Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/06/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/06/2024

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Bankwana

    Masu bin mu a wannan shafi na kai tsaye, a nan muka kawo ƙarshen rahotannin na yau.

    Ku tara gobe Litinin domin samun wasu sabbin labaran.

  2. Shugaban Congo ya sha alwashin kawar da ƴan tawaye

    Shugaban Congo, Felix Tishikedi ya sha alwashin kare ƙasarsa tare da samar da zaman lafiya a gabashin ƙasar.

    Shugaban ya bayyana cewa maƙiyan ƙasar ne ke ɗaukar nauyin ayyukan ƙungiyoyin ƴan tawaye a Congo.

    Kalaman nasa na zuwa ne bayan da ƴan tawayen M23 suka sake ƙwace iko da wani gari a gabashin Jamhuriyar Dimokadiyyar Congon.

    Ƙwace garin na zuwa ne, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke ƙoƙarin ƙarƙare ayyukan dakarunsu a yankin kudancin lardin Kivu mai makwabtaka.

  3. Euro 2024: Ingila ta doke Slovekia ta kai kwata fainal

  4. Amurka ta yi allawadai da harin Gwoza

    Gwamnatin Amurka ta yi allawadai da harin ƙunar baƙin wake da aka kai garin Gwoza na jihar Borno a ranar Asabar, inda mutum 18 suka mutu, wasu da dama suka samu raunuka.

    Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya bayyana harin a matsayin tashin hankali.

    “Irin wannan hari na tsabar rashin imani da tausayi ne ɗan Adam....kuma hari ne da ke tunatar da mu babbar barazanar da ta'addanci ke yi a nahiyar,'' inji saƙon da ofishin jakadancin Amurkan ya fita a ranar Lahadi.

    Mutane fiye da 30 ne suka samu rauni a harin na ranar Asabar, wanda ake ganin yana cikin mafiya muni a ƴan watannin nan.

    Rahotanni sun ce wata mata ce ta tayar da bam a jikinta, a tsakiyar ƴan biki.

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno ta ce daga baya kuma wani bam ɗin ya fashe a wajen jana'izar waɗanda suka mutu a na farkon.

  5. Fursunoni sun fasa gidan yari a Pakistan

    Hukumomi a Pakistan sun ce wasu fursunoni, ciki harda waɗanda ake zargi da aikata ta'addanci sun yi yunƙurin guduwa daga gidan yari.

    Sun ce an kashe ɗaya daga cikin fursunonin, yayin musayar wuta da jami'an tsaro.

    Wani jami'in yankin Rawalakot ya ce fursunonin sun yi amfani da bindiga wajen neman guduwa daga gidan yarin.

    Ƴan sanda sun yi gaggawar tare duk hanyoyin fita daga birnin, kuma an ƙaddamar da bincike.

    Gidajen yarin Pakistan sun yi ƙaurin suna wajen cunkoso da rashin kula da walwalar fursunoni yadda ya kamata, da kuma zargin cin zarafin ɗan adam da ya yawaita.

    A baya ma, ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai sun sha shirya fasa gidajen yarin da kuɓutar da fursunoni a ƙasar.

  6. Gwamnatinmu ba za ta lamunci zubar da jinin ƴan ƙasa ba - Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi allawadai da harin ƙunar baƙin waken da ya kashe aƙalla mutum 18 a garin Gwoza na jihar Borno.

    Shugaba Tinubu a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce harin babban abin tashin hankali.

    “Masu tayar da rikici su sani cewa za su fuskanci hukunci daidai da su, kuma waɗannan matsoratan da ke kai wa mutane hari, su sani cewa gwamnatinmu ba za ta zura ido ana zubar da jinin jama'a da kuma jefa su cikin tsoro da fargaba ba'' inji sanarwar da kakakin shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale, ya fitar.

    Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan mutanen da harin ya ritsa da su, yana mai cewa harin wata alama ce cewa maharan suna fuskantar matsin lamba daga jami'an tsaro dake aikin daƙile ayyukan maharan.

  7. MDD ta fara tattaunawa da Taliban a kan makomar Afghanistan

    Wakilan Majalisar Dinkin Duniya sun fara wata tattaunawa da tawagar Taliban da sauran ƙungiyoyi a game da makomar Afghanistan.

    Wannan ce tattaunawa ta farko da Majalisar Dinkin Duniya ta yi da Taliban, tun bayan da ƙungiyar ta ƙwace mulki, shekaru uku da suka wuce.

