanonin barasar.

    Sanarwar ta ce za a dakatar da sayar da barasar ne har zuwa wani lokaci da ba a ambata ba.

    Dalinlin da aka bayar na hana shan barasar shi ne, giya kan janyo a ki bin dokar da aka sanya ta annobar korona.

    A makon da ya gabata, gwamnatin kasar ta jaddada sanya dokar kulle mai tsanani a Gabarone babban birnin kasar, na mako biyu domin shawo kan cutar.

    Kasar ta tabbatar da mutum 804 da ke dauke da korona ya zuwa yanzu, kuma tuni mutum biyu suka mutu daga cikinsu.

  15. Rashin tabbas kan farashin man fetur a Najeriya

    Tun bayan kara farashin man fetur da gwamnatin Najeriya ta yi daga naira 133 zuwa 138.62 ko wacce lita daya, farashin man yake ta tangal-tangal a gidajen man kasar.

    Kamfanin NNPC ya raba wata sanarwa ga masu kamfanonin man da masu dakon man, wadda ke dauke da sanarwar karin da aka samu.

    Hakan dai ya sanya mafi yawan kamfanin dakwon mai irinsu DAFMAN da IPMAN sanar da karin farashin mai ga mambobinsu.

    IPMAN ya ba da sanarwar duk wasu manbobinsa su sayer da man kan naira 150 ko wacce lita daya.

    Wakilinmu na Kano Khalifa shehu Dokaji ya zagaya wasu gidanjen mai don ganin yadda akje sayar da man.

    Sai dai ya ce babu wani takamaiman farashi da za a ce ko wa na sayer da man shi akai.

    Wasu gidajen man sun kara nasu farashin kamar haka:

    Sai dai kuma a gefe guda wasu kalilan sun yi na su karin amma bai kai wanda IPMAN ta ba da sanarwar mambobinta su yi ba.

    Ko a watan Yuni sai da gwamnatin Najeriya ta kara firashin man fetur daga N140.80 zuwa N143.80 a duka kan lita guda.

    Gabanin nan farkon watan Afrilu 2020, gwamnatin ta sanar da ragin firashin man zuwa N123.50 a duk lita guda, lokacin da ake tsaka da faduwar farashin man a kasuwar duniya saboda cutar korona.

    Sama da shekaru 20 firashin mai bai taba zama daidai ba a Najeriya. Wani lokaci ya hau wasu lokutan kuma a samu ragi.

  16. An kashe gobarar da ta yi barna a kasuwar Ajman da ke Dubai

    Masu kashe gobara a Dubai da Sharjah da kuma Umm Al Quwain sun hada hannu wajen kashe gobarar da ta yi barna a rukunin shagunan da ke Ajman.

    Gobarar ta tashi ne a yankin kasuwar kayan lambu a Ajman a ranar Laraba da yamma.

    Sai dai cikin awa uku aka samu damar shawokanta kuma babu wanda ya jikkata ko ya rasu a lamarin kamar yadda jami’ai suka bayyana.

  17. Saudiyya za ta kai kayan agaji Lebanon

    Sarki Salman na Saudiyya ya bayar da umarnin kai kayan agajin gaggawa kasar Labanon sakamakon abin da ya faru a Beirut a ranar Talata.

    Kamfanin dillancin labarai na kasar SPA ne ya rawaito hakan yana kafa hujja da wata sanarwar manema labarai da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a ranar Alhamis.

    Za a bayar da agajin ne ta hannun kungiyar ba da agaji ta Sarki Salman din ga wadanda wannan masifa ta shafa.

    Kuma tuni sashen likitoci na kungiyar da ke yankin kasar ta Labanon ya isa bayan fashewar da manyan motocin daukar marasa lafiya.

    Akwai tawagar likitoci ta Al-Amal da ke da alaka da kungiyar KS a Arsal ita ma ta na nata kokarin a aikin ceto wadanda abin ya ritsa da su.

    Za a kai jini babban asibitin Beirut ga masu bukta.

    Cikin sanarwar ma’aikatar harkokin waje ta kasar ta ce “Saudiyya za ta ci gaba da nuna goyon baya wajen ganin an taimakawa wadanda wannan al’amari ya shafa, kuma muna rokon Allah ya ji kan wadanda suka riga mu gidan gaskiya a wannan masifa.”

  18. Gobara ta kona masu cutar korona a India

    Masu fama da korona takwas ne suka mutu yayin wata gobara da ta tashi a wani asibiti a birnin Ahmedabad da ke yammacin India, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

    Wutar ta tashi ne a wajen sashen kula da masu bukatar kulawa ta musamman da misalign karfe 3:00 agogon kasar a ranar Alhamis.

    Wani jami’I ya yi ta zagaye a tsukukun wurin da wutar ta tashi, kamar yadda Rajesh Bhatt wani babban jami’in kashe gobara ya bayyana wa BBC.

    “Jami’in da ya rika kai-komo cikin sashen cikin dimaucewa kuma sai wutar ta ci gaba da yaduwa sakamakon haka,” in ji shi.

    ‘Yan sanda sun ce sun tsare wani babban daraktan asibiti domin fara bincike.

  19. An sanya dokar ta ɓaci a Gambia

    Shugaban Gambia Adama Barrow ya sanya dokar ta baci a fadin kasar na tsawon kwana 21 sakamakon karuwar annobar cutar korona a kasar.

    Shugaban ya ce iyakokin kan tudu da sararin samaniyar kasar za su ci gaba da kasancewa a rufe, sai dai za a bar jirgin daukar kaya ya ci gaba da aiki, da jami’an diflomasiyya da kuma masu zuwa kasashen waje neman magani.

    Kasar tana da masu dauke da cutar kusan 700 kuma tuni 16 cikinsu suka mutu.

    Mataimakin shugaban kasar da kuma wasu ministoci uku na cikin masu dauke da cutar, sai dai da aka yi wa shugaban kasar gwaji a ranar Litinin sakamakon ya nuna baya dauke da cutar.

    An rufe duka wuraren ibada a fadin kasar, amma ana barain ‘yan shekarar karshe a makarantun fadin kasar suje domin rubuta jarrabawa wadda za a fara daga 17 ga watan Agusta.

    Ana kulle duka shaguna da kasuwanni domin a rika yi musu feshin magani ko wacce ranar Lahadi

  20. Buɗewa

    Daga nan sashen Hausa Muke muku Barka da safiya. Ku kasance da mu domin kawo muku labarai da rahotanni kai tsafe a wannan shafin namu.

    Abubuwan da suka shafi Najeriya Nijar da sauran kasashen Nahiyar ta Afrika da ma sauran kasashen duniya baki daya.