Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

MDD za ta sake gina wuraren tarihi da aka lalata a Mali

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. Mu kwana lafiya

    Nan muka kawo ƙarshen rahotannin a wannan shafi.

    Umar Mikail ke muku fatan mu kwana lafiya - da fatan za mu haɗu gobe da safe.

  2. WHO ta gargadi Rasha kan rigakafin cutar korona

    Hukumar lafiya ta duniya ta bukaci Rasha da ta bi dokokin da aka shata wurin samar da rigakafi mai inganci.

    Hakan ya biyo bayan matakin da Rasha ta bayyana na fara bada rigakafin cutar Korona ga yan kasarta a watan Oktoba.

    Ministan lafiyar Rasha ya ce wata cibiyar samar da rigakafi a kasar ce ta samar da rigakafin da za a tabbatar da ingancinsa a cikin wannan watan.

    Mai magana da yawun WHO, Christian Lindmeier ya ce duk wani rigakafi da aka samar sai an tabbatar ya bi matakan gwajin da aka shata kafin a fara anfani dashi.

    Masana kimiyya a kasashe da dama na nuna shakku kan yadda Rasha ta yi ikirarin samar da rigakafi cikin kankanin lokaci, inda suke zargin akwai lauje cikin nadi.

  3. Hukuncin kisa ga duk wanda ya aikata fyaɗe a Bauchi

    Gwamnatin Jihar Bauchi na shirin kafa wata doka da ake kira BAP, wadda tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da laifin yi wa yara ƙanana Fyade.

    Haka ma doka ta tanadi ɗaurin rai-da-rai ga wanda ya yi wa babbar mace fyade da kuma ɗaurin shekara 20 ga waɗanda suka yi wa mace ɗaya taron dangi.

    Wannan dai na zuwa ne yayin da hukumomin ‘yan sanda a jihar suka ce sun samu rahotannin aikata fyade har 21 a cikin wata dayan da ya wuce kaɗi.

    Ko a jiya ‘yansanda sun sanar da kama wani mutum da suke zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara uku fyade.

  4. MDD za ta sake gina wuraren tarihi da aka lalata a Mali

    Majalisar dinkin duniya ta sha alwashin sake gina wuraren tarihi da aka rusa a Mali biyo bayan shekaru da aka shafe ana rikici.

    Hukumar kula da ilimi da al'adu ta majalisar wato UNESCO ta ce masu rajin kare muhalli sun bada dala miliyan daya don sake gina kauyuka talatin da ke yankin Dogon.

    Rikici musamman a tsakiyar Mali ya sa anyi asarar dadaddun wurare masu cike da tarihi da aka samar shekaru aru aru da suka gabata.

  5. Wani bam ya tashi a Beirut na Lebanon

    Wani bam ya tarwastse a babban birnin Lebanon, Beirut yayin da ake jiran yanke kan kisan tsohon firaministan ƙasar Rafik Hariri a shekarar 2005.

    Rahotanni sun ce fashewar ta faru ne a kusa da tashar jirgin ruwa da ke birnin, sannan wasu rahotannin suka ce an ji ƙara ta biyu.

    Mahukunta na fargabar cewa waɗanda suka ji rauni na da yawa.

    Wani bidiyo da aka wallafa a intanet ya nuna wani baƙin hayaƙi ya turnuƙe sama sannan kuma ya yi ɓarna.

    Wata kotun Majalisar Ɗinkiun Duniyta ce ke shirin bayar da hukunci game da shari'ar, wadda ake zargin mutum huɗu bayan an aikata kisan ta hanyar tashin wani bam a mota.

  6. Kungiyar tsofaffin dalibai ta tallafa wa asibiti a Nijar

    Kungiyar tsofaffin dalibai ta makarantar sakandare ta CEG Tasawa ajin 1980 ta bayar da tallafin kayan aikin asibiti ga asibitin garin na Baratou.

    Kayayyakin suka hada da kayan tiyatar haihuwa da kayan aikin ido da sauransu.

    Dakta Mourtala, shi ne shugaban asibitin garin na Tasawa da ya karbi wadannan kaya kuma ya nuna jin dadinsa tare da bayyana amfanin taimakon ga asibitin da ya ce dama yana da bukata.

