Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 07/07/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 07/07/2024

Taƙaitattu

  • Hamas ka iya amincewa da matakin kawo ƙarshen yaƙin Gaza
  • 'Yan bindiga sun yi garkuwa da 'yan jarida biyu tare iyalansu a Kaduna
  • 'Babu gudu ba ja da baya kan ficewarmu daga Ecowas'
  • Sabuwar shekarar Musulunci: Wasu jihohin Najeriya sun ayyana hutu ranar Litinin
  • Shugabannin ƙasashen Ecowas za su yi taro a Abuja

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulƙadir Mukhtar

  1. Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutum 22 a Katsina

    Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane 22 a garin Runka da ke ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

    Rahotanni sun ce maharan sun afka masu ne tsakar dare lokacin da yawancin jama’a ke barci.

    Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Hon. Abdul Jalale Haruna Runka ya ce: ''Abubuwa ne gasu nan babu daɗi, ana ta ƙoƙarin tattarewa amma mu kanmu abin ya ɗaure mana kai saboda duk wani inda muke samun information cewa gasu nan zasu fito, babu wani information da aka samu ba kamar yadda aka saba a baya da ake samun bayanin cewa suna nan tafe. Wannan kawai sai dai aka gansu a tsakiyar gari''

    Ya yi bayanin cewa a yanzu sun duƙufa domin nazarin yadda lamarin ya faru da kuma irin matakan da ya dace a ɗauka a kai.

    Shugaban ƙaramar hukumar Safana, Abdullaye Sani Safana ya ce yanzu haka suna da tabbacin cewa maharan suna riƙe da mutum 22 ''Da sun fi haka, amma akwai waɗanda suka dawo cikin dare da kuma safiyar Lahadi, a cikin su''

    Ya kuma bayyana yaƙinin cewa al'umma za su ci gaba da bayar da haɗin kai da goyon baya domin ganin an ceto waɗanda aka yi garkuwa dasu.

    Shugaban ƙaramar hukumar ya ce tuni aka jibge jam'an tsaro domin aikin kwato mutanen da kuma tabbatar da ba a sake samun irin hakan ba a nan gaba.

  2. An sake zaɓar Tinubu a matsayin shugaban Ecowas

    An sake zaɓar shugaban Najeriya Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasasen yammacin Afirka, shekara ɗaya bayan ya ƙarɓi ragamar shugabancin ƙungiyar.

    Shugaban Najeriyar ya ƙara samun wa'adin mulkin ne a yayin taron shugabannin ƙungiyar karo na 65, a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja, a ranar Lahadi.

    Ecowas ta yi fama da dambarwar juyin mulki a ƴan shekarun nan.

    Da yake jawabi, shugaba Tinubu ya buƙaci mambobin Ecowas su mayar da hankali wajen bayar da gudunmuwar su ta fannin kuɗaɗen gudanarwar ƙungiyar wanda ake amfani dasu wajen yaƙi da ayyukan ta'addanci.

    Ya ce: “Yayin da muke shirin ƙaddamar da shirin Ecowas na amfani da dakarunta na ko ta kwana wajen yaƙi da ta'addanci, dole in jaddada cewa akwai buƙatar a fitar da kuɗaɗe domin aiwatar da tsare-tsaren mu.''

    Tun da farko a ranar Lahadin, hukumar ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka, Ecowas ta yi gargaɗin cewa yankin, zai iya wargajewa bayan da ƙasashen Burkina Faso da Mali da kuma Nijar dake ƙarƙashin mulkin soji suka sanar da ficewar su daga ƙungiyar.

    Shugaban hukumar, Omar Touray, matakin da ƙasashen uku suka ɗauka barazana ce ga ƙungiyar mai shekara hamsin.

    Da ya ke jawabi a babban taron ƙungiyar a Abuja, Mr Touray ya ce ƙungiyar ta kafa makomar ta ne a kan mabobinta.

    Ya ce kafa wata sabuwar ƙungiya zai iya kawo cikas ga huɗɗar kasuwanci babu shamaki, da kuma zirga-zirga a tsakanin mutane miliyan ɗari huɗu na yankin.

    Ya kuma yi gargaɗin cewa ƙasashen uku na fuskantar barazanar zama saniyar ware saboda matakin da suka ɗauka, lamarin da kuma ya ce zai yi illa ga shirin yaƙi da matsalar tsaro da ta addabi ƙasashen yankin.

