Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 11/07/2027

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 11/07/2027

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza

  1. Mu kwana lafiya

    Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Juma'a.

    Za mu kawo sababbin rahotonni gobe da safe a wani shafin.

  2. 'Yansandan Filato sun gurfanar da mutanen da ake zargi da kisan matafiya daga Zariya

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Filato ta gurfanar da mutum 20 a gaban kotu da take zargi da kisan matafiyan nan 'yan jihar Kaduna a garin Mangun na jihar ta Filato.

    Tuhume-tuhumen da aka karanta musu sun ƙunshi haɗa baki wajen aikata laifi, da ji wa mutane rauni, da kisan kai da gangan waɗanda rundunar ta ce sun saɓa wa kundin shari'ar manyan laifuka na jihar.

    Mai shigar da ƙara Samuel Idowu Ikutanwa ya zargi mutanen da haɗa baki wajen aikata kisan da mugayen makamai, ciki har da adduna da gatari da kuma man fetur.

    Mai shari'a Boniface Ingyou ya ɗage zaman shari'ar zuwa 13 ga watan Oktoba tare da bayar da umarnin ci gaba da tsare waɗanda ake zargin a gidan yari.

  3. An kama shugaban makarantar da ya yi wa ɗalibai mata tsirara don gano masu yin al'ada

    An kama shugaban makaranta da wata malamai mata a garin Thane da ke jihar Maharashta ta ƙasar Indiya.

    Ana zargin mutanen biyu ne da cire wa ɗalibai mata kaya domin duba ko suna jinin al'ada ko kuma a'a, bayan ganin ɗishi-ɗishin jini a bangon ban-ɗaki.

    Ƴansanda sun ɗauki matakin ne bayan mahaifiyar ɗaya daga cikin ɗaliban kimanin 15 ta shigar da koke kan lamarin.

    Makarantar na ƙunshe ne da ɗalibai kimanin 600, wadanda ke karatu daga matakin nazare zuwa sakandare.

    Lamarin dai ya faru ne a ranar Talata a gundumar Shahpur na birnin Thane.

    A ranar Laraba iyayen yara sun yi zanga-zanga a harabar makarantar sannan suka buƙaci gwamnatin yankin ta hukunta masu hannu a lamarin.

    Bayan haka ne ƴansanda suka sanya ido kan mutum 8 da ake zargi, inda a yanzu suka kama shugaban makarantar da kuma wata malama.

    Ƴansandan na zargin mutanen da cin zarafi da kuma keta mutuncin ɗaliban kamar yadda yake ƙunshe a doka.

    Bayanin ƴansanda ya nuna cewa lamarin ya faru ne tsakankanin ƙarfe 10 zuwa 12 na rana a ranar 8 ga wannan wata na Yuli, lokacin da shugaban makarantar ya tara yara mata ɗalibai na makarantar su 125 a ɗakin taro na makarantar.

    Daga nan ne aka kunna masu bidiyon jinin da aka gani a ban-ɗaki, sannan aka tuhume su da ɓata bangon da jinin al'ada.

    Bayanin ya ce daga nan ne aka umarci malamai mata na makarantar su tafi da ɗaliban ban-ɗaki su cire musu kaya domin gano waɗanda ke jinin al'ada.

    Lamarin, a cewar bayanin ya girgiza ɗaliban.

    Wasu daga cikin iyayen sun ce yaransu sun ƙi zuwa makaranta sanadiyyar kaduwar da suka yi.

  4. Sauye-sauyen da zan kawo a Kano Pillars - Ahmed Musa

    Sabon shugaban gudanarwa na Kano Pillars, Ahmed Musa ya ce hana 'yan wasa yin caca kan wasanni na cikin abubuwan da suka kawo don gyaran ɗa'a a kungiyar.

  5. Yunƙurin tsagaita wuta a Gaza na gab da rushewa - Hamas

    Hukumomin Falasɗinawa sun shaida wa BBC cewa tattaunawar da ake yi a ƙoƙarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza tsakanin Hamas da Isra'ila na gab da rushewa.

    Dama dai ɓangarorin biyu na gudanar da tattaunawar ne a Qatar.