    Kungiyar da ta kafu daga wani dan gungu na sada zumunta a shafukan sada zumunta, ta fara ne da gangami don taimaka wa juna musaman tsoffin 'yan makarantar ta CEG Tasawa kafin ta zama babbar kungiya.

  7. Yadda aka bude makarantun sakadare a Najeriya

    Yadda aka bude makarantun sakandare domin ‘yan aji shida da za su zana jarabawar WAEC a Najeriya. Dalibai da malamansu sun halarta a makarantar GDSS Dutse da ke Abuja.

  8. Abin da yasa muka kori matuka jirgi 70 daga aiki - Air Peace

    An kori akalla matukan jirgin saman kamfin Air Peace da ke Najeriya 70, a wani mataki na sauya tsarin aiki da kamfani ya bayyana a matsayin mai mahimmanci domin ya ci gaba da aiki.

    Kamfanin jirgin ya ce zabi biyu ne kawai da shi: ko dai ya yi kori wasu ma'aikatan kuma ya rage albashin wadanda suka yi ragowa ko kuma ya yi durkushewar da ba zai iya biyan albashin ba da kuma wasu ayyuka, sai ya zabi na farko.

    A makonnin baya, shugaban kamfanin Air Peace Allen Onyema, ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta samar da wasu kudaden tallafi ga kamfanonin jiragen domin su ci gaba da tsayawa kan kafafunsu.

    Sai dai babu kamfanonin jiragen sama cikin wani tallafin kudi na dalar Amurka biliyan 6 da gwamnatin ta ware saboda cutar korona, wanda zai bai wa bangarorin kasuwanci da yawa damar neman aron kudi domin rage raɗaɗin annobar korona.

    A wata sanarwa da ya fitar mai magana da yawun kamfanin Stanley Olisa ya ce da farko rage albashi aka fara yi domin ci gaba da aiki amma daga baya suka ga hakan ba zai yi aiki ba yadda suke bukata.

  9. Ana samun ci gaba a yaƙi da korona a Amurka - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka ta fara ganin alamun ci gaba mai mahimmanci a yaki da cutar korona.

    Yana magana ne yayin da adadin wadanda cutar ta kashe a kasar ke cigaba da karuwa in da zuwa yanzu ya zarce dubu dari da hamsin da biyar.

    Mista Trump ya fadawa wani taron manema labarai cewa an samu raguwar kusan kashi shida cikin dari a yawan wadanda cutar ta harba a makon da ya gabata.

    Yace Indiya ma na da babbar matsala kamar yadda abin yake a sauran kasashe, sai dai na lura bana jin hakan a labarai.

    Tun da farko shugaban ya soki daya daga cikin manyan mashawartan likitocinsa, Deborah Birx, wacce ta ce a yanzu cutar ta yadu a fadin kasar kuma hakan babbar barazana ce da tafi ta bullar ta tun da farko.

  10. Dole mahajjata su killace kansu bayan kammala Hajji

    Dukkan alhazan da suka yi aikin hajji a bana za su killace kansu a gida na mako biyu duk da matakan kariyar da suka bi yayin ibadar, kamar in da jaridar Arabnews ta ruwaito.

    An samar da wata sarka da zata rika bibiyar duk abin da suke yi yayin killace kansu da za su yi tare da daukar bayanan lafiyarsu ta hanyar amfani da wata manhaja da ake kira “Tatamman”.

    An dai umarci duk maniyyatan na wannan shekara da su sanya ita wannan sarka gabanin fara aikin hajji na bana, domin tabbatar da bin dokar killace kai da kuma sauran dokokin da aka shimfida domin dakile yaduwar cutar.

    Ana dai samun raguwar masu kamuwa da cutar a kasar. Inda yanzu masu cutar suke gaza 2,000 kwanki goma a jere.

    A ranar Litinin an ba da rahoton kamuwar mutum 1,258 wanda ya kai dadin masu cutar a kasar 280,093 ya zuwa yanzu.

  11. Buhari yana ganawa da hafsoshin tsaro a fadarsa

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana jagorantar taro kan sha'anin tsaro a fadarsa da ke Abuja, babbarn birnin kasar, a cewar mai taimaka masa kan shafuan zumunta.

    Sakon da Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce hafsoshin tsaron kasar da sauran manyan masu ruwa da tsaki kan tsaro a gwamnatinsa na cikin mahalarta taron.

