Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Korona: Najeriya za ta gwada magungunan gargajiya 3

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Mustapha Musa Kaita and Halima Umar Saleh

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo karshen kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin kanun labaran da muka wallafa a wannan shafin:

    • An kori 'yan sanda huɗu daga aiki saboda kashe baƙar-fata a Amurka
    • Ban taba mika ikona ga Abba Kyari ba - Buhari
    • Ministar Abuja 'ta bayar da albashinta don kuɓutar da fursunoni'
    • Faransa ta haramta amfani da hydroxychloroquine don maganin korona
    • Za a bude masallatai da coci-coci a Afirka Ta Kudu
    • Za a dawo da zirga-zirgar jirage tsakanin biranen Saudiyya
    • Yaɗuwar korona na raguwa a Saudiyya
    • Za a fitar da matakan buɗe makarantu a Najeriya
    • Covid-19: Mutum 87 sun sake warkewa a Legas
    • Sojojin Najeriya sun sake kashe 'yan bindiga 30 a Zamfara

    Ku duba ƙasa domin karanta labaran da wasu muhimmai...

  2. Korona: Najeriya za ta gwada magungunan gargajiya 3

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta zaɓi wasu magungunan gargajiya uku cikin da dama da aka yi iƙirarin suna yin maganin cutar korona domin yin gwaji da kuma bincike a kansu.

    Shugaban kwamitin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa kan yaƙi da cutar korona Boss Mustapha ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba.

    Ya bayyana cewa ma'aikatar lafiya ta ƙasar ce ta zaɓi magungunan bayan an tattauna da masu bincike da kuma masana kimiyya.

  3. 'An sallami duka masu korona a Zamfara'

    Hukumomi a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce yanzu babu wanda ke dauke da cutar korona a jihar, don haka ma sun sallami mutanen da suka yi saura a cibiyar killace mutane da ke jihar.

    Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Yahaya Muhammad Kanoma ya shaida wa BBC cewa mutum takwas ne kawai suka yi saura a jihar kuma ya zuwa yanzu duk sun sallame su.

    Mutum biyar ne cutar ta kashe a jihar ta Zamfara tun bayan bullarta.

  4. Sojojin Najeriya sun sake kashe 'yan bindiga 30 a Zamfara

    Dakarun rundunar Hadarin Daji ta sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe 'yan bindiga 30, tare da ƙona wurin ajiyar kayayyakinsu.

    A wata sanarwa da Shelkwatar Tsaron Najeriya ta fitar, ta bayyana cewa an kai harin ne a dajin Doumborou da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin ƙasar.

    Ta bayyana cewa bayanan sirrin da aka tattara ne suka kai ga zuwa dajin, kuma 'yan bindigar na amfani da dajin wajen ajiyar kayayyakinsu.

    Jihohin Zamfara da Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a Najeriya.

    Sai dai a 'yan kwanakin nan bayan umarnin da shugaban Najeriya ya bayar na kakkaɓe 'yan bindiga a jihar Katsina, sojojin ƙasar na samun nasara wajen yaƙi da 'yan bindigar da ke yankunan Zamfara da jihar ta Katsina.

  5. Covid-19: Mutum 87 sun sake warkewa a Legas

    An sallami mutum 87 da suka warke daga korona a Legas a ranar Laraba.

    Gwamnatin jihar ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter inda ta bayyana cewa 40 daga cikin waɗanda aka sallama mata ne sai kuma 47 maza.

    Jihar Legas ce dai kan gaba a yawan masu cutar korona inda a yanzu haka mutum 3,756 suka kamu da cutar korona a jihar kamar yadda hukumar NCDC ta sanar a ranar Talata.

  6. Kungiyar ADF ta kashe mutum 38 a gabashin Congo

    Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa a kalla mutum 38 suka mutu sakamakon wani hari da wata kungiyar 'yan bindiga ta kai a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo.

    Mutanen sun mutu ne a wasu jerin hare-hare da kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) ta kai a lardunan Ituri da kuma Arewacin Kivu.

    Rahotanni sun bayyana cewa kusan fararen hula 500 kungiyar ADF ta kashe tun bayan da sojoji suka kaddamar da yaƙi kan kungiyar.

    Kungiyar ADF ta fara ne a matsayin kungiyar da ke ikirarin jihadi, sai dai ana ganin a halin yanzu, ta sauya inda ta dosa.