    Ɗaya daga cikin jami'an gwamnatin Falasɗinawa da ke cikin tattaunawar ya ce Isra'ila ta sa lamarin ya tsaya cak bayan tura tawaga maras ƙarfi, wadda ba za ta iya zartar da komai ba.

    Ya kuma ce Isra'ila, cikin buƙatunta na son a kafa wasu tuddan mun-tsira da za su kwashe fili mai yawa na yankin Gaza.

    A jiya Alhamis Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce yana sa ran za a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana 60 cikin ƴan kwanaki.

  6. Ma'aikatar harkokin wajen Amurka za ta sallami ma'aikata sama da 1,300

    Ma'aikatar harkokin waje ta Amurka za ta tura takardun kora ga ma'aikatanta fiye da 1,300.

    Wannan na daga cikin tsarin shugaban ƙasar Donald Trump na gyara ɓangaren aikin gwamnati na ƙasar wanda ya ce na ƙunshe da ma'aikata fiye da yadda ake buƙata.

    Cikin waɗanda za a kora har da ma'aikata da ke aiki a cikin Amurka waɗanda ke aiki a ɓangaren inganta dimokuraɗiyya, da kare hakkin ɗan'adam da kuma sanya ido kan laifukan yaƙi.

    Wani saƙo da aka tura wa ma'aikatan ya ce rage yawan ma'aikatan ba zai shafi ma'aikatan da ke tsantsar aikin diflomasiyya ba.

    Masu lura da lamurra na ganin cewa matakin zai raunana tsarin Amurka na dankwafe ƙarin tasirin da China ke da shi a duniya da kuma yunƙurin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

    A farkon wannan makon ne kotun ƙoli ta Amurka ta amince cewa gwamnatin Trump za ta iya ci gaba da shirinta na rage yawan ma'aikatan gwamnati.

  7. Ƙaruwar ƴan gudun hijra na jefa garin Tawila na Sudan cikin mummunar matsala

    Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta ƙasar Norway ta ce yawaitar ‘yan gudun hijira da ke tserewa zuwa garin Tawila a arewacin Darfur na jefa garin cikin mummunar matsalar jin kai.

    A cewar hukumar, sama da mutum 380,000 ne suka tsere daga hare-hare masu tashin hankali a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke kusa da birnin, El Fasher, inda aka tabbatar da samun matsananciyar yunwa.

    Yawancin waɗanda suka tsere mata ne, da yara da kuma masu buƙata ta musamman, kuma sun iso garin a ƙafa.

    Lamarin ya kusa fin ƙarfin ƙungiyoyin agaji kuma akwai fargabar cewa zuwan damina ka iya janyo ɓarkewar cutar kwalera da kuma ƙarin yunwa.

  8. Iran za ta iya gyara cibiyoyin nukiliyarta da Amurka ta illata - Isra'ila

    Wani babban jami'in Isra'ila ya ce ƙasar ta yi imanin cewa Iran za ta iya sake gyara makamashin ingantaccen makamashin uranium ɗin ta da ke binne a ƙarƙashin ƙasa a ɗaya daga cikin cibiyoyin nukuliyarta uku da sojojin Amurka suka kai wa hari a watan da ya gabata.

    Da yake jawabi ga taron manema labarai a Amurka, jami'in ya ce ba lallai ne harin na Amurka ya gama lalata makamashin da ke Isfahan ba, amma kuma ya ce duk wani yunƙuri da Iran za ta na gyara makamashin zai fuskanci hare-haren Isra'ila.

    Donald Trump dai ya sha nanata cewa hare-haren da Amurka ta kai wa Iran a watan Yunin da ya gabata ya lalata cibiyoyin nukiliyar ƙasar, kamar yadda wasu hukumomin leken asirin Amurka suka tabbatar da hakan.

    Iran ta musanta yunƙurin ƙera makaman kare dangi sannan ta ce shirinta na inganta sinadarin uranium na zaman lafiya ne.

