Rufewa
Masu bibiyarmu a nan za mu kawo karshen shirin namu da ke kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar coronavirus a Najeriya da sassan duniya. Da fatan za ku kasance da mu gobe da safe idan Allah ya tashe mu.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.
Nasidi Adamu Yahaya, Awwal Ahmad Janyau and Halima Umar Saleh
Masu bibiyarmu a nan za mu kawo karshen shirin namu da ke kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar coronavirus a Najeriya da sassan duniya. Da fatan za ku kasance da mu gobe da safe idan Allah ya tashe mu.
An kai Firai ministan Burtaniya, Boris Johnson bangaren kulawar gaggawa ga marasa lafiyar da ta tsananta.
Boris Johnson ya nemi sakatern harkokin wajen Burtaniya, Dominic Raab ya kula da ayyukan ofishinsa.
A ranar Lahadi ne dai aka kai Boris Johnson, asibiti domin yin gwaji kwana 10 bayan ya kamu da cutar coronavirus, a cewar fadar shugaban.
An kai shi wani asibiti a Landan a daren Lahadi dauke da alamomin cutar ciki har da zafin jiki.
A ranar 27 ga watan Maris ne dai Boris Johnson ya kamu da coronavirus, a cewar fadarsa ta Downing Street.
Mr Johnson ya nuna alamun cutar saisa-saisa kuma tuni ya killace kansa a fadar Downing Street.
Wata sanarwar da fadar ta fitar ta ce "Sakamakon gwajinsa ya nuna yana dauke da cutar, kuma ya yi gwajin ne bisa shawarar da babban likitan gwamnatin kasar Farfesa Chris Whitty ya ba shi.''
Sai dai zai ci gaba da jan ragamar gwamnatin na yaki da cutar kamar yadda sanarwar ta kara.
Ma'aikatan Hukumar Inshorar Lafiya Ta Ingila NHS ne suka yi masa gwajin a fadar tasa.
A wani sakon Twitter da ya wallafa, Boris Johnson ya ce: ''Cikin sa'a 24 da suka gabata ina ta jin alamun cutar sama-sama kuma an yi min gwaji ya tabbata ina dauke da coronavirus.
Kasar Faransa ta samu karin mutanen da suka mutu guda 833 a cikin sa'o'i 24.
Alklauman dai sun kunshi na mutanen da suka mutu a asibitoci and gidajen reno.
Yanzu haka adadin wadanda suka mutu sakamakon coronavirus a Faransa ya kai mutum 8,911.
Hakan na nuni da cewa Faransar ce ke biye wa Spaniya da Italiya wajen yawan mutanen da annobar ta kashe.
Sarakunan gargajiya na al’ummar arewacin Najeriya da ke a jihar Legas sun yi kira ga ‘yan arewa mazauna jihar da su kasance ma su bin doka da oda, musamman a wannan lokaci da cutar coronavirus ke bazuwa.
Hakan dai ya biyo bayan rahotannin da ke nuni d acewa ana samun wasu na cudanya domin gudanar da ibada, duk da gwamnatin jihar ta nemi a kiyaye haduwar jama'a fiye da guda biyu domin gudun yaduwar cutar ta coronavirus.
'Yan makaran da malamansu a birnin Kano sun fara anfani da gidajen rediyo domin watsa karatuttuka a yayin da ake ci gaba da rufe makarantu saboda cutar coronavirus.
Mafi yawancin daliban da ke shiga shirin dai 'yan aji shida ne na sakandire da ke shirin zana jarrabawar kammala makarantar.
Daliban na yin nazarin darussan Ingilishi da kimiyya da Lissafi da dai sauran su.
Tuni dai wasu daga cikin gwamnanin jahohin arewacin kasar suka fara amfani da sabuwar dabarar ta ci gaba da bayar da darasi ga daliban makarantu da ke zaune a gida.
Ko gabanin hukumomin ma su fara, tuni wasu dai-dai-kun mutane suka fara daukar nauyin irin wannan shirin na karatu daga nesa, a Kano da ma wasu makotan jahar.
Sama da mutum 10,000 cutar coronavirus ta kashe a Amurka, a cewar jami’arJohns Hopkins da ke bin diddigin annobar cutar a duniya.
Yanzu adadin mutum 10,335 suka mutu, sama da mutum 347,000 ke dauke da cutar a Amurka.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya snaar da sake samun karin mutum biyu da aka sallama daga cibiyar killace masu coronavirus da ke Yaba a birnin Legas.
Babajide wanda ya snar da hakan a shafinsa na Twitter ya ce wadanda aka sallamar mata ne guda biyu bayan da aka sake yi musu gwajin cutar coronavirus har sau biyu kuma aka ga ba sa dauke da kwayar cutar.
Gwamnan ya ce yanzu haka akwai mutum 31 da suka warke daga cutar kuma aka sallame su.
