Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An kammala jana'izar George Floyd

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

    Mun zo karshen labarai da rahotannin da muke gabatarwa a yau. Sai ku tare mu ranar Juma'a domin samun sabbin bayanai kan abubuwan da ke faruwa a duniya.

    Da fatan kun ji dadin abubuwan da muka kawo muku.

    Kada ku manta za ku iya ci gaba da karanta laaran da muka gabatar muku, idan kuka leka kasan wannan shafi.

    Mu kwana lafiya.

  2. An kammala jana'izar George Floyd

    Bayan limanin coci ya gama addu'o'i, jama'ar da suke wurin sun mike tsaye inda suka rika tafi da hannayensu a yayin da ake kida.

    Bayan kidan ya yi kasa, sai Rebarand Sharpton ya bukaci a yi shiru na dan wani lokaci - minti takwas da dakika 46, wato daidai tsawon lokacin da George Floyd ya shafe a kasa lokacin da dan sanda ya danne masa wuya da gwiwarsa.

    "A yayin da muka yi tsit na minti takwas, ku yi tunani kan abubuwan da suke faruwa da George inda yake kwance tsawon minti takwas yana rokon Allah ya kubutar da shi," in ji Rebaranda Sharpton.

    "Ba za mu ci gaba da rayuwa irin wannan ba."

    Daga nan ne mutanen da suka halarci jana'izar suka rufe idanunsu, suka kuma rarrashi juna, sannan suka yi addu'ar Allah Ya jikansa.

  3. Zanga-zanga ta sa za a sassauta dokar kulle a Senegal

    Senegal ta sanar cewa za ta sasauta dokar kulle da ta hada da ta tafiye-tafiye tsakanin jihohi bayan an kwashe dare biyu ana zanga-zanga.

    'Yan sanda sun tsare mutum fiye da 200 inda suka yi musu tambayoyi bayan zanga-zanga a yankuna daban-daban na kasar.

    Masu zanga-zangar sun bukaci a sassauta dokar hana fita da gwamnati ta sanya a watan Maris sakamakon annobar korona.

    Ministan Cikin Gida na kasar Aly Ngouille Ndiaye ya ce za a sassauta dokar hana fita daga 12 na dare zuwa karfe 5 na safe kowacce rana.

    Ana sassauta dokar tafiye-tafiye sannan za a bude wuraren motsa jiki da gidajen rawa nan ba da dadewa ba.

  4. Chelsea na shirin dauko Timo Werner

    Chelsea na tattaunawa da RB Leipzig kan a sayar mata da Timo Werner.

    Ana ta alakanta dan wasan mai shekara 24 dan kasar Jamus da cewar zai koma Liverpool ya kuma ce yana alfahari da jin dadin wannan batun.

    Werner ya ci kwallo 25 a gasar Bundesliga a kakar nan ya kuma ci wa tawagar Jamus kwallo 11 a wasa 29 da ya yi.

    Olivier Giroud ne kadai mai ci wa Chelsea kwallo da ke da lafiya, bayan da Tammy Abraham ke jinya tun cikin watan Janairu.

  5. 'Yan sanda uku sun gurfana a kotu kan mutuwar George Floyd

    A daidai lokacin da ake jana'izar George Floyd, 'yan sandan da ake zargi da sun taimaka wajen kashe shi kuma sun shiga kotu.

    'Yan sandan da ake zargi da laifin taimaka wa wajen kisan su ne Thomas Lane da J Alexander da Kueng da Tou Thao.

    Idan aka kama su da laifin, akwai yiwuwar za su iya shafe shekaru 40 a gidan yari a tsare. An saka kuɗin belin su kan dalar Amurka miliyan 1.

    Sai dai dan sandan da ya murƙushe Floyd har ya mutu wato Derek Chauvin zai gurfana a kotu ne daban a ranar 8 ga watan Yuni.

  6. Lauyan George ya buƙaci a ci gaba da fitowa zanga-zanga

    Lauyan da ke kare George ya yi kira da a fito a yi zanga-zanga kan zalunci da mugunta da ake yi.

    Ya ce irin zalunci da rashin imani da aka ga 'yan sandan nan sun yi a wannan bidiyon ba abin a ƙyale bane.

    Ya yi kira ga Amurkawa da kada su goyi bayan zalunci.

