Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'An kashe sojoji 20 da farar hula 40 a Borno'

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau:

    • Mutane na gudun hijira a yankunan Katsina
    • Rasha da Turkiyya za su tattauna kan rikicin Libya
    • An iske jarumin Bollywood Singh Rajput a mace a gidansa
    • Saudiyya za ta yanke shawara kan makomar hajjin 2020
    • Cutar korona ta kashe mutum 100 a rana ɗaya a Iran
    • Za a fara killace masu korona a taragon jirgin ƙasa a Indiya
    • Buhari ya bayar da umarnin shuka bishiyoyi miliyan 26 a arewacin Najeriya
    • Jami'ai sun rufe rukunin shagunan Jabi a Abuja
    • 'An kashe sojoji 20 da farar hula 40 a Borno'

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta labaran da wasu muhimmai:

  2. An yi garkuwa da mata 10 a Mozambique

    Rahotanni daga arewacin Mozambique na cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da a ƙalla yan mata goma, a wani hari kusa da garin Mocimboa da Praia.

    Tun a ƙarshen shekarar 2017 ne aka fara kai hare-hare a yankin Cabo Delgado mai arziƙin iskar gas da ke kan iyakar Tanzania.

    Ba wannan ne karo na farko ba da masu iƙirarin jihadin ke sace mata ba.

    Akasarin hare-haren da ake kai wa a arewacin na Mozambique ƙungiyar IS ce ke ɗaukar nauyin su.

  3. 'An kashe sojoji 20 da farar hula 40 a Borno'

    A kalla sojoji 20 da farar hula sama da 40 aka kashe a wasu tagwayen hare-hare da aka kai a jihar Borno da ke arewacin Najeriya.

    Mazauna yankin sun shaida cewa 'yan bindiga masu ɗauke da muggan makamai ciki har da na harba roka suka shiga garin Monguno, wanda a nan matattarar ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasashen waje suke.

    Hare-haren da aka kai a Monguno da Nganzai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan 'yan tayar da ƙayar baya sun kashe a kalla mutum 81 a wani hari da suka kai a ƙauyen Gubio. Kungiyar ISWAP wadda ke iƙirarin jihadi a ƙasashen yammacin Afirka ta fito fili ta ɗauki nauyin kai duka hare-haren uku.

    A garin Mongunu, wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana cewa mayaƙan sun ƙone matattarar hukumomin bayar da agaji na Majalisar Dinkin Duniya tare da kuma ƙona wani ofishin 'yan sanda.

    A garin Nganzai, mayaƙan sun shiga garin ne kan babura da kuma motoci ƙirar akori kura inda suka kashe mazauna ƙauyen fiye da 40.

    Rahotanni sun bayyana cewa ɗaruruwan farar hula ne aka raunata inda kuma asibitin garin ya cika maƙil har ake tilasta wa wasu masu raunuka da su tsaya a waje.

    Mayaƙan sun rarraba takardu ga mazauna garin mai ɗauke da gargaɗi inda aka yi rubutun da Hausa, suka gargaɗe su da kada su yi aiki da sojoji ko kuma ƙungiyoyin bayar da agaji na ƙasashen waje.

    Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da kai wannan harin a wata sanarwa da ta fitar.

    Sai dai a wani ɓangaren sojojin Najeriya sun mayar da martani kan wannan hari inda suka jinjina wa sojojin ƙasar bisa namijin ƙoƙarin da suka yi wurin daƙile harin da aka kai a Mungonu. Sanarwar da sojojin suka fitar ta ce babban hafsan sojojin ƙasa na Najeriyar ya ji daɗi matuƙa kan yadda sojojin suka yi fatafata da mayaƙan da kuma ƙwato wasu makamansu.

  4. Jami'ai sun rufe rukunin shagunan Jabi a Abuja

    Kwamitin da ke yaƙi da cutar korona a Abuja babban birnin Najeriya ya kulle rukunin shagunan sayar da kayayyaki na Jabi wanda aka fi sani da Jabi Lake Mall.

    Hukumar gudanarwa ta birnin tarayya ce ta sanar da hakan a shafin Twitter inda ta ce an ɗauki wannan matakin ne bayan saɓa dokokin da kwamitin shugaban ƙasa ya kafa na yaƙi da cutar.

    Ɗaya daga cikin abubuwan da ya sa aka kulle rukunin shagunan har da saɓa dokar taron jama'a.