    Wakilan Majalisar Dinkin Duniya a Doha sun jaddada cewa tattaunawar da Taliban wata hanya ce ta samun daidaito a kan muhimman abubuwa, amma hakan ba ya nufin sun amince da gwamnatin su.

    Za su tattauna a kan tattalin arziki da kuma shawo kan ya duwar miyagun ƙwayoyi.

    Rashin sanya mata a cikin tawagar Taliban ɗin ya janyo suka daga jagororin kare haƙƙin mata da kuma ƴan siyasa.

    Amma Majalisar Dinkin Duniya za ta yi wata tattaunawar ta daban da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma wakilan mata a ranar Talata.

  8. Shugaban Afirka ta Kudu zai sanar da majalisar zartarwa

    Shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa ya shirya gabatar da majalisar zartarwar sa a yau, bayan cimma yarjejeniya da ƙawancen jam'iyyun siysa.

    An shafe kwanaki ana tattaunawa tsakanin ANC da sauran jam'iyyun da ake neman kafa gwamnatin haɗin kan dasu.

    ANC ta amince ta kafa gwamnatin haɗin kan ne bayan ta gaza samun yawan kujerun da take buƙata domin kafa gwamnati ita kaɗai a majalisar dokokin ƙasar.

    Wannan ne karon farko a cikin shekara 30 da ANC ta gaza samun gagarumin rinjaye a majalisar.

    Jayayyar da aka samu tsakanin ANC da Democratic Alliance daga ɓangaren adawa ta yi barazana ga aiwatar da yarjejeniyar.

  9. Abba Kabir ya nuna damuwa kan hukumomin Karota da REMASAB

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa kan yadda ma'aikatun tsaftar muhalli da ta karota ke gudanar da ayyukansu a jihar.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya yumarci ma'aikatun biyu su gabatar da cikakken bayanan kayayyakin aikinsu domin tabbatar da ingancinsu.

    Gwamnan ya bayar da umarnin ne bayan wata ziyarar ba-zata da ya kai hukumomin, inda ya tarar da gazawar ma'aikatun tare da jami'an hukumomin.

    Abba Kabir ya nuna damuwarsa kan yadda hukumomin ke gudanar da ayyukansu, duk da irin kuɗin da ya ce gwmnati na zubawa a ma'aikatun'', in ji sanarwar.

    A hukumar tsaftar muhalli ta jihar, gwamnan ya tarar da motocin kwashe shara bakwai ne kawai ke aiki daga cikin 30 da hukumar ke da su, kamar yadda ya samu motocin loda wa manyan motoci (felloda) uku ne kawai ke aiki daga cikin 15 da ma'aikatar ke da su.

    Sanarwar ta cea lokacin ziyarar an shaida wa gwamnan cewa ma'aikatan dindindin 10 ne kawai hukumar ke da su, yayin da sauran duka na-wucin gadi ne.

    Abba Kabir ya kuma nuna damuwarsa kan halin da ma'aikatan wucin gadin suke ciki, wanda ya bayyana da zalunci ne mutum ya yi shekara 20 a matsayin ma'aikacin wucin-gadi.

    Haka kuma a ma'aikatar kula da dokokin titi ta Karota, gwamna ya tarar da motoci masu yawa da suka lalace.

    Inda ya buƙaci hukumar ta gaggauta kai masa cikakken rahoton motocin da ma'aikatar ke da su

    Abba Kabir ya ce yadda gwamnati ke zuba makudan kuɗi a hukumar tsaftar muhallin a nuna irin muradin da gwamnati ke da shi wajen tabbatar da tsaftar muhalli, to amma ya ce hukumar ta gaza yin abin da ya dace.

  10. Abin da ya sa gwamnati ke neman bahasi daga wurin sarkin Katsina

    Gwamnan jihar Katisna Mallam Dikko Umar Radda ya buƙaci Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya yi masa bayanin dalilin rashin halartar wasu hakiman masarautarsa bikin hawan sallah da aka gudanar a masarautar.

    Kwamishinan yaɗa labarai da al'adun gargajiya na jihar, Dakta Bala Salisu Zango ya tabbatar wa BBC cewa ba wata gagarumar matsala aka samu tsakanin gwamna da sarkin ba, face kawai batu ne na neman bahasi kan gazawar wasu hakimai wajen halartar hawan sallah duk da shirin da aka yi tun farko.

