Amurka na fama da karancin makamai- Pentagon
Ma’aikatar tsaron Amurka ta ce yaƙin da ƙasar ke yi da Iran ya jawo ƙarancin wasu makamai da kuma tsaiko wajen sake cike ma’ajiyar makamai. Hakan dai ya ci karo da ikirarin Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya sha musanta cewa ƙasar na fuskantar ƙarancin makamai.
Wani rahoto daga babban mai sa ido mai zaman kansa na Ma’aikatar Tsaron Amurka, ya ce ƙasar ta kashe sama da dala biliyan ashirin da biyu kan makamai tsakanin watan Fabrairu zuwa Yunin shekarar nan. Rahoton ya ce hakan ya jawo ƙarancin wasu muhimman makamai a ma’ajiyar sojojin ƙasar.
Sai dai Shugaba Trump ya sha cewa makaman Amurka basu da iyaka, ba za a iya karar da su ba, inda ya karyata rahotannin da ke cewa akwai ƙarancinsu.
Rahoton sabon binciken ya kuma bayyana cewa akwai matsaloli a masana'antun da ke kera makamai, lamarin da ke kawo tsaiko wajen sake samar da su, sai dai bai bayyana adadin makaman da suka rage a hannun sojojin Amurka ba.
A yayin yaƙin, sojojin Amurka sun yi amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango, da makaman kariya daga hare-haren ta sama na makamai masu linzami na Iran.
Wani bincike da cibiyar CSIS ta fitar a ƙarshen watan Yuli ya nuna cewa adadin wasu makamai masu kare sararin samaniya, ya ragu sosai.
Rahoton ya ce Ma’aikatar Tsaron Amurka na ƙoƙarin sauƙaƙa hanyoyin sayen makamai da kuma rage lokacin da ake ɗauka wajen kera su, domin magance ƙarancin. Yaƙin ya kuma jawo asarar kayan yaƙi da aka kiyasta kudinsu da dala biliyan uku da digo bakwai.
Jimillar kuɗin da Amurka ta kashe kan yaƙin tsakanin 28 ga Fabrairu zuwa 30 ga Yuni ya kai sama da dala biliyan talatin da uku.
A farkon yakin Shugaba Trump ya sha cewa yaƙin ba zai dauki lokaci ba, sai dai a baya-bayan nan ya ce akwai yiwuwar yaƙin bai ƙare ba sai bayan zaɓen rabin wa’adin mulki na Amurka da za a gudanar a watan Nuwamba.
Wasu kuri’un jin ra’ayin jama’a kuma sun nuna cewa yaƙin bai samu karɓuwa sosai tsakanin Amurkawa ba.