  7. Za a fitar da matakan buɗe makarantu a Najeriya

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba da jimawa ba za ta fitar da tsare-tsare na buɗe makarantu a faɗin ƙasar.

    Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne ya tabbatar da haka a wani taron manema labarai kan cutar korona na ranar Laraba.

    Ganin cewa yau ce ranar yara a ƙasar, Mustapha ya jaddada cewa sakamakon girman annobar korona ce ta sa aka rufe makarantu wanda an yi hakan ne domin daƙile yaduwar cutar.

    Ya kuma bayyana cewa Kungiyar Iyayen Yara da Malamai wato PTF na tattaunawa kan wannan lamari kuma ma'aikatar ilimi ta tarayya za ta fitar da matakai waɗanda za a bi domin sake buɗe makarantu.

  8. Minti Daya Da BBC Na Rana: 27/05/2020

    Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren labaran.

  9. Amurka za ta sa baki kan rikicin iyakar China da Indiya

    Shugaba Donald Trump ya ce Amurka shirye take ta shiga tsakani a rikicin kan iyaka da ya barke tsakanin Indiya da Chana.

    Shugaban ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa Amurka ta sanar da kasashen biyu cewa za ta iya samar musu da mafita kan takaddamar da ta kunno kai tsakaninsu.

    Wannan shi ne karon farko da wani shugaba ya saka baki kan dambarwar, bayan da kafafen yaɗa labarai a Indiya suka ruwaito cewa dubban sojoji daga bangarorin biyu na shirin gwabzawa a yankin Kashmir da kuma arewa maso gabashin kasar.

    Hukumomin Indiya sun ce sojojin China sun kutsa kan iyakar ƙasar da ke Ladakh, to amma gwamnatin Beijing ta ce tana ɗaukar matakan kare kan iyakarta ne.

    Ƙasashen biyu sun haɗa kan iyaka da tsawon ta ya kai kilomita 3,400 kuma tuntuni ake ja in ja kan ikon mallakar wani yanki.

  10. Ministan Lafiya ya kamu da korona a Zambia

    Ministan Lafiya na ƙasar Zambia, Chitalu Chilufya ya kamu da cutar korona, shi ne minista na biyu da ya kamu da cutar a ƙasar.

    An bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai da hukumomin ƙasar suka yi domin bayar da bayanai kan cutar

    A makon da ya gabata ne ministar watsa labarai ta ƙasar Dora Siliya ta fito ta bayyana cewa tana ɗauke da cutar korona, ta yi haka ne domin kawar da tsangwamar da ake yi wa jama'a kan cutar, kamar yadda ya shaida a wata tattaunawa da BBC.

    A kwanaki biyar da suka gabata, mutum 137 ne suka kamu da cutar ta korona a Zambia inda a halin yanzu, mutum 1,057 ne suka kamu da cutar a ƙasar.

    Mutum bakwai ne cutar ta kashe a ƙasar.

  11. Yaɗuwar korona na raguwa a Saudiyya

    Ana dai samun raguwa a yawan waɗanda suke kamuwa da cutar korona a Saudiyya, haka zalika kuma ana samun ƙarin yawan waɗanda ke warkewa daga cutar a kullum a ƙasar.

    Ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa mutum 1,815 ne suka kamu da cutar korona a ranar Laraba, a halin yanzu waɗanda suka kamu da cutar a ƙasar sun kai 78,541 kamar yadda ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta bayyana.

    Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa a halin yanzu, jumullar mutum 51,022 ne suka warke daga cutar ta korona bayan mutum 2,572 sun warke a ranar Laraba.

    Ƙasar ta bayyana cewa mutum 14 sun sake mutuwa sakamakon cutar inda jumullar waɗanda suka mutu sakamakon cutar sun kai 425.

  12. Ya kamata gwamnati ta shawo kan ukubar da iyalan 'yan Boko Haram ke ciki - Amnesty

    Kungiyar kare hakkin bil'adam ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomi a Najeriya da su shawo kan ukubar da iyalan 'yan kungiyar Boko Haram ke shiga.

    A rahoton da ta fitar, Amnesty International ta ce yaran da ke karkashin yankunan da Boko Haram ke iko sun shafe sama da shekaru 10 suna fuskantar azabtarwa da cin zarafi da auren dole da kuma mayar da kananan yara mayakan kungiyoyin ta'addanci.