    ''Gwamnanmu mutum ne mai sha'awar abubuwan da suka shafi al'adun gargajiya, kuma Katsina jiha ce da ta yi fice a ɓangaren hawa na sarakuna, kamar lokacin bukukuwan Sallah da Sallar Gani, to da lokacin sallah ya ƙarato sai gwamna ya nemi yadda za a inganta hawan Sallah a masarautar, aka ba shi shawarar tallafa wa masarautun da kuɗi da kuma goyon bayan gwamnati, amma duk da goyon bayan da gwamnati ta bai wa hakiman, wasu ba su fito hawan Sallar ba, wannan shi ne dalilin da ya sa gwamna ya nemi jin bahasi'', in ji kwamishinan yaɗa labaran.

    A cikin kwanakin nan ne wata takarda da gwamnan ya aika wa mai martaba sarkin Katsina ta karade shafukan sada zumunta.

    Takardar ta bukaci mai martaba sarkin Katsina Abdulmumini Kabir ya yi bayani kan abin da ya sa wasu hakimai suka ki halaryar hawan sallah a birnin Katsina.

    A lokacin da ya yi wa BBC karin bayani, kwamishinan yaɗa labaran jihar Katsina ya ce gwamnati ta riga ta zauna da sarakunan jihar biyu (Na Daura da na Katsina) gabanin hawan sallah, saboda yadda za ta taimaka musu wajen gudanar da hawan sallar, amma sai wasu hakimai ba su fito ba, don haka gwamnati tana da damar jin dalilin rashin fitowarsu.

    ''Kamar kai ne a ka bayar da aiki, kuma sai ba a yi maka ba, to mene ne aibu idan ka nemi jin bahasin dalilin rashin yi maka aikin?"

    Kwamishinan ya tabbatar da cewa babu wata matsala tsakanin gwamnatin jihar da masarautar Katsina.

    Wannan tuhuma dai ta haifar da shakku da fargaba a zukatan mutanen jihar waɗanda ke zargin cewa gwamnan na shirin fasalta masarautar domin sauke wasu hakiman tare da musanya su da wasu da ke kusanci da ita.

    To sai dai kwamishinan ya ce babu ƙanshin gaskiya game da zargin, yana mai cewa ''wannan tunanin mutane ne, kuma ba za ka hana mutane faɗin abin da ke bakunansu ba''.

    Ya ƙara da cewa su masarautun gargajiya a ƙarƙashin ikon gwamnatin jiha suke a kowace jiha, kuma gwamna na da madar yin duk abin da ya ga dama kan masarautun.

    ''Babu inda gwamnatin Katsina ta ce za ta fasa wata masarauta a jihar nan, amma kuma wannan ba yana nufin gwamnati ba ta da ikon da za ta yi hakan ba'', in ji kwamishinan.

    ''Iko ne na gwamna ya yi yadda yake so bisa daidai a jiharsa, muddin zai yi wa al'ummar jiharsa daɗi'', in ji shi.

    ''Masarauntun gargajiya a ƙarƙashin ikon gwamna suke a kowace jiha, kuma duk abin da gwamna yake ganin zai yi wa al'ummarsa daɗi to fa zai yi shi, amma dai gwamnatin Katsina ba ta taɓa cewa za ta fasa wata masarauta a jihar Katsina ba''.

    Rikici tsakanin sarakuna da gwamnoni dai wani abu ne da ke neman zama ruwa dare musamman a wasu yankunan arewacin Najeriya.

    Ko a baya-baya nan ma an ga yadda ake ta kai ruwa rana a Kano kan batun masarautun jihar bayan da gwaman jihar Abba Kabir ya sauke sarakunan jihar tare da naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon sarkin Kanon, bayan gyaran dokar masarautu da majalisar dokokin jihar ta yi.

    Haka a makon da ya gabata, gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya aike da ƙudurin gyaran dokar masarautu gaban majalisar dokokin jihar domin yi mata gyaran fuska, wani abu da wasu ke ganin tamkar rage wa Sarki Musulmi ƙarfin iko ne.

    Masu sharhi dai na ganin cewa galibi abin da ke janyo samun saɓani tsakanin sarakunan gargajiya da gwamnonin jihohi, shi ne zargin rashin nuna goyon baya ga jam'iyyun gwamnonin a lokacin yaƙin neman ba.

    To amma kwamishinan yaɗa labaran ya ce a jihar Katsina babu wannan matsalar, domin a cewarsa sakarunan Daura da na Katsina ba su tsunduma kansu harkokin siyasar jihar ba.

    ''Sarakunan jiharmu biyu na Daura da na Katsina sun ja girmansu, sun kare mutuncinsu ba su shiga harkokin siyasa ba'', in ji shi.

  11. 'Yan tawayen M23 sun sake ƙwace iko da wani gari a DR Kongo

    'Yan tawayen M23 sun sake ƙwace iko da wani gari a gabashin Jamhuriyar Dimokadiyyar Kongo.

