Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotannin kai-tsaye kenan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe da safe idan Allah ya kai mu. Kafin nan za ku iya karanta dukkanin labaran da muka wallafa idan kuka yi ƙasa.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.
Nasidi Adamu Yahaya, Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin kai-tsaye kenan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe da safe idan Allah ya kai mu. Kafin nan za ku iya karanta dukkanin labaran da muka wallafa idan kuka yi ƙasa.
Mambobin Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa a Najeriya (NEC) fannin tsaro za su yi wata ganawa ranar Talata biyo bayan harin da 'yan Boko Haramn suka kai wa Gwamnan Borno Babagana Zulum a Larabar da ta wuce.
Wata wasiƙa da Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya rubuta wa Zulum wadda kuma jaridar Daily Trust ta rawaito a ranar Litinin, ta ce 'yan majalisar za kuma su gana da shugaba Muhammadu Buhari.
Kazalika Gwamna Fayemi wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya ya ce za su gana da hafsoshin tsaron ƙasar domin tattauna abin da ya kira "mummunan yanayi".
Gwamnonin sun kuma nuna goyon bayansu ga Gwamna Zulum da kuma al'ummar Borno game da hare-haren baya-bayan nan.
Gwamna Babagana Zulum ya zargi sojojin Najeriya da yi masa zagon ƙasa bayan wani hari da 'yan Boko Haram suka kai masa, abin da ya sa dole ya bar ziyarar aiki da ya yi niyyar kaiwa garin Baga na Jihar ta Borno.
Daukacin sojoji 98 da suke cikin wani jirgin sama da ya kauce wa hanya ya sauka a cikin tabo sun samu tsira da rayukansu a wani hatsarin da ba a san dalilin afkuwarsa ba.
Haka nan kuma babu wani wanda ya ji rauni.
Sai dai ana cewa jirgin samfurin TJXC 130 ba zai sake yin amfani ba.
Jirgin ya tashi daga birnin Yaounde zuwa garin Maroua ɗauke da sojoji.
A Najeriya, rundunar sojin saman kasar za ta samar da jirage marasa matuka domin karfafa sojoji a yakin da suke yi a shiyyar arewa maso gabas da kuma arewa maso yammacin kasar.
Masana harkokin tsaro da dama sun dade suna jaddada muhimmancin samar da jiragen da sauran kayan yaki na zamani.
Hafsan sojin saman Najeriya, Air Vice Marshal Sadik Abubakar ne ya yi wannan albishir ga sojojin kasar da ke fagen fama, a wajen wata liyafar sallah a Katsina, wadda aka shirya da nufin kara musu kwarin-gwiwa, kuma ana sa ran isowar jiragen nan ba da dadewa ba.
Hafsan ya gargadi `yan bindiga da su tuba, su yada makamansu, saboda suna gab da rasa maboya a cikin dazukan Najeriya.
Tsohon Sarkin Spain, Juan Carlos zai bar ƙasar a cewar fadar masarautar, makwanni bayan an zarge shi da cin hanci.
Juan Carlos mai shekara 82 ya bayyana hakan a wata wasiƙa da ya aike wa ɗansa, Felipe, wanda ya bai wa kujerar mulkin shekara shida da suka wuce.
Ya ce zai bayyana kansa idan 'yan sanda na son su bincike shi.
A watan Yuni ne Kotun Ƙolin Spain ta ƙaddamar da bincike kan zargin wata kwangilar ginin titin jirgin ƙasa a Saudiyya.
Babu tabbacin ko yaushe ne tsohon basaraken zai bar ƙasar ko kuma inda zai koma da zama.
Ɗalibai a birnin Mecklenburg-Western na ƙasar Jamus sun zama na farko da suka koma makarantu a ƙasar tun bayan afkuwar annobar korona.
Ministan Ilimi Anja Karliczek ya yi kira da a samar da takunkumi a cikin makarantu amma dukkanin matakin yana wuyan gwamnatocin jihohi ne.
A lokacin da cutar na kan ganiyarta a Jamus, makarantu sun riƙa yin karatu a tsittsinke ko kuma ta intanet.
Wannan shi ne abin da ya fi kusa da komawa kamar a da kafin annobar.
Fiye da fursunoni 300 ne har yanzu ba a gano ba waɗanda suka tsere daga gidan yarin Afghanistan bayan wani hari da ƙungiyar IS ta kai a garin Jalalabad da ke gabashin ƙasar.
Mahukunta sun ce an kama fiye da fursuna 1,000 tun bayan harin amma har yanzu ba a gano wasu ba.
'Yan bindigar sun kutsa kai cikin ginin ne yayin da wasu daga cikinsu ke tsare da wani kantin sayar da kayayyaki da ke kusa da shi.
