Iraƙi ta sanar da sake buɗe iyakokinta da Iran
Iraƙi ta sanar da sake buɗe wasu hanyoyi uku a kan iyakarta da Iran, bayan da aka rufe su sakamakon wani harin jirgi mara matuƙi da aka kai kan bututun jigilar man fetur na Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ce mashigar Al-Shayb da ke lardin Maysan, wadda ake kira Chazaba a Iran, za ta koma karɓar fasinjoji daga yau.
Haka kuma, za a sake buɗe mashigar Shalamcha da ke lardin Basra, yayin da za a dawo da harkokin kasuwanci a wurin daga baya a cikin wannan makon.
A mashigar Mandali da ke lardin Diyala, za a dawo da harkokin kasuwanci daga ranar Talata. Ana kiran mashigar da Somar a Iran.
Gwamnatin Iraƙi ta rufe iyakoki da Iran na ɗan lokaci a ranar Asabar, bayan gano wurin da aka harba wani jirgi mara matuƙi daga ƙasarta zuwa Saudiyya.