Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Buhari ya ba Sheikh Pantami Ministan Sadarwa

A ranar Larabar nan ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ke rantsar tare da bai wa sabbin ministoci 43 ma'aikatun da za su jagoranta, a sabon zangon mulkinsa na biyu.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Karshen rahotonnin, Rantsar da ministoci

    Masu sauraro nan muka kawo karshen rahotonnin ka-tsaye game da rantsar da ministocin gwamnatin Buhari karo na biyu.

    Ku ci gaba da kasancewa da mu a shafukanmu na Facebook da Twitter da Instagram domin samun karin wasu labaran.

    Umar Mikail ne da Usman Minjibir ke maku sallama.

  2. Ra'ayoyinku daga Twitter

  3. Ministoci da mukamansu

    1- Uchechukwu Ogah (Abia) - Ministan Ma'aikatar Tama da Karafa

    2- Muhammad Musa Bello (Adamawa) - Ministan Abuja

    3- Godswill Akpabio (Akwa Ibom) - Ministan Neja Delta

    4- Chris Ngige (Anambra) - Ministan Kwadago

    5- Sharon Ikeazor (Anambra) - Karamar Ministan Muhalli

    6- Adamu Adamu (Bauchi) - Ministan Ilimi

    7- Mariam Katagum (Bauchi) - Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari

    8- Timipre Sylva (Bayelsa) - Karamin Ministan Man Fetur

    9- George Akume (Benue) - Ministan Ayyuka Na Musamman da Harkokin Kasashen Waje

    10- Mustapha Baba Shehuri (Borno) - Karamin Ministan Noma da Raya Karkara

    11- Goddy Jedi Agba (Cross River) - Karamin Ministan Lantarki

    12- Festus Keyamo (Delta) - Karamin Ministan Neja Delta

    13- Ogbonnaya Onu (Ebonyi) - Ministan Kimiyya da Fasaha

    14- Osagie Ehanire (Edo) - Ministan Lafiya

    15- Clement Anade Agba (Edo) - Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare

    16- Otunba Richard Adeniyi Adebayo (Ekiti) - Ministan Masana'antu da Zuba Jari

    17- Geofery Onyeama (Enugu) - Ministan Harkokin Kasashen Waje

    18- Ali Isa Ibrahim Pantami (Gombe) - Ministan Sadarwa

    19- Emeka Nwajiuba (Imo) - Karamin Ministan Ilimi

    20- Suleiman Adamu (Jigawa) - Ministan Albarkatun Ruwa

    21- Zainab Shamsuna Ahmed (Kaduna) - Ministar Kudi

    22- Mohammed Mahmoud (Kaduna) - Ministan Muhalli

    23- Sabo Nanono (Kano) - Ministan Harkokin Noma

    24- Bashir Magashi (Kano) - Ministan Tsaro

    25- Hadi Sirika (Katsina) - Ministan Sufurin Jiragen Sama

    26- Abubakar Malami (Kebbi) - Ministan Shari'a

    27- Ramatu Tijani (Kogi) - Karamar Ministar Abuja

    28- Lai Mohammed (Kwara) - Ministan Yada Labarai da Al'adu

    29- Gbemisola Saraki (Kwara) - Karamar Ministar Sufuri

    30- Babatunde Raji Fashola (Lagos) - Ministan Ayyuka da Gidaje

    31- Adeleke Mamora (Lagos) - Karamin Ministan Lafiya

    32- Mohammed H. Abdullahi (Nasarawa) - Karamin Ministan Kimiyya da Fasaha

    33- Zubairu Dada (Niger) - Karamin Ministan Harkokin Kasashen Waje

    34- Olamilekan Adegbiti (Ogun) - Ministan Ma'adanai da Karafa

    35- Tayo Alasoadura (Ondo) - Karamin Ministan Kwadago

    36- Rauf Aregbesola (Osun) - Ministan Harkokin Cikin Gida

    37- Sunday Dare (Oyo) - Ministan Matasa da Wasanni

    38- Pauline Tallen (Plateau) - Ministar Harkokin Mata

    39- Rotimi Amaechi (Rivers) - Ministan Sufuri

    40- Mohammed Maigari Dingyadi (Sokoto) - Ministan Harkokin 'Yan Sanda

    41- Saleh Mamman (Taraba) - Ministan Lantarki

    42- Abubakar B. Aliyu (Yobe) - Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje

    43- Sadiya Umar Faruk (Zamfara) - Ministar Jin-kai da Walwalar 'Yan kasa

  4. An samu sababbin ma'aikatu

    Shugaba Buhari ya kirkiro sababbin ma'aikatu biyu. Su ne:

    Humanitarian Affairs (ma'aikatar jin-kai) da kuma Police Affairs (ma'aikatar harkokin 'yan sanda)

  5. An bai wa Pantami ministan sadarwa

    Isa Ali Pantami shi ne ministan sadarwa na tarayyar Najeriya.

    Janar Bashir Magashi shi ne ministan tsaro.

