Shugaban Senegal Macky Sall ya ce za a janye dokar hana fita da aka sanya a kasar sakamakon bullar cutar korona daga yau Talata.
Cikin jawabin da ya yi ta talbijin, shugaban ya kuma sanar da bude tashoshin jiragen sama daga 15 ga watan Yuli amma tare da sanya tsauraran matakan kariya.
Mr Sall ya kuma yi gargadin cewa ci gaban tattalin arzikin zai kasance cikin tafiyar hawainiya daga kashi 6.8 cikin 100 zuwa kashi 1.1 cikin 100 saboda illar da annobar korona ta haifar.
Ya yi kira ga mutane su koma gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba domin tada komadar tattalin arzikin kasar.
Ma'aikata za su fara aiki daga karfe 8:00 na safe zuwa karfe 5:00 na yamma amma wuraren shakatawa za su ci gaba da zama a rufe.
Haka nan za a ci gaba da rufe kasuwanni sau daya a sati domin tsaftace su. Sanya takunkumin fuska kuwa dole ne a bainar jama'a da ofisoshi da tashoshin mota da shaguna.
A yanzu haka shugaban na killace na tsawon makwanni biyu bayan ya yi mu'amala da wani da ya harbu da korona. Killacewar za ta zo karshe ne a mako mai zuwa.
Ya zuwa yanzu kasar ta Senegal ta tabbatar da mutum 6698 da suka kamu da cutar, 108 kuma sun mutu.