  5. Buhari ya bayar da umarnin shuka bishiyoyi miliyan 26 a arewacin Najeriya

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin shuka bishiyoyi miliyan 26.

    Ya bayar da umarnin ne ga hukumar da ke kula da shuka itatuwa a yankunan da ke da barazanar kwararowar hamada.

    Shugaban ya bayar da umarnin ne domin ciki alƙwarin da ya ɗauka na shuka bishiyoyin a yayin taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 74.

    Za a shuka bishiyoyin ne a jihohi takwas na arewacin Najeriya da suka haɗa da Borno da Jigawa da Katsina da Sokoto da Yobe da Kebbi da Kano da kuma Zamfara.

  6. Za a fara killace masu korona a taragon jirgin ƙasa a Indiya

    Gwamnatin Indiya ta kira taron gaggawa na duka shugabannin jam'iyyun ƙasar wanda za a yi a gobe Litinin don tattauna yadda za a shawo kan cutar korona a birnin Delhi.

    Ministan cikin gida na ƙasar Amit Shah ya bayyana cewa za a yi amfani da taragai 500 na jirgin ƙasa domin samun wuraren da za a kwantar da mutum 8,000 a babban birnin ƙasar.

    A ranar Juma'a, Kotun Koli ta ƙasar ta caccaki Delhi da wasu jihohi uku kan cewa ana wulakanta masu ɗauke da cutar korona kamar dabbobi.

    Akwai rahotanni da ke cewa marasa lafiya na zuwa asibiti daban-daban domin neman wurin kwanciya.

    A halin yanzu, sama da mutum dubu tara cutar ta kashe a Indiya, inda ake samun sabbin mutane kusan dubu 12 da ke kamuwa da cutar a kullum.

  7. Ƴan a ware sun ƙwace miliyoyin daloli a Babban Bankin Yemen

    Ƴan a ware a Yemen sun ƙwace roron kuɗi kimanin dala miliyan ɗari biyu da hamsin da aka gabatar wa Babban Bankin ƙasar.

    Babban Bankin ƙasar Yemen ya ce wani ayarin ƴan a ware ne ya kwashi kuɗin inda mayaƙan suka fice ta tashar ruwan Aden a ranar Asabar tare da yin gargaɗi kan mummunan hatsarin da zai biyo baya.

    Ana tunanin a Rasha aka buga kuɗin a aka ɗauko a hanyar ruwa zuwa Babban Bankin Yemen.

    Ƴan a waren da ke suka yi iƙirarin kafa gwamnati a yankin kudancin Yemen a watan Afrilu sun ce sun ƙwace ƙudin ne da nufin hana cin hanci da rashawa.

  8. Cutar korona ta kashe mutum 100 a rana ɗaya a Iran

    Gwamnatin Iran ta ce sama da mutum 100 cutar korona ta kashe a rana ɗaya, wanda shi ne karon farko da yawan masu cutar ya haura mutum ɗari tun watan Afrilu.

    Ma'aikatar lafiya ta Iran ce ta sanar da sabbin alƙalumman inda ta ce mutum 107 suka mutu cikin sa'a 24.

    Yanzu adadin kusan mutum 9,000 cutar ta kashe a Iran.

    A watan Fabrairu cutar ta fara ɓulla a Iran a birnin Qom lamarin da ya sa gwamnati ta kafa dokar kulle kafn ta sassauta a watan Afrilu saboda taɓarɓarewar tattalin arziki.

  9. Saudiyya za ta yanke shawara kan makomar hajjin 2020

    Ministan harakokin lamurran addini da kuma haɗin kan addinai na Saudiyya Sahibzada Noor-ul-Haq Qadri ya ce a ranar Litinin ne 15 ga watan Yuni gwamnatin ƙasar za ta yanke shawara ta ƙarshe game da makomar Hajjin 2020.

    Da yake bayani a wani taron tuntuba a ranar Alhamis, ministan ya ce gwamnatin Saudiyya za ta ɗauki matakin da ya fi dacewa saboda maniyyata aikin Hajji, sannan gwamnatin ta daɗe tana nazari tare da duba hanyoyi da dama game da aikin Hajjin.

    Ya ce ana ci gaba da maharawa game da yadda za a tafiyar da aikin Hajjin a ma’aikatarsa, yana mai cewa Hajjin ba za ta kasance kamar yadda aka saba ba domin za a rungumi matakai na kaucewa yaɗuwar cutar korona.