Kusan mutum 30 aka kashe mafi yawansu fararen hula tare da 'yan bindigar guda 10.
Gidan yarin na tsare da wasu mayaƙan IS ne da Taliban da kuma sauran masu laifuka, kuma harin na zuwa ne kwana ɗaya bayan jami'an gwamnatin Afghanistan sun ce sun kashe wani babban jagoran IS.
Mutumin nan dan Tanzania da ya taba yin nasarar hako koren dutse mai daraja a kwanakin baya, ya sake yin nasara a karo na biyu.
Saniniu Laizer, ya hako dutse mai nauyin kusan kilo giram 7, wanda darajarsa ta kai kusan shilling biliyan biyar, kwatankwacin Dala miliyan biyu.
An gudanar da gagarumin bikin wannan nasara a wurin hakar ma’adinai da ke Mirerani.
Nasarar da Laizer ya samu ta zama tamkar zaburarwa ga ‘yan uwansa kanana masu hakar ma’adinai bayan samun wata nasarar a karo na biyu.
Sanye da suturar gargajiya ta ‘yan kabilar Maasai, da tsohon takalmi a kafarsa wanda aka yi shi da tayar mota, Laizer ya shaida wa dandazon mutanen da suka zo taya shi murna cewa zai yi amfani da wani banagre na kudin don gina makaranta da asibitin da al’umar yankin za su ci gajiya.
Miloniyan dare daya dai ya fito ne daga kabilar Massai wadanda suka yi fice a fannin kiwo.
A wani mataki na karfafa wa sauran masu hakar ma’adinai gwiwa, ministan albarkatun kasa na Tanzania ya shaida wa mutanen da yawancinsu kananan masu hakar ma’adinai ne cewa su ci gaba da gudanar da aikinsu ba tare da fargabar komai ba saboda gwamnati a shirye take ta sayi abin da suka hako.
Sai dai duk da wannan jawabi wasu daga cikinsu na korafin har yanzu ba a biya su kashi 10 cikin hakkokinsu ba, wasu na ganin ba lalllai ne masu kamfanonin hakar ma’adinai su biya su hakkokin nasu ba.
A watan Yuni da ya wuce ne Laizer ya kafa tarihin samun manyan duwatsu masu daraja da nauyinsu ya kai kilogiram 14 da waya 13, wanda shi ne irinsa mafi girma da aka taba samu a kasar Tanzania.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Borussia Dortmund ta bai wa Manchester United nan da 10 ga watan Agusta a matsayin wa'adi na sayen ɗan wasan gabanta Jadon Sancho.
Ƙungiyar ta Bundesliga ta faɗa wa Man United cewa tana buƙatar aƙalla fan miliyan 100 a kan ɗan wasan mai shekara 20 ɗan ƙasar Ingila.
Har yanzu ba a cimma matsaya ba kan farashi, wanda za a biya lokaci zuwa lokaci.
Dortmund ta saka wa'adin ne saboda ba ta son abin da zai shafi shirye-shiyenta na sabuwar kakar wasa ta 2020-2021.
Wasu masu gadin gidan cin abinci guda biyu sun mutu bayaan sub yi yunurin hana wani ɗan ƙunar bakin wake tayar da bam ɗin da ke jikinsa a Mogadiushu, babban birnin Somalia.
Mai ɗauke da bam ɗin ya tayar da shi bayan masu gadin sun tunkare shi.
Kwastomomi da yawqa sun ji raunin, wanda aka kai a unguwar Hamar Jajab.
Babu wata ƙungiya da ta ɗauki nauyin harin amma ƙungiyar masu ɗauke da makamai ta al-Shabab ta sha kai hare-hare irin waɗannan a kan fararen hula da sojoji.
Hukumomi a Sudan sun ce akalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu kuma wasu dubban gidaje suka ruguje sakamakon ambaliyar ruwan sama a karshen mako.
Ministan cikin gida Eltrafi Elsdik ya ce kimanin gidaje 3,500 ne abin ya shafa, ko dai sun ruguje baki daya ko kuma wani bangare na su.
Mamakon ruwan da ya sauka a makon jiya ya janyo faduwar katangar Blue Nile wanda hakan ya haifar da asarar gidaje sama da 600.
Sudan ta saba fuskantar matsalar ruwa kamar da bakin kwarya tsakanin watan Yuni da Oktoba, wanda ke haifar da gagarumar ambaliyar ruwa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum 70 ne suka hallaka a bara tsakanin wadannan watannin.
Gwamnatin Jamus ta kira zanga-zangar da aka yi a birnin Berlin a karshen mako game da matakan kariyar cutar korona da ta dauka a matsayin “Abin da ba za a amince da shi ba”.
