Hukumar Binciken Laifuka ta Amurka, FBI, ta ce za ta gudanar da bincike kan mutuwar wani bakar-fata a jihar Minnesota bayan wani bidiyo ya nuna yadda dan sanda ya danne wuyansa.
A cikin bidiyon an ji mutumin, wanda yake da kimanin shekara 40, yana ihu sannan yana ta gaya wa dan sanda da ya danne shi da gwiwar kafarsa cewa "ba na iya numfashi."
Rundunar 'yan sandan Minneapolis ta ce tana bincike kan laifin.
Wannan lamari ya tuna wa mutane abin da ya faru da wani bakar-fata mai suna Eric Garner, wanda ya mutu lokacin da aka tsare shi a shekarar 2014.
An shake wuyan Garner da wani karfe inda ya rika cewa "Ba zan iya yin numfashi ba" kusan sau goma sha biyu.
Wannan kalami nasa ya zama wani furuci da masu fafutuka suka rika yi a wajen zanga-zangar kyamar cin zarafin da 'yan sanda suke yi wa bakaken-fata a Amurka.
Rundunar 'yan sandan Minnesota ta amince cewa mutumin ya mutu ne sakamakon danne shi da dan sandan ya yi.