Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Idan ba a yi hankali ba za mu rufe Legas – Sanwo-Olu

Wannan shafi yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a duniya game da cutar korona da ma wasu labarai da suka shafi rayuwarku.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    Da fatan an sha ruwa lafiya, Allah Ya karbi ibadunmu. A nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai-tsaye sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.

    Da fatan za ku kasance da mu tare da bibiyarmu a Facebook da Twitter da Instagram

  2. Idan ba a yi hankali ba za mu rufe Legas – Sanwo-Olu

    Gwamnatin Legas ta yi gargaɗin cewa za ta kafa dokar kulle idan har mutane suka ci gaba da saba sharuddan da aka shata bayan sassauta dokar fita

    Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya ce duk da aikin faɗakar da al’umma da aka yi amma abin takaici sai ka ga dandazon jama’a a bankuna da kasuwanni a sassan jihar suna saɓa ƙa’ida.

    “Za a tilasta mana ɗaukar mataki marar daɗi na kulle jihar gaba ɗaya idan har mutanen Legas suka ci gaba da saɓa dokokin.”

    Ya kuma ce za a kama duk ɗan okada da kuma motocin fasinja da ke zirga-zirga idan suka ci gaba da saɗa dokokin da aka shata.

  3. Obama ya caccaki Trump kan yaƙi da korona

    Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana yadda wanda ya gaje shi yake yaƙi da annobar korona a matsayin wani mummunan yanayi mai rikitarwa.

    A wata tattaunawa da mambobin gwamnatinsa ta intanet da aka kwarmato, Mista Obama ya ce tunanin Donald Trump ya tsaya ne kawai a gare shi, bai damu da kowa ba.

    Cutar korona ta fi yin kisa da yaɗuwa a Amurka, kuma ta fi yin ƙamari a New York.

    A cikin bayanan da aka kwarmato, Obama ya ce matakin janye tuhumar da ake yi wa tsohon mai ba Trump shawara kan sha’anin tsaro Michael Flynn wanda ya amsa yi wa hukumar FBI karya, hatsari ne ga doka.

  4. Buhari ya jajantawa Tambuwal kan rasuwar ƙanin mahaifinsa

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajantawa al'ummar jihar Sokoto kan rashin Sheikh Haruna Waziri Usman wanda Allah Ya yi wa rasuwa yana da shekara 96.

    Sheikh Usman wanda shi ne babba a gidan waziri Tambuwal kuma ƙani ne ga mahaifin gwamna Tambuwal ya rasu ne bayan ya daɗe yana fama da rashin lafiya

    Sanarwar da fadar shugaban ƙasa ta fitar ta ce, "jihar sokoto da ƙasa baki ɗaya sun yi rashin babban malami"

    Shugaba Buhari ya yi masa addu'ar neman gafarar Ubangiji tare da ba iyalan Waziri Tambuwal haƙurin babban rashin da suka yi.

    Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisa dukkaninsu sun jajantawa gwamna Tambuwal kan rasuwar Sheikh Haruna Waziri Usman a sakon da suka tura a Twitter inda suka dauka cewa mahaifinsa ne.

  5. Mutum 500 sun kamu da korona a ma’aikata daya a Ghana

    Hukumomin lafiya a Ghana sun ce sama da mutun ɗari biyar ne da ke aiki a wata ma'aikatar ƙere-ƙere suka kamu da cutar korona.

    A yanzu yawan masu cutar a Ghana ya ƙaru da kashi 30 a cikin kwana daya.

    Yanzu adadin waɗanda suka kamu a Ghana sun zarta 4,000, wanda shi ne adadi mafi yawa a yammacin Afrika.

    Ghana ta fi kowace ƙasa yin gwaji a duk fadin yankin Afrika ta yamma.

  6. Filin Maracanã na Brazil zai koma asibitin korona

    Filin Maracana da ke Rio de Janeiro - ɗaya daga cikin manyan filayen kwallon kafa a duniya zai koma asibitin korona.

    An yi wani gini na wuccin gadi a filin wanda zai ɗauki gado 400 daga ƙarshen mako mai zuwa.

    Sannan za a bude wani asibitin a Olympic Park.

    Brazil na ɗaya daga cikin ƙasashen da cutar korona ta fi yaɗuwa a duniya.

