Fafaroma Leo XIV ya nuna damuwa kan jerin hare-haren da ake ci gaba da kai wa a sassan Najeriya, inda ya bayyana alhininsa kan asarar rayuka tare da buƙatar hukumomi su ɗauki ƙwararan matakai domin kare rayuwakan al’umma.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Fafaroman ya ce ya samu labarin hare-haren da ke “cike da baƙin ciki da damuwa,” yana mai cewa an kai hare-haren ne kan al’ummomi daban-daban lamarin da ya janyo asarar rayuka masu yawa.
“Na samu labarin hare-haren da aka kai wa wasu al’ummomi a Najeriya wanda ya haifar da mummunar asarar rayuka, wannan labarin na da matuƙar baƙin ciki da damuwa. Ina miƙa addu’ata da ta'aziyya ga dukkan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon tashin hankali da ta’addanci,” in ji Fafaroman.
Ya ƙara da cewa yana fatan “hukumomin da abin ya shafa za su ci gaba da aiki da cikakkiyar jajircewa domin tabbatar da tsaro da kare rayuwar kowane ɗan kasa.”
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar munanan hare-hare a wasu sassan Najeriya, inda jihar Kwara ta fi fuskantar mummunan haron ƴanbindiga.
A tsakanin ranakun 3 zuwa 4 ga Fabrairun 2026, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ƙauyukan Woro da Nuku da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara, abin da mazauna yankin suka bayyana a matsayin kisan kiyashi.
Rahotanni sun nuna cewa mutum 162 ne suka mutu, sai dai jami’an yankin da waɗanda suka tsira daga harin na cewa adadin wadanda aka kashe ya haura 200, yayin da ake ci gaba da gano gawarwaki a dazukan da ke kewaye da yankin.
Amma kuma, ‘yan sanda da gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, sun tabbatar da mutuwar musulmai 75.
Biyo bayan harin, Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin tura ƙarin sojoji zuwa yankin.