Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya, Lahadi, 02/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sassan duniya kai tsaye, na Lahadi, 02/03/2025

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Isra'ila ta amince da tsawaita tsagaita wuta a Gaza saboda azumi da bikin Passover

    Gwamnatin Isra'ila ta amince da tsawaita wa'adin tsagaita wuta a zirin Gaza na tsawon mako shida domin gudanar da azumin watan ramadan da kuma bikin Passover na Yahudawa.

    A jiya Asabar ne matakin farko na tsagaita wutan ya ƙare.

    Wakilin BBC ya ce Isra'ila na son a sako duka mutanen da aka yi garkuwa da su nan take ita kuma Hamas na son a ci gaba da mataki na biyu wanda ya ƙunshi tsagaita wuta na dindindin da kuma janyewar sojojin Isra'ila daga Gaza.

    Hamas dai ba ta yi wani tsokaci kan shirin tsawaita tsagaita wutan na wucin gadi ba.

  2. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Lahadi, inda za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su X da Facebook da Instagram domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.