  7. Lauyan George ya yi magana mai sosa zuciya

    Benjamin Crump, wanda shi ne lauyan gidan su Marigayi George ya yi bayanai masu sosa zuciya.

    Ya bayyana cewa "ba wai annobar korona ba ce ta kashe George, annobar nuna wariyar launin fata ce ta kashe shi."

    Ya yi godiya ga sauran lauyoyi da suka tashi tsayin daka wajen ganin cewa an gudanar da adalci.

  8. Manyan mawaƙa da 'yan siyasa sun halarci jana'izar George

    Tuni dai 'yan uwa da abokan arziƙi na George Floyd suka hallara a wurin jana'izar.

    'Yan majalisa da dama da kuma manyan masu fina-finai da mawaƙa a Amurka sun halaraci wurin jana'izar.

    Cikin shahararrun waɗanda suka halarci wurin akwai Ludacris da TI da Tiffany da Kevin Hart.

    Cikin 'yan siyasar ƙasar da suka halarci wurin har da Ilhan Omar da Magajin Garin Minneapolis Jacob Frey da kuma gwamnan Minnesota Tim Walz.

  9. Wasu daga cikin hotunan jana'izar George Floyd

  10. 'Duka masu korona a Sokoto sun warke'

    Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa duka masu cutar korona da ke jihar sun warke.

    A wani saƙo da ma'aikatar lafiya ta jihar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa sauran mutum biyar da ke jinyar cutar a jihar an sallame su domin tafiya gida wurin iyalansu.

    Tun farkon ɓullar cutar a jihar, mutum 116 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, sai kuma mutum 14 cutar ta yi sanadin mutuwar su.

  11. Me masu zanga-zangar ke buƙata?

    Kawo ƙarshen rashin imani da 'yan sanda ke nuna wa baƙar fata ne jigon abin da suke nema a faɗin ƙasar.

    Sai dai ba shi kaɗai ba ne. Wannan ɗin ka iya zama babba daga ciki amma yadda aka ɗebi shekaru masu yawa ana cin mutuncin baƙken fatar Amurka.

    A shafukan sada zumunta, waɗanda ke goyon bayan gwamnati na ta kira ga mahukunta da su gaggauta kawo ƙarshen wariyar - daga ɓangaren jami'an tsaro zuwa ɓangaren kiwon lafiya.

  12. 'Yan zanga-zanga 51 aka kama a Amurka zuwa yanzu

    Ministan Shari'a na Amurka William Barr ya ce jami'an tsaron gwamantin tarayya sun kama mutum 51 zuwa yanzu daga cikin masu zanga-zangar kisan George Floyd.

    A wani jawabi da ya gudanar a wurin taron manema labarai, Barr ya ce a bayyane take ƙarara cewa Amurkawa da yawa sun yanke ƙauna daga sahihancin tsarin tuhumar masu laifi na ƙasar.

    Sannan ya aminta cewa an yi zanga-zangar lumana a wasu wuraren amma abin ya zama tashin hankali a wasu wuraren.

    Sai dai ya zargi "masu tsattsauran ra'ayi" irin su Antifa, waɗanda ya ce suna "amfani da macin" don cimma buƙatarsu.

  13. Ana shirye-shiryen jana'izar George Floyd

    Da misalin ƙarfe 1:00 na rana agogon Amurka za a yi jana'izar George Floyd a Minneapolis, wanda mutuwarsa ta janyo zanga-zangar ɓacin rai ta tsawon fiye da mako guda a faɗin ƙasar.

    Wane ne George Floyd?

    Kafin bidiyon George Floyd da ya ɓulla - inda aka ga wani ɗan sanda ya maƙure masa wuya da gwiwarsa - ya tayar da ƙura, rayuwarsa na cikin ƙangin talauci.

    Ya ɗan samu ɗaukaka a shekarar 1992 lokacin da ya buga wa ƙungiyar Yates High School Lions wasan ƙarshe a gasar zari-ruga a Jihar Texas.

    Kazalika ya fuskanci matsaloli a rayuwasa lokacin da aka kama shi bisa zargin yin fashi a shekarar 2007, inda ya shafe shekara biyar a gidan yari.

