Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Rikici na barazana ga ƙungiyar Save the Children a Sudan

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Asabar idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ci gaba da bin mu a shafinmu na Facebook ko Twitter ko Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan wasu labaran da muka wallafa, ko kuma tafka muhawara.

    Da fatan za a ci gaba da shagulgulan Sallah lafiya..

  2. Rikici na barazana ga ƙungiyar Save the Children a Sudan

    Ƙungiyar agaji ta Save the Children, ta ce tashin hankalin da ke ta haɓaka a yankin Darfur na Sudan ya tilasta mata rufe wasu asibitocinta biyu da kuma wani ofishinta, wanda hakan ya sa yara 14,000 ba za su rika samun kulawar da suke bukata ba.

    Kungiyar ta ce, wadannan cibiyoyi nata su kaɗai ne suke samar da abinci da kula da lafiyar yara a yankin.

    An kai hare-hare da dama a yammacin Darfur a ‘yan makonnin nan, inda ko a satin da ya gabata, wasu mutane kusan 500 ɗauke da makamai suka far wa yankin Masterei, inda suka kashe sama da mutum 60.

    Gwamnatin Sudan na tura ƙarin dakaru yankin na Darfur a ƙoƙarin dakatar da tashin hankalin, wanda ya raba dubbai da muhallinsu.

  3. Mutum biyu sun mutu a hatsarin jirgin ƙasa a Portugal

    An tabbatar da mutuwar mutum biyu a wani hatsarin jirgin ƙasa da ya faru a ƙasar Portugal.

    Jirgin wanda ya sauka daga layin dogo a gundumar Coimbra ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyu tare da raunata akalla mutum 30.

    Jirgin ya nufi arewa yayin da ya yi karo da wani taragon jirgin gyara a garin Soure.

    Magajin garin Soure, Mário Jorge ya shaida wa kafafen yaɗa labarai na ƙasar cewa lamarin ya faru ne misalin 3:30 na rana.

    Lokacin da hatsarin ya faru, akwai fasinjoji 240 a cikin jirgin wanda shi ne ma fi sauri a ƙasar.

  4. An ɗage zaɓen 'yan majalisa a Hong Kong saboda korona

    An ɗage zaɓen 'yan majalisa a Hong Kong da kusan shekara ɗaya sakamakon ƙara bazuwar cutar korona.

    A baya dai an saka watan Satumbar 2020 a matsayin lokacin da za a gudanar da zaɓen.

    Shugabar gwamnatin yankin na Hong Kong Carrie Lam ta bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne a yunƙurin kare rayukan al'umma.

    Sai dai masu caccakar gwamnatin na ganin cewa an fake da cutar ta korona ne domin hana yin wannan zaɓen wanda zai iya sa gwamnatin wadda ke goyon bayan Beijing ta sha kaye.

    Amurka ma ta yi tir da wannan matakin da Hong kong ɗin ta ɗauka.

    Za a ƙara tura wasu jami'an lafiya daga China zuwa Hong Kong ɗin domin taimakawa wurin yaƙi da cutar korona.

  5. Adadin mutanen da suka mutu a Florida ya girgirza jihar

    Mutum 257 jihar Florida ta ƙididdige sun mutu a sa'o'i 24 da suka gabata - da kuma ƙaruwar masu kamuwa da cutar a kwanaki huɗu a jere.

    Wannan shi ne adadi ma fi yawa da aka taɓa samu sun mutu a jihar tun bayan ɓullar cutar a jihar.

    Sama da mutum 9,000 aka sanar sun kamu da cutar a ranar Juma'a wanda hakan ya kawo adadin waɗanda suka kamu da cutar a jihar ya kai mutum 470,000.

    Florida ita ce jiha ta biyu a yawan masu cutar korona a Amurka.

    Sama da mutum 150,000 suka mutu a Amurka tun bayan bullarta.

  6. Napoli ya sayi ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen

    Ɗan wasan gaban Najeriya Victor Osimhen zai fara shiga gasar Serie A ta Italiya bayan wani kulob na Italiyan ya saye shi.

    Kulob ɗin Napoli dai ya tabbatar da siyan ɗan wasan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

    Ɗan wasan gaban ya ci ƙwallaye 18 a wasanni 38 da ya buga a gasar Ligue 1 a kulob ɗin da ya baro na Lille a kakar 2019-2020.

    Ɗan wasan mai shekaru 21 an haife shi a jihar Legas da ke kudancin Najeriya a ranar 28 ga watan Disambar 1998.

  7. Yadda wasu Alhazai ke aski kafin cire Haramin su

  8. Hajj 2020: Yadda Mahajatta ke jifan shaiɗan

    Mahajatta kenan ke jifan shaiɗan, a garin Mina da ke gabashin birnin Makkah.

