Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Erdogan ya ziyarci Hagia Sophia kafin fara Sallar Juma'a mako mai zuwa

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter domin duba wasu labaran da kuma tafka muhawara.

  2. Iran ta dakatar da hukuncin kisa ga wasu mutum uku

    Iran ta dakatar da zartar da hukuncin kisa ga wasu mutum uku da aka same su da laifin shiga cikin mummunar zanga-zangar ƙin jinin ƙarin kuɗin man fetur a watan Nuwambar bara.

    Daya daga lauyoyinsu ya ce an amince da buƙatarsu ta sake yi musu shari'a.

    Matakin ya soke hukuncin da Kotun Ƙolin kasar ta yanke a makon jiya, wanda ya tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke musu.

    Hukuncin ya harzuka mutum miliyan bakwai suka shiga wani gangami na Internet suna masu adawa da shi, abin da masu sharhi ke cewa ya nuna irin yadda hukumomi suke sassautowa kan al'amura.

  3. Erdogan ya ziyarci Hagia Sophia kafin fara Sallar Juma'a mako mai zuwa

    Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci Hagia Sophia a birnin Santanbul kwanaki kaɗan gabanin Musulmi su fara sallah a cikinsa, karon farko tun shekarun 1930.

    Shugaban ko da ya isa wurin, ya duba yadda ake shirye-shiryen Sallar Juma'a a masallacin wadda ake sa ran fara yi ranar 24 ga watan Yuli.

    A farkon watan nan ne Mista Erdogan ya sanya hannu kan wata doka cewa an mayar da wajen masallaci, bayan wata kotu ta soke matsayinsa na gidan tarihi.

    Matakin ya janyo caccaka daga Kungiya Tarayyar Turai, da Asusun Kula da Ilimi da Fasaha da Al'adu na Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO da ma Kiristoci da dama.

    An dai gina Hagia Sophia ne a matsayin cocin Kiristoci, kafin daga baya a mayar da ginin masallaci a ƙarni na 15, a zamanin Dular Usmaniya.

  4. Waɗanda korona ta kashe a Amurka sun haura 140,000

    Adadin mutanen da suka mutu a Amurka saboda cutar korona ya zarta 140,000 - kusan kashi ɗaya cikin hudu na yawan wadanda cutar ta yi ajalinsu a duniya.

    Sai dai Shugaba Trump ya yi watsi da shaidu (daga jami'ar Johns Hopkins) da ke nuna cewa Amurka ce ƙasar da aka fi mutuwa daga cutar korona a duniya.

    A wata hira da gidan talabijin na Fox News, Trump ya kafe cewa kasarsa ɗaya daga cikin ƙasashen da cutar ba ta yi kisa ba.

    Ya ce ƙaruwar masu cutar da ake ganowa a yanzu yana da dangantaka ne da ƙarin gwaje-gwaje da ake yi.

  5. Masu sasanci sun ba da shawarar kafa gwamnatin haɗin gwiwa a Mali

    Masu shiga tsakani da ke ƙoƙarin sasanta rikicin Mali sun bayar da shawarar kafa gwamnatin haɗin gwiwa da kuma kotun tsarin mulki, duk a yunƙurin kawo sasanci tsakanin 'yan adawa da shugaban ƙasar Boubakar Keita.

    Sai dai 'yan adawa a ƙasar sun ƙi amincewa da wannan yunƙuri sakamakon ko a baya ma sai dai shugaban ƙasar ya yi musu irin wannan alƙawari.

    A makon da ya gabata ne dai masu shiga tsakani daga Yammacin Afrika ciki har da Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan suka je ƙasar domin kawo sasanci.

    An daɗe ana zanga-zanga a ƙasar inda masu zanga-zangar ke buƙatar shugaban ƙasar ya sauka sakamakon gazawarsa wurin daƙile ta'addanci da cin hanci da rashawa da kuma matsin tattalin arziƙi na Mali.

  6. An kama sama da matasa 50 da suka je wani casu a Bolivia

    'Yan sanda a Bolivia sun kama sama da matasa 50 yayin wani casu da ya gudana a birnin Santa Cruz, wanda ke da masu cutar korona da yawa sama da ko ina a ƙasar.

    'Yan sanda sun ce casun da aka shirya ya gudana ne a wani ɓoyayyen gida, kuma an shirya shi ne ta kafar sada zumunta domin kauce wa tarkon mahukunta.

    Sama da mutum 56,000 ne aka tabbatar suna ɗauke da cutar a Bolivia, ciki har da shugaban kasar na riƙon kwarya Jeanine Áñez, da wasu manyan ministoci.

    Lardin na Santa Cruz shi ne ke da rabin masu cutar da aka ruwaito ƙasar na da su.

  7. Da alamun taron EU ba zai cimma matsaya ba

    Shugabannin Tarayyar Turai suna wani taro a birnin Brussels, domin shawo kan rarrabuwar kan da ke tsakaninsu na yadda nahiyar za ta farfado bayan annobar korona.

    Tattaunwar - wadda ta hadar da kasafin kudin tarayyar mai tsawo na gaba -- ta tsallaka zagaye na uku -- na ranar da ba a tsara da ita ba.

    Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi gargadin cewa shugabannin ba za su iya cimma yarjejeniyar ba a yau.

  8. Kotu a Congo ta ɗaure tsohon magajin garin Brazzaville

    Wata kotu a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo ta ɗaure tsohon magajin garin Brazzaville wato Christian Okemba.

    Kotun ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyar sakamakon samunsa da laifin cin hanci.

    An zabi Christian Okemba a matsayin magajin gari shekaru uku da suka gabata, kuma an zarge shi da tura kuɗin ƙasa da suka kai dalar Amurka miliyan biyu zuwa asusun ajiyar bankinsa.

    Sai dai lauyansa ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ta yanke.

  9. Covid-19: Sama da mutum 105,000 'yan sanda suka kama a Zimbabwe

    'Yan sanda a Zimbabwe sun bayyana cewa sama da mutum 105,000 suka kamu tun bayan fara kullen annobar korona a watan Maris a ƙasar.

    Duk da an sassauta dokar kullen a Zimbabwe, duk da haka ana zargin mutane da dama da karya doka.

    Wani mai magana da yawun 'yan sanda a ƙasar ya ce a kwanaki biyu da suka gabata, sama da mutum 1,000 aka kama sakamakon laifin ko dai rashin saka takunkumi ko kuma zirga-zirga ba tare da dalili ba.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama na zargin gwamnatin Zimbabwe da amfani da dokar kulle domin musgunawa 'yan adawa da kuma kama 'yan gwagwarmaya - abin da gwamnatin ta musanta.

    Duk da matsin tattalin arziƙi da ake fama da shi a ƙasar, ana ci gaba da kira kan a fito zanga-zanga a ƙasar.

    Sai dai da alama Shugaba Emmerson Mnangagwa ba zai lamunci caccaka ba, kuma idan mutane suka fito zanga-zanga za a kama da dama daga cikinsu.

  10. Turkiyya ta dakatar da jiragenta daga zuwa Iran

    Ƙasar Turkiyya ta dakatar da jiragenta daga zuwa Iran sakamakon ƙara bazuwar cutar korona a ƙasar.

    An ruwaito mai magana da yawun hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Iran Reze Jafarzadeh na cewa an ɗauki wannan matakin ne sakamakon fargabar korona.

    Mutum 209 suka mutu a rana guda a Iran ɗin, tare da wasu sabbin mutum 2,182 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

    Sama da mutum 14,000 cutar ta kashe a ƙasar tun bayan ɓullarta.

    Jiragen Turkiyya sun ci gaba da zuwa Iran tun a ranar 11 ga watan Yuni bayan dawo da jigilar jirage a ƙasar.

  11. Labarai da dumi-dumi, Ministan harkokin wajen Najeriya ya kamu da korona

    Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya kamu da cutar korona.

    Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter inda ya ce an tabbatar da ya kamu da cutar bayan an yi masa gwajin cutar karo na hudu.

    A saƙon da ya wallafa, ministan ya ce a yanzu haka ya kama hanyarsa ta zuwa wurin killace masu ɗauke da cutar.

  12. Benjamin Netanyahu ya fada tsaka mai wuya

    Za a fara sauraren karar Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a farkon shekara mai zuwa.

    Mai shari'ar da ke sauraren karar Rivkah Friedman Feldman yayin zaman na yau ya ce za a kirawo shaidar farko da zai zo ya bayyana a bin da ya sani kan wannan shari'a a watan Janairu.

    Tuhuma uku ake yi wa Mista Netanyahu wadanda suka hadar da cin hanci da rashawa da zamba da kuma ha'inci.

    Lauyan da ke kare Netanyahu wanda bai halarci zaman kotun ba na yau, ya nemi da a dage zaman kotun saboda annobar korona.

    Ya karyata zargin cewa ya yi alfarma domin a ba shi kyautuka da kuma samun goyon bayan 'yan jarida.

    A ranar Asabar ne daruruwan mutane suka taru a wajen gidan Netanyahu da ke birnin Jerusalem, suna kira da ya sauka daga mukaminsa.

  13. Halin da ake ciki kan annobar korona a duniya

    An tabbatar da mutum sama da miliyan 14 da ke dauke da wannan cuta yayin da wadanda suka mutu dalilin cutar suka haura 600,000 tun kan annobar ta gama bayyana, in ji bayanan jami'ar Johns Hopkins mai bibiyar sha'anin korona.

    Ga wasu bayanai kan halin da wasu kasashen duniya ke ciki a yau Lahadi:

    • An samu mutuwar mutum58 a Philippines kuma karin 2,2,41 sun kamu
    • Mutum uku ne kacal suka mutu a Australia, wanda yakai adadin matattun 122
    • Karin mutum 95 sun hallaka a Rasha kuma sabbin 6,109 sun kamu
    • 16 ne suka sake kamuwa a China, 13 kuma a lardin Xinjiang
    • A Hong Kong sabbin mutane 108 ne suka kamu
    • Pakistan ta ce mutum 46 sun mutu kuma 1,579 sun kara kamuwa, in ji kamfanin dillancin labarai na PTI
    • Mutum 209 sun kara mutuwa a Iran, 2,182 kuma sun kamu da cutar in ji hukumomi
  14. Rasha ce ke ƙoƙarin yi wa Buratniya kutse - Dominic Raab

    Sakataren Burtaniya Dominic Raab ya kara nanata zargin da ake yi wa Rasha na kokarin kutse domin satar muhimman bayanai kan kokarin samo rigakafin annobar korona, ya na bayyana hakan a matsayin wani abin mamaki kuma abin alawadai.