    Za a iya cewa Floyd wanda ya mutu ranar 25 ga watan Mayun 2020, yana ƙoƙarin yin rayuwa ne irin ta kowanne Ba'amurke cike da ƙalubale.

  14. ECOWAS ta tallafa wa Najeriya da kayan kiyaye haɗura

    Ƙungiyar ECOWAS - mai haɓaka tattalin arzikin ƙsashen Afirka ta Yamma - ta tallafa wa Ma'aikatar Agaji da Ci Gaban Al'umma ta Najeriya da kayan aiki.

    Wata sanarwa da ma'aikatar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce tallafin zai tafi ne kai-tsaye ga hukumar NEMA mai bayar da agajin gaggawa a Najeriya.

    Kwamishinar Ci Gaban Al'umma ta ECOWAS ce Dr. Fatima ta miƙa wa Babban Sakatare a Ma'aikatar Agaji da Ci Gaban Al'umma, Alhaji Jalal Arabi, kayayyakin.

    Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙirƙiri Ministry of Humanitarian Affairs, Disaster Management and Social Development bayan shiga zangonsa na biyu a watan Mayun 2019.

  15. Ana taro don tara kuɗin samar da riga-kafin cutuka a Landan

    An fara gudanar da taron samar da riga-kafin cutuka na duniya a birnin Landan, da nufin tara kudin da suka kai dala biliyan bakwai domin yaƙi da cutuka masu kisa.

    Za a yi amfani da kudaden ne wajen yi wa miliyoyin yara a duniya allurar riga-kafin cutuka kamar su kyanda da cutar shan inna.

    Da yake bayani yayin bude taron, Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce "wannan wata fafutika ce ta zamaninmu".

    Boris Johnson ya ce domin tabbatar da an yi nasara kan annobar korona, dole ne a hada kai da kamfanoni da kungiyoyi irinsu WHO domin samar da riga-kafin.

    Cutar korona ta janyo tsaiko wajen aikin riga-kafin da ake yi a kusan kasashe 70 – kuma akalla yara miliyan 8 ne ba za su samu riga-kafin ba a wannan shekarar a fadin duniya.

  16. Kotu ta yi watsi da dakatar da 'yan majalisar dokokin jihar Kano

    Wata kotun tarayya da ke jihar Kano a arewacin Najeriya, ta yi fatali da dakatarwar da Majalisar dokokin jihar ta yi wa 'ya'yanta biyar bisa zargin keta dokokin majalisar.

    A watan Maris ne shugaban majalisar, Abdulazeez Gafasa ya sanar da dakatar da Garba Ya'u Gwarmai da Labaran Audu Madari da Isyaku Ali Danja da Bello Muhammad da kuma Salisu Ahmad Gwangwazo bayan sun ki amincewa da kudurin cire tsohon Sarkin Kano Muhammad Sanusi na II.

    An dakatar da 'yan majalisar ne zuwa wata shida, ko da yake nan-take suka garzaya kotu don kalubalantar dakatarwar.

    Da yake yanke hukunci ranar Alhamis, Mai shari'a Lewis Alagoa ya ce dakatarwa da aka yi wa 'yan majalisar ta saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

    Ya ce sun dauki matakin ne saboda yunkurin da 'yan majalisar suka yi na dauke sandar majalisar.

  17. 'Yan majalisar wakilan Najeriya sun ƙi amincewa a riƙa yi wa masu fyade dandaƙa

    'Yan majalisar wakilan Najeriya sun ki amincewa da wani kudirin doka da ya so a rika dandake duk mutumin da aka samu da laifin yin fyade a kasar.

    Gidan talbijin na Channels TV ya ce 'yan majalisar sun dauki matakin ne a zaman da suka yi ranar Alhamis, bayan daya daga cikinsu, Mr James Faleke, ya bukaci a rika yanke hukuncin dandaka kan masu fyade.

    Sai dai 'yan majalisar sun bukaci Babban Sufeton 'yan sandan kasar ya gaggauta gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa wata dalibar Jami'a a jihar Edo, Uwa Omozuwa, bayan an yi mata fyade.

    Kazalika sun bukaci a hukunta wasu mutum 12 da suka shafe wata biyu suna yi wata 'yar shekara 12 fyade a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin kasar.

    Masu rajin kare hakkin yara a Najeriya na ganin cewa za a ci gaba da fuskantar matsalar fyade ga kananan yara a kasar matukar gwamnati ba ta fara aiwatar da hukuncin kisa a kan masu aikata irin wannan laifi ba.

  18. Twitter ya zargi Trump da shirga ƙarya

    Kamfanin Twitter ya zargi shugaban Amurka Donald Trump da yin karya, a cikin daya daga cikin labaran da shafin ya wallafa.

    Matakin - wanda ya zargi shugaban da yin karya - yana kunshe ne a sakon Twitter da Mr Trump ya wallafa game da tsohon Sakataren tsaronsa.

    Mr Trump ya wallafa sakon Twitter cewa shi ya sanya wa James Mattis sunan "Mahaukacin kare" sannan daga baya ya kore shi daga aiki.

    Sakon na Twitter ya ce tsohon Sakataren Tsaron na Amurka ya sauka daga mukaminsa, kuma tun kafin Trump ya hau mulki aka sanya masa sunan "Mahaukacin kare".

    Hakan ya faru ne bayan a makon jiya Twitter ya sanya wata alama ta duba sahihancin wasu sakonni da Shugaba Trump ya wallafa, sannan ya ce shugaban yana goyon bayan tashin hankali.

    Twitter ya dauki matakin ne kwana guda bayan James Mattis ya soki shugaban ƙasar da cewa yana jawo rarrabuwar kawunan mutane da gangan musamman game da yadda yake daukar mataki bayan kisan wani bakar fata, George Floyd, a hannun 'yan sandan Amurka.

    Ya ce ya ji taƙaici kan yadda Mista Trump ke yi wa lamarin zanga-zangar da ake yi kan kisan Mr George Floyd riƙon sakainar kashi.

  19. Labaran duniya cikin minti ɗaya...

    • 'Yan majalisar dokokin Pakistan biyu sun mutu sakamakon cutar korona ranar Laraba. Mutuwar ta faru ne bayan samun ƙari mafi girma na mutanen da suka kamu da cutar, inda sabbin mutum 4,772 suka harbu da ita
    • Jarirai kusan miliyan 80 ne suka rasa samun allurar riga-kafin da aka saba yi musu musamman a Afirka da Asiya saboda annobar krona. Wannan gargaɗi na masana na zuwa ne yayin da Birtaniya ke ƙoƙarin yin taron neman tallafi don yi wa yara riga-kafi a faɗin duniya
    • Hukumomi a Ethiopia sun ce 'yan mata fiye da 100 aka yi wa fyade sannan aka kai su asibiti a babban birnin kasar, Addis Ababa, tun da cutar korona ta barke a kasar. Shugabar ofishin kula da harkokin mata da yara a Addis Ababa, Almaz Abraham, ta ce ana samun karin matsalar cin zarafin mata saboda rufe makarantu
    • Ɗan wasan gaban Real Madrid Gareth Bale ba ya son barin ƙungiyar don komawa gasar Premier League. Wakilinsa Jonathan Barnett ya ce da yiwuwar ɗan wasan mai shekara 30 ya kammala sana'ar kwallonsa a birnin Madrid
  20. Mutum 7,000 sun tsere daga sansanin 'yan gudun hijira a Nijar

    Hukumar Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta ce mutane sama da dubu bakwai sun tsere daga matsugunansu a Jamhuriyyar Nijar.

    Hakan ya faru ne sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai a wani yankin da aka tsugunar da 'yan gudun hijirar kasar Mali da kuma 'yan Nijar wadanda tashin hankali na cikin gida ya raba da muhallansu.

    Dama mutane sama da dubu talatin da biyar ne ke samun mafaka a yankin na Itikane da ke jihar Tahoua.

    Galibin wadanda suka tseren 'yan gudun hijira ne 'yan kasar Mali.

    Wani mai magana da yawun hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Nijar, Jean Sebastien Josset ya shaida wa BBC cewa yanzu dubban mutanen da suka tsere na wani matsuguni na wucin gadi kusa da garin Telemce, kimanin kilomita 27 daga inda aka kai harin.

    Jami'in hukumar ta UNHCR ya ce mutanen na matukar bukatar muhimman kayayyakin rayuwa, kamar ruwa da abinci da kuma kayayyakin kiwon lafiya.