Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/12/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. An kashe sojojin Burundi 20 a rikicin kan iyaka

    Rahotanni daga gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo sun ce an kashe sojojin Burundi aƙalla 20 a fafutukar ƙwace garin Kamanyola, inda Congo da Burundi da kuma Rwanda suka yi iyaka.

    Mayaƙan M23 sun ƙwace iko a garin, inda suka fatattaki dubban dakarun Congo masu samun goyon bayan sojin Burundi.

    Faɗan ya tilastawa fararen hula da dama barin yankin zuwa Rwanda, kwanaki bayan yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ta jagoranci ƙullawa tsakanin Rwanda da Congo.

    Rahotanni sun ce lamarin ya ƙazance sosai.

  2. Hukumar kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil da hodar ibilis a Lagos

    Hukumar kwastam ta Najeriya, NCS, ta kama wani jirgin ruwan ƙasar Brazil, MV San Anthonio a tashar jirgin ruwa ta Legas ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 25.5.

    An ɗaure ƙwayar ne a cikin wasu ƙunshi guda 24 kuma an sanya su a cikin jakunkuna biyar da aka ɓoye a cikin jirgin.

    Shugaban hukumar kwastam na yankin, kwanturola Emmanuel Oshoba, ya ce jami’an leƙen asirin hukumar ne suka kai samamen tare da haɗin gwiwar hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA.

    A cewar Oshoba, bayanan sirri da aka samu sun nuna cewa, bayan da jirgin ya tashi daga Brazil, ya tsaya a Honduras da Guatemala da wasu wuraren da aka san su da fataucin miyagun ƙwayoyi.

    Yayin da yake mika wa hukumar ta NDLEA ƙwayar da aka kama domin gudanar da bincike, Oshoba ya sanar da cewa an tsare jirgin.

  3. Mu na ci gaba da tattaunawa kan samun zaman lafiya - Zelensky

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yayi tattaunawa mai armashi ta waya da wakilin shugaba Trump, Steve Witkoff, da kuma sirikin shugaban, Jared Kushner.

    Wakilan Ukraine a tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin Trump ke jagoranta a birnin Miami ma sun shiga tattaunawar ta waya.

    Mr Zelensky ya ce sun tattauna yadda za a tabbata Rasha ta cika sharuɗɗan da aka yi tanadi a yarjejeniyar zaman lafiyan.

    Moscow dai ta jajirce a kan matsayarta, kuma tana ci gaba da kai hare-hare Ukraine.

  4. Za a ɗauki mataki kan masu POS da ba su yi rajista ba a Najeriya

    Hukumar kula da harkokin kamfanoni ta Najeriya (CAC) ta yi barazanar cewa za ta sake daƙile wasu masu aikin POS da ba su yi rijista ba a Najeriya daga ranar 1 ga watan Janairun 2026.

    A wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, hukumar ta ce dole ne a yi wa duk wani kamfanin PoS rijista da hukumar ko kuma a rufe shi nan take.

    Ta yi gargaɗin cewa babu wani mai POS da za a bar shi ya yi aiki ba tare da rajistar CAC ba, inda ta ƙara da cewa hukumomin tsaro za su tilasta bin dokar a faɗin ƙasar.

    Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, wannan dabi’a da ta saɓawa doka da wasu kamfanonin harkokin kuɗi na zamani (Fintech) ke taimakawa, na jefa tsarin hada-hadar kudi da jarin ƴan kasar cikin haɗari, inda ta jaddada cewa dole ne a taka masu burki.

  5. Netflix zai sayi wani ɓangaren Warner Bros akan farashin $72bn

    Netflix ya amince ya sayi ɓangaren shirya fina-finai na Warner Bros Discovery akan dala biliyan 72 a wata babbar yarjejeniyar da za ta sauya yadda ake gudanar da al'amura a masana'antar fina-finai ta Hollywood.

    Kamfanin ya kasance wanda ya yi nasarar sayen Warner Bros bayan doke abokan hamayyarsa Comcast da Paramount Skydance bayan fafatawar da aka yi.

