Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da zai kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/09/2024

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed, da Umar Mikail

  1. Tsohon ministan sufuri a Singapore ya amsa laifi a tuhumar rashawa

    Tsohon ministan sufuri a Singapore ya amsa laifi a tuhumar rashawa da aka gabatar a kansa a rana ta farko da soma wannan shari'a da ta kasance mafi girma kan ɗansiyasa da aka taɓa gani cikin shekaru 50.

    An zargi S Iswaran da karɓar nagoron da kuɗaɗensu ya kai dala dubu 400, ciki har da tiketin jirgi da biya masa kuɗin zaman Otel da tiketin zuwa taron makaɗa da bukukuwan sharholliya.

    Yana fuskantar tuhume-tuhume 35 ciki har da rashawa amma mai gabatar da ƙarar ya rage su zuwa biyar, da huɗu na karɓar kyaututuka a matsayinsa na ma'aikacin gwamnati, ɗaya kuma na yi wa shari'a karan-tsaye.

    S Iswaran ya taka muhimmiyar rawa a lokacin da yake minista, musamman ta fuskar kai manyan harkokin kasuwanci ga Singapore.

  2. Za mu bijiro da tsarin da zai kawo ƙarshen rikicin Isra'ila da Hezbollah

    Gwamnatin Biden ta ce za ta gabatar da tsari mai ƙarfi da zai kawo ƙarshen rikici a Lebanon a taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniya na wannan makon a New York.

    Gwamnatin ta kuma ce za ta tura ƙarin jami'an tsaro ƙalilan zuwa yankin.

    Babban Jami'in harkokin ƙetare a ƙungiyar Tarayyar Turai, Joseph Borrell, ya yi gargaɗi cewa rikicin na neman rikiɗewa zuwa gagarumin yaƙi.

    Ya ce fararan hula ke ɗanɗana kuɗarsu a wannan yaƙi, don haka Tarayyar Turai na aiki tuƙuru wajen dakatar da ƙazancewar rikici, sai dai babban abin da ake fargaba da gab da tabbata.

    Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya nuna matuƙar damuwarsa kan tsaron fararan-hula, a kudancin Lebanon da kuma arewacin Isra'ila.

  3. Gwamnatin Najeriya ta ce an samu na'ukan cutar polio guda 70 a jihohi 14 na arewacin ƙasar

    Najeriya na fuskantar ƙaruwar yaɗuwar sabuwar na'uin cutar polio ta cVPV2, kamar yadda Hukumar Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta bayyana.

    Babban daraktan hukumar, Dokta Muyi Aina ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja a wani taro da ya yi da shugabannin addini, wanda hukumar ta shirya tare da haɗin gwiwar Gidaunar Sultan wato Sultan Foundation for Peace and Development.

    Ya ce an samu jimillar na'uin 2 cVPV2 guda 70 a ƙananan hukumomi 46 a jihohi 14 na arewacin Najeriya.

    A cewarsa, "wannan na nuna cutar na cigaba da yaɗuwa saboda ƙarancin aiwatar da allurar riga-kafi. Dole a canja wannan tsarin. Dole mu tabbatar kowace mace ta samu kula a lokacin da take ɗauke da juna biyu, sannan ya zama ƙwararru ne suke amsar haihuwa, sannan mu tabbatar kowane jariri na kammala allulorinsa na riga-kafi kamar yadda aka tsara."

    Ya yi kira ga shugabannin addini da su ƙara ƙaimi domin tabbatar da shirin allurar riga-kafi na tafiya daidai.

  4. China ta yi wa tattalin arzikinta garambawul

    Babban Bankin Ƙasar China ya ƙaddamar da wasu sabbin tsare-tsaren bunƙasar tattalin arzikin ƙasar da ke cikin yanayin tangal-tangal.

    Ya rage yawan kuɗaɗe a asusun ajiyarsa da kuma zabtare haraji kan wasu kuɗaɗe na lamuni da kashi 50 cikin ɗari.

    Gwamnan Bankin, Pan Gongsheng, ya ce maƙassudin hakan shi ne ba da lokaci mai tazara domin cinikin kadarori ba tare da hakan ya shafi farashin kayayyaki a kasuwanni ba, da kuma samar wa mutane rangwame.

    China dai ita ce ta biyu mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya, kuma har yanzu ba ta farfado daga illar da annobar korona ta yi mata ba.

  5. Shugaban Ukraine zai gabatar da jawabin neman ƙarin goyon baya MDD

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, na shirin gabatar da jawabi a zauren kwamitin tsaro na MDD a birnin New York, inda zai nemi ƙarin goyon-baya domin samun gallaba a yaƙi da Rasha.