  6. Bikin rantsar da ministoci, Buhari na bayani

    Shugaba Muhammdu ne yake bayaninsa a yanzu, inda yanzu ne za mu san ma'aikatar da za a bai wa kowane minista.

  7. Bikin rantsar da ministoci

    Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya gama bayani yanzu, inda ya ce gwamnatin za ta mika kasafin kudin kasar na shekarar 2020 da zarar 'yan majalisun tarayya sun dawo daga hutun da suke yi.

  8. Bikin rantsar da ministoci

    Wannan shi ne rukunin karshe na ministocin da aka rantsar a yau, daga su an gama rantsuwar.

    Yanzu za mu jira mu ji ma'aikatun da za su rike har zuwa nan da shekara hudu masu zuwa.

  9. Bikin rantsar da ministoci, Bayanin Shugaba Buhari

    Yanzu haka dai mutane a ciki da wajen Najeriya sun kagu su ji bayanin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda a cikinsa ne zai bayyana ma'aikatun da kowanne minista zai rike.

    Saboda haka ba abin mamaki ba ne idan muka ce bayanin Shugaban shi ne mafi muhimmanci a wannan taron na yau.

  10. Bikin rantsar da ministoci

    Wani rukunin kenan na ministocin suke shan rantsuwar kama aiki.

  11. Ministoci mata guda bakwai ne daga cikin 43

    • Sharon Ikeazor daga Anambra
    • Ambasada Maryam Katagum daga Bauchi
    • Gbemi Saraki daga Kwara
    • Ramatu Tijani daga Kogi
    • Pauline Tallen daga Filato
    • Zainab Ahmed daga Kaduna
    • Sadiya Farouq daga Zamfara.
  12. Bikin rantsar da ministoci, Jerin sunayen ministoci

    • Sheikh Isa Ali Pantami - Gombe
    • Sanata Godswill Akpabio - Akwa Ibom
    • Alhaji Sabo Nanono - Kano
    • Rauf Aregbesola tsohon gwamnan - Osun
    • George Akume - tsohon gwamnan - Benue
    • Timipre Sylva - tsohon gwamnan - Bayelsa
    • Sanata Olorunnibe Mamora - Legas
    • Sunday Dare - Oyo
    • Festus Keyamo - Delta
    • Sanata Tayo Alasoadura - Ondo
    • Mustapha Buba Jedi Agba -
    • Olamilekan Adegbite - Ogun
    • Mohammed Dangyadi - Sokoto
    • Abubakar Aliyu - Yobe
    • Sale Mamman - Taraba
    • Muhammed Mamood - Kaduna
    • Uce Ogar - Abia
    • Emeka Nwajuiba - Imo
    • Akpa Udo
    • Clement Abam
    • Zubair Dada
    • Adeniyi Adebayo - Ekiti
    • Mohammed Abdullahi
    • Osagie Ehenere
    • Bashir Salihi Magashi - Kano
  13. Bikin rantsar da ministoci, Bikin rantsar da ministoci

    Wani rukuni na ministocin kenan suke shan rantsuwar kama aiki, yayin da Shugaba Muhammdu Buhari yake tsaye daga wurin zamansa yana sauraronsu.

    Kuma bayan haka kowannensu zai je gaban teburin Shugaba Buhari domin ya saka hannu a wani littafin rajista, inda daga baya shi kuma Buharin zai sa nasa hannun domin karbar rantsuwarsu.

  14. Bikin rantsar da ministoci

    Za ku iya kallon yadda bikin rantsuwar yake gudana kai-tsaye a shafinmu na Facebook.

  15. Bikin rantsar da ministoci, Rantsuwa

    Ana ci gaba da rantsar da sabbin ministoci

  16. Bikin rantsar da ministoci, Rantsuwa

    Shugaba Buhari ya fara rantsar da jami'an gwamnati, inda aka fara da rantsar da Sakataren Gwamnati, Boss Mustapha.

  17. Bikin rantsar da ministoci, Fuskokin ministoci

    Tsohon ministan Kwadago, Chris Ngige a hannun hagu tare da tsohon ministan birnin Abuja, Muhammad Bello lokacin da suke shan rantsuwar kama aiki a zangon mulkin Buhari na farko. Su ma sun shiga NextLevel.

  18. Bikin rantsar da ministoci, Fuskokin ministoci

    Tsohon ministan Shari'a na Najeriya, Abubakar Malami shi ma ya samu dawowa domin shiga NextLevel.

  19. Bikin rantsar da ministoci, Fuskokin ministoci

    Sabon minista Emeke Nwajuiba daga jihar Imo a tsakiyar wasu jami'an gwamnati lokacin da aka ba su bita dangane da yadda sabuwar gwamnatin Buhari za ta gudana, a Abuja.

  20. Bikin rantsar da ministoci, Fuskokin ministoci

    Wasu sabbin ministoci da suka hada da tsohon shugaban hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa, NITDA, Dr Isa Ali Pantami, lokacin da ake yi musu bitar kama aiki a Abuja.