  3. An yi bikin tunawa da mutanen da aka kashe a zanga zangar Kenya

    Ɗaruruwan ƴan Kenya sun halarci wani biki a Nairobi domin tunawa da mutanen da aka kashe a zanga zangar adawa da tsare-tsaren gwamnati.

    Mutanen sun taru a filin wasa na Uhuru, inda suka riƙa rera waƙe da rawa, yayin da mawaƙa ke baje kolin su.

    Sun kuma bayyana waɗanda aka kashen a matsayin jarumai da suka sadaukar da kai wajen tabbatar da adalci a ƙasa.

    An kuma baje kolin sunayen mutum 39 da aka ce an kashe a lokacin zanga zangar.

    Jama'ar Kenya sun gufdanar da zanga zanga ne a sassan ƙasar domin nuna adawa da yunƙurin ƙarin haraji da gwamnati ta yi.

    Shugaban Kenya, William Ruto ya sha alwashin ɗaukar mataki kan duk ɗan sandan da aka samu da amfani da ƙarfin da ya wuce ƙa'ida.

  4. Amurka za ta kammala kwashe dakarunta daga Nijar a ranar Lahadi

    Rundunar sojin Amurka za ta kammala kwashe dakarunta da kayan aikin su daga barikin sojin sama ta babban birnin jamhuriyar Nijar a ranar Lahadi.

    Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta umarci dakarun Amurkan su fita daga ƙasar, bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.

    Nijar tana cikin ƙasashen da Amurka ta ƙulla ƙawancen yaki da ƙungiyoyi masu riƙe da makamai a yankin Sahel, kafin daga baya ƙasar ta koma sabuwar ƙawance da Rasha.

    Wannan yunkuri ya jefa Amurka a cikin tsaka mai wuya.

    Yanzu haka dai Amurka ta fara tunanin wajen da za ta mayar da cibiyar ajiye jiragen sama marasa matuki da a baya ta jibge a Najeriya.

    Rahotanni sun ce Amurka ta matsar da wasu daga cikin jami'anta dake Nijar ɗin zuwa wasu ƙasashen yammacin Afirka, yayin da mafi yawan su zasu koma Turai.

    Akwai kuma wasu rahotannin da ke cewa Rasha ta jibge dakarun ta a wasu cibiyoyin da Amurka ta kwashe dakarunta.

  5. Gwamna mace ta farko a Tokyo ta kama hanyar yin tazarce

    Wata ƙuri'ar jin ra'ayi ta nuna cewa gwamnar Tokyo, Yuriko Koike ta kama hanyar lashe wa'adin mulki na uku a jere a zaɓen da aka yi ranar Lahadi.

    Mai shekara 71 da haihuwa, wadda ita ce gwamna mace ta farko a birni mafi yawan jama'a a Japan, tana fatan samun sabon wa'adin mulki na shekara huɗu.

    Nasarar ta, sassauci ce ga Firaiminista Fumio Kishida da jam'iyyarsa ta LDP, masu goyon bayan zarcewar gwamnar.

    A 2016 aka fara zaɓen ta, kuma ta lashe wa'adin mulki na biyu a 2020.

    Gwamnar wadda ta ke a bangaren masu ra'ayin riƙau ta yi nasarar jagorancin birnin Tokyo a lokacin da aka yi fama da annobar Corona, da kuma yayin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics 2021.

    Batun karancin haihuwa na daga cikin manyan abubuwan da suka mamaye yaƙin neman zaɓen da aka yi a birnin, kuma duk wanda ya yi nasara zai yi fafutukar ganin ya kawo sauyi a kai.

  6. An samu fitowar masu zaɓe sosai a zagaye na biyu na zaɓen Faransa

    Mutane sun fito sosai domin kaɗa ƙuri'a a zagaye na biyu na zaɓen majalisar dokokin Faransa.

    An yi hasashen cewa zaɓen zai kafa tarihi a matsayin wanda aka fi samun fitar masu kaɗa ƙuri'a a cikin shekara 40.

    Fiye da kashi 85 na Kujeru Majalisar dokokin ne ake takara a kansu.

    Ana gudanar da zaɓen ne cikin tsauraran matakan tsaro saboda irin yaƙin neman zaɓen da aka gani, inda wasu ƴan takarar suka riƙa kai wa juna hari.

