Ɗaya daga cikin manyan batutuwan da aka riƙa yi a tsawon gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyi - wato Clup World Cup, shi ne kuɗin da za a bayar ga waɗanda suka yi nasara a gasar.
An ware dala miliyan 1000 kwatankwacin fam miliyan 726 da za a bai wa ƙungiyoyi 32 da suka shiga sabuwar gasar, inda za a raba dala miliyan 525 a tsakanin dukkanin ƙungiyoyin da suka fafata, sannan za a bayar da dala miliyan 475 da za a bayar daidai da ƙoƙarin da ƙungiya ta yi.
An bai wa ƙungiyoyin Turai tsakanin dala miliyan 12.81 da miliyan 38.19 saboda zuwa gasar kawai, yayin ƙungiyoyin da suka je daga Latin Amurka aka ba su dala miliyan 15.21, su kuwa ƙungiyoyin nahiyar Amurka ta Arewa da ta tsakiya da Asia da kuma Afirka - miliyan 9.55, su kuwa ƙungiyoyin Oceania aka ba su dala miliyan 3.58.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ba ta tabbatar da ainahin kuɗin da ta bai wa ɗaiɗaikun ƙungiyoyin Turai ba na shiga gasar, illa an yi amfanbi da ƙididdigar shafin intanet da ke bayar da bayanan kuɗaɗe na wasan ƙwallon ƙafa- The Swiss Ramble aka fitar da alƙaluman.
Ƙungiyar gasar Premier ta Ingila Chelsea ce ta yi nasara a wasan ƙarshe na gasar inda ta doke PSG da ci 3-0.
Ladan kuɗin da ƙungiyoyin suka samu ya taimaka musu sosai musamman ma Chelsea da Manchester City.
Chelsea ta kashe fam miliyan 198 wajen sayen 'yanwasa zuwa yanzu a wannan bazarar, wajen sayen irin su Joao Pedro da Liam Delap, kuma ta mayar da fam miliyan 84 daga cikin wannan kuɗin a sakamakon kuɗin da aka ba ta a gasar.
Haka ita ma Manchester City duk da ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ta yi waje da ita daga gasar tun da farko-farko, to amma ta samu kuɗin da ta mayar da kusan kashi 35 cikin ɗari na kuɗin da ta kashe a bazara - wato ta mayar da fam miliyan 31 da ta kashe wajen sayen Rayan Ait-Nouri daga Wolves.