    Warner Bros ya kasance mai iko da manya manyan fina-finai da suka haɗa da Harry Potter da Game of Thrones, da kuma dandalin nuna fina-finai na intanet HBO Max.

    A halin yanzu dai ana jiran yarjejeniyar ta sami amincewar hukumomin da ke kula da gasar kamfanoni a Amurka.

    Wasu daga cikin masana'antar fina-finai, ciki har da Writers Guild of America, sun soki yarjejeniyar, suna masu cewa za ta yi mummunan tasiri kan ma'aikata.

    Yayin da yarjejeniyar da aka amince da ita ta kasance kan wani ɓangare na kasuwancin Warner Bros, abokin hamayyar Netflix, Paramount ya gabatar da tayin siyan kamfanin gabaɗaya, gami da hanyoyin sadarwa, a cikin Oktoba.

    Warner Bros ya yi watsi da wannan tayin kafin ya sanya kansa a kasuwa.

  6. Senata Ndume ya buƙaci Tinubu ya janye sunayen jakadu

    Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriya, Ali Ndume, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya janye jerin sunayen jakadun da ke gaban majalisar a halin yanzu, bisa zargin cewa an saba wa ƙa’idar tsarin tarayya da kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada.

    A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne majalisar dattawa ta karɓi jerin sunayen waɗanda shugaba Tinubu ke neman ya naɗa, waɗanda aka miƙa wa kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ƙasashen waje domin tantance su.

    Sai dai Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar ya ce jerin sunayen ya ci karo da sashe na 14(3) na kundin tsarin mulkin ƙasar, wnda ya buƙaci a yi daidaito tsakanin ɓangarorin ƙasar wurin bayar da muƙaimai.

    Ya ce yayin da wasu jihohin ke da mutum uku ko huɗu, wasu kuma ba su da ko guda ciki har da jihar Gombe.

    “A wannan lokaci na rayuwar gwamnatinsa, dole ne shugaba Tinubu ya guji yanke shawarar da za ta iya haifar da rikicin ƙabilanci ko kuma haifar da rashin yarda tsakanin al'umma.

    "Ina roƙonsa da ya janye jerin sunayen, ya kuma gabatar da sabbin sunayen waɗanda aka zaɓa wanda zai dace da tsarin mulkin ƙasa," in ji shi.

  7. 'Yanmajalisar Rivers da suka koma APC maƙiyan dimokuraɗiyya ne - PDP

    Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi Allah wadai da ficewar 'yanmajalisar dokokin jihar Rivers 17 daga cikinta zuwa APC mai mulkin Najeriya.

    Sakataren PDP na ƙasa Ini Ememobong ya faɗa cikin wata sanarwa cewa 'yanmajalisar sun nuna kansu "a matsayin maƙiyan dimokuraɗiyya saboda barin jam'iyyar da aka zaɓe su".

    A ranar Juma'a ne 'yanmajalisar 17 tare da kakakin majalisar suka sanar da barin jam'iyyar, wadda ta daɗe tana fama da rikicin cikin gida a jihar da ke kudancin Najeriya.

    "Za a ci gaba da tuna mambobin majalisar Rivers a matsayin maƙiyan dimokuraɗiyya kuma waɗanda suka wulaƙanta majalisa," in ji Mista Ememobong.

  8. Rasha ta ƙaddamar da munanan hare-hare kan Ukraine cikin dare

    Rasha ta ƙaddamar da munanan hare-hare ta sama kan Ukraine yayin da ake ci gaba da tattaunawar tagaita wuta tsakanin Amurka da Ukraine ɗin a kwana na uku.

    Rasha ta harba jirage marasa matuƙa 653 da makamai masu linzami 51, waɗanda jami'an Ukraine suka ce sun kakkaɓe akasarinsu.

    Ɗaya aga cikinsu ya faɗa kan wani gini a tashar jirgin ƙasa da ke garin Festiv a kusa da birnin Kyiv, inda ya lalace ginin.