  7. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu 07/07/2024

  8. Isra'ila ta kashe wani babban jami'in Hamas a Gaza

    Harin da Isra'ila ta kai kan wata makaranta a birnin Gaza ya kashe wani babban jami'in ƙungiyar Hamas.

    Kafar yaɗa labaran Hamas ta ce an kashe Ehab al-Ghussein tare da wasu mutum uku a hari kan makarantar da ɗaruruwan Falasɗinawa ke neman mafaka a cikinta.

    Ehab al-Ghussein shi ne tsohon kakakin ma'aikatar cikin gida na Hamas, inda a baya-bayan nan kuma ya riƙe muƙamin mataimakin mistan ƙwadago.

    Rahotonni sun ce harin ya faɗa kan wasu azuzuwa biyu a makarantar.

    Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a faɗin Gaza, yayin da ƙungiyar Hezbollah ke ci gaba da kai hare-haren rokoki kan iyakar arewacin Isra'ilar.

  9. Giwa ta raunata mutum 13 a Sri Lanka

    Aƙalla mutum 13 ne suka jikkata a Sri Lanka bayan wata giwa da ake bikin addinin Hindu ta ita ta ƙwace, lamarin da ya sa mutane suka tarwatse da gudu bayan sun firgita.

    Bidiyon da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna ɗaya daga cikin masu kula da giwar na ƙoƙarin kama jelarta a wani yunƙurin na dagakar da ita.

    A wasu lokutan giwayen kan firgita a lokacin da ake tsaka da bukukuwan, sakamakon ihu da sowar mutane ko kuma kiɗe-kiɗen bukukuwan.

  10. Isra'ilawa za su yi zanga-zanga a faɗin ƙasar don matsa wa gwamnati lamba

    Isra'ilawa na shirya gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar, domin matsa wa gwamnati lamba ta cimma yarjejeniya da ƙungiyar Hamas don tabbatar da sakin sauran Isra'ilawan da Hamas ɗin ke tsare da su a Gaza.

    A baya an shafe tsawon wata tara ana gudanar da zanga-zanga a ƙasar, bayan Harin da Hamas ta jagoranta ranar 7 ga watan Oktoba.

    Masu zanga-zangar sun yi ta toshe tituna tare da hana ministocin gwamnati shiga shiga gidajensu.

    A kwanakin baya-bayan nan ne dai fatan cimmar yarjejeniyar ya taso, duk da cewa Isra'la na ci gaba da kai hare-hare cikin Gaza kan ƙungiyoyin Falasɗinawa masu ɗauke da makamai.

    A kan iyakar arewacin Isra'ila kuwa, ƙungiyar Hebollah ta Lebanon ta harba ƙarin rokoki.

  11. A yau Amurka za ta kammala kwashe dakarunta da ke birnin Yamai

    A yau ne Amurka ke kammala kwashe dakarunta daga sansanin sojin samanta da ke Yamai, babban birnin Nijar, inda a yanzu sansani ɗaya ne kawai da ke birnin Agadez ya rage mata.

    A watan Maris, gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da yanke alaƙar ƙawancen soji da Amurka, tun daga lokacin ne kuma ta mayar da hankali wajen ƙulla sabon ƙwance da Rasha.

    Nijar ɗin ta kuma saka wa'adin zuwa 15 ga watan Satumba, ga duka sojojin Amurka da ke ƙasar da su fice.

    A yanzu Amurka na son ƙwashe kashi biyu cikin uku na dakarun nata da kuma kayan aikinsu zuwa ƙarshen watan Yulin da muke ciki, kamar yadda yarjejeniyar ta nuna.

    Kafin juyin mulkin da sojoji suka yi a bara, Nijar ta kasance muhimmiyar ƙawar Amurka a yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.

  12. Kotu ta umarci Sadiya ta faɗi yadda aka kashe kuɗin tallafi naira biliyan 729

    Babbar kotun tarayyar da ke Legas ta umarci tsohuwar minsitar jinƙai, Sadiya Umar Farouk, da ta yi bayanin yadda aka kashe naira biliyan 729 na tallafin da aka raba wa talakawan ƙasar na tsawon wata shida.

    Cikin hukuncin da ya yanke, mai shari'a Deinde Isaac Dipeolu ya kuma umarci tsohuwar ministar ta wallafa sunaye da bayanan mutanen da suka amfana da tallafin da jihohin da aka raba, da yawan kuɗin da akla raba akowace jiha.

    Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci da rashawa ce ta gurfanar da Sadiya Farouk a gaban kotun, inda ta buƙaci kotun ta tilasta mata bayar da bayanan, kasancewar kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba ta 'yancin samun bayanan.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, SERAP ɗin ta ce ta samu kwafin hukuncin da kotun da yi ranar Juma'a.

    Alƙalin kotun ya ce kotu ta tilasta wa tsohuwar ministar bayar da bayanan, kasancewa kundin tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadin bayar da bayanai ga kowane ɗan ƙasa ciki har da SERAP.

    ''Don haka kotu ta umarci tsohuwar ministar ta yi bayanin yadda ta kashe naira biliyan 729 wajen raba wa talakawan Najeriya miliyan 24.3 a shekarar 2021'', kamar yadda hukuncin ya nuna.

    Mai shari'a Dipeolu, ya kuma ce dole ne tsohuwar ministar ta yi wa SERAP cikakkun bayanan hanyoyin da aka bi wajen zaɓo mutanen da suka amfana da tallafin.

    Sannan kotun ta kuma umarci ministar ta yi bayanin hikimar biyan naira 5,000 ga talakawan ƙasar miliyan 24.3, wanda adadin kuɗin ya kai kashi biyar cikin 100 na kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2021.

    Tun da farko dai lauyan tsohuwar ministar ya buƙaci kotun ta yi watsi da buƙatar ƙungiyar ta SERAP, to sai dai alƙalin kotun bai amince da buƙatar lauyan tsohuwar ministar ba.

  13. Shugabannin ƙasashen Ecowas za su yi taro a Abuja

    Shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka za su gudanar da taro a Najeriya yau Lahadi, yayin da wasu ƙasashen yankin ke fama da rikicin siyasa.

    Taron nasu na zuwa ne kwana guda bayan ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso suka sanar da yanke hulda da ƙungiyar Ecowas.

    Ana sa ran batun ficewar ƙasashen uku daga ƙungiyar da kuma kafa runduna tsaro ta musamman don yaƙi da matsalar tsaro da yankin ke fuskanta ne za su kankane taron na Ecowas da za a yi a Abuja fadar gwamnatin jihar.

    Wasu daga cikin shugabannin ƙasashen yankin ne dai suka kira taron na yau da nufin sasantawa da jagororin mulkin sojin ƙasashen uku.

    A taron da shugabannin Mali da Nijar da Burkina Faso suka gudanar jiya a birnin Yamai, Shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ya ce ƙasashen uku ba za su koma cikin ƙungiyar Ecowas ba, bayan da suka zargi ƙungiyar da haɗa kai da Faransa.

    Sojojin mulkin ƙasashen sun kori dakarun Faransa daga ƙasashensu, sannan suka koma ƙulla ƙawance da Rasha.

    Amurka ce ƙasa ta baya-bayan nan daga ƙasashen Yamma da za ta janye dakarunta daga Nijar, bayan da ƙasar ta soke yarjejeniyar ƙawance sojinta da Amurka.

  14. Sabuwar shekarar Musulunci: Wasu jihohin Najeriya sun ayyana hutu ranar Litinin

    Wasu jihohin Najeriya sun ayyana gobe Litinin 8 ga watan Yuli, a matsayin ranar hutu ga ma'aikata don murnar shiga sabuwar shekarar musulunci ta 1446 Bayan Hijira.

    Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Kano ta fitar ta hannun kwamishinan yaɗa labarai, Baba Dantiye, ta ce Litinin ta zama ranar hutu ga ma'aikatan jihar, sannan gwamnan jihar ya yi kira ga al'ummar jihar su ɗorawa kan kyawaan ayyukan da suke gudanarwa.

    Ita gwamnatin jihar Borno, cikin sanarwar da muƙaddashin gwamnan jihar, Umar Kadafur, ya fitar, ya sanar da hutun ranar Litinin domin girmama shigar sabuwar shekarar ta Musulunci.

    Haka gwamnan jihar Osun da ke kudancin ƙasar, Ademola Adeleke ya sanar da hutu a ranar, tare da sanar da cewa zai jagoranci taron tattaki a wani ɓangare na bukukuwan shigar sabuwar shekarar.

