Aarchbishop na Douala a Jamhuriyyar Kamaru ya kaddamar da maganinsa da ya yi ikirarin cewa yana maganin cutar korona.
Shafin ActuCameroun ya ce Monsignor Samuel Kleda babban malamin mabiya addinin Kirista ne a Kamaru ya raɗa wa magungunansa da ya ce suna maganin korona sunan Elixir Covid da kuma Adsak Covid.
Ya kuma yi ikirarin warkar da kusan mutum 3,000 masu dauke da cutar korona da magungunansa da ya yi amfani da wani ganyen itacen da ake kira "Mafura" a Kamaru.
A cewar Jaridar an gudanar da bikin kaddamar da maganin ne a ranar Asabar a birnin Douala.
Sannan yana bayar da maganin ne kyauta a mujami'un ɗarikarsa a biranen Yaounde da Garoua da Bertoua da Buea da Bafoussam da Bamenda.
Bishop Kleda ya ce yana sauraren hukumomin lafiya a Kamaru ya ji abin da za su ce bayan sun dauki samfurin maganinsa domin tabbatar da ingancinsa.
Hukumar Lafiya ta duniya dai ta yi gargadi kan amfani da maganin da ba ta tabbatar da ingancinsa ba, yayin da har yanzu ake binciken maganin da zai warkar da cutar korona.