    Haka ma kungiyar ta ce yaran na fadi tashin tsira da rayuwarsu ba ya ga rashin ilimi da suke fuskanta.

    Ta kuma zargi sojojin Najeriya da azabtarwa da kuma tsare kananan yara.

    To amma tun bayan fitar rahoton babu wani martani daga rundunar sojin ta Najeriya.

  13. Za a dawo da zirga-zirgar jirage tsakanin biranen Saudiyya

    Kamfanin zirga-zirgar jiragen saman Saudiyya zai fara jigila da jirage 60 a cikin kasar a matakin farko na dawo da ayyukansa a ranar Lahadi 31 ga watan Mayu, a cewar jaridar Saudi Gazette.

    Saudiyya za ta kuma hada kai da Hukumar da ke sa ido kan jiragen sama ta kasar GACA, inda za ta fadada ayyukansa.

    Matakin na zuwa ne bayan da GACA ta amince da cewa a dawo da zirga-zirgar jiragen bayan da Saudiyya ta sassauta wasu dokokin kulle.A matakin farkon, za a fara zirga-zirgar jiragen ne a biranen Riyadh da Jeddah da Dammam da Madinah da Qassim da Abha da Tabuk da Jazan da Hail da Al-Baha da kuma Najran.Amma sanarwar ta kara da cewa dokar hana zirga-zirgar jirage tsakanin kasar da kasashen duniya za ta ci gaba da aiki.

  14. Za a bude masallatai da coci-coci a Afirka Ta Kudu

    Shugaban kasar Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanar da cewa za a bude wuraren ibada ranar 1 ga watan Yuni tare da daukar tsauraran matakai don hana yaduwar cutar korona.

    Za a nemi masallatai da coci-coci da sauran wuraren ibada da su tabbatar da cewa mutane suna bayar da tazara da juna.

    Mutum 50 kawai za a dinga bari suna halarta, ya danganta dai da girman wajen iabadar.

    Za a bukaci dukkan masu ibadah su sanya takunkumi da kuma tsaftace hannayensu.

    Shugaba Ramaphosa ya gamsu da rawar da malaman addini ke takawa a cikin al'umma da suka hada da bayar da shawarwari da yin addu'a.

    Ya ce annobar ta yi mummunan tasiri kan yanayin ibadun mutane da dama, kuma ya kira dage takunkumin mataki na uku na sassauta tsauraran matakan kulle.

    Shugaban ya sanar da cewa za a yi addu'a ta kasa baki daya a ranar 31 ga watan Mayu.

    Tun a watan Maris aka rufe wuraren ibadah a lokacin da kasar ta shiga cikin dokar kulle. Wasu malaman addini sun ci gaba da yin ayyukan ibadun ta intanet.

    Zuwa yanzu dai Afirka Ta Kudu tana da mutum 24,264 da suka kamu da cutar korona - kuma ita ce kasar da ta fi yawan masu cutar a nahiyar Afirka - sannan tuni mutum 524 suka mutu sakamakon cutar.

  15. Kanun labaran duniya na baya-bayan nan

    Ga wasu kanun labaran duniya na baya-bayan nan

    • Hukumar Tarayyar Turai za ta kafa wani gagarumin asusu na farfado da tattalin arziki na kimanin dala miliyan 825 don taimaka wa wajen magance ''matsalolin da ba a yi hasashensu ba.'' Tattalin arzikin kasashe 27 na EU ya yi rugu-rugu sakamakon annobar cutar korona, amma dama kasashen da ke kudanci ana bin su dumbin basussuka tun kafin annobar.
    • A hannu guda kuma Fraansa ta sanar da shirin ceto masana'antar motoci ta kasar da annobar ta yi wa illa. Ta kuma dakatar da likitoci daga amfani da maganin zazzabi na hydroxychloroquine don magance cutar korona
    • Yankin Latin Amurka ya zamo sabuwar cibiyar annobar a duniya. Yawan mace-macen da ake yi a Brazil a yanzu ya fi na ko ina a duniya, kuma wani bincike ya yi gargadin cewa mace-macen zai nunka sau biyar nan da watan Agusta.
    • A Burtaniya, Firai Minista Boris Johnson zai sha tambayoyi daga wajen 'yan majalisa a yayin da yake ci gaba da fuskantar matsin lamba saboda karya dokokin kulle da mai ba shi shawara na kut-da-kut dinsa ya yi.
    • Yawan wadanda suka kamu da cutar korona a duniya zuwa yanzu ya haura miliyan 5.5, yayin da fiye da 349,000 suka mutu.
  16. Yadda aka ceto mata 'yan Najeriya da aka yi safararsu daga Lebanon

    Shugabar hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriya Julie Okah-Donli, ta shaida wa BBC yadda aka ceto mata 50 daga bauta a Lebanon.