    Sai dai bai yi karin bayani kan abubuwan da suke tattaunawa ba.

    Aana wannan taro ne kwanakin kadan bayan gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya zargi jami'an tsatron kasar da yin zagon ƙasa a yunkurin magancer matsalar Boko Haram.

  12. Willian zai tafi Arsenal, Man Utd za ta ɗauko Grealish

    Dan wasan Chelsea Willian, mai shekara 31, ya ki sanya hannu kan kwangilar karin shekara biyu a kungiyar kuma ya tattauna da Arsenal, wacce ta amince ta ba dan wasan na Brazil kwangilar shekara uku kamar yadda ya so.(Guardian)

    Kazalika Arsenal na son dauko dan wasan Bayern Munich dan kasar Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 28, da kuma dan wasan Atletico Madrid dan kasar Ghana Thomas Partey, mai shekara 27.(Times - subscription required)

    Dan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang yana so kungiyar ta sayo dan wasan Barcelona dan kasar Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23.(Le10 Sport)

    Karanta cikakken labarin wasannin a nan:

  13. Mutum 800 sun mutu a India a kwana daya

    Sama da mutum 800 ne suka mutu a India a ranar Litinin saboda cutar korona,Wanda wannan ne sabon adadi mafi yawa da aka taba samu a duniya cikin awa 24.

    An kuma fi samun karin masu kamuwa da cutar a India sama da ko wacce kasa a duniya.

    Fitaccen shugaban ‘yan adawar nan na kudancin India, K Siddaramaiah shi ma na cikin wadanda suka kamu da cutar.

    Shi ne fitaccen mutum na baya-bayan nan da aka tabbatar ya kamu da cutar a India, wadanda suka hadar da ministan cikin gida Amit Shah.

    Karuwar masu kamuwa da cutar a India wata alama ce ta yadda kasar ke ta fadi tashin shawo kan annobar, duk ka ci gaba da take yi da sake sassauta dokar kullen da take yi da kuma bude harkokin kasuwanci.

    Mamakon ruwan sama da ake fuskanta da kuma ambaliyar ruwa a wasu sassan kasar na daga cikin dalilan da ke kara ta’azzara matsaloli a kasar.

  14. Za a kori 'yan kwallon da suka yi tari a cikin fili

    ‘Yan wasan da suka yi wa ‘yan uwansu tari da gangan ko kuma jami’in wasa za a iya korar su daga fili, in ji hukumar kungiyoyin kwallon kafa FA da kuma mai tsara dokar kwallon kafa.

    Hukumomar Ifab ta ce zai zama laifi idan mutum ya yi amfani da wata alama ta zagi ko wani yare na nuna walakanci ga dan uwansa dan wasa da kuma alkalan wasa.

    Ta kara da cewa “ Amma duk da duka wadan nan laifukan alkalin wasa ne ke da damar yanke hukunci kana bin da yake gani ko gaskiya ne.”

  15. Ma’aikatan MDD sun yi hadarin jirgi a Mali

    Mutum 11 ne suka jikkata ciki harda ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya bayan wani hadarin jirgi, jirgin majalisar ya yi wata mummunar sauka a wuyace a filin jirgin sama na Gao da ke gabashin Mali, in ji MDD.

    Jirgin ya bar babban birnin Bamako ne a safiyar Litinin dauke da ma’aikatan MDD hudu da kuma ma’aikatan jirgin bakwai.

    Jirgin yayi mummunar lalacewa kamar yadda sanarwar majalisar ta bayyana.

    Amma ta ce za a yi bincike domin gano musabbabin hadarin.

    Jacdec wanda ke bibiyar harkokin jiragen sama ne ya wallafa hotunan hadarin jirgin a shafinsa na Twitter.

  16. Za a sake buɗe masallatai a Algeria

    Shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune ya umarci firaiminstansa da ya duba yiyuwar sake bude masallatai a kasar.

    Shugaban kasar, yayin wata tattaunawa da kwamitin tsaro na kasar, ya umarci Firaiminista Abdelaziz Djerad da ya fara mai da hankali kan manyan masallatai da za su iya daukar mutane kamar 1,000.

    Ya na cewa ,manyan masallatai za su bayar da damar ba da tazara tsakanin masu ibada tare da sanya takunkumi.