    Ma’aikatar lamurran addinin ta Saudiyya ta kuma ce ta bayar da umurni bincike kan ƙiyasin kuɗaɗen aikin hajji, idan har Saudiyya ta yanke shawarar taƙaita yawan maniyyatan da za su yi aikin Ibadaar da kuma adadin kwanakin da mahajjaci zai yi.

  10. Buhari ya faɗa muna ina kuɗaɗen da ya ƙwato suka shiga - SERAP

    Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a Najeriya ta buƙaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da ƴan Najeriya sunayen mutanen da suka sace naira biliyan 800 da ya ce gwamnatinsa ta ƙwato.

    Ƙungiyar ta ce ta aika wa shugaban wasika ne ta neman bayanai game da sanin waɗanda suka sace ƙuɗaden da kuma abin da gwamnatinsa ta yi da kuɗin da kuma lokacin da aka ƙwato kuɗaɗen.

    Ta kuma buƙaci shugaban ya ba hukumomin yaki da cin hanci da rashawa umurnin ƙaddamar da bincike kan zargin da ta yi cewa an raba wa wasu mutane kimanin naira biliyan 51 daga cikin kuɗaden da da gwamnati ta ce ta ƙwato.

    Zuwa yanzu babu wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban ƙasa game da buƙatar da ƙungiyar ta ce ta aika wa shugaban ƙasa.

    A sanarwar da ta wallafa a shafinta, ƙungiyar ta ce, "shugaban ƙasa ne da kansa a jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya ya bayyana cewa hukumomin da ke yaƙi da cin hanci da rashawa sun kwato sama da naira biliyan 800."

    Ƙungiyar ta ce bayanan da ta ke nema za su tabbatar da gaskiya kan inda ƙuɗaɗen suke tare da ba ƴan Najeriya damar fahimtar tasirin ayyukan da aka gudanar da kuɗaɗen.

  11. An iske jarumin Bollywood Singh Rajput a mace a gidansa

    Ƴan sanda a Indiya sun ce sun iske ɗaya daga cikin fitattun jaruman Bollywood Sushant Singh Rajput a gidansa da ke Mumbai

    Suna tunanin jarumin mai shekara 34 ya kashe kansa ne wanda aka ruwaito kafin mutuwarsa cewa yana fama da da matsalar damuwa.

    Ya fito a fina-finai kamar Kai Po Che and M.S Dhoni -- tarihin ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan kuriket a Indiya.

    A kwanakin da suka gaba ne kuma aka isko gawar manajan jarumin Disha Salian a mace.

    Abokan sana'arsa da kuma masoyansa da dama ne suka yi jimamin rashinsa a Twitter tare da yin ta'aziyya ga iyalinsa.

  12. Rasha da Turkiyya za su tattauna kan rikicin Libya

    Ana sa rai ministocin wajen Turkiyya da na Rasha za su tattauna kan ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin da ake gwabzawa a Libya, yayin wata ganawa da za su yi ranar Lahadin nan a birnin Istanbul.

    Gwamnatin birnin Ankara da takwararta ta Moscow na goyon bayan ɓangarori daban-daban na rikicin, wanda ya yi sanadin raba dubun dabatar mutane daga gidajensu tun daga watan Afrilun bara.

    Turkiyya na mara baya wa gwamnati mai sansani a Tripoli, babban birnin ƙasar, yayin da Rasha ke goyon bayan Janar Khalifa Haftar, wanda ya fuskanci ɓacin rana cikin ƴan makwannin nan a hannun dakarun gwamnati.

    Duka Turkiyya da Rasha a baya-bayan nan sun ce suna son ɓullo da wnai yanayi na tattaunawa da sasanta tsakani.

  13. Mutane na gudun hijira a yankunan Katsina

    Al'ummomin ƙauyukan yankin Katsina musamman mata da yara na ci gaba da tserewa daga gidajensu saboda ƴan fashin daji da suka addabe su da hare-hare.

    Wani mazaunin yankin Hassan Mohammed Daudawa ya shaida wa BBC cewa mutanen sun koma rayuwa a cikin azuzuwan wasu makarantun Boko na yankin Funtua da sauran yankunan da ba a cika kai hare-hare ba.