    A wani jawabi da ya yi wa manema labarai a birnin Washington, babban jami'in na Isra'ila - wanda ya ki a bayyana sunansa - ya ce bayanan sirri sun nuna cewa yawancin makamashin Uranium da Iran ta inganta na binne a Isfahan, wanda Amurka ta kai wa hari a ranar 22 ga watan Yuni.

    Jami'in bai bayyana damuwa game da zarginsa kan yunƙurin Iran ɗin, Inda ya ce za su iya ganowa idan har Iran ta yi yunƙurin ci gaba da inganta makamashin.

    A cewar jami'in, ƙiyasin da Isra'ila ta yi ya gano cewa shirin nukiliyar Iran ya samu koma-baya na shekaru biyu.

  9. Mayaƙan Kurɗawa sun fara ƙone makamansu

    ’Yan ƙungiyar mayaƙan Kurdawa da suka kwashe shekaru suna tayar da ƙayar baya a Turkiyya, sun ƙone makamansu a wani biki na farko da ke nuna cewa sun fara ajiye makamai.

    Bikin ƙona makaman da aka gudanar a yankin Kurdistan na Iraqi, ya nuna matakin farko na wani tsari da zai ɗauki watanni, da ƙungiyar PKK za ta ajiye makamanta baki ɗaya.

    Ƙungiyar da aka daɗe ana zarginta da kwashe shekara fiye da 40 tana kai hare-hare a sassan Turkiyya, ta ce za ta rungumi zaman lafiya da dimokraɗiyya, domin cigaba da kare haƙƙin ƴan ƙabilar ƙurdawa a ƙasar.

    Majalisar dokokin Turkiyya ta kafa wani kwamiti da zai duba yadda za a sake haɗa mambobin ƙungiyar da al’umma, tare da duba makomar waɗanda ke gidajen yari ciki har da shugaban ƙungiyar, Abdullah Ocalan.

  10. 'Ya kamata shugabancin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ƴan Kudu'

    Ministar al'adu ta Najeriya, Hannatu Musawa ta ce ya kamata shugabancin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ƴan kudancin Najeriya a wa'adin mulki mai zuwa domin tabbatar da daidaito da adalci.

    Kodayake kundin tsarin mulkin Najeriya, bai yi tanadinsa ba, manyan jam'iyyun ƙasar na bin tsarin karɓa-karɓa tsakani kudanci da arewacin ƙasar.

    Cikin wata hira da gidan talbijin na Channels ranar Juma'a, Hannatu Musawa ta ce ya kamata mulki ya ci gaba da zama a hannun ƴan kudancin ƙasar indai adalci ake son yi.

    A shekarar 2023 ne Shugaba Tinubu - wanda ɗan kudancin ƙasar ne - ya karɓi mulki daga Muhamamdu Buhari ɗan arewaci - da ya shafe shekara takwas a kan karagar mulki.

    “Abu ne na fahimta, bayan shekara takwas na Buhari daga arewa ya kamata su ma ƴan kudu su yi shekara takwas, domin samar da adalci'', in ji ministar

    A baya-bayan nan ma an ambato tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom na cewa ba zai goyi bayan ɗan takara daga arewacin ƙasar ba.

    Batun karɓa-karɓa tsakanin arewaci da kudancin Najeriya, wani al'amari da aka jima ana muhawara kansa a fagen siyasar Najeriya.

    Wani abu da masana ke cewa yana mayar da tsarin dimokraɗiyyar ƙasar baya.

  11. Asibitin Nasser ya ce ya daina karɓar masu raunuka saboda ƙawanyar sojojin Isa'ila

    Babban asibiti guda ɗaya tilo da ya rage da ke aiki a Gaza, Nasser ya ce ya dakatar da karɓar waɗanda suka jikkata tun a daren da ya gabata, bayan da sojojin Isra'ila suka yi masa ƙawanya.

    Wani ma'aikacin asibitin da ke Khan Younis ya ce tankokin yaƙin Isra'ila sun kusanci asibitin da ƴar tazarar mitoci, inda tuni wasu kayan aikin suka daina aiki saboda rashin an fetur.

    Tawagwar likitocin Amurka da ke asibitin ta ce gwanayen harbi daga nesa na harbin mutanen da ke cikin asibitin.