    Mayaƙan na M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun kutsa garin Kirumba a yau Lahadi, kwana guda bayan ƙwace wani garin a yankin arewacin lardin Kivu

    Garin Kirumba na fama da tashe-tashen hankula tun 2021, a lokacin da masu tayar da ƙayar baya suka ƙaddamar da hare-hare a yankin.

    Ƙwace garin na zuwa ne, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke ƙoƙarin ƙarƙare ayyukan dakarunsu a yankin kudancin lardin Kivu mai makwabtaka.

    Fiye da dakarun Majalaisar Dinkin Duniya 2,000 ne suka fice tun watan Afrilu,a wani ɓangare na janyewar dakurun, inda ake sa ran kawo ƙarshen ayyukan dakarun zuwa ƙarshen shekarar da muke ciki.

  12. Serap ta buƙaci CBN ya yi bayanin ɓatan N100bn na kuɗin da suka lalace

    Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta buƙaci gwamnan babban bankin ƙasar, Mista Olayemi Cardoso ya yi bayani kan ''yadda fiye da naira biliyan 100 na takardun kuɗin da suka lalace - da sauran kuɗi masu yawa da ke jiran tantancewa a rassan CBN ɗin - suka yi ɓatan dabo.

    Cikin wata wasiƙa da ƙungiyar ta wallafa a shafnta na intanet, ta ce ta samu zarge-zargen ne cikin rahoton shekara-shekara da babban mai binciken kuɗi na ƙasa ya fitar a 2022.

    “Rahoton babban mai binciken kuɗin na 2022 ya nuna cewa, tun a 2017 CBN ke ci gaba da taskance fiye da naira biliyan 100 na takardun kuɗin da suka lalace ko suka yi dauɗa, da wasu kuɗi masu yawa da ke jiran tantancewa a rassan CBN''.

    Rahoton babban mai binciken kuɗin na fargabar cewa an karkatar, ko an sake maido da ''lalatattun takardun kuɗin da kuɗaɗen masu datti'' da aka tsara cewa za a ƙone su.

    Ƙungiyar ta ce zarge-zargen da ke cikin rahoton babban mai binciken kuɗin ya nuna yadda CBn din ya saɓa wa kundin tsarin mulki da dokar CBN da dokokin cin hanci na ƙasa da ma na duniya.

    Haka kuma ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnan na CBN ya yi ƙarin haske ''kan inda naira biliyan 7.2 da aka ware domin gina resehn bankin a Dutse a shekarar 2010, da kuma naira biliyan 4.8 da aka ware don sabunta resehn CBN na birnin Abeokuta a shekarar 2009.

    Serap ɗin ta kuma buƙaci CBN ya wallafa sunayen 'yan kwangilar da aka bai wa ayyukan, kuma suka gaza aiwatar da su.

    Ƙungiyar ta kuma ce CBN din ya yi wa jama'a bayani kan wasu basukan da bankin ya bai wa wasu jihohin ƙasar.

  13. Adadin mutanen da suka mutu a harin Gwoza ya kai 18

    Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar Borno (SEMA) ta ce mutum 18 ne suka mutu a harin bom da wasu da ake kyautata zaton 'yan ƙunan ɓakin wake ne suka tayar a wurin taron biki ranar Asabar a Gwoza da ke jihar.

    Cikin rahoton aukuwar lamarin da hukumar ta fitar, babban daraktan hukumar, Barkindo Saidu ya ce mutum 48 ne suka samu munanan raunuka a harin, wanda ya kasance ɗaya daga cikin mafiya muni a baya-bayan nan.

    Shugaban hukumar Barkindo Saidu ya fitar ya ce “A gaban idona, da misalin ƙarfe 3:00 na rana, bom na farko ya tashi a Gwoza, wanda wata mace ta tayar bayan ta kutsa cikin taron bikin''.

    Bayan tashin bom na farko, wanda ya jikkata fiye da mutum 30, tare da kashe wasu, sai na biyu ya sake tashi a kusa da babban asibitin yankin, in ji Barkindo Saidu.

    ''A yayin da mutane ke yi wa waɗanda suka mutu jana'iza, sai bom na uku ya tashi, inda nan ma wata mace ta tayar da shi tare da kashe wasu'', in ji daraktan na SEMA.

    Ya ƙara da cewa bom na huɗu ya fashe ne a asibiti, wanda wata matashiya ta tayar a lokacin da jami'an hukumar da likitoci ke taimaka wa waɗanda hare-haren farko suka jikkata.