Dubban mutane ne suka fito zanga-zangar "ranar ‘yanci", yayin da masu zanga-zangar ke cewa sanya takunkumi na take hakkinsu da kuma ‘yancinsu.
Ulrike Demmer wanda shi ne kakakin shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel ya ce, masu zanga-zangar da ba su sanya takunkumi ba da wadanda ba su ba kuma su ba da tazara ba ”sun take hakkinsu na damar zanga-zanga”.
Rahotanni sun ce wasu daga cikin masu zanga-zangar na da tunanin cutar Covid-19 din karya ce, akwai kuma sauran mutanen da suka fito zanga-zangar saboda rashin gamsuwa da matakan gwamnati.
‘Yan sanda sun tarwatsa zanga-zangar, suna cewa wadanda suka shirya zanga-zangar ba su mutunta dokokin kariyar da aka shimfida a bi ba. An jikkata jami’ai kuan 45.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa ‘yan sanda sun kama mutum 133 yayin zanga-zangar.
Masu fafutuka a Tanzaniya sun ce sabuwar dokar intanet da aka sanya a kasar, wani bangare ne na take wa al'umma hakkinsu na fadin albarkacin bakinsu.
Karkashin sabuwar dokar, shiryawa ko tsarawa ko kuma goyon bayan duk wani nau'i na zanga-zanga a intanet ya zama haramtaccen abu a kasar.
Sabuwar dokar kuma ta harammta turawa ko kuma yaɗa duk wani labari game da cutar korona ba tare da izinin gwamnati ba.
Masu aiko labarai sun ce dokar kuma ta bayar da damar a gurfanar da mutane kan dun wani abu da suka rubuta ko suka tura a kafafen sada zumunta irin su dandalin Whatsapp.
Masu rajin kare hakkin dan adan sun ce, tun da shugaba John Magufuli ya karbi ragamar kasar shekara biyar baya yake take hakkin kafafen yada labarai da kungiyoyin fararen hula da kuma daidaikun da ke caccakar gwamnati.
Likitoci a Zimbabwe sun ce ana fuskantar karancin ma'aikatan lafiya a kasar yayin da masu cutar korona ke da ɗa karuwa.
Dkta Rashida Ferreand, wata likita ce a wani babban asibiti da ke Harare babban birnin kasar, ta shaida wa BBC cewa likitoci da ma'aikatan jinya kalilan ne ke aiki, sakamakon yajin aiki da ma'aikatan lafiya ke yi a kasar, wanda aka fara tun kafin bullar annobar korona cikin kasar, sannan kuma akwai karancin kayayyakin kariya a asibitocin kasar.
Akwai dai mutum kusan dubu hudu da aka tabbatar sun kamu da cutar korona, inda saba'in daga cikinsu suka mutu, amma likitoci sun ce za a iya samu karuwar masu mutuwa saboda cutar idan aka yi la'akari da halin da ake ciki a kasar.
An sake dawo da jigilar jiragen kasa da kasa a Kenya da Somalia da Rwanda da kuma Togo.
A ranar 1 ga watan Agustan da muke ciki ne aka sake bude filin jiragen kasa da kasa a Kenya duk da fama da cutar korona da ake yi wadda ke ci gaba da karuwa a kasar.
Jirgin farko da ya tashi daga babban birnin kasar Nairobi ya doshi birnin Landan ne.
Haka ita ma Rwanda ta bude filayen jiragenta domin saukar jirage daga kasashen duniya.
Amma a Somalia yau ne aka sake bude filayen jirgin.
Filin tashin jirage na babban birnin Lome na kasar Togo shi ma an sake bude shi ne tun a ranar 1 ga watan Agusta.
Cutar korona ce ta janyo koma baya tare da dakatar da ayyukan jirage daga na cikin gida har na wajen, sai dai kasashe da dama tuni suka dawo da ayyukan jiragen na cikin gida. A yanzu kuma ake ta dawo da ayyukan na kasa da kasa.
Arsenal na son dauko dan wasan Sevilla mai shekara 27 dan kasar Brazil Diego Carlos a yayin da koci Mikel Arteta ke shirin yi wa kungiyar garambawul a bazara.(Telegraph - subscription required)
A cikin wannan makon Arsenal za ta yi tayin bai wa dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31, £250,000 duk mako a yunkurinta rarrashinsa ya zauna a kungiyar.(Mirror)
Sai dai Aubameyang yana so Arsenal ta sayo manyan 'yan wasa kafin ya amince ya sabunta kwangilarsa bayan ya taimaka wa kungiyar wajen lashe Kofin FA karo na 14.(Le10 Sport, via Metro)
An yi wa kocin Tottenham Jose Mourinho tayin dauko dan wasan Watford dan kasar IngilaTroy Deeney, mai shekara 32, domin maye gurbin Harry Kane.(Mail)
Aston Villa na son dauko dan wasan Liverpool mai shekara 25 dan kasar Belgium Divock Origi a bazara.(Sun)
Liverpool ta sha gaban Paris St-Germai na fafatawar da suke yi ta dauko dan wasan Bayern Munich Thiago Alcantara kuma yanzu 'akwai yiwuwar' ta sayo dan wasan na Sufaniya.(Mundo Deportivo, via talkSPORT).