    Mazauna yankin sun bayar da rahoton cewa a yanzu sojojin ISra'ila janyewa daga yankin, yayin da asibitin ke duba yiwuwar ko zai iya ci gaba da karɓar majinyata.

    Isra'ila na ci gaba da ƙaddamar da hare-hare a faɗin Gaza, inda aka bayar da rahoton kashe mutum aƙalla 16 ciki har da masu jiran tallafi.

  12. Yadda na tsallake rijiya da baya a lokacin Jonathan - Shettima

    Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce shi ne mutumin da aka fi ''ɓata wa suna'' a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan.

    Yayin da yake jawabi a lokacin ƙaddamar a littafin tsohon ministan shari'ar ƙasar, Mohammed Bello Adoke da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, Shettima ya ce Jonathan ya taɓa kawo shawarar cire shi daga muƙaminsa na gwamnan jihar Borno.

    Amma sai tsohon ministan ƙasar, kuma babban lauyan gwamnati, Mohammed Bello Adoke ya ba shi shawarar kauce wa yin hakan.

    Shettima ya ce Adoke ya nuna jarumta wajen faɗa wa Jonathan cewa kundin tsarin mulki bai ba shi damar cire ko da zaɓaɓɓen kansila, balle gwamna sukutum.

    Kawo yanzu dai tsohon shugaban ƙasar, GoodLuck Jonathan bai mayar da martani dangane da iƙirarin na Kashim Shettima ba.

    A watan Mayun 2013 ne Jonathan ya ayyana dokar ta ɓaci kan jihohin da ke fama da rikicn Boko Haram da suka haɗa da Borno da Yobe da kuma Adamawa, to amma bai dakatar da gwamnonin ba.

    Kashim Shettima ne gwamnan jihar Borno har tsawon wa'adi biyu, daga 2011 zuwa 2019, kuma ya mulki jihar a daidai lokacin da rikicin Boko Haram ya munana a yankunan arewa maso gabashin Najeriya.

  13. Hukumar Alhazan Najeriya ta fara shirin aikin hajjin 2026

    Hukumar Alhazan Najeriya ta fara shirhin aikin hajjin 2026 mai zuwa, jin kaɗan bayan kammala aikin hajjin bana.

    Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Pakistan ne ya bayyana haka lokacin ganawa da manema labarai ranar Alhamis a Kano.

    “Mun samu umarni daga hukumomin Saudiyya cewa kowace ƙasa ta hanzarta tsara shirin aikin Hajji mai zuwa domin kuwa ba za su lamunci jinkiri ba;'' in ji shi.

    Shugaban hukumar ya ce yanzu abin da suke jira shi ne amincewar hukumomi kan kuɗin kujerar aikin hajjin 2026, domin sanar wa maniyyata.

    A shekarar da ta gabata dai alhazan Najeriya sun biya naira miliyan takwas da ɗoriya.

    Farfesa Pakistan ya yi kira ga maniyyan ƙasar su hanzarta biyan kuɗin da zarar hukumar ta bayyana kuɗin kujera.

  14. Bafarawa ya kafa sabuwar ƙungiyar haɗin kan arewacin Najeriya

    Wasu shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki daga shiyyar arewacin Najeriya ke cigaba da ƙara ƙaimi wajen ganin an samar da haɗin kai tsakanin al’ummomin yankin.

    Shugaban kwamitin amintattu na sabuwar ƙungiyar, wanda kuma shi ne tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya shaida wa BBC cewa manufar ƙungiyar shi ne hadin kai da amincewa da juna.

    Ya ce sabuwar ƙungiyar ba ta siyasa ba ce, kuma babu ruwanta da siyasa.

    ''Ƙungiya ce ta haɗin kan mutanen Arewa, da wayar da kan ƴan yankin su daina bari ana amfani da su wajen cimma muradun siyasa'', a cewar Bafarawa.

    Akwai ƙungiyoyi da dama dai aka kafa da nufin kare muradun ƴan arewa, to sai dai wasu na ganin babu wani tasiri da ƙungiyoyin ke yi.