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenky ya ce harin "ba shi da wani amfani ta mahangar soja kuma su ma Rashawan suna sane da haka".

    Ma'aikatar kula da makamashi ta Ukraine ta ce Rasha ta hari tashoshin lantarki a yankuna takwas na ƙasar a hare-haren na yau Asabar, abin da ya jawo ɗaukewar wutar.

  9. Me ya sa ƙungiyar Kano Pillars ta kasa kataɓus a kakar bana?

    A ranar Laraba 3 ga watan Disamba ne ƙungiyar Rivers United ta jihar Rivers ta doke Kano Pillars da ci ɗaya mai ban haushi, lamarin da ya ƙara fama ciwon da ke damun magoya bayan ƙungiyar ta Kano.

    A wasan na mako na 15 a wasannin gasar cin kofin Firimiyar Najeriya, Rivers United ta zura ƙwallo a ragar Pillar ne a minti 88 a fara wasan, bayan magoya bayan ƙungiyar ta Masu Gida sun fara tunanin komawa da maki ɗaya, sakamakon da ya sa ƙungiyar ta ƙara zama daram a ƙarshen teburi.

    Zuwa yanzu ƙwallo bakwai suka zura tun daga fara gasar ta bana, amma an zura mata ƙwallo guda 17 a ragarta. Ke nan ƙwallo 10 ne ya raba tsakanin waɗanda ta jefa, da waɗanda aka jefa mata.

    A cikin wasa takwas na ƙarshe da ta buga, nasara ɗaya kawai ta samu, inda ƙungiyar ta doke ƙungiyar Ikorodu City da ci biyu da ɗaya a ranar 24 ga watan Nuwamban bana a filin wasa na Muhammad Dikko.

    A ranar Lahadi kuma za ta karɓi baƙucin Kun Khalifat a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina, kuma ko ta yi nasara za ta ci gaba da zama ta ƙarshen teburi.

  10. 'Yanbindiga sun harbe mutum 11 a Afirka ta Kudu

    'Yanbindiga sun kashe aƙalla mutum 11 a ɗakin kwanansu da ke Pretoria babban birnin Afirka ta Kudu.

    Cikin waɗanda suka mutu akwai yara biyu masu shekara uku da bakwai.

    Kazalika, maharan sun raunata mutum 14 lokacin da suka buɗe wuta kan mutanen da ke shaƙatawa da tsakar dare a unguwar Saulsville.

    Rundunar 'yansanda ta ce zuwa yanzu ba ta kama kowa ba kuma ba ta kai ga gano daliln kisan ba.

  11. An samu cigaba a tattaunawar zaman lafiya kan yaƙin Ukraine - Amurka

    Manyan wakilan Amurka da na Ukraine sun nemi Rasha ta nuna "aniya da gaske ta neman zaman lafiya mai ɗorewa" bayan gaza samun wani cigaba a tattaunawar da aka yi a Moscow a farkon mako.

    Wakilin Amurka na musamman Steve Witkof da Rustem Umerov na Ukraine sun shafe kwana biyu suna ganawa, wadda suka bayyana a matsayin "mai cike da cigaba" a Florida.

    Wata sanarwa da suka fitar ta ce kawo ƙarshen yaƙi ya dogara da niyyar Rasha ta "ɗaukar matakan tsagaita wuta da dakatar da kashe-kashe".

    A yau Asabar za a ci gaba da tattaunawar. A zaman baya, ɓangarorin sun amince da tsarin tsaron da za a aiwatar da zarar an ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta.

  12. Faɗa ya sake ɓarkewa tsakanin Pakistan da Afghanistan

    Faɗan kan iyaka ya sake ɓarkewa tsakanin dakaru Pakistan da na gwamnatin Taliban ta Afghanistan, inda kowane ɓangare ke zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Mazauna garin Spin Boldak na Afghanistan sun tsere daga gidajensu, wanda ke kan iyakar ƙasashen mai tsawon kilomita 2,600.