    A lokacin zantawa da tashar ABC, Mista Zelensky ya ce daftarin da ya tsara gabatarwar zai ya ƙunshi neman ƙarin tallafin kuɗaɗe, makamai da tabbacin tsaro daga ƙasashen Yamma, wanda yake da tabbacin za su tursasawa Rasha hawa teburin Sulhu.

    Mista Zelensky na kuma shirin gabatar wa babban taron MDD buƙatunsu ne a yau Talata.

    Shi ma Shugaba Biden na Amurka a yau zai gabatar da jawabinsa na ƙarshe a matsayinsa na shugaban ƙasa a zauren MDD a game da yaƙin Ukraine.

  6. Jirgin ruwan Masar ya kai makamai Somalia

    Wani jirgin ruwan Masar ya kai makamai zuwa ƙasar Somalia kamar yadda wani jami'in tsaro a babban birnin ƙasar, Mogadishu ba bayyana.

    Ministan Tsaron Somalia, Abdulƙadir Mohamed Nur ya bayyana godiyarsa ga Masar a kafofin sadarwa, amma bai bayyana adadin makaman ba.

    Wannan ne karo na biyu da Masar ta kai wa Somalia makamai a cikin wata ɗaya a daidai lokacin da dangantaka ke ƙara tsami tsakanin ƙasar da maƙwabciyarta kuma tsohuwar ƙawarta Ethiopia.

    Wannan ya sa ita kuma Masar, wadda ta daɗe tana takun-saƙa da Ethiopia ta yi amfani da damar wajen ƙara kusantar Somalia, wanda hakan ya ƙara ta'azzara tashin hankalin.

    An ga jirgin ruwan yana sauke manyan makamai da motocin yaƙi kamar yadda Reuters ta ambato daga wani jami'in tsaro a ƙasar.

    Wakilin BBC da ke Mogadishu shi ma ya gane wa idonsa yadda ake sauke makaman, sannan aka kwasa zuwa cikin gari.

    A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Nur ya ce, "Somalia ta wuce lokacin da za a jan akalarta sannan wai sai ta jira amincewar wata ƙasa kafin ta yi alaƙa da wata ƙasar. Muna san abubuwan da muke so, sannan za mu zaɓa ƙawayenmu da maƙiyanmu. Muna godiya Masar."

  7. Na yi da-na-sanin rashin sayen Arsenal - Dangote

    Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce yanzu lokaci ya wuce da zai saya ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal da ke Ingila, inda ya ce zai cigaba da zama mai goyon bayan ƙungiyar a duk lokacin da take wasa.

    Dangote ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Bloomberg, inda ya ce yana kallon wasannin ƙungiyar sosai.

    "A zantawarmu ta baya na ce da zarar na kammala aikin gina matatar man fetur ɗina zan koma batun sayan Arsenal. Amma yanzu lokacin wannan maganar ya wuce domin komai yanzu ya yi tsada, sannan yanzu ƙungiyar tana ƙoƙari sosai, amma a wancan lokacin da na yi maganar ƙungiyar ba ta kan ganiya."

    Da aka tambaye shi ko ya yi da-na-sanin rashin sayan ƙungiyar a wancan lokacin, sai ya ce, "gaskiya na yi da-na-sani, amma kuma a lokacin na fi buƙatar kuɗin wajen kammala aikin da na ɗauko na gina matatar man fatur ɗin nan sama da sayan Arsenal ɗin. Da na saya ƙungiyar a lokacin a kan kuɗi Dala miliyan 2, amma kuma wataƙila da ban kammala aikin matatar ba. A lokacin zaɓi ne ko dai in kammala aikin gina matatar, ko kuma in saya Arsenal."

    A shekarar 2020 ce Dangote ya bayyana ƙudurinsa na sayan ƙungiyar ta Arsenal da zarar ya kammala aikinsa na gina matatar men fetur.

  8. An kashe fitattun ƴanbindiga Kachalla Sani Black da Sharme

    Rahotanni na nuna cewa an kashe ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Sani Black a Zamfara.

    Ƴan sa-kai ne suka fafata da ɗanbindigar, suka kashe shi, suka ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, da wasu ƙudade.

    Kafar PRNigeria ta ruwaito cewa bayan kashe ɗanbindigar, an kuma kashe ƴaƴansa biyu a fafatawar da aka yi a yankin Magama Mai Rake da ke ƙaramar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.

    Kachalla Sani Black fitaccen ɗanbindiga ne da ya addabi yankin Chabi da Ɗan Sadau a ƙaramar hukumar Maru da wasu yankuna na arewacin Zamfara da Kaduna da Neja da Kebbi.

    Rahotanni sun ce yana da daba mai yawa da suka haura 150, sannan kuma a dabarsa a kan samu labarin yi wa mata fyade bayan an yi garkuwa da su.

    A wani labarin kuma, rikicin cikin gida ya ci wani fitaccen ɗanbindigar mai suna Kachalla Tukur Sharme a Kaduna.