Ga wasu bayanai na baya-bayan nan daga Amurka da Canada
Zuwa yanzu masu dauke da coronavirus a Amurka sun kai 337,000 - fiye da na kasashen Italiya da Spaniya idan an hade. Yayin da Canada ke da mutum 15,900
Dakta Nasir Sani-Gwarzo wani fitacce kan harkar lafiya a Najeriya, ya ce yin sirace da ruwan zafi ba ya hana kamuwa da coronavirus amma zai iya taimakawa wajen jika makogwaro.
"Ita coronavirus cuta ce da take yaduwa ta hanci ko baki sai ta gangara makogwaro inda za tai ta hayayyafa har ta shiga huhu" a cewarsa.
Dakta Sani-Gwarzo ya ce idan ana yawan yin sirace, makogwaro zai zama a wanke ba tare da wata majina ba kuma wannan na iya taimakawa wajen hana cutar yaduwa, amma yin siracen ba ya maganin cutar.
Haka kuma shan ruwan dumi na taimakawa makogwaro wajen tsaftace shi da wanke shi yadda ya kamata ko da mutum ba ya dauke da wata cuta, amma Dakta Sani-Gwarzo ya ce ''wannan ba shi zai hana kamuwa da cutar ba kuma ba zai yi maganin cutar ba ga wanda ya kamu.''
Wata 'yar fim a Tunusiya ta ce masu taar da kayar baya na mata barazanar kashe ta bayan da ta fara sakin bidiyo a intanet tana rawar kada kugu da niyyar nishadantar da mutane a yayin da suke zaune a gida saboda rufe kasar da aka yi don hana yaduwar coronavirus.
Nermine Sfar ta ce wasu 'yan kungiyar al-Qaeda ne da ke zaue a kasar suke aike mata da sakon barzanar.
Rawar da take yi a intanet din kullum da daddare kai tsaye na jan hankalin mutane sosai da ke kallo.
Sfar ta ce ba kawai don ta nishadantar da mutane take rawar ba, tana kuma yi ne don sa su zama a gida.
Ba boyayyiya ba ce ita a kasar, a bara ma tana cikin wadanda suka tsaya takarar shugabancin kasar.
A fadin duniya, an mayar da filayen wasa asibitocin bayar da kulawar gaggawa yayin da yaduwar annobar coronavirus ta sa asibitoci suka yi kadan kuma ma'aikatan lafiya suka rasa wuraren da za su sa marasa lafiyar da yawansu ke karuwa.
Ganin yadda suke da sarari sosai, ana ganin filayen wasa a matsayin wuraren da suka dace a kafa asibitocin wucin gadi.
Don haka bayan shekara biyu ana aikin gyara shi, filin wasa na Onikan da ke Legas a Najeriya - wanda ya kamata ya zama cibiyar wasanni a kasar - a yanzu, za a bude shi a matsayin wurin killace masu fama da cutar Covid-19.
Legas ce cibiyar annobar a Najeriya - kuma jihar, wadda ta samu kanta a wani yanayi na neman inda za ta kafa cibiyoyin killace masu dauke da cutar, ta mayar da filin wasan mai iya daukar mutum 5,000 zuwa asibiti, a kokarinta na yaki da yaduwar cutar.
Filin wasan na iya daukar gadajen asibiti 110, kuma gwamnatin jihar Legas ce ta gina shi tare da hadin gwiwar wani banki, don rage nauyi ga cibiyar killace masu dauke da cututuka masu yaduwa da ke Yaba.
Tsohon Shugaban harkokin wasanni na jihar, Kweku Tandoh, ya kare matakin amfani da filin wasan bayan sukar da wasu 'yan jarida a bangaren wasanni suka yi wa matakin, wadanda ke ganin rashin dacewarsa.
"Babu wani laifi don an yi amfani da filin wasan saboda wannan lamari na gaggawa," ya ce wa BBC. "Abu ne da ake yi a fadin duniya. Ana amfani da filayen wasa na Real Madrid da na Maracana duk a matsayin asibitoci na wucin gadi.
'Yan sanda a Kamaru sun ce wasu 'yan kunar bakin waken kungiyar Boko Haram sun kashe mutum bakwai a harin da suka kai a wani gari da ke kan iyaka da Najeriya.
Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce 'yan kungiyar ta Boko Haram biyu sun tayar da bama-baman da ke jikinsu a garin Amchide ranar Lahadi da daddare.
Rahotanni sun ce cikin wadanda aka kashe har da dagacin garin.
Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka ta ce ya zuwa ranar 6 ga watan Afrilu coronavirus ta kashe mutum 442 a kasashe 51 mambobin kungiyar tarayyar Afirka.
Sanarar da hukumar ta fitar a Twitter ta ce mutum 9457 suka kamu da cutar a kasashen yayin da mutum 848 suka warke.
Afirka na cikin nahiyoyin da ba a samu gagarumar illar cutar ba.
Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta gargadi mazauna jihar cewa za ta hana su damar fita daga gidajensu kwata-kwata idan suka ci gaba da bijire wa dokar hana fita.
Muyiwa Adekeye, mai magana da yawun gwamnatin jihar, ya ambato mataimakiyar gwamnan Kaduna, Dr Hadiza Balarabe tana cewa gwamnati ta lura mutane suna bijire wa dokar ta hana fita.
A cewar mataimakiyar gwamnan, za a hana mutane damar da aka ba su ta fitowa tsakanin karfe uku na ranar ko wacce Talata zuwa Laraba domin sayen kayan abinci da sauran abubuwan bukata idan suka ci gaba da yin biris da dokar gwamnati.
Mutum biyar aka tabbatar sun kamu da coronavirus a Kaduna, ciki har da gwamnan jihar Nasir El-Rufai.
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya sanar da cewa za a haramta shiga da fita daga Nairob tsawon mako uku daga ranar Litinin karfe hudu a agogon GMT domin hana yaduwar coronavirus.
Daga bisani ranar Laraba za a haramta shiga da fita daa birnin Mombasa da yankuna kamar Kilifi da Kwale.
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar mutum goma da cutar coronavirus ta kashe tun bayan bullarta kasar.
Dakta Idi Illiassou Mainassara, ministan lafiya na Jamhuriyar Nijar ya ce mutum 13 suka warke a cikin 184 da suka kamu da wannan annoba zuwa yanzu.
Alkaluman da jami'ai suka fitar a jiya Lahadi na cewa mutum 40 sun sake kamuwa da cutar ta coronavirus.
Ministan lafiyar ya ce mutanen da suka rasu akasarinsu wadanda dama ba su da lafiya ne da ke fama da matsalar zuciya da huhu da ciwon suga.
“Lokacin da suka kamu ba su zo wurin likita ba da wuri, sai daga baya,” inji shi.
‘Yan sanda a Kamaru sun ce mayakan Boko Haram sun kashe mutum bakwai a wani harin kunar bakin wake da suka kai wani kauye da ke kan iyaka da Najeriya.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ya ce mayakan Boko Haram biyu sun tarwatsa kansu ne a kauye Amchide a daren lahadi. Rahotanni sun ce Hakimin garin na cikin wadanda aka kashe.
Masu zanga-zanga a birnin Abidjan a kasar Ivory Coast sun lalata cibiyar da ake ginawa domin gwajin cutar coronavirus.
Mazauna unguwar Yopougon sun yi koken cewa ana gina cibiyar ne cikin unguwar da ke da cunkosun jama’a, kusa da gidajensu.
Wani bidiyo a kafafen sadarwa na Intanet sun nuna yadda wasu gungun mutane suke lalata ginin tare da tarwatsa kayayyakin ginin.
Wani Jami’in ma’aikatar lafiya ya ce ana gina cibiyar ne domin gwaji, ba wajen kula da masu coronavirus ba.
Mutum 261 aka tabbatar da suna dauke da cutar Covid 19 a Ivory Coast, yayin da mutum 3 suka mutu.
Kimanin mutum miliyan 24 suk kalli jawabin da Sarauniyar Ingila ta gabatar ga al’ummar Birtaniya.
Yawan mutanen ya lunka adadin wadanda suka kalli jawabanta na baya-bayan nan kan kirsimeti, inda mutum miliyan bakwai suka kalla.
Ta godewa ma’aikatan da ke yaki da coronavirus, tare da yin kira ga jama’a su kasance “masu hadin kai da juriya”
Adadin yawan wadanda suka kalli jawabin a kafar talabijin, shi ne na biyu mafi girma a 2020 zuwa yanzu, ko da yake ba a san yawan wadanda suka kallo a kafar intanet ba
Sama da mutum miliyan 27 suka kalli jawabin Boris Johnson Firaministan Birtaniya lokacin da yake bayyana matakan yaki da coronavirus.
Dan wasan kwallon kafar Kamaru da West Ham Alex Song ya yi ritaya daga buga wa kasarsa tamaula bayan da aka cire sunansa daga jerin 'yan wasan da za su fafata a gasar cin Kofn Afirka.
Dan wasan mai shekara 27 wanda yanzu yake Barcelona a matsayin aro, zai samu zarafin buga wa West Ham kwallo a wannan watan bayan tattaunawarsa da Kamaru kan buga gasar Kofin Afirka ta ci tura.
Ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa:"Ba zan daina kaunar kasata ba har abada. Ina son samun lokaci na mayar da hankali wurin buga tamaula a gida sannan na sake gina sana'ata ta kwallon kafa a West Ham United."
Song bai buga wa Kamaru kwallo ba tun lokacin da aka fitar da shi a wasan da suka yi da Croatia a matakin rukuni na gasar cin Kofin Duniya ta 2014.