    Sauran jihohin da suka sanar da hutun a gobe Litinin sun haɗa da Oyo da Kebbi da Kwara da Jigawa.

  15. Amsoshin Takadunku 06/07/2024

    A cikin shirin namu na wanna makon - wanda Ibrahim Yusuf Mohammed ya gabatar - za ku ji abinda kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce kan sarakunan addini da na gargajiya.

    Haka kuma shirin ya amsa tambaya game da tarihin shugaban mulkin sojin Nijar na farko, Janar Seyni Kountche.

  16. 'Yan bindiga sun yi garkuwa da 'yan jarida biyu tare iyalansu a Kaduna

    Masu garkuwa da mutane sun sace 'yan jarida biyu tare da matansa da 'ya'yansu a jihar Kaduna.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar 'yan jarida ta ƙasa, NUJ reshen jihar ta fitar, ta ce lamarin ya faru ne ranar Asabar da daddare a gidajensu a unguwar Danhono da ke yankin ƙaramar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

    Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare lokacin da 'yan bindigar suka shiga unguwar riƙe da makamai suna harbin kan mai tsautsayi.

    Ƙungiyar NUJ ta kaɗu da labarin garkuwa da 'yan jaridun biyu da ta ce suna aiki ne da jaridun 'The Nation' da kuma 'The Blue Print' da kuma iyalan nasu.

    Ƙungiyar ta kuma yi Allah wadai da faruwar lamarin, tare da yin kira ga jami'an tsaro a jihar su jajirce wajen kuɓutar da su.

    Jihar Kaduna na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro, inda a wasu lokuta 'yan bindiga ke kai hare-hare tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.

    Ko a watan Maris na wannan shekarar ma wasu 'yan bindiga suka kai hari makarantar Kuriga da ke jihar, tare da sace ɗalibai fiye da 100, kodayake daga baya ukumomi sun kuɓutar da su bayan shafe wasu kwanaki.

  17. Ƙasashen Gabas ta Tsakiya sun taya sabon shugaban Iran murna

    Saudiyya ta jagoranci ƙasashen gabas ta tsakiya wajen taya Masoud Pezeshkian murnar lashe zaɓen shugaban ƙasar, cikin wani yanayi mai ban mamaki.

    Sarki Salman na Saudiyya ya bayyana fatansa na ci gaba da samun bunƙasar dangantakar da ke tsakanin ƙasashenmu biyu.

    Ita ma Hadaddiyar Daular Larabawa, da sarakunan Qatar da Kuwait da kuma sarkin Bahrain duka sun mika nasu sakonnin taya murnar.

    Kungiyar Tarayyar Turai ta ce a shirye ta ke ta yi hulɗa da sabuwar gwamnatin bisa manufar EU.

    Mista Pezeshkian - mai ra'ayin kawo sayin - ya samu nasara da rata mai yawa a ranar Juma'a.

    Sabon shugaban, wanda likitan zuciya ne, ya yi yaƙin neman zaɓe kan alƙawarin sauƙaƙa takunkuman ƙasar, da saukaak dokokin da aka sanya kan rayuwar jama'a da kuma rage karfin hukumar Hisbah.

  18. Hamas ka iya amincewa da matakin kawo ƙarshen yaƙin Gaza

    Akwai alamun cewa kungiyar Hamas za ta iya cimma matsaya da Isra'ila don kawo ƙarshen yakin Gaza.

    Rahotannin daga wasu majiyoyi masu alaƙa da ƙungiyar da kuma Masar sun ce Hamas ta amince da daftarin yarjejeniyar na Washington, sannan ta jingine buƙatar sai lallai Isra'ila ta yi alƙawarin kawo ƙarshen yakin kafin a ci gaba da tattaunawa.

    To sai dai har yanzu, sai an jira an ga ko gwamnatin Isra'ila za ta amince da wannan, sannan ko ita ma za ta sassauta a kan matsayarta ta ci gaba da yaƙin bayan ƙarewar tsagaita wuta.

    Tun da farko dai sojojin Isra'ila sun tabbatar da cewa sun kai wani hari ta sama kan wata makarantar da Majalisar Dinkin Duniya ke kula da ita a Gaza, lamarin da ya janyo mutuwar yan ba ruwana 16.

  19. Assalamu alaikum

    Masu bin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Sai ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.