  7. Farashin buhun shinkafa zai koma N16,000 a Kano

    Hukumar sauraron kararrakin jama'a da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ta cimma yarjejeniya da kungiyar masu sarrafa shinkafa game da farashi.

    Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ya shaida wa BBC cewa bayan sun tilasta wa ‘yan kasuwa sassauta farashin suga yanzu kuma sun waiwayi bangaren shinkafa.

    Ya ce kungiyar masu sarrafa shinkafa ta jihar Kano RIFAN ta amince ta sassauto da farashi zuwa N15,500 ga ƴan kasuwa duk buhu 50KG, yayin da su kuma su sayar wa mutane kan farashin N16,000 duk buhu.

    Ya ce ƙungiyar ta amince ta samar da tirela 30 duk mako domin al’ummar Kano, kuma mutum ba zai iya sayen sama da buhu biyu ba.

    Ya ce hakan zai yi maganin masu ɓoye kaya da tsula wa kayayyaki farashi mai tsada.

  8. Maza sun fi haɗarin kamuwa da korona fiye da Mata - Bincike

    Masana kimiyya a Birtaniya na bincike don gano ko ƙarfin kwayoyin halittar bil'adama na da tasiri wurin yaƙar cutar korona a jikinsa.

    Bincike ya nuna cewa maza sun fi shiga haɗarin kamuwa da cutar akan mata.

    Wata ƙwararriya kan daukewar al'adar mace Dr Louise Newson ta ce ƙarfin sinadarin istrogin da ke taimakawa mata a lokacin jima'i na ba su kariya daga cutar.

    A cewar Dr Newson ''Jikin mata na da wata dama da maza ba su da ita wurin yaƙar cutuka, kuma kwayoyin halittar da ke yaki da cutuka a jikin dan adam na da sinadarin istrogen a cikinsu wanda kuma na mata ya fi ƙarfi.

    "Wannan ne ya sa zai yi wahala cutar korona ta yi tasiri a jikin mace mai ciki lura da ƙarfin sinadarin istrogen da jikinta ke samarwa," in ji ta.

    Wata tawagar masu bincike daga jami'ar Kings College da ke London ta samar da wata manhaja da sama da mutun miliyan uku ke amfani da ita wurin fahimtar idan akwai alamun cutar Korona a jikinsu.

  9. 'An kama ƴan kasar waje 28 ƴan leken asirin Boko Haram'

    Rahotanni sun ce rundunar sojan Najeriya ta kama mutum 28 da ake zargi ƴan leken asiri ne na ƙungiyar Boko Haram game da ayyukan rundunar.

    PRNigeria ta ce wasu majiyoyin tsaro sun shaida mata cewa waɗanda ake zargin sun hada da 'yan Najeriya da kuma 'yan kasashen waje, waɗanda yanzu haka ke fuskantar binciken kwakwaf daga rundunar sojan ta Najeriya.

    Rahotannin sun ce an kama ƴan leken asirin na Boko Haram ne bayan wani hari da kungiyar ISWAP ta kai kan dakarun sojan Najeriya a garin Diffa na Jamhuriyar Nijar. A ranar Alhamis rundunar ta ce ta kashe tare da kama dakarun kungiyar da suka kai harin.

    ISWAP ta ce ta kashe sojojin Najeriya biyar tare da raunata wasu da dama a harin da ta kai wa ƙaramin sansanin sojan. Sai dai bayanan da PRNigeria ta tattara sun nuna cewa sojojin ba sa cikin sansanin a lokacin da ƙungiyar ta kai harin, sun fita aikin yaki da ta'addanci.

    Majiyar ta bayyana cewa dakarun ƙasar Chadi sun dakata da shiga yakin da Najeriya ke yi da Boko Haram a yankin Tafkin Chadi ƙarƙashin haɗakar dakarun ƙasashe ta MNJTF.

    Tun a watan Maris Shugaban Chadi Idris Deby ya ce dakarun kasarsa ba za su sake shiga ayyukan yaƙi da ta'addanci ba a wata ƙasa da ba ta su ba bayan wani hari da ya ce dakarunsa sun kai da ya kashe ƴan Boko Haram kusan 1,000 a Tafkin Chadi.

  10. Kwamishinan Lafiya na jihar Kano ya warke daga korona

    Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce gwaji ya tabbatar da kwamishinanta ba ya ɗauke da cutar korona.

    Wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta wallafa a Twitter ta ce an sallami Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa daga asibitin da ake killace masu cutar korona bayan sakamakon gwaji guda biyu sun tabbatar da ba ya dauke da cutar.

    Sai dai sanarwar warkewar kwamishinan ta zo da mamaki, inda wasu ke ganin an boye cewa ya kamu da cutar korona.

    Amma a cikin sanarwar, Dr Tsanyawa ya gode wa al’ummar jihar Kano kan addu’oi da saƙwannin fatan alheri yayin da yake karbar magani a cibiyar killace masu cutar korona.

    A ranar Alhamis ne aka sallami shugaban kwamitin yaƙi da cutar korona Farfesa Abdulrazaq Garba Habib bayan ya warke daga cutar a Kano.

    Ya ce ya kamu da cutar ne yayin da yake aikin kwamitin yaki da cutar korona a Kano. Kuma ya shafe kusan wata daya yana jinya.

  11. Pantami ya ba wa Hukumar NCC umarni a Twitter

    Ministan sadarwa na Najeriya Isa Ali Pantami ya umurci hukumar da ke kula da harakokin sadarwa ta ƙasa NCC ta ɗauki matakai kan ƙorafe ƙorafen da ake kan yadda wasu kamfanonin sadarwa ke wawushe kudaden mutane masu amfani da layukansu.

    Pantami ya ba NCC umurnin ne a Twitter bayan gabatar masa ƙorafin ta kafar Twitter.

    Wanda ya gabatar da ƙorafin a shafinsa mai suna Aminu OFS Muhammad ya shaida wa ministan cewa ya shafe lokaci a yayin da ake cikin kulle yana bibiyar yadda ake cajar mutane kuɗi idan sun tura saƙon kar-ta-kwana.

    Ya ce abin da ya gano shi ne duk saƙon da mutum ya tura na shafi ɗaya maimakon a caje shi kuɗin saƙo ɗaya sai a caje shi kuɗin saƙo uku.

    A martaninsa, Pantami ya bukaci NCC ta ɗauki mataki kan ƙorafen ƙorafen da ya ce sun yi yawa tare da umurtar hukumar ta hukunta kamfanonin da ya kira 'masu yaudarar kwastamominsu."

    Bayan bayar da umurnin a Twitter, nan take shafin Twitter na NCC ya amsa umurnin na minista.

  12. Coronavirus: Karin mutum shida sun warke a Abuja

    Wasu mutum shida da ke jinyar cutar korona a Abuja sun warke kuma an sallame su bayan gwaji ya nuna ba sa dauke da cutar.

    Ministan Birnin Tarayya Abuja ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter yau Asabar, inda ya ce jumillar wadanda suka warke din a Abuja sun zama 46 ya zuwa bkarfe 10:00 na safiyar Asabar.

    Mohammed Musa Bello ya jinjina wa ma'aikatan lafiya "bisa jajircewarsu" sannan ya ce suna kara azama a yaki da cutar.

    Ya zuwa daren ranar Juma'a mutum 336 ne suka kamu da cutar korona a Abuja sannan hudu daga cikinsu suka rasu.

  13. Motoci 791 aka hana shiga Legas da Ogun tun daga Litinin

    Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya (FRSC) ta ce ta hana motoci 791 shiga jihohin Ogun da Legas cikin kwana biyar, yayin da take aikin tabbatar da dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohin kasar.

    Kwamandan hukumar na jihohin, Mista Samuel Obayemi ne ya bayyana hakan ranar Asabar a wata hira da kamfanin dillancin labarai na NAN, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya ruwaito.

    Obayemi ya ce ma'aikatan hukumar sun tasa keyar ababen hawa 149 daga iyakokin Legas da kuma 642 a kan iyakokin Ogun tun daga ranar Litinin - ranar farko ta dokar - zuwa Juma'a.

    Ya ce dakarun hukumar sun samu rahoton hatsarin mota sau tara, wadanda suka yi sanadiyyar rasa ran mutum uku da kuma raunata 26 a wannan tsakanin.

  14. Masana kimiyya sun rude a kan illar rikidar kwayar cutar korona

    Masu bincike a Amurka da Burtaniya sun gano daruruwan hanyoyin da cutar dake harfar da korona take iya rikida.