    A yanzu sun koma Najeriya kuma an killace su.

    Ms Okah-Donli ta shaida wa shirin rediyo na Focus on Africa cewa matan sun tuntubi hukumomin Najeriya ne inda suka bukaci taimako, su kuma hukumomin suka ba su shawarar kai kansu ga ofishin jakadancin kasar da ke Lebanon.

  17. Yawan masu dauke da cutar korona a Afirka

    Zuwa yanzu kasashe 55 ne cutar korona ta bulla a Afirka sannan yawan wadanda suka kamu da cutar a nahiyar sun kai haura 187,000.

    Ga dai alkaluma cutar kai tsaye idan kuka latsa nan za ku ga yadda suke.

  18. An kai mai barkwanci kotu kan yi wa shugaban kasa dariya

    Wani mai wasan barkwanci a Tanzaniya Idris Sultan ya bayyana a gaban kotun majistare da safiyar ranar Laraba a birnin Dar es Salaam, kwana takwas bayan kama shi.

    Za a tuhumi Sultan da laifukan intanet, da lalata shaidu da kuma amfani da layin wayar da aka yi wa rijista da sunan wani, kamar yadda mai magana da yawun 'yan sanda ya shaida wa BBC ranar Litinin.

    A ranar Talatar makon da ya gabata ne aka kama shi, bayan da wani bidiyo ya yadu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta, inda aka ga mai barkwancin yana yi wa wani tsohon hoton Shugaba John Magufuli dariya.

    'Yan sanda sun zarge shi da keta dokar laifukan intanet da kuma tsokanar shugaban kasa, a cewar lauyansa Bennedict Ishabakaki.

    Mafi yawan masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta amfani da maudu'in #FreeIdrisSultan (a saki Idris Sultan) tare da sanya hotonsa a shafukansu don nuna goyon baya.

    A bara ma an kama Sultan bayan da ya yi ta yada wani hotonsa da na shugaban kasar.

    Kama shi da aka yi ya zo a matsayin tuni na baya-baya nan kan dokokin intanet wadanda masu fafutuka suka bayyana a matsayin masu tsanani da kuma tauye 'yancin albarkacin baki.

  19. Faransa ta haramta amfani da hydroxychloroquine don maganin korona

    Faransa ta haramta amfani da hydroxychloroquine a matsayin maganin da za a rika bai wa masu fara da cutar korona a kasar.

    Hukumomin da ke ba da shawara sun ce maganin ka haifar da wata mummunar rashin lafiyar ta daban – kuma a baya ana amfani da shi ne a kan masu fama da rashin lafiya ta musamman.

    A ranar Litinin, Hukumar Lafiya ta Duniya ta dakatar da amfani da maganin kan masu cutar korona na wani dan lokaci, bayan masu bincike sun ce zai iya kara hadarin mutuwa da wuri ga marasa lafiyar.

    Shugaba Trump ya ce yana amfani da maganin a matsayin rigakafin cutar korona, kuma tun lokacin da ya furta hakan ya dakata da amfani da shi.

  20. Ministar Abuja 'ta bayar da albashinta don kuɓutar da fursunoni'

    Minista a ma'aikatar Birnin Tarayya Abuja, Ramatu Aliyu, ta ce ta bayar da albashinta a watan Mayun 2020 domin a fitar da fursunoni biyar da ke gidan yarin Kuje a wajen Abuja.

    A sakon da ministar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta dauki matakin ne lokacin da ta kai ziyarar karamar Sallah gidan yarin.

    Ta kuma kai kayan abinci ga mazaunan gidan yarin, inda ta yi musu addu'a.

    Najeriya da na fama da cunkoson a gidajen yarinta, ko da yake a kwanakin baya Shugaba Buhari ya yi afuwa da daruruwan fursunoni domin gudun kada su kamu da cutar korona.