    Mahajattan suna jifan shaiɗan ɗin tare da bayar da tazara, saɓanin sauran shekaru da ake yi a cunkushe.

  9. Sojan da ya yi mankas da giya ya harbe mutum 12

    Wani soja da ya sha barasa ya yi mankas, ya buɗe wa wasu fasinjoji wuta a kan hanya a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.

    Rahotanni sun bayyana cewa sojan ya yi ajalin mutum 12 sa'annan kuma jama'a da dama suka samu raunuka.

    Ɗaya daga cikin waɗanda sojan ya hallaka akwai wata yarinya 'yar shekara biyu.

    Wannan lamari dai ya faru ne a ranar Alhamis a kudancin lardin Kivu da ke gabashin ƙasar.

    An daɗe ana zanga-zanga kan sojojin Congo da ke a garin Sange, inda aka toshe hanyoyi da dama.

  10. Yadda aka yi Babbar Sallah a Nijar

  11. Yadda aka yi Sallar Idi a Kamaru

    Al'ummar kasar Kamaru sun bi sahun sauran Musulmin duniya wajen gudanar da Sallar Idi ranar Juma'a.

    Wakilinmu a Yaounde Muhamman Babalala ya aiko mana da hotonan yadda aka gudanar da sallar a wasu masallatan.

    A masallacin Tudun Madarasa, Limam Malam Agouda ne ya shugabanci sallar Idi.

    Haka lamarin yake a masallacin As Salam a unguwar Hausawa ta Briqueterie a Yaoundé.

    Yana daya daga cikin masallatai 11 da aka tantance domin gudanar da sallar idi.

    Dukkan limaman sun yi kira ga al'umma su ci gaba da kula da addini, da kare lafiyarsu a wannan zamani a cutar Covid-19.

  12. An kama fitacciyar marubuciya Tsitsi Dangarembga

    Fitacciyar marubuciya 'yar kasar Zimbabwe Tsitsi Dangarembga ta wallafa sakon da ke cewa jami'an tsaro sun kama ta a Harare, babban birnin kasar.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa masu daukar hoto sun ga lokacin da aka kama ta.

    Ya kara da cewa 'yan sanda sun yi awon gaba da ita da wata mace lokacin da suke zanga-zanga a wajen birnin.

    An ce sunan macen Julie Barnes.

    Marubuciyar ta wallafa hotonsu tare lokacin da aka kama su.

    Jami'an tsaro sun yi ta kai komo a kan tituna suna sanya ido gabanin zanga-zangar kyamar gwamnati da aka shirya gudanarwa kuma mutane sun kauracewa Harare da wasu manyan biranen kasar.

    Dangarembga, wacce a makon nan aka sanya ta cikin wadanda ke takarar lashe gasar rubutu ta Booker Prize da littafinta mai suna This Mournable Body, ta shahara wajen caccakar gwamnati.

  13. COVID-19: Ganduje ya yi kira a dauki matakan kariya

    Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya kira ga al'umma su ci gaba da bin matakan kariya da hukumomin lafiya suka bayar na kare kai daga kamuwa daga cutar coron virus.

    Ya yi kiran ne ranar Juma'a bayan kammala Sallar Idi.

    Kazalika ya yi kira da a ci gava da addu'ar neman zaman lafiya musamman jihohin da ke makwabtaka da jihar kamarsu Katsina, Zamfara, Kaduna, Sokoto da kebbi.

    Gwamnan ya yi sallar Idi ne tare da mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran manyan jami'an gwamnati.

  14. Buhari ya yi Sallah a gida, ya yabi Musulmi da Kirista

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gudanar da Sallar Idi a fadarsa domin yin biyayya ga tsarin kula da lafiya sakamakon annoar korona.

    Shugaban ya kuma yi layya kamar yadda addinin Musulunci ya bukata.

    Tun da farko a sakonsa na Sallah ga 'yan kasar, Shugaba Buhari ya yaba wa Musulmi da Kirsita bisa hakurinsu a wannan lokaci na cutar korona.

    Sakon, wanda kakakinsa Garba Shehu ya aike wa manema labarai, ya ambato shugaban na Najeriya yana yaba wa "Musulmi da Kirista saboda bin dokokin kare kai daga kamuwa da COVID-19 don ya zama riba ga dukkan al'umma."

    “A bangarenmu, za mu ci gaba da fito da hanyoyin da za su sauwakawa mutane radadin da suke ciki sanadin wadannan dokoki," in ji Shugaba Buhari.