  15. Fiye da magidanta 200 ne suka rasa gidajensu saboda ambaliya a Kebbi

    Fiye da magidanta 200 ne suka rasa gidajensu bayan wata mummunar ambaliya ta auka wa ƙauyen Zogirma a yankin ƙaramar hukumar Bunza da ke jihar Kebbi.

    Ambaliyar - wadda ta auku sakamakon mamakon ruwa sama - ta lalata gidaje da gonaki da shaguna da sauran dukiyoyi masu yawa, lamarin da sa ɗaruruwan mutane ke neman mafaka, kamar yadda jaridar Punch ta ambato.

    A farkon makon nan ne hukumar hasashen yanayi ta ƙasar Nimet ta yi gargaɗin samun ambaliya a wasu jihohin ƙasar sakamakon ruwan sama da ta yi hasashen samu.

  16. Ba za mu karɓi ƴanciranin Venezuela da Amurka za ta kora ba - Najeriya

    Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya ce ƙasar ba za ta lamunci matsin lambar da Amurka ke yi mata na karɓar ƴan ciranin Venezuela da Amurkan ke son ƙwasa tare da mayar da su Najeriya.

    Cikin wata hira da gidan Talbijin na Channels, Yusuf Tuggar ya ce ƙasar na da ''nata matsalolin'' don haka ba za ta amince a kawo mata muwaten wata ƙasa ba da aka kora da Amurka.

    Matakin na Amurka na zuwa ne kwana biyu bayan da Amurka ta sanar da sauye-sauyen tsarin bai wa ƴan Najeriya bizar masu yawon buɗe ido da ƴan kasuwa, matakin da gwamnatin Najeriyar ta nuna rashin jin daɗinsa.

    Gwamnatin Trump dai na ƙokarin kwashe baƙin hauren da suka je ƙasar, musamman baƙaƙen fata domin mayar da su wata ƙasa ta baƙaƙen fata.

  17. Jami'an tsaro sun yi artabu da ƴanbindiga a Mariga da ke jihar Neja

    Al'ummomin garuruwan Maigoge da Dan-Auta da Beri na yankin ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja, sun kwana cikin tashin-tashina, har mafi rijayen su sun tsere zuwa cikin dazuka, wasu sun yi gudun hijira, wasu ma ba a san inda su ke ba.

    Al'amarin na da nasaba ne da artabun da aka daɗe ana yi tsakanin ƴanbindiga da jami'an tsaron Najeriya a daren Alhamis.

    Wani mutumin yankin, wanda ke cikin halin damuwa da firgici a inda ya sami mafaka ya shaidawa BBC cewa alummar yankin sun shiga cikin halin kaka-ni-ka-yi.

    ''Matanmu da mazajen mu da yaran mu duk basa gari, wasu na Minna wasu na Kontagora wasu na Mariga wasu na Tegina ko wajen gari, wani ma bai san inda yake ba'', in ji shi.

    Ya kuma ce wasu da ba su da mota na samun mafaka ne a cikin dazuka ko duwatsu kuma a cikin kashi 100 na mazauna yankin, kashi 90 sun tsere, yayin da kashi 10 ne kawai suka rage.

  18. Mun kakkaɓo jiragen Ukraine marasa matuƙa fiye da 150 - Rasha

    Rasha ta ce ta kakkabo jiragen sama marasa matuƙa na Ukraine sama da 150 a yankunanta cikin dare.

    Ba a dai bayar da cikakken bayani kan wata ɓarna da wannan hari ya yi ba.

    Hakan ya biyo bayan hare-haren bama-bamai da ɗaruruwan jiragen Rasha marasa matuƙa da makamai masu linzami suka kai wa Ukraine ne cikin kwanakin nan.

    A jiya alhamis Shugaba Zelensky ya ce ya yi tattaunawa mai ma'ana da Shugaba Trump game da tallafa wa Ukraine da makamai, wanda suka haɗa da na'urorin makami mai linzami nau'in Patriot da ke da muhimmanci ga tsaronta.

  19. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, Hajji babbar rana kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Barkanmu da sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku labaran yadda duniya ta wayi gari.