    Wani ma'aikacin lafiya a garin Kandahar ya faɗa wa BBC pashto cewa an kai gawar mutum huɗu asibitin yankin tare da raunata wasu mutum huɗu. An kuma raunata wasu mutum uku a Pakistan.

    Ƙasashen biyu sun yi ta gwabzawa a 'yan watannin nan, yayin da Taliban ke zargin Pakistan da kai hare-hare ta sama cikin Afghanistan.

    Ɓangarorin biyu sun tabbatar da fafatwar a cikin dare amma sun zargi juna da fara kai harin da ya jawo ɓarin wutar na kusan awa huɗu.

  13. Gwamnatin Kano na zargin 'yansiyasa da hannu a kama Muhuyi Magaji

    Gwamnatin Kano ta tabbatar da kama Muhuyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ranar Juma'a, inda ta yi zargi wasu 'yansiyasa da hannu a kamen nasa.

    Wata sanarwa daga ofishin Kwamashinan Shari'a Abdulkarim Maude ta ce jami'an 'yansanda ne suka kama lauyan a ofishinsa da ke kan titin Zariya da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, kuma suka tafi da shi hedikwatarsu da ke Bompai.

    Kwamashinan ya siffanta kamen da "abin damuwa sosai" wanda "ya yi kama da yanayin aikin soja". Ya yi iƙirarin cewa dakaru kusan 40 ne ɗauke da makamai suka je kama Muhuyi.

    "Kwamashinan ya nuna cewa akwai yiwuwar lamarin yana da alaƙa da binciken da ake yi wa wasu manyan 'yansiyasa," in ji sanarwar.

    Abdulkarim Maude ya kuma yi kira ga rundunar 'yansandan Najeriya ta yi cikakken bayani game da dalilin kama Muhuyi.

  14. Akpabio ya sake maka Natasha a kotu kan zargin ɓata suna

    Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya shigar da Sanata Natasha Akpoti ƙara a kotu kan zargin ɓata masa suna yana mai neman ta biya shi diyyar naira biliyan 200.

    Sanata Natasha mai wakiltar jihar Kogi ta tabbatar da karɓar sammacin a shafukanta na sada zumunta, inda ta nuna jin daɗinta tana mai cewa ta samu damar bayyana hujjojinta kan zargin yunƙurin lalata da ta zarge shi da yi a baya.

    "Yau 5 ga watan Disamban 2025, na karɓi sabon sammacin kotu kan ƙarar diyya ta naira biliyan 200 da Sanata Godswill Akpabio ya kai ni game da ɓata masa suna da zargin lalata," a cewar Natasha.

    "Na yi farin ciki da Sanata Akpabio ya taso da wannan batu saboda kwamatin ɗa'a na majalisa ya ƙi amincewa ya saurare ni kan batun sakamakon matar Akpabio ta shigar da ni ƙara a kotu."

    A watan Fabrairun 2025 ne Natasha ta zargi Akpabio da neman yin lalata da ita bayan rikicin da ya ɓarke a tsakaninsu, wanda ya kai ga dakatar da ita daga zaman majalisar na tsawon wata shida.

  15. Ƙasashen Musulmi sun soki Isra'ila kan shirin korar Falasɗinawa daga Gaza

    Ƙasashen Musulmi da dama sun soki shirin Isra'ila na buɗe mashigar iyakar Gaza da Masar ga Falasadinawan da ke son fita daga zirin kawai.

    A wata sanarwa ta haɗin gwiwa da Masar da wasu kasashe bakwai suka fitar, sun ce matakin tamkar wani yunkuri ne na korar Falasdinawa daga kasarsu.

    Ƙasashen sun yi kira da a buɗe mashigar ta kowane bangare - na shiga da kuma fita - kamar yadda shirin zaman lafiya na Shugaba Trump ya tanada.

    A baya Isra'ila ta ce za ta yi hakan ne kawai idan aka mayar mata da gawar mutum na karshe da ya rage cikin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza.

  16. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na yau Asabar.

    Ku biyo mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.