    Ya zargi Rasha da cin dunduniyar hadin kan duniya na samar da rigakafi, yana cewa da alama kasuwanci ta ke son mayar da wannan abu.

    Mista Raab ya yi watsi da musantawar da jakadan Rasha a Burtaniya Andrei Kelin ya yi kan wannan kutse.

  15. Jami'an lafiya a Iran sun yi watsi da ikirarin Rouhani kan yawan masu korona

    Mutum 209 sun mutu a Iran yayin da wasu 2,182 suka kamu da cutar korona ciki kwana guda.

    A cikin sabbin mutanen da aka yi wa gwaji an kwantar da 1,324, in ji mai magana da yawun ma'aikatar lafaiya na kasar.

    Ana ta shawartar mutane da su guji taruwa waje guda, subi dokokin da aka shimfida na ba da tazara da sanya takunkumi.

    A jiya ma shugaban kasar Hassan Rouhani ya ce mutum miliyan 25 ne suka kamu da wannan cuta a kasar.

    Ya kuma yi gargadin cewa wasu karin miliyan 35 ka iya kamuwa nan da 'yan watanni masu zuwa.

    Sai dai a yau dinnan jami'an lafiya sun yi watsi da ikirarin na shi suna cewa, wannan adadin na wadanda aka gwada ne a wani mataki na gano cutar wanda kuma ba za a dogara da shi ba wajen bayyana halin da ake ciki yanzu.

    A ranar Juma'a ministan lafiya na Iran ya ce mutane 13,791 ne suka mutu ta sanadin cutar.

  16. An sanar da sabbin dokokin kulle a Hong Kong

    A bayan mun kawo muku rahoton cewa Hong Kong ta samu karin sabbin masu cutar korona 100.

    Shugaban gwamnatin yankin Carrie Lam ta sanar da cewa yanzu za a rika yin gwajin masu cutar 10,000 a ko wacce rana.

    Ta kuma sanar da cewa hukumomi za su mayar da sanya takunkumi wajibi a bainar jama'a.

    Tuni dama aka sanya dokar sanya takunkumin a wajen ababan hawan jama'a.

    A makon da ya gabata ne gwamnati kasar ta dawo da dokar ba da tazara, tare da wuraren shan barasa, da na motsa jiki da kungiyoyin.

    Kuma an kara tsawaita dokar kullen a yanzu.

  17. Cutar korona ta ƙara ɓulla a jihar Zamfara

    Hukumar da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta sanar da mai dauke da cutar korona na farko a Zamfara tun bayan sanar da kawo karshenta a jihar.

    Mutumin na cikin karin sabbin mutum 653 da hukumar ta snaar a daren a sabar cewa suna dauke da wannan cuta.

    Kamar yadda ta saba wallafawa a shafinta na tuwita ko wacce ranar hukumar ta bayyana jihar zamfara da Cross River da Borno da Yobe a matsyin jihohin da suka samu karin mutum duga a ranar Asabar.

    Sai dai a gefe guda kuma, hukumomin lafiya a jihar ta Zamfara sun nuna tababa kan wannan batu.

    Yahaya Muhammad Kanomana shi ne kwamishinan lafiya na jihar, a wata hira da ya yi da BBC ya ce wannan mutumi ba a Zamfara ya kamu da wannan cuta ba zuwa ya yi da ita daga kasar Malesiya.

    Ya ce mara lafiyar ne ya kai kansa ga jami'an lafiya na Zamfara domin a yi masa gwaji, daga baya kuma aka tabbatar yana dauke da cutar.

    "Ba mu killace shi ba, amma mun fara bibiyar wadanda ya yi mu'amala da su, nan gaba za mu kai shi cibiyar killace marasa lafiya ta Yariman Bakura."

    Zamfara ce dai jiha ta farko a Najeriya da ta bayyana kawo karshen annobar korona a kasar, kafin daga bisani wasu jihohin da ba su fi biyu ba suna su yi irin wannan ikirari.

    Masu dauke da cutar korona a Najeriya yanzu sun kai 36,107 kuma mutum sama da 14,000 sun warke yayin da 778 suka mutu sanadiyyar wannan annoba.

  18. Buɗewa

    Masu biyayarmu da fatan an wayi gari lafiya, Buhari Muhammad Fagge ne ke muku barka da wannan lokaci.

    Ku kasance da mu domin kawo muku labarai da rahotanni da suka shafi Najeriya da Nijar da Kamaru har ma da Chadi.

    Ciki za mu kawo muku labaran sauran nahiyoyin duniya baki daya.