Sai da safenku
- Marubuci, Ahmad Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 24 ga watan Yulin 2025.
Haruna Kakangi, Aisha Babangida da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Jami'ai a Siriya sun ce aƙalla mutum shida sun rasa rayukansu yayin da ɗaruruwa suka jikkata a arewa maso yammacin lardin Idlib sakamkon wata fashewa.
Ba a dai san abin da ya haifar da fashewar ba, wadda ta afku a cibiyar ajiyar makami da ke birnin Maarrat Misrin.
An kai waɗanda suka samu raunuka asibitocin da ke kusa, an kuma umarci jama'a su ƙauracewa yankin da lamarin ya faru.
Yin tattaki kafa 7,000 a kullum shi kaɗai yana ƙara wa kwakwalwa lafiya da kuma taimakawa mutum daga kamuwa da cututtuka daban-daban, kamar yadda wani bincike ya gano.
Abu ne mai kyau bayan da aka amince da tattakin kafa 10,000 a can baya, a matsayin iya adadin ya kamata mutum ya yi.
Bincike wanda aka wallafa a mujallar lafiya ta The Lancet, ya gano cewa yin tattaki kaɗan ma yana da alfanu wajen rage barazanar kamuwa da cutuka masu tsanani, ciki har da kansa da cutar mantuwa da kuma cutukan zuciya.
Karanta cikakken labarin a nan...
An samu rahotannin kashe aƙalla mutum 16 a rikici tsakanin ƴantawayen M23 da Rwanda ke goyon baya da dakaru a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo.
Al'amarin na zuwa kwanaki biyar bayan gwamnatin Kinshasa da ƴantawayen M23 sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Qatar.
Mazauna Masisi sun ce lamarin ya rutsa da fararen hula da dama.
Kafofin yaɗa labarai a arewacin lardin Kivu sun zargi mayakan M23 da yunkutin ƙwace ƙauyuka da dama a wannan makon, abin da kakakin ƴan tawayen ya musanta.
Sabon shugaban jam'iyyar APC, Nentawe Yilwatda, ya ɗau alwashin ɗaukar matakai don ganin ya ƙara janyo gwamnonin babbar jam'iyyar adawa ta PDP zuwa cikin jam'iyyar mai mulki.
Yilwatda ya bayyana haka ne yayin tattaunawa a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, jim kaɗan bayan zama shugaban APC.
Ya ce baya ga ƴan jam'iyyar PDP da zai janyo zuwa APC, har da wasu ƴaƴan jam'iyyun adawa.
"Abun da na fi mayar da hankali a yanzu shi ne ganin haɗin kan jam'iyyar mu," in ji shi - inda ya ce zai tabbatar da cewa jam'iyyar ta yaɗa manufofinta yadda ya kamata.
Sabon shugaban jam'iyyar ta APC ya ce duba da irin tarihi da yake da shi a fannoni daban-daban, yana da ƙwarewar da ta kamata wajen jagorantar jam'iyyar mai mulki.
Isra'ila ta ce za ta dawo da masu shiga tsakanin da ta aika zuwa wurin tattaunawar tsagaita wuta a Gaza, sakamakon martanin da Hamas ta mayar wa masu shiga tsakanin.
An kwashe sama da makonni biyu masu shiga tsakani na Qatar da Masar na neman yin sulhu ta bayan fage da fatan kulla yarjejeniyar da Amurka ke mara wa baya na dakatar da faɗa da kuma sako mutanen da aka yi garkuwa da su.
Wakilin Shugaba Trump a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff, ya je Italiya domin ganawa da manyan jami'an Isra'ila da kuma na Qatar.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan abin da ya kira watsi da yankin arewacin Najeriya, inda ya ce shugaban ya fi mayar da hankali kan gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wajen taron shawarwari na masu ruwa da tsaki a jihar Kano na 2025 - wanda aka gudanar yau Alhamis, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
"Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan," in ji Kwankwaso.
Karanta cikakken labarin a nan
Motocin agaji na hukumar kula da ƴan gudun hijirar Falasɗinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Unrwa, kusan motocin agaji 6,000 ɗauke da abinci da magunguna ne ke jira don samun izinin shiga Gaza, a cewar shugaban hukumar.
A ranar 20 ga watan Yuli, Falasɗinawan da ke zaman mafaka a wata makarantar ƴan mata da Unrwa ta tanada suka gudanar da zanga-zanga kan batun yunwa da suke ciki.
Shugaban hukumar hukumar ya ce ɗaya cikin yara biyar a birnin Gaza na fama da rashin abinci mai gina jiki.