    Sharme ya mutu ne a sanadiyar rigimar da ta ɓarke a tsakanin dabarsa da wata dabar a wani waje da ake kira 'Hambakko' da ke tsakanin dajin Rijana da dajin Kaso, wadda ta yi sanadiyar tserewar wasu wadanda aka yi garkuwa da su.

    A wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya fitar, ya ce Sharme na ya jagoranci sace ɗaliban makarantar Bethel Baptist High School da ke Kaduna su 121.

    Sharme ya daɗa yana addabar yankin Rijana da Kasarami da Jaka da-Rabi da Millenium City da Maraban Rido da Kujama da sauran garuruwan Jihar Kaduna.

    Sanarwat ta ƙara da cewa wasu ƴanbindigar sun ji rauni a fafatawar.

  9. Hare-haren Isra'ila sun kashe kusan mutum 500 a Lebanon

    Ɗaruruwan ƴan Lebanon ne hare-haren Isra'ila ya kashe a cigaba da cigaba da luguden wuta da ƙasar ke yi da Lebanon.

    Rahotanni na nuna an kashe kusan mutum 492, sannan an raunata sama da 1,645 a ƙasar Lebanon, kamar yadda Ma'aikatar Lafiyar ƙasar ta bayyana.

    Wannan shi ne karon-batta mafi muni tsakanin Isra'ila da Hezbollah tun bayan da suka fara takun-saƙa a shekarar 2006'

    Tuni dubban fararen hula suka tsere daga gidajensu domin tsira daga hare-haren a daidai lokacin da Isra'ila ta ce ta kai hari a wuraren Hezbollah guda 1,300.

    Tun farko, Firaiministan Isra'ila, Benjamin Natanyahu ya yi kira ga fararen hula a Lebanon da su matsa daga wuraren da Isra'ilar take luguden wuta, sannan sojojin Isra'ila sun riƙa aika saƙonni ta wayar salula ga fararen hular suna nanata saƙon na Natanyahu.

    Rahotanni a Lebanon sun nuna cewa Isra'ila na harin wani babban kwamandan Hezbollah mai suna Ali Karaki ne da ke Kudancin Lebanon, amma har yanzu babu tabbacin ko sun kashe shi, duk da cewa Hezbollah ta ce yana ƙalau.

    Ita ma dai Hezbollah ta aika da sama da rokoki 200 a arewacin Isra'ila.

    A ɗaya gefen kuma, Amurka ta ce za ta aika da ƙarin dakaru zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce za su yi hakan ne domin hana ta'azzarar yaƙe-yaƙe domin mutane su koma gidajensu lafiya.

  10. Lokaci ya yi da za a daina biyan tallafin man fetur a Najeriya - Dangote

    Shugaban matatar man fetur ta Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce lokaci ya yi da gwamnatin Najeriya za ta daina biyan kuɗin tallafin man fetur.

    Dangote ya bayyana hakan ne a wata tattaunawarsa da Blomberg a ranar Litinin, inda ya ce biyan tallafin na sa gwamnatin "kashe kuɗaɗen da bai kamata ba," wanda hakan ya sa akwai buƙatar a dakatar da shi, sannan ya ƙara da cewa ita kanta gwamnatin Najeriya ba za ta iya cigaba da biyan kuɗin tallafin ba.

    "Ina tunanin lokaci ya yi da za a daina biyan kuɗin tallafin nan domin dukkan ƙasashe sun daina biya.

    "Farashin man fetur ɗinmu kusan kashi 60 ne farashin ƙasashen da muke maƙwabtaka da su, kuma iyakokinmu babu cikakken tsaro. Don haka ba za a iya cigaba da kashe irin kuɗaɗen nan ba," kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da Bloomberg.

    Dangote ya ƙara da cewa man fetur ɗin da matatarsa ke fitarwa zai taimaka wajen rage wa Naira nauyi.

    Ya ce, "Batun tallafin fetur magana ce babba. Idan ka bayar da tallafi a kan wani abu, wasu sai su riƙa ƙara yawan abun domin su samu ƙarin kuɗaɗe sannan sai nauyin ya ƙare a kan gwamnati. Zai fi dacewa a daina biya baki ɗaya.

    "Matatarmu za ta magance matsaloli da dama. Za ta bayyana asalin adadin man fetur da ake amfani da shi a Najeriya saboda babu wanda zai iya faɗa maka a yanzu adadin litar man fetur da ake amfani da shi. Wasu za su ce maka lita miliyan 60 a kullum, wasu suna cewa bai kai ba. Amma mu yanzu za mu iya kididdigewa. Sannan za mu saka na'urorin bibiyar motocinmu domin tabbatar da cewa a Najeriya suke sauke man."