    A ƴan kwanakin nan ƴan bindiga masu fashin daji sun tsawwala hare-hare a yankunan karkara na Katsina inda ko a ranar Juma'a sun shiga garin Mazoji na karamar hukumar Matazu suka kashe Mai Garin Papu Alhaji Dikko Usman Mazoji bayan sun kashe Hakimin Ƴantumaki a makon da ya gabata wanda ya haifar da zanga-zanga a garin.

    Maharan sun kuma sun kuma shiga garin Ƴankara da sauran kauyuka a karamar hukumar Faskari da kuma wasu ƙauyuka na Batsari inda suka kashe mutane suka kuma tafi da wasu da dabbobi.

    Ga Hirar Abdou Halilou da Hassan Mohammed Daudawa

  14. NCDC na son a kaucewa shiga taron da ya haura mutum 20

    Hukumar da ke daƙile cutuka masu yaduwa a Najeriya ta ce shiga taron mutane ne ke ƙara bazuwar cutar korona.

    Hukumar ta yi kira ga ƴan kasar su ƙauracewa shiga duk wani taron da ya haura mutum 20. Kuma duk wani taron da mutum zai shiga ya kasance ya bayar da tazara akalla mita biyu tsakaninsa da na kusa.

    Hukumar ta ce waɗanda ke halartar wurin biki da casu suna jefa rayukan mutane cikin hatsari.

  15. Buratai ya jinjinawa sojojin Najeriya kan murƙushe harin Monguno

    Babban hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Tukur Buratai ya jnjinawa sojojin ƙasar kan ƙokarin da ya ce sun yi na murƙushe harin da Boko Haram ta kai a Monguno da ke jihar Borno

    A sanarwar da rundunar sojin ta Najeriya ta wallafa a Twitter ta ce, Janar Buratai ya yaba wa sojojin kan ƙwazonsu na fatattakar mayaƙan Boko Haram da suka kawo hari a Monguno a ranar Asabar.

    Sanarwar ta ce an baya ga kashe ƴan Boko Haram da dama an kuma kama wasu daga cikinsu tare da makamansu.

    Sai dai wasu rahotanni sun ce an kashe sojoji da fararen hula da dama a harin na Monguno na ranar Asabar

    Da tsakar ranar Asabar ne mayaƙan Boko Haram suka sun far wa garin Monguno, inda suka riƙa harba bindigogi da rokoki. Mazauna Monguno sun ce an shafe lokaci suna jin ana musayar wuta

    Harin dai na zuwa kwana uku bayan wani makamancinsa da aka kai kan garin Gubio da ya yi sanadin mutuwar kimanin mutum 80.

  16. Mutum 501 sun kamu da korona cikin sa'a 24 a Najeriya

    Mutum 501 ne aka tabbatar sun kamu da cutar korona a Najeriya a ranar Asabar bayan mutum 627 sun kamu da cutar a ranar Juma'a.

    Cutar na ƙara yaɗuwa bayan sassauta dokar da jihohi suka yi da kuma rashin kiyaye shawarwarin hukumomin lafiya.

    Yanzu adadin masu cutar a Najeriya ya kai 15,682, amma an sallami 5101 daga cikinsu bayan sun warke daga cutar a cewar hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta kasar, NCDC.

    Alkalumman hukumar kuma sun ce mutum 407 cutar ta kashe a ƙasar.

  17. Ina ya fi dacewa a saka takunkumi?

    Sabuwar dokar saka takunkumi za ta fara aiki a ranar Litinin a Ingila inda aka tilastawa mutane yin amfani da takunkumi a motocin sufuri.

    Haka ma ma'aikatan asibiti da masu jinya da ziyara dole su saka takunkumi.

    Wannan na daga cikin sabbin shawarwarin hukumar Lafiya ta duniya inda ta ce a dinga saka takunkumi a taron jama'a inda ba za a iya bayar da tazara ba.

    Kamfanin Uber zai bukaci direbobinsa da fasinja saka takunkumi daga ranar Litinin. Haka ma a Wales da Scotland an shawarci mutane su dinga saka takunkumi a wuraren da ke da cunkosun jama'a inda yin nesa da nesa zai yi wahala.

  18. Buɗewa

    Barkanmu da safiyar Lahadi da fatan kun wayi gari lafiya kuma za ku kasance da mu a wannan shafi da za mu kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya bibiyarmu a shafukanmu na Facebook da Twitter da Instagram