    Haka kuma firaiministan zai duba yiyuwar sake bude wasu wuraren harkokin jama’a, ciki har da bakin ruwa da wuraren shakatawa domin samar da damar hutawa.

    Tun a watan Maris ne aka rufe masallatai da wuraren shakatawa a kasar a wani mataki na shawo kan annobar korona.

    Algeria dai na da kusan mutum 30,000 da aka tabbatar sun kamu da wannan cuta.

  17. An daina tururuwar shiga jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna

    Kusan mako guda tun da aka ci gaba da jigilar fasinjoji a jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna, mutum 5,000 ne kadai suka yi amfani da jirgin.

    Hakan ya nuna cewa jirgin ƙasan da a baya mutane ke tururuwar shiga, a yanzu babu fasinjoji sosai.

    An rufe tashoshin jiragen kasa a fadin Najeriya na tsawo watanni hudu sakamakon annobar korona.

    Manajan tashar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, Victor Adamu ya bayyana cewa an samu karancin fasinjoji a tashar.

    Kafin cutar korona jiragen na jigilar mutum dubu hudu zuwa biyar a kullum amma a yanzu ana maganar fasinja dubu biyar ne a cikin mako guda.

    Hukumomi a Najeriya sun rage yawan fasinjojin da za a dauka a ko wanne tarago saboda ba da tazara domin kaucewa yaduwar cutar korona.

    Kuma a kara kudin hawa jirgin kasa sakamakon rage yawan fasinjojin da ake dauka.

  18. Wata mata ta haifi 'yan biyar a Somalia

    Wata mata a Somalia ta haifi 'yan biyar a asibitin Recep Tayyip Erdogan da ke Mogadishu, babban birnin kasar.

    Ba kasafai ake haifar 'yan biyar kuma sakon da mahukuntan asibitin suka wallafa ya ce matar da jariranta suna cikin koshin lafiya.

    Ba a bayyana sunan matar ba.

    Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta tattaunawa kan haihuwar, inda suka rika tambaya kan jinsin jariran, halin da iyalinsu ke ciki, da kuma ko za ta iya rainon jariran.

  19. Masu keta dokar kulle za su biya tarar Naira miliyan daya da dubu 300

    Mahukunta a jihar Victoria da ke kudu maso gabashin Australia sun fito da tsattsauran hukunci da za a rika yi wa duk wanda aka samu da kin bin umarnin killace kansa.

    Daga yanzu duk wanda aka kama da irin wannan laifi zai biya tarar kusan dala dubu uku da dari biyar, kwatankwacin Naira miliyan daya da dubu dari uku da ashirin da takwas a kudin Najeriya.

    Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Victoria., Shane Patten, ya ce kusan sau uku ko sau hudu kenan a makon jiya, "muna fasa tagogin motar mutane domin fito da su, saboda kin bayar da sunayensu da bayanansu, ba ma son yin hakan."

    Shi ma gwamnan jihar, Daniel Andrews, ya ce kusan mutane dari takwas ne ke gararamba a gari duk da shawarar da aka ba su ta killace kansu a gida.

  20. Mutumin da aka yi yunkurin halakawa ya tsaya takara a Tanzania

    Jam'iyyar hamayya ta Chadema a Tanzania ta tsayar da fitaccen dan hamayyar kasar Tundu Lissu takarar shugabancin kasar a zaben da za a gudanar a watan Oktoba.

    Ya tsere daga kasar bayan ya tsallake rijiya da baya sakamakon yunkurin da aka yi na halaka shi a Dodoma, babban birnin kasar a watan Satumba na 2017.

    Sai dai ya samu munanan raunuka abin da ya sa aka kwantar da shi a wani asibit da ke kasar Belgium inda ya koma kasar a makon jiya.

    Yanzu zai fafata da shugaban kasar John Magufuli.

    An tsayar da Mr Lissu takara ne bayan ya nunawa abokan hamayyarsa cewa shi mutum ne da zai iya ja da shugaba mai ci.

    Ya samu kuri'a 405 cikin kuri'a 442 da aka kada.

    Mutumin da ya biyo bayansa shi ne tsohon ministan harkokin shakatawa na kasar Lazaro Nyalandu, wanda ya kuri'a 36.