    “Kawo yanzu mutum 18 ne suka suka mutu, da suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara da mata masu juna biyu. Mutum 19 da suka samu munanan raunuka an kai su babban asibitin Maiduguri domin basu kulawar gaggawa” in ji Saidu.

    Ya kuma ce akwai wasu ƙarin mutum 23 da ke jiran rakiyar sojoji domin kai su asibitin.

    Tuni dai sojoji suka sanya dokar hana fita a faɗin ƙaramar hukumar Gwoza, sakamkon hare-haren.

  14. 'Yan sanda sun bayar da umarnin kama motoci marasa lamba a Abuja

    Rundunar 'yan sandan birnin tarayyar Abuja, ta bayar da umarnin kama duka motoci marasa lamba da ke yawo a faɗin birnin.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Josephine Adeh ta fitar, ta ce kwamishin 'yan sandan birnin, CP Benneth C. Igweh ne ya bayar da umarnin don kakkaɓe ayyukan ɓata-gari da ke fakewa da tuƙin mota suna cutar da al'umma.

    “Rundunar 'yan sandan birnin Abuja ta damu matuƙa kan yadda ake tuƙa wasu motoci a birnin da lamba ɗaya kacal a jikinsu, da ma waɗanda ba su da lambar har fiye da lokacin da doka ta yarje, wato ƙarfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na maraice, kamar yadda sashe na 25 (5) na dokar sufurin birnin Abuja ta 2005 ta tanada'', in ji sanarwar.

    'Yan sandan sun kuma aike da makamancin wannan gargaɗi ga masu sayar da motoci, sannan ta yi kira a gare su don kauce wa ajiye motocinsu a wurin da doka ba ta amince da hakan ba.

    Sanarwar ta ce an ɓullo da dokar ce domin kakkaɓe ayyukan ɓata-garin da ke fakewa da hakan wajen cutar da al'umma.

    “Ba sabon abu ba ne yadda ake samun matsalar fashi a cikin motocin da aka fi sani da ‘one chance,’ inda galibi ke amfani da motoci marasa lamba ko masu lamba guda wajen aikata laifin. Wannan aika-aika na ci gaba da sanya fargaba a zukatan al'umma, waɗanda ke ci gaba da aza ayar tambaya kan abin da ya sa har yanzu 'yan sanda suka kasa magance matsalar'', in ji 'yan sandan.

  15. MDD ta ce halin da Falasɗinawa ke ciki a arewacin Gaza ya munana

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce halin da Falasɗinawa a arewacin zirin Gaza ke ciki ya munana, bayan ci gaba da faɗan da ake yi a yankin Shuja'iyya da ke makwabtaka da Zirin.

    Jami'an agaji sun ce sama da farar hula 80,000 ne suka rasa matsugunansu tun bayan sabunta kai hare-haren a ranar Alhamis da ta gabata.

    Ana faɗa a Shuja'iyya da Talil Hawa da Talil Sultan da ke kusa da Rafah, takamaimai ba mu san dalilin da ya sa ake kai hare-haren nan ba.

    A baya-bayan nan Isra'ila ta yi iƙirarin kakkaɓe mayaƙan Hamas, amma yanzu ta ce suna da ƙwararan shaidun da ke nuna Hamas na sake haɗa kan 'ya'yanta.

    Sojin Isra'ilar sun ce ana gwabza faɗan ta sama da ƙasa.

  16. Mayaƙan RSF sun karɓe iko da babban birnin jihar Sennar

    Dakarun RSF da ke yaƙi da gwamnatin Sudan, sun ce sun karbe iko da babban birnin yankin kudu masu yammacin ƙasar.

    RSF sun mamaye Singa, babban birnin jihar Sennar mai tashar ruwa.

    Rahotanni na cewa mazauna birnin na ta tserewa daga muhallansu cikin motoci, ya yin da hotunan kafafen sada zumunta ke nuna mutane sanye da kakin soja da na 'yan sanda sun mamaye gine-ginen gwamnati, su na a harbi ta sama da yin kabbara.

    Dakarun na RSF ne ke iko da mafi yawan sassan Khartoum, babban birnin ƙasar, da wsu yankuna a kudu maso gabashin ƙasar.

    Karɓe iko da birnin Singa babbar barazana ce ga sojojin Sudan, da garuruwan da ke ƙarƙashinsu.

  17. Sallama

    Masu bin shafin mu a wanan shafi barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiya, tare da fatan sake kasancewa da ku a wannan lokaci.

    Ku biyo a shafunkanmu na sada zumunta domin tafka muhawa kan labaran da muke wallafawa