A wani sako da ya wallafa a shafin X, Philippe Lazzarini ya ce "yawancin yaran da muka gani sun jigata sannan suna cikin fargabar iya mutuwa idan ba su samu kulawar da suke buƙata ba".
"Iyaye na cikin yunwar da ba za su iya kula da ƴaƴansu ba", in ji shi, inda ya ƙara da cewa "wannan matsala da ake ciki tana shafar kowa".
Jami'an lafiya na Unrwa na "rayuwa ne kan cin abinci sau ɗaya a rana," in ji shi, inda ya ce akwai wasu ma'aikatans da ke tsuma lokacin aiki.
Wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta bai wa Sufeto-Janar na ƴansandan Najeriya da kuma kwamishinan ƴansandan jihar da su biya masu zanga-zangar EndSars diyyar miliyan 10, saboda take ƴancinsu.
Mai shari'a Musa Kakaki da yake yanke hukunci, ya ce an musgunawa masu zanga-zangar kuma an take musu ƴancin da kundin mulki ya ba su yayin da suke maci na tunawa da waɗanda aka kashe lokacin zanga-zangar ranar 20 ga Oktoban, 2024.
"Duk da cewa jami'an tsaro na da ƴancin da kundin mulki ya ba su na tabbatar da doka da oda, amma bai kamata su yi amfani da ƙarfi fiye da ƙima ba wanda ya saɓa wa dimokraɗiyya da kuma doka," in ji mai shari'a Kakaki.
Waɗanda suka shigar da ƙara a gaban kotun sun haɗa da Hassan Taiwo Soweto, Uadiale Kingsley, Ilesanmi Kehinde, Osopale Adeseye, Olamilekan Sanusi, da Miss Osugba Blessing da sauransu.
Akwai wasu ƙungiyoyi kare hakkin ɗan'adam da dama da suka mara musu baya irinsu Education Rights Campaign, Take It Back Movement (TIBM), da kuma Campaign for the Defence of Human Rights.
Rasha da Ukraine sun kai wa juna hare-haren jirage marasa matuƙa inda aka kashe mutum biyu a Rasha da uku a Ukraine, bayan kammala zagaye na uku na tattaunawar tsagaita wuta da aka yi a Istanbul.
A yankin Kharkiv da ke gabashin Ukraine, an samu gawarwaki uku daga ɓaraguzan wani gida da aka kai wa hari, yayin da wasu mutane da dama suka jikkata a biranen Cherkasy da Zaporizhzhia.
Haka kuma, harin ya shafi wata kasuwa da ke Odesa, inda gobara ta tashi a sassa daban-daban na birnin.
A nata ɓangaren, Rasha ta ce mutum biyu ne sun mutu a harin kuma 11 suka jikkata sakamakon a birnin Sochi da ke yankin Krasnodar.
Wani sabon hari da Rasha ta kai Kharkiv da safe ya jikkata mutum 33.
Wakilan ƙasashen biyu sun gana a Istanbul domin cimma tsagaita wuta amma ba a samu wani ci gaba ba amma dai sun amince da musayar fursunoni 1,200 da kuma miƙa gawarwakin sojojin Ukraine 3,000 da suka mutu.
Kowane ɓangare ya zargi dayan da ƙin amincewa da shawarwarin da aka gabatar.
Gwamnan Kivu ta Kudu, Patrick Busu bwa Ngwi Nshombo, ya bayyana cewa an ceto mutum 12 a wurin haƙar ma’adinai da ya rufta a Lomera da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo a ƙarshen mako.
A cewarsa, har yanzu ana ci gaba da aikin ceto, amma ba a tantance yawan waɗanda suka mutu ko suka ɓace ba tukuna.
“Muna ƙoƙarin gano yawan mutanen da har yanzu ba a gan su ba,” in ji gwamnan yayin ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya faru a ranar Laraba.
Lamarin ya faru ne a wani wurin haƙar ma’adinai na zinare da hannu da ke Lomera, inda hukumomi ke ƙiyasta cewa aƙalla mutum 4,786 ne ke aiki a yanayi mai haɗari da tsanani.
Tun daga lokacin da lamarin ya faru gwamnan ya ba da umarnin rufe dukkanin ramukan da abin ya shafa,
Kwamitin zartarwa na Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ya amince da nadin Farfesa Nentawe Yilwalda daga jihar Filato a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na kasa.
An cimma matsayar ne yayin taron kwamitin zartarwar na kasa da ya gudana a Abuja.
Taron wanda ke gudana a fadar shugaban kasar, na samu halartar Shugaba Bola Tinubu da kuma gwamnonin jam'iyyar.