    Sai dai har yanzu babu ko hanya daya da ta bayyana me hakan zai haifar game da bazuwar cutar cikin mutane da kuma yadda tasirin allurar riga-kafinta za ta kasance.

    Cutuka na rikidewa - wannan ne abin da suke yi.

    Tambayar anan ita ce, wacce ce daga cikin rikidar ke yin wani abu domin sauya hadari da kuma yadda ake kamuwa da cutar?

    Binciken da ya gabata daga Amurka ya ce daya daga cikin rikidar da cutar take - D614G - zai iya mamaye ko'ina a nan gaba kuma ya kara girman hadarin kamuwa da cutar.

  15. Karin mutum fiye da 10,000 sun kamu da korona a Rasha

    Rasha ta sake samun mutum 10,817 da suka harbu da cutar korona cikin sa'a 24 da suka gabata, abin da ya habaka jumillar adadin zuwa 198,676.

    Kwamitin yaki da cutar a kasar ya ce mutum 104 sun mutu a cikin kankanin lokaci, kuma adadinsu ya kama 1,827 jumilla.

    Tun daga ranar Lahadi ne adadin masu kamuwa da cutar ya rika karuwa da 10,000 - yanzu Rasha ce ta biyar a yawan masu cutar a duniya.

    Aranar Alhamis ta wuce Faransa (mai mutum 176,202) da Jamus (mai mutum 170,588), sannan tana bin Birtaniya a baya mai 212,629, a cewar alkaluman jami'ar Johns Hopkins.

  16. Najeriya ta samu adadi mafi yawa na kwana guda da suka kamu da korona

    An sake samun adadi mafi na mutanen da suka harbu da cutar korona a Najeriya cikin kwana guda, inda mutum 386 suka kamu, abin da ya kai jumillar adadin nasu zuwa 3,912.

    Hukumar NCDC mai dakile yaduwar cutruka a Najeriya ta ce karin mutum 176 ne suka harbu a Jihar Legas, sai 65 a Kano da kuma 31 a Katsina.

    A Jumlace, Jihar Legas ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar da mutum 1667, sai Kano mai 547, Abuja mai 336, Borno mai 142, Katsina mai 137, Bauchi mai 117, Ogun mai 113 da kuma Gombe mai 110.

    Mutum 117 ne suka rasa rayukansu a Najeriya, yayin da 679 suka warke daga cutar da ake yi wa lakabi da Covid-19.

  17. Covid-19: Samari sun fi 'yan mata karya dokar kulle

    Masana yadda dan Adam yake tunani sun ce samari sun fi yiwuwar karya dokar kulle fiye da ‘yan mata, a wani bincike da suka gudanar kan matasa 2,000 masu shekara tsakanin 13 zuwa 24.

    Rabin maza 'yan tsakanin shekara 19 zuwa 24 sun fita waje, inda suka gana da abokai da ‘yan uwa wadanda ba a gida daya suke zaune da su ba lokacin dokar kulle.

    Su mata 'yan tsakanin wadannan shekarun kashi 25 ne suka dauki irin wannan mataki.

    Masu binciken na Jami’ar Sheffield da kuma Jami’ar Ulster sun yi kira ga gwamnati ta matsa kaimi wajen wayar da kan matasa a kan illolin kin yin biyayya ga dokar kulle.

  18. Kusan mutum miliyan hudu sun kamu da korona a duniya

    Sabbin alkaluma daga Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka mai bibiyar yaduwar annobar korona sun ce mutum kusan miliyan hudu ne suka harbu da cutar a fadin duniya, yayin da kusan dubu 300 suka rasa rayukansu.

    Adadin mutum miliyan 3,951,905 ne suka harbu tun bayan bullarta a watan Disambar bara a birnin Wuhan na kasar China.

    Kazalika dubu 275,067 sun mutu sakamakon cutar, sai kuma miliyan 1,330,209 da suka warke.

    Kasashe biyar da suka fi fama da wadanda cutar ta harba:

    Amurka:1,283,929

    Spaniya: 222,857

    Italiya: 217,185

    Birtaniya: 212,629

    Rasha: 198,676

  19. Maraba

    Jama'a barkammu da sake saduwa a shafinmu na rahotanni kai-tsaye.

    Ku biyo mu domin sanin abubuwan da ke wakana a duniya musamman game da cutar korona.

    Umar Mikail ke muku maraba.