Sama da 'yan Najeriya 7,000 ne aka mayar kasar daga kasashen waje, wadanda suka makale a kasashen duniya daban-daban sakamakon dokar kulle da aka sanya saboda annobar korona.
Ko a ranar 1 ga watan nan da muke ciki sai da Babbar mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin waje da 'yan Najeriya mazauna ketare, Abike Dabiri ta wallafa a shafinta na Twitter cewa jirgi na biyar daga Amurka ya sauka a filin jirgi na Murtala Muhammad da ke Legas, ya kuma sauke mutum 300 wanda hakan yakai adadin mutanen da aka dakko daga Amurkan 1,430
Gwamnatin Najeriya ta ce ta kuma dawo da wasu ma'aikatan lafiya 170 daga wasu kasashen Afrika da suka hadar da Rwanda Uganda da kuma Tanzania.
Duk da cewa an yi musu gwaji an tabbatar ba su dauke da cutar, amma za su killace kansu na tsawon mako biyu domin tabbatar da bin ka'idojin da aka shimfida na yaki da wannan cutar a kasar.
Ya zuwa yanzu Najeriya na da masu cutar korona sama da 43, akwai kuma sama da mutum 22 da ke kwance a cibiyoyin killace masu cutar korona suna jinya a faɗin ƙasar.
Jami'iyyar FPI ta da tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo ke ciki ta ki tsayar da shi a matsayin dan takararta na shugabancin kasar a zaben watan Oktoba mai zuwa.
Ta dauki matakin ne bayan jita-jitar da aka rika yadawa cewa tsohon shugaban kasar Ivory Coast zai iya koma kasar domin kara tsayawa takarar shugabanci.
Mista Gbagbo na zaune ne a Belgium, bayan wanke shi da kotun manyan laifuka ta duniya ta yi daga zargin aikata laifuka a bara.
Babbar jam’iyyar ta dauki tsohon firaiministaMista Gbagbo, Pascal Affi N'Guessan a matsayin dan takararta.
Ana yi wa wannan zaben kallon wata babbar dama ga kasar wajen tsayawa ga kafafuwanta tun bayan yakin farar hula da aka yi shekara 10 da ta wuce.
Hakan ya faru ne sakamakon kin amince da Mista Gbagbo ya yi da ya sauka daga mukaminsa bayan kin yarda da a yi zabe da ya yi.
Ana kallon zaben na watan Oktoba zai zo da turjiya, sakamakon kokarin da shugaban kasar mai ci ya ke yin a ci gaba da mulki, sai dai ‘yan adawa na cewa tsarin mulkin kasar ya haramta masa sake tsayawa takara a karo na uku.
Akwai tsohon shugaban kasar Henri Konan Bedie cikin ‘yan takarar zaben mai zuwa.
Sojoji biyar ne suka mutu a wasu tagwayen hare-hare da aka kai a tsakiyar Mali wadanda ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai su.
Rundunar sojin kasar ce ta wallafa hakan a wani sako a shafinta na Twitter cewa an kai hari kan dakarunta da ke tsakanin yankin Gomacoura da kauyen Diabaly, sai kuma hari na biyu da aka kai sansanin da ke yankin na Gomacoura.
Manyan makamai aka yi amfanin da su aka kai harin, in ji rundunar.
Wasu soji da dama sun samu raunuka haka kuma an lalata motoci da yawa. Tuni aka kara tura wasu dakaru zuwa yankin, in ji sanarwar rundunar.
Har yanzu dai ba a san ko wanene ya kai harin ba.
Mali na ta fama da hare-haren masu ikirarin jihdi, ko a watan Yuni sai da aka kashe mata soji 24 a wasu jerin hare-hare wadanda suka watsu zuwa makwabtan kashe na Burkina Faso da Nijar.
Kasar dai na fama da rikicin siyasa – inda ‘yan hamayya ke kira da shugaban kasar Ibrahim Keïta ya sauka daga mukaminsasaboda gaza kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga da zargin cin hanci da rashawa da ake masa.
‘Yan adawar sun yi watsi da tattaunawar da aka yi a watan jiya wadda shugabannin kasashe biyar daga yammacin Afrika suka halarta.