  15. Zambia ta soke gasar lig sakamakon cutar korona

    Hukumar kwallon kafar Zambia, Faz, ta soke gasar lig sakamakon ci gaba da yaduwar cutr korona.

    Sakatare Janar Adrian Kashala ya ce za a kammalar gasar lig ranar 6 ga Agusta yadda kafin lokacin duukan kungiyoyin kwallon kafar kasar sun kammala wasanni 27.

    An koma wasan lig ne mako biyu da suka wuce bayan an dakatar da gasar a watan Maris sakamakon annobar korona.

    Kungiyoyin kwallon kafa biyu, Forest Rangers da Napsa Stars, sun bayar da rahoton samun masu dauke da cutar korona sosai a tsakaninsu, inda daya ke da mutum 28 yayin da dayar ke na mutum 19.

    “Yaduwar da cutar korona ke ci gaba da yi a kwanakin nan ta yi tasiri sosai kan harkokin lafiyar kasar,” in ji sanarwar da Mr Kashala ya fitar.

    Mr Kashala ya kara da cewa hukumar kwallon kafar ta yanke shawarar cewa za a soma kakar wasa ta 2020/2021 ranar 17 ga watan Oktoba.

    Kawo yanzu mutum 5,555 C aka tabbatar sun kamu da cutar korona a Zambia inda ta yi ajalin mutum 41.

  16. Jimenez zai tafi Man Utd, Bale zai ci gaba da zama a Madrid

    Dan wasan gaban Mexico Raul Jimenez, mai shekara 29, yana kan hanayarsa ta zuwa Manchester United bayan Wolves ta amince da yarjejeniyar £27m domin dauko dan wasan Braga dan kasar Portugal mai shekara 27 Paulinho.(RTP, via Express)

    Tsammanin da ake yi wa Jadon Sancho na tafiya Manchester United ya matso kusa, a yayin da Borussia Dortmund ta ce za ta yarda da tayin farko na £60m da aka yi mata kan dan wasan na Ingila mai shekara 20.(Independent)

    Chelsea ta gabatar da bukatarta ta dauko golan Barcelona dan kasar Jamus mai shekara 28 Marc-Andre ter Stegen.(Cadena Ser, via Mail).

    Latsa nan don karanta cikakken labarin wasannin.

  17. 'Cutar korona ta yi ajalin minista a Zimbabwe'

    Rahotanni sun ambato shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa yana cewa cutar korona ce ta yi ajalin Ministan Harkokin Gona na kasar Perence Shiri.

    Ya bayyana haka ne ga taron mutanen da ke alhinin mutuwar ministan, wanda ya jagoranci kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe.

    Jaridar Herald ta gwamnatin kasar ta ambato Shugaba Mnangagwa yana cewa sakamakkon gwajin da aka yi wa ministan ya nuna cewa yana dauke da cutar korona gabanin rasuwarsa.

    Za a binne Mr Shiri a yau Juma'a bisa dokokin Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya, a cewar shugaban kasar.

    Ministan mai shekara 65 ya mutu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke Harare, babban birnin kasar ranar Laraba.

  18. Ganduje ya sa Malamai 300 su yi addu'a ta kan cutar korona

    Gwamnatin jihar Kano da ke Najeriya ta shirya wata addu’a kan cutar korona da kuma matsalar tsaron da ake fama da ita a wasu makobtan jihar.

    An gudanar da taron addu’ar an gudanar da shi ranar Alhamis ne a fadar gwamnatin Kano.

    Malamai kusan 300 ne suka halarci gabatar da addu'ar.

    Khalifa Shehu Dokaji ya tambayi Mallam Mohammed Garba, Kwamishinan Yaɗa Labarai na gwamnatin jihar Kano manufar yin addu'o'in a wannan lokaci.

    Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraren rahoton:

  19. An sallami Sarki Salman na Saudiyya daga asibiti

    Sarki Salman na Saudiyya ya bar asibiti da ke birnin Riyadh bayan shafe kwana 10 yana samun kulawar likitoci.

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta wallafa wani hoton bidiyo a shafinta na Twitter da ke nuna lokacin da Sarkin ke barin asibitin inda yake dogara sanda.

    Ya samu rakiyar wata tawaga da ta haɗa da ɗansa Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman.

  20. Barka da Sallah

    Daga nan Sashen Hausa na BBC muke yi muku barka da Sallah.

    Da fatan kun wayi gari lafiya. Ku kasance tare da mu a duk wannan rana domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman game da bukukuwan Sallah, da aikin Hajji, da ma sauran labaran da suka shafi rayuwarku.

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake tare da ku.

    Kuna iya tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.