Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
A madadin sauran Abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 12/07/2024.
Umar Mikail da Usman Minjibir
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
A madadin sauran Abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Jam'iyyar NNPP a Najeriya ta sauya alama ko tambarinta da a baya aka santa da shi.
Yayin da yake jawabi a taron manema labarai a Abuja, babban birnin ƙasar, jagoran jam'iyyar na ƙasa Sanata Rabi'u Kwankwaso ya ce jam'iyyar ta ɗauki matakin ne don masalahar magoya bayanta.
Sanata Kwakwanso ya ce a baya sun sha samun ƙorafi daga magoya bayan jam'iyyar cewa ba sa iya gane ta a lokutan zaɓe.
Jagoran jam'iyyar ya ce hukumar zab en ƙasar ta sahale wa jam'iyyar sabon tambarin.
Sabon tambarin jam'iyyar yanzu hoton littafi ne da hular 'yan jami'a a tsakiyar wata tuta mai launin ja da ratsin fari a tsakiyarta.
A baya dai hoton kayan marmari ne a jikin tambarin jam'iyyar.
Jam'iyyar dai ce dai ke mulkin jihar Kano da ke arewacin ƙasar, inda kuma take da 'yan majalisun tarayya da na dattawa.
Jam'iyyun siyasa a Afirka ta Kudu sun yi kiran gudanar da bincike kan sabbin zarge-zargen rashawa da ake yi wa shugaban jam'iyyar EFF, Julius Malema.
Waɗanda ke buƙatar 'yan sanda su gudanar da binciken sun haɗa da jam'iyyar DA wadda ta shiga gwamnatin haɗaka da ANC a watan da ya gabata.
Hujjar da aka bai wa tsohon shugaban bankin da ya durƙushe,Tshifhiwa Matodzi, sun nuna cewa Mista Malema da mataimakinsa, Floyd Shivambu sun riƙa karɓar karɓar cinhancin dubban ɗaruruwan daloli tun 2017.
Mista Malema da mataimakinsa dai sun sha musanta zarge-zargen.
Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta ce ta yi maraba da hukuncin kotun ƙolin ƙasar wadda ta umarci gwamnonin su daina riƙe wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu da ake ware musu daga asusun gwamnatin tarayya.
Shugaban ƙungiyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kwara, AbdulRazaq AbdulRahman ya ce ƙungiyarsu za ta yi biyayya ga hukuncin kotun, yana mai cewa a yanzu lauyoyinsu sun buƙaci kwafin hukuncin kotun wanda za yi nazari a kai.
Ya ƙara da cewa gwamnonin na murna da karkasa iko dangane da 'yancin ƙananan hukumomin.
''Hakan zai rage wa gwamnoni nauyi, mutane ba su san yadda jihohi ke kashe maƙudan kuɗi wajen ɗaukar ɗawainiyar ƙananan hukumomi ba '', in shugaban ƙungiyar gwamnonin ƙasar.
Da dama dai na ganin wannan hukunci zai shafi jihohin ƙasar, musamman yadda suka saba riƙe kuɗin ƙanannan hukumomin da kuma ayyukan da suke yi.
To sai dai gwamnan na Kwara ya kare matakin da cewa hakan ba zai shafi jihohin ba, musamman jiharsa ta Kwara da ya ce dama ƙananan hukumomi na da 'yanci, saboda dama a cewarsa ba ɓarnatar da kuɗin ƙananan hukumomin gwamnonin ke yi ba.
''Don haka yanzu sai ƙananan hukumomin su ci gaba da riƙe kansu, musamman a wannan lokaci da ake dab da tabbatar da mafi ƙanƙantar albashi, su tabbatar suna biyan albashin ma'aikata sannan sarakunan gargajiya su sami kashi 5 cikin 100 kuɗin da ake bai wa ƙaramar hukumar, waɗannan su ne manyan batutuwan''.
Wani ɓangare na hukuncin shi ne haramta wa jihohin rusa zaɓɓaɓun shugabannin ƙananan hukumomin.
Kan wannan batu shugaban ƙungiyar gwamnonin ya ce wannan zai shafi wasu gwamnonin, musamman waɗanda ba su da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin a yanzu.
A ranar Alhamis ne dai kotun kolin ƙasar ta yanke hukuncin bayan da gwmanatin tarayya ta shigar da gwamnonin ƙara don su bai wa ƙananan hukumomin 'yanci, bayan da aka zargi gwamnonin da riƙe kuɗaɗen nasu.
An shaida wa BBC cewa tattaunawar tsagaita wuta a Gaza da ake yi a Qatar da Masar ta ƙare ba tare da samun nasara ba.
Wani babban jami'in Falasdinu ya zargi Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da yi wa tattaunawar zagon ƙasa.
Kawo yanzu dai Isra'ila ba ta ce komai ba game da batun, to amma gwamnatin ƙasar ta gindaya wasu sharudda don cimma yarjejeniya, ciki har da damar Isra'ila na ci gaba da yaƙi a Zirin Gaza har sai ta cimma muradunta a yaƙin.
Masu shiga tsakani daga ɓangarorin Isra'ila da Hamas za su ci gaba da tuntuɓar juna, kuma ana fatan sake zama domin tattauanwar a nan gaba.
Shugaban jam'iyyar Democrat a majalisar wakilai ta Amurka, Hakeem Jeffries, ya gana da Shugaba Joe Biden, don tattauna damuwar 'yan majalisar wakilan ƙasar ke da shi game da takararsa.
Ana ganin Mista Jeffries "a fakaice" na da ra'ayi iri ɗaya da na takwarorinsa.
Kusan 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar Democrats 20 ne kawo yanzu suka yi kira ga Mista Biden ya haƙura da takarar bayan rashin kataɓus a muhawarar da ya yi da Donald Trump a watan da ya gabata.
Kafofin yada labaran Amurka sun ce da dama daga cikin masu bai wa jam'iyyar Dimokrat tallafi sun ce za su riƙe kusan dala miliyan casa'in na gudummawar da aka alƙawarta idan Mista Biden ya ci gaba da kasancewa a takarar.
An zaƙulo aƙalla gawarwakin mutum 11 daga cikin wata bola a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya, bayan da mazauna yankin suka ankarar da hukumomi.
Shaidu sun ce da yawa daga cikin gawarwakin na mata ne, yayin da ka daddatsa wasu daga ciki.
Kawo yanzu dai ba san abin da ya haddasa mutuwar mutanen ba, yayin da rahotonni ke nuna cewa akwai wasu ƙarin gwarwakin.
'Yansanda sun ce an zaƙulo gawarwakin mutum shida - dukansu mata - da aka yayyaka wasu sassan jikinsu, bayan da suka soma ruɓewa.
Jami'an tsaro sun killace wurin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
Sufeta-janar na ƴansandan Kenya ya ajiye muƙaminsa bayan makonnin da aka kwashe ana gudanar da zanga-zanga a ƙasar, lamarin da haifar da mutuwar mutane sama da 40.
Ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama sun zargi ƴansanda da harbin masu zanga-zanga, inda wasu suka mutu, sannan aka kama wasu ɗaruruwa.
Zanga-zanga ta ɓarke a Kenya a tsakiyar watan da ya gabata domin nuna adawa da shirin gwamnati na ƙara kuɗaɗen haraji.
Masu zanga-zanga sun kutsa cikin ginin majalisar dokokin ƙasar jim kaɗan bayan da ƴan majalisa suka amince da dokar mai cike da ruɗani.
Matakin da shugaban ƙasar William Ruto ya ɗauka na janye dokar ba ta sanya masu zanga-zangar sun saduda ba.
A ranar Alhamis shugaban ya sallamai da dama daga cikin ministocinsa inda ya sanar da shirinsa na kafa gwamnatin da za ta ƙunshi ɓangarori da dama.
Har yanzu akwai shirye-shiryen ci gaba da zanga-zangar.
Aƙalla ɗalibai 16 ne suka mutu bayan ruftawar ginin mai hawa biyu a wata makaranta a birnin Jos na jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya ranar Juma'a da safe.
Rahotonni sun ce ɗalibai masu yawa ne suka jikkata, yayin da ɗaliban da malamai suka maƙale a cikin ginin.
Ginin na makarantar Saint Academy - da ke unguwar Busa-buji a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa - ya rufta ne a lokacin da ɗaliban ke ɗaukar darussa.
Iyayen yara sun cika harabar makarantar bayan faruwar lamarin, domin sanin halin da 'ya'yansu ke ciki, yayin da waɗanda suka ga gawarwakin 'ya'yansu suka kiɗime.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) na ci gaba da aikin ceto domin zaƙulo sauran mutanen da ginin ya danne.
Kawo yanzu an gano gawargwaki aƙalla 16, to sai dai har yanzu ba a san adadin mutanen da suka mutu ba.
Akwai dai fiye da ɗalibai 1,000 a makarantar. Kawo yanzu dai ba a san dalilin da ya haddasa ruftawar ginin ba
Iyayen ɗalibai sun garzaya asibitin birnin Jos domin sanin halin da 'ya'yansu ke ciki.
Likitoci na kira ga al'umma su bayar da gudunmowar jini domin ceto rayukan ɗaliban da aka kai asibitin.
Mai Shari'a K. Dagat na Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Borno ya yanke wa mutum uku masu sana'ar canjin kuɗi ɗaurin shekara ɗaya a gidan yari saboda ba su da lasisi.
Sai dai alƙalin ya ba su zaɓin biyan tarar naira 100,000.
Hukumar yaƙi da rashawa EFCC ce ta gurfanar da mutanen; Buba Ahmadu Aliyu, da Mohammed Mustapha, da kuma Muhammad Zarami bayan kama su a birnin Maiduguri ranar Talata.
Alƙalin ya kama su da laifin ɗaya tilo da EFCC ke tuhumar su da shi na gudanar da sana'ar canjin kuɗaɗen waje ba tare da lasisi daga Babban Bankin Najeriya CBN ba.
Hukumomi a Nijar sun saka dokar hana fita a yankin Tillaberi bayan fursunoni da dama sun tsere daga wani gidan yari mai tsananin tsaro kuma da ke tsare da masu iƙirarin jihadi.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis lokacin da mutanen suka gudu daga gidan yarin na Koutoukale mai nisan kilomita 50 daga Yamai babban birnin ƙasar, in ji ma'aikatar harkokin cikin gida ta Nijar.
An yi nasarar daƙile yunƙurin ɓalla gidan yarin a 2016 da kuma 2019.
Dakarun sojin Nijar na fama da hare-haren masu iƙirarin jihadi a yammacin ƙasar, a gefe guda kuma suna kare aikin shugabanninsu da ke mulki bayan juyin mulkin da Janar Tchiani ya jagoranta a shekarar da ta gabata.
Ma'aikatar ba ta fayyace yawan fursunonin da suka gudu ba a lamarin na jiya.
Sai dai kuma ana fargabar cikin waɗanda suka tsere akwai mayaƙa na ƙungiyoyin al-Qaeda da Islamic State.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya Nema na can tana aikin ceto mutanen da ginin wata makaranta ya danne a birnin Jos na jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya.
National Emergency Management Agency ta ce ginin na makarantar Saint Academy mai hawa biyu ya rikito ne a safiyar yau Juma'a, inda ya kashe ɗaliban da ba a tabbatar da adadinsu ba zuwa yanzu.
Rahotonni sun ce ginin ya faɗi da misalin ƙarfe 11:00 yayin da ɗaliban ke tsaka da rubuta jarabawa a unguwar Busa Buji da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
Za mu kawo muku ƙarin bayani da zarar mun samu.
Sudan ta nemi duka 'yan ƙasar waje su fice daga birnin Khartoum cikin kwana 10, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Sudan (Suna) ya ruwaito a jiya Alhamis.
"Shugaban sashen 'yan ƙasar waje da kuma shige da fice a Khartoum, Kanar Nizar Khalil, ya bai wa 'yan ƙasar wajen umarnin fita daga Khartoum cikin kwana 10 domin kare tsira da rayukansu daga yaƙi," a cewar rahoton na Suna.
Akasarin birnin na Khartoum - da ya haɗa da tsakiya da kuma biranen unguwannin Bahri da Omdurman - na ƙarƙashin ikon RSF, ƙungiyar da take ta yaƙi da dakarun gwamnatin ƙasar tun Afrilun 2023.
Gwamnatin ƙasar ta soja ta yi yaƙi da 'yan ƙasar wajen da suka shiga ba bisa ƙa'ida ba, tana mai zargin su da taimaka wa ƙungiyar ta RSF.
A ranar 8 ga watan Yuli hukumomi sun tsare 'yan ƙasar waje 154 da ake zargi sun shiga ta ɓarauniyar hanya. Sai dai RSF ta musanta zargin.
Wani rahoton bincike da hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun bai wa jami'an gwamnatin ƙasar naira biliyan 721 (dala biliyan 1.26) a matsayin cin-hanci a 2023.
Rahoton ya ce 'yan Najeriyar sun ba da cin-hancin ko kuma rashawa sau miliyan 87, amma adadin ragi ne idan aka kwatanta da miliyan 117 da suka bayar a 2019.
Cikin duka 'yan Najeriyan da suka ga aƙalla wani jami'in gwamnati ɗaya cikin wata 12 kafin gudanar da binciken a 2023, kashi 27 sun bai wa jami'in hanci.
Idan aka kwatanta da abin da aka saba gani a baya, hakan na nufin yawan biyan rashawa a Najeriya ya ragu kaɗan zuwa kashi 23 tun daga 2019, lokacin da aka samu kashi 29 da suka ba da hanci.
A wuraren da kuma aka tambayi cin-hanci amma mutane suka ƙi bayarwa, an ba da cin-hancin fiye da sau ɗaya cikin haɗuwa uku (kashi 34 cikin 100) a 2023.
Sai dai kuma kashi 70 cikin 100 na mutanen da aka nemi su ba da rashawar a 2023 sun ƙi bayarwa sama da sau ɗaya.
Kazalika, binciken ya gano cewa raguwar ba da rashawar ta fi yawa a yankin arewa maso yammacin Najeriya da kashi 76, duk da cewa sauran yankunan sun samu sama da kashi 60 cikin 100.
Ƙudirin da ke neman ƙirƙiro sabuwar jiha a yankin kudu maso gabashin Najeriya ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai.
Ƙudirin yana neman a ƙara jihar Etiti a yankin mai jihohi biyar kuma 'yanmajalisa Amobi Ogah (LP, Abia), Miriam Onuoha (APC, Imo), Kama Nkemkama (LP, Ebonyi), Chinwe Nnabuife (YPP, Anambra), da kuma Anayo Onwuegbu (LP, Enugu) ne suka gabatar da shi.
Ogah ya ce niyyarsu ita ce kawo ƙarshen abin da aka daɗe ana tattauna a kai na yawan jihohi a yankin nasu. Suna so ne a yanki jihar daga jihohin yankin na Anambra, Imo, Ebonyi, Abia, and Enugu.
Yayin zaman na jiya Alhamis, an amince da ƙudirin ne a mataki na biyu ba tare da wata muhawara ba daga 'yanmajalisar, inda suka amsa amincewa lokacin da Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas ya nemi kaɗa ƙuri'a da baki.
A ranar Laraba ma Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila ya gabatar da ƙudirin neman ƙirƙiro jihar Tiga daga Kano a arewa maso yammacin ƙasar.
Shugaban Colombia, Gustavo Petro, ya ce za a kawo karshen tashe-tashen hankuli a ƙasarsa nan da kwana ɗaya da a ce Majalisar Dinkin Duniya (MDD) za ta halasta amfani da hodar iblis a hukumance a duk fadin duniya.
Da yake jawabi a hukumar samar da zaman lafiya ta MDD a birnin New York, Mista Petro ya ce ribar da ake samu daga fataucin hodar iblis ta haramtacciyar hanya ne ke rura wutar rikicin.
"Abin takaici ne yadda akasarin kasashe ba za su amince da halasta shan irin wadannan kayayyaki ba, sabili da dalilai na siyasa," in ji shi.
Colombia ce babbar mai samar da hodar iblis a duniya, yayin da Peru da Bolivia ke biye mata baya.
Ba kawai kungiyoyin masu aikata laifuka ne ke rike da hanyoyin safarar miyagun kwayoyin kasar ba, har ma da kungiyoyin 'yan tawaye, wadanda suka shafe shekara 60 suna yaki da sojojin kasar.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce ya himmatu wajen inganta rayuwar ma'aikatan ƙasar ta hanyar ba su albashi mai kyau da kuma inganta wuraren ayyukansu.
Shugaban na wannan magana ne yayin da yake tattaunawa da haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC da kuma ta 'yankasuwa TUC a fadarsa a yammacin Alhamis.
"Ina sane da duk abubuwan da ke faruwa a kusa da ni," a cewarsa. "Ma'aikacin da ke cikin farin ciki shi ne mai himma, kuma al'umma ta dogara ne kan ma'aikacin da ke cikin walwala."
Sai dai kuma ya nemi 'yanƙasa su rage buri game da sabon mafi ƙanƙantar albashin, wanda gwamnati da 'yan ƙwadagon ke tattaunawa a kai.
"Dole ne a yi abu daidai ruwa daidai tsaki. Kafin mu daddale kan mafi ƙanƙantar albashi dole ne mu duba tsarin. Me ya sa za mu dinga ƙara albashi duk shekara biyar? Me ya sa ba shekara biyu ko uku ba? Wace matsala muke da ita a yau? Ko za mu iya magance ta gobe?"
Bayan kammala tattaunawar, Shugaban NLC Joe Ajaero ya ce kowa yana nan kan bakarsa a yanzu; gwamnati na tayin N62,000, su kuma suna neman N250,000. Amma za su sake zama da gwamnatin a mako mai zuwa.
Shugaban mulkin soja na Burkina Faso Ibrahim Traore ya zargi maƙwabtansu Ivory Coast da Benin da shirya maƙarƙashiya domin tayar da fitina a ƙasarsa.
"Zan sake faɗa, ba mu da wata matsala da mutanen Ivory Coast, amma muna da matsala da shugabannin da ke mulkin ƙasar," in ji Traore a jiya Alhamis.
Ya ƙara da cewa Adbijan ce "ke ɗaukar nauyin yunƙurin tayar da fitina" a Burkina Faso. Traore ya kuma yi iƙirarin cewa Faransa ta kafa sansanoni a Benin domin horar da 'yantawaye.
Ya yi iƙirarin cewa yana da wani "sauti da aka naɗa na wakilan Faransa a Benin da ke gudanar da ayyuka daga sansanin 'yanta'adda" kuma "suke taimaka musu da magani".
Wannan ne kalamai mafiya girma da Kyaftin Traore ya yi tun bayan jita-jitar juyin mulki da aka yi a watan da ya gabata, kuma an yaɗa jawabin a kafar talabijin ɗin ƙasar ta RTB TV.
Shugaba Biden ya nace cewa ya cancanci wa'adi na biyu a kan karagar mulki duk da damuwar da 'yan jam'iyyarsa ke nunawa kan shekarunsa da kuma lafiyar ƙwaƙwalwarsa.
A wani taron manema labarai da aka sanya wa ido sosai na farko da ya gudanar ba tare da takarda ko allon karatu ba cikin wata takwas, Mista Biden ya ce har yanzu shi ne ɗan takarar da ya fi dacewa ya buge Donald Trump a zaɓen kasar na watan Nuwamba.
Sai dai, tun ba a je ko'ina ba shugaban ya sake kwatawa, inda ya kira Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da sunan Shugaba Putin na Rasha.
Haka nan, ya sake kiran mataimakiyarsa Kamala Harris a matsayin Donald Trump.
Wakilin BBC ya ce wasu na hasashen cewa ana sa ran samun ƙarin mutane da dama da za su fito fili su nemi Biden ya haƙura bayan da aka kammala taron ƙungiyar ƙawancen tsaro ta Nato.
Barkanmu da hantsin Juma'a - babbar rana.
Umar Mikail da Usman Minjibir ne ke muku maraba da sake haɗuwa a shafin rahotonni kai-tsaye.
Ku biyo mu har zuwa daren yau domin sanin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman ma a Najeriya